-
“Hikima Mai-Fitowa Daga Bisa” Tana Aiki Kuwa A Rayuwarka?Ka Kusaci Jehobah
-
-
11 Mene ne za ka yi idan ka ji ka yi wa ɗan’uwa mai bi laifi? Yesu ya ce: “Idan kana cikin ba da baiko a kan bagaden hadaya, a nan ka tuna cewa ɗan’uwanka yana da wata damuwa game da kai, sai ka ajiye baikonka a gaban bagaden tukuna, ka je ka shirya da ɗan’uwanka. Sa’an nan ka zo ka ba da baikonka.” (Matiyu 5:23, 24) Za ka yi amfani da wannan gargaɗi ta wajen ɗaukan zarafi ka je wajen ɗan’uwanka. Da wane nufi? Don ka “shirya” da shi.b Domin ka yi haka, kana bukatar ka fahimci, kar ka musanci, fushinsa ba. Idan ka dumfare shi da nufin sulhuntawa kuma ka riƙe wannan hali, hakika dukan wani rashin fahimta za a warware shi, ba da haƙuri yadda ya dace, kuma a yi gafara. Sa’ad da ka ɗauki zarafin ka sulhunta, kana nuna cewa hikima ta Allah ce take ja-gorarka.
-
-
“Hikima Mai-Fitowa Daga Bisa” Tana Aiki Kuwa A Rayuwarka?Ka Kusaci Jehobah
-
-
b Furucin Helenanci da aka fassara “ka shirya” yana nufin “daina zama maƙiyin amma a ƙulla abuta; a sasanta matsaloli da sake soma yin abokantaka ko kuma yin abubuwa da haɗin kai.” Domin burinka ka kawo canji ne, ka cire, idan zai yiwu, fushi daga zuciyar da aka yi wa laifi.—Romawa 12:18.
-