Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w01 11/1 pp. 14-18
  • Ka Kiyaye Zuciyarka

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Kiyaye Zuciyarka
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ana Bukatar Gwadawa ta Kullum
  • Menene Maganarmu Take Bayyanawa?
  • Menene Ayyukanmu Suke Nuna?
  • Idonmu Sosai Yake?
  • ‘Ka Bauta wa Jehovah da Sahihiyar Zuciya’
  • Ka Samu Zuciya Da Jehovah Yake So
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Ka Ci Gaba Da Bauta Wa Jehobah Da Zuciya Ɗaya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Kana Da “Zuciya Wadda Za Ta San” Jehobah?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Ta Yaya Za Ka Iya Kiyaye Zuciyarka?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
w01 11/1 pp. 14-18

Ka Kiyaye Zuciyarka

“Ka kiyaye zuciyarka gaba da dukan abin da ka ke kiyayewa: gama daga cikinta mafitan rai su ke.”—MISALAI 4:23.

1, 2. Me ya sa muke bukatar kiyaye zuciyarmu?

WANI tsoho a tsibirin Caribbiya ya fito daga mafakarsa bayan wani bala’in guguwa. Yayin da yake kallon ɓarna da ta yi, ya fahimci cewa wani itace mai girma da ke gaban gidansa shekaru da yawa ba ya wurin kuma. Yana mamaki, ‘Me ya faru haka, yayin da ƙananan itatuwa da ke wurin ba abin da ya same su?’ Ganin kututturen itacen da ya faɗi, ya ba da amsa. Ciki itacen da kamar yana da ƙarfi ya ruɓe, guguwar ce ta fallasa wannan lalacewar da ba a gani a waje.

2 Bala’i ne yayin da mai sujjada ta gaskiya wanda kamar ya tsaya da ƙarfi a hanya ta Kirista ya fāɗi ga gwajin bangaskiya. Littafi Mai Tsarki ya faɗi daidai cewa, “tunanin zuciyar mutum mugunta ne tun daga ƙuruciyarsa.” (Farawa 8:21) Wannan yana nufin cewa in ba tare da kasancewa a farke ko da yaushe ba, za a iya jarabtar har ma zuciya mai kyau ga yin abin da ba shi da kyau. Tun da yake babu zuciyar mutum ajizi da ba ta da lalata ta ɗabi’a, muna bukatar mu yi biyayya ga wannan gargaɗi: “Ka kiyaye zuciyarka gaba da dukan abin da ka ke kiyayewa.” (Misalai 4:23) Ta yaya za mu kiyaye zuciyarmu ta alama?

Ana Bukatar Gwadawa ta Kullum

3, 4. (a) Waɗanne tambayoyi za a iya yi game da zuciya ta zahiri? (b) Menene zai taimake mu mu gwada zuciyarmu ta alama?

3 Idan ka je wurin likita don ya gwada ka, ƙila zai gwada zuciyarka. Lafiyar jikinka, haɗe da zuciyarka, sun nuna cewa kana samun isashen abubuwan gina jiki? Yaya ƙarfin jininka yake? Zuciyarka tana aiki kullum, tana da ƙarfi kuwa? Kana wasan motsa jiki daidai wajibi? Kana danna zuciyarka da alhini?

4 Idan zuciya ta zahiri na bukatar gwadawa a kai a kai, zuciyarka ta alama fa? Jehovah yana auna ta. (1 Labarbaru 29:17) Ya kamata mu yi hakan. Ta yaya? Ta yin tambayoyi irinsu: Zuciyata tana samun isashen abinci na ruhaniya ta wurin nazari da kaina kullum da kuma halartar taro? (Zabura 1:1, 2; Ibraniyawa 10:24, 25) Saƙon Jehovah shi ne damuwa ta musamman a zuciyata kamar “wuta mai-ƙonewa a kulle cikin ƙasusuwana,” yana motsa ni na sa hannu cikin aikin wa’azin Mulki da aikin almajirantarwa? (Irmiya 20:9; Matta 28:19, 20; Romawa 1:15, 16) Na motsa na mazakuta, ina sa hannu a wasu fanni na hidima ta cikakken lokaci yayin da ya yiwu? (Luka 13:24) A wane irin yanayi na ke saka zuciyata ta alama? Ina neman cuɗanya da mutane da zuciyarsu haɗaɗɗiya ce cikin bauta ta gaskiya? (Misalai 13:20; 1 Korinthiyawa 15:33) Bari mu lura da wata kasawa da sauri kuma mu yi gyara nan da nan.

5. Wane amfani mai kyau gwajin bangaskiya zai iya kawowa?

5 Sau da yawa muna fuskantar gwajin bangaskiya. Wannan yana ba mu zarafin lura da yanayin zuciyarmu. Ga Isra’ilawa da suke bakin shiga Ƙasar Alkawari, Musa ya ce: “Ubangiji Allahnka ya bishe ka dukan shekara arba’in ɗin nan cikin jeji, domin shi sauke girman kanka, ya innace ka, ya san abin da ke cikin zuciyarka, ko kana so ka kiyaye dokokinsa ko ba za ka yi ba.” (Kubawar Shari’a 8:2) Sau da yawa ba ma mamakin yadda muke ji, sha’awa, ko yadda muke aikata yayin da muke fuskantar yanayi ko jaraba da ba mu yi tsammaninsu ba? Gwaji da Jehovah ya ƙyale ya faru, babu shakka zai iya sa mu gane kasawarmu, yana ba mu zarafi mu yi gyara. (Yaƙub 1:2-4) Bari mu yi bimbini kuma mu yi addu’a game da yadda muke aikatawa ga gwaji!

Menene Maganarmu Take Bayyanawa?

6. Mecece batutuwa da muke son tattaunawa take bayyana game da zuciyarmu?

6 Yaya za mu san abin da yake zuciyarmu? Yesu ya ce: “Mutum nagari daga cikin ajiya mai-kyau ta zuciyatasa ya kan fito da abin da ke mai-kyau; mugu kuwa daga cikin mugunyar ajiyatasa ya kan fito da abin da ke mugu: gama daga cikin yalwar zuciya bakinsa ya ke zance.” (Luka 6:45) Abin da muke maganarsa nuni ne mai kyau na abin da ke zuciyarmu. Sau da yawa muna magana game da abin duniya da abin da muka cim ma wajen sana’a? Ko kuma zancenmu koyaushe a kan abubuwa ta ruhaniya da makasudi na ruhaniya ne? Maimakon magana game da kuskuren wasu, muna da nufin ƙyale su? (Misalai 10:11, 12) Muna magana da yawa game da mutane da aukuwar rayuwarsu amma yi magana kaɗan game da al’amuran ruhaniya da ɗabi’u? Wannan alama ce cewa muna nuna damuwa da bai kamata ba ga rayuwar mutane?—1 Bitrus 4:15.

7. Wane darasi game da kiyaye zuciyarmu za mu iya koya daga labarin ’yan’uwan Yusufu goma?

7 Ka yi la’akari da abin da ya faru a wani babban iyali. ’Ya’yan Yakubu goma manya “ba su iya yi . . . maganar lafiya ba” ga ƙaninsu Yusufu. Me ya sa? Suna ƙishi domin babansu ya fi son shi. Daga baya, lokacin da aka albarkaci Yusufu da mafarkai daga Allah, da ya nuna yana da amincewar Jehovah, suka “ƙara ƙinsa.” (Farawa 37:4, 5, 11) Abin baƙin ciki, suka sayar da ƙaninsu zuwa bauta. Sa’an nan a ƙoƙarin su rufe muguntarsu, suka ruɗe babansu ya yi tunanin cewa dabbar daji ce ta kashe Yusufu. ’Yan’uwan Yusufu goma sun kasa kiyaye zuciyarsu a wannan lokacin. Idan muna saurin sukān wasu, wannan alamar hassada ko kishi ne a zuciyarmu? Muna bukatar mu kasance a farke mu bincika abin da ke fitowa daga bakinmu kuma mu yi saurin cire nufi da bai dace ba.

8. Menene zai taimake mu mu bincika zuciyarmu idan mun fāɗa ga yin ƙarya?

8 Ko da “ba shi yiwuwa Allah ya yi ƙarya,” mutane ajizai suna ƙarya. (Ibraniyawa 6:18) “Dukan mutane maƙaryata ne,” in ji mai Zabura. (Zabura 116:11) Har ma manzo Bitrus ya yi ƙarya wajen musanta Yesu sau uku. (Matta 26:69-75) A bayyane, dole mu mai da hankali mu guji ƙarya, domin Jehovah ba ya son “harshe mai-ƙarya.” (Misalai 6:16-19) Idan za mu fāɗa ga yin ƙarya, zai yi kyau mu bincika abin da ya sa. Domin tsoron mutum ne? Tsoron horo ne ya sa? Wataƙila ba ma son a ɓata sunanmu ko kuma son kai ne matsalar? Ko menene ne dai, ya dace mu yi tunani a kan batun, cikin tawali’u mu yarda da kasawarmu, mu roƙi Jehovah ya gafarta mana, mu nemi ya taimaka mana mu sha kan kumamancin! Wataƙila “dattiɓan ikilisiya” ne za su fi ba da taimakon nan.—Yaƙub 5:14.

9. Menene addu’o’inmu za su iya bayyana game da zuciyarmu?

9 A amsa roƙon saurayi Sarki Sulemanu don hikima da sani, Jehovah ya ce: “Da shi ke wannan yana cikin zuciyarka, ba ka kuwa roƙi arziki ko wadata, ko girma . . . , hikima da sani an ba ka: zan kuma ba ka arziki da wadata da girma.” (2 Labarbaru 1:11, 12) Daga abin da Sulemanu ya roƙa da abin da bai roƙa ba, Jehovah ya san abin da ke zuciyar Sulemanu. Menene addu’o’inmu ga Allah ke bayyana game da zuciyarmu? Addu’o’inmu suna nuna muna son mu samu sani ne, hikima da fahimi? (Misalai 2:1-6; Matta 5:3) Abubuwan Mulki suna zuciyarka? (Matta 6:9, 10) Idan addu’o’inmu sun zama muna yi ne kawai, wannan za ta iya zama alama ce cewa muna bukatar ɗaukar lokaci mu yi bimbini a kan ayyukan Jehovah. (Zabura 103:2) Dukan Kiristoci suna bukatar su kasance a farke su gane abin da addu’o’insu ke bayyanawa.

Menene Ayyukanmu Suke Nuna?

10, 11. (a) Daga ina ne zina da fasikanci ke somawa? (b) Menene zai taimaka mana kada mu ‘yi zina cikin zuciya’?

10 Ayyuka sun fi kalmomi murya. Babu shakka ayyukanmu suna faɗan abubuwa da yawa game da abin da muke a ciki. Alal misali, a al’amuran tarbiyya, kiyaye zuciya ta ƙunshi fiye da guje wa yin fasikanci ko zina kawai. A Huɗubarsa a kan Dutse, Yesu ya ce: “Dukan wanda ya duba mace har ya yi ƙyashinta, ya rigaya ya yi zina da ita cikin zuciyatasa.” (Matta 5:28) Ta yaya za mu guji yin zina har a zuciyarmu?

11 Uban iyali mai aminci Ayuba ya bar misali wa Kiristoci maza da mata da suke da aure. Ayuba babu shakka yana sha’ani kawai ne da budurwoyi har ma ya taimake su yayin da suke bukatar taimako. Amma wannan mutum mai aminci bai yi tunanin soyayya da su ba. Me ya sa? Domin ya ƙudura niyyar ba zai dubi mata da ƙyashi ba. Ya ce: “Na yi wa’adi da idanuna,” in ji shi. “Yaya fa zan yi sha’awar budurwa?” (Ayuba 31:1) Bari mu yi irin wa’adin nan da idanunmu kuma mu kiyaye zuciyarmu.

12. Ta yaya za ka yi amfani da Luka 16:10 wajen kiyaye zuciyarka?

12 “Wanda ya ke da aminci cikin ƙanƙanin abu mai-aminci ne cikin mai-yawa,” in ji Ɗan Allah, “kuma wanda ba shi da gaskiya cikin ƙanƙanin abu ba, mara-gaskiya ne cikin mai-yawa.” (Luka 16:10) Hakika, muna bukatar mu bincika halinmu cikin al’amura da kamar ƙanana ne, ko waɗanda suke faruwa a ɓoye cikin iyalinmu. (Zabura 101:2) Yayin da muke zama cikin gidanmu, muna kallon telibijin, muna da Intane, muna mai da hankali mu bi gargaɗin Nassi cewa: “Fasikanci, da dukan ƙazanta, ko sha’awa, kada a ko ambata a cikinku, gama haka ya kamata ga tsarkaka; ko dauɗa, ko kuwa zancen wauta, ko alfasha, waɗanda ba su dace ba”? (Afisawa 5:3, 4) Nuna ƙarfi da ake yi a telibijin ko a wasannin bidiyo fa? “Ubangiji yana gwada mai-adalci,” in ji mai Zabura, “amma mai-mugunta da mai-son zalunci ransa yana ƙinsu.”—Zabura 11:5.

13. Wane kashedi aka bayar yayin da muke bimbini a kan abin da yake fitowa daga zuciyarmu?

13 “Zuciya ta fi komi rikici, cuta gareta ƙwarai irin ta fidda zuciya,” Irmiya ya faɗakar. (Irmiya 17:9) Wannan zuciya mai cuta za ta iya bayyana kanta, yayin da muke ba da hujjar kuskurenmu, rage laifuffuka, cire aibi mai tsanani, ko kuma zuguiguita abin da muka cim ma. Zuciya mai rikici na iya kasancewa da yanayi biyu na zuciya—leɓuna na faɗin wani abu, ayyuka na nuna dabam. (Zabura 12:2; Misalai 23:7) Yana da muhimmanci mu kasance da gaskiya yayin da muka bincika abin da ke fitowa daga zuciya!

Idonmu Sosai Yake?

14, 15. (a) Menene ido da ke “sosai”? (b) Ta yaya sa ido ya zama sosai take taimaka mana mu kiyaye zuciya?

14 “Fitilar jiki ido ne,” in ji Yesu. Ya daɗa: “Idan fa idonka sosai ne, dukan jikinka za ya zama da haske.” (Matta 6:22) Idon da ke sosai yana mai da hankali a makasudi ɗaya, ko nufi, ba ya kaucewa daga makasudin. Hakika, ya kamata mu kafa idonmu a ‘biɗan mulkin da adalcin Allah.’ (Matta 6:33) Menene zai faru wa zuciyarmu ta alama idan idonmu ba sosai ba ne?

15 Yi la’akari da al’amarin neman abin rayuwa. Biyan bukatun iyalinmu farilla ce ta Kirista. (1 Timothawus 5:8) Idan an jarabe mu da sha’awar bin salon zamani, mafi kyau, abubuwa mafi ban sha’awa a batun abinci, sutura, wurin kwanciya, da wasu abubuwa fa? Wannan ba za su saka zuciya da azanci cikin bauta ba, da ke sa mu yi sujjada ba da zuciya ɗaya ba? (Zabura 119:113; Romawa 16:18) Me ya sa za mu shagala wajen kula da bukatu na jiki har da rayuwarmu ta zama game da iyali, kasuwanci, da abubuwan duniya ne kawai? Ka tuna da shawara da aka hure: “Ku yi hankali da kanku, kada ya zama zukatanku su yi nauyi da zarin ci da maye da shagulgula na wannan rai, har ranan nan ta hume ku, ba labari, kamar tarko: gama hakanan za ta humi dukan mazaunan fuskar duniya.”—Luka 21:34, 35.

16. Wace shawara Yesu ya bayar game da ido, kuma me ya sa?

16 Ido hanyar magana ce na musamman ga azanci da zuciya. Abin da ya mai da hankali a kai zai iya taɓa tunaninmu, motsawar zuciyarmu, da ayyukanmu. A yin amfani da furci na alama, Yesu ya yi nuni ga ikon jarabar gani kuma ya ce: “Kuma idan idonka na dama yana sa ka yi tuntuɓe, ka cire shi, ka yar: gama gara gareka gaɓanka ɗaya ya lalace, da a jefa jikinka ɗungum cikin Jahannama.” (Matta 5:29) Dole a guji zuba ido a kan abubuwa da ba su dace ba. Alal misali, ba za a bar shi ya ga abubuwa da aka shirya don motsa ko ta da ƙyashi na ƙazanta da sha’awa ba.

17. Ta yaya yin amfani da Kolossiyawa 3:5 ta taimaka mana mu kiyaye zuciyarmu?

17 Hakika, ba ido ba ne kaɗai hanyar da muke da ita na sadawa da duniya. Wasu gaɓaɓuwa, irin su taɓawa da ji, suna da nasu aikin, muna bukatar mai da hankali da gaɓaɓuwan jiki da suka daidaita da waɗannan kuma. Manzo Bulus ya yi gargaɗi: “Ku matarda gaɓaɓuwanku fa waɗanda ke a duniya; fasikanci, ƙazanta, kwaɗayi, mugun guri, da sha’awa, watau bautar gumaka ke nan.”—Kolossiyawa 3:5.

18. Waɗanne abubuwa ya kamata mu yi game da tunani da bai dace ba?

18 Sha’awa da ba ta dace ba takan soma a gefen azancinmu da ke ɓoye. Tunani a kan irin wannan na daɗa mummunar sha’awa, yana taɓa zuciya. “Sa’annan, lokacinda sha’awa ta habala, ta kan haifi zunubi.” (Yaƙub 1:14, 15) Mutane da yawa sun yarda cewa hanyar nan ne sau da yawa tsiranci take faruwa. Yana da muhimmanci mu ci gaba da cika azancinmu da abubuwa ta ruhaniya! (Filibbiyawa 4:8) Kuma idan tunani da bai dace ba ya zo cikin zuciyarmu, ya kamata mu yi ƙoƙari mu cire shi.

‘Ka Bauta wa Jehovah da Sahihiyar Zuciya’

19, 20. Yaya za mu yi nasara a bauta wa Jehovah da sahihiyar zuciya?

19 A tsufarsa, Sarki Dauda ya gaya wa ɗansa Sulemanu: “Sulemanu ɗana, ka san Allah na ubanka, ka bauta masa da sahihiyar zuciya da yardan rai kuma: gama Ubangiji yana binciken dukan zukata, ya kuma gāne dukan sifofin tunani.” (1 Labarbaru 28:9) Sulemanu kansa ya yi addu’a don “zuciya mai-hikima.” (1 Sarakuna 3:9) Duk da haka, ya fuskanci kalubalen riƙe irin zuciyar a duk rayuwarsa.

20 Idan za mu yi nasara a wannan, muna bukatar mu samu zuciya ba kawai wanda Jehovah yake so ba amma mu kiyaye ta kuma. Don mu cim ma wannan, dole mu sa tunasarwar Kalmar Allah kusa da zuciyarmu—‘a tsakiyarta.’ (Misalai 4:20-22) Ya kamata mu sa ya zama halinmu mu dinga gwada zuciyarmu, cikin addu’a muna tunanin abin da kalmominmu da ayyuka suke bayyanawa. Tunanin nan yana da wani amfani ne idan ba mu nemi taimakon Jehovah ya gyara kowanne kumamanci da muka gano ba? Yana da muhimmanci mu yi tsaro sosai a kan abin da muke tunaninsa! A yin haka, muna da tabbaci cewa “salama kuwa ta Allah, wadda ta fi gaban ganewa duka, za ta tsare zukatan[mu] da tunanin[mu] cikin Kristi Yesu.” (Filibbiyawa 4:6, 7) Hakika, bari mu ƙudura niyyar kiyaye zuciyarmu fiye da kome da za a kiyaye kuma mu bauta wa Jehovah da sahihiyar zuciya.

Ka Tuna?

• Me ya sa yake da muhimmanci mu kiyaye zuciya?

• Ta yaya bincika abin da muke faɗa zai taimake mu kiyaye zuciyarmu?

• Me ya sa ya kamata mu sa idonmu ya zama “sosai”?

[Hotuna a shafi na 15]

Menene koyaushe muke magana game da shi a hidimar fage, a taro, da kuma a gida?

[Hotuna a shafi na 17]

Ido da ke sosai ba ya kauce hankali

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba