Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • ijwbq talifi na 149
  • Mene ne Ma’anar Furucin Nan “Ido a Maimakon Ido”?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Mene ne Ma’anar Furucin Nan “Ido a Maimakon Ido”?
  • Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Amsar Littafi Mai Tsarki
  • Mene ne manufar dokar “ido a maimakon ido”?
  • Dokar “ido a maimakon ido” ta shafi Kiristoci ne?
  • Ra’ayin karya game da dokar “ido a maimakon ido”
  • Idonka Sarai ne Kuwa?
    Hidimarmu Ta Mulki—2010
Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
ijwbq talifi na 149
Idon wani mutum

Mene ne Ma’anar Furucin Nan “Ido a Maimakon Ido”?

Amsar Littafi Mai Tsarki

Dokar nan “ido a maimakon ido” tana cikin dokokin da Allah ya ba Isra’ilawa ta hannun Musa, kuma Yesu ya yi kaulinsa a hudubarsa a kan dutse. (Matiyu 5:38; Fitowa 21:​24, 25; Maimaitawar Shari’a 19:21) Hakan yana nufin cewa, sa’ad da ake hukunta masu laifi, ya kamata hukuncin ya yi daidai da laifin da mutumin ya yi.a

Dokar ta shafi hukunci a kan wanda ya ji ma wani rauni da gangan. A dokar da aka ba da ta hannun Musa an ba da umurni game da mutumin da ya ji ma wani rauni da gangan, cewa: “Idan ya karya masa kashi, shi ma za a karya masa kashin. Idan ya cire wa wani ido, shi ma za a cire nasa idon. Idan ya balle wa wani hakori, shi ma za a balle nasa hakorin. Irin raunin da ya yi wa wani, haka za a yi masa.”​—Littafin Firistoci 24:20.

  • Mene ne manufar dokar “ido a maimakon ido”?

  • Dokar “ido a maimakon ido” ta shafi Kiristoci ne?

  • Ra’ayin karya game da dokar “ido a maimakon ido”

  • Yesu ya daidaita ra’ayin da bai dace ba

Mene ne manufar dokar “ido a maimakon ido”?

Dokar “ido a maimakon ido” ba ta ba mutane ’yancin daukan fansa da kansu ba. A maimakon haka, ya taimaka wa alkalai su rika yanke hukuncin da ya dace, ba tare da wuce gona da iri ko kuma saukaka hukuncin da ya kamata su yanke ba.

Kari ga haka, dokar za ta hana mutum yi wa wani lahani da gangan ko yin makarkashiya ko kuma kulle-kulle. “Sauran mutanen [wadanda suke bin dokokin Allah] za su ji, su ji tsoro, kuma nan gaba ba za su kara aikata irin wannan laifi a cikinku ba.”​—Maimaitawar Shari’a 19:20.

Dokar “ido a maimakon ido” ta shafi Kiristoci ne?

A’a, wannan dokar ba ta shafi Kiristoci ba. Tana cikin dokokin da Allah ya ba Isra’ilawa ta hannun Musa, kuma mutuwar Yesu ta kawar da wannan dokar.​—Romawa 10:4.

Duk da haka, dokar ta sa mu san ra’ayin Allah. Alal misali, Allah yana son adalci da shari’ar gaskiya. (Zabura 89:14) Dokar ta kuma nuna ka’idar Jehobah cewa ya kamata a hukunta masu laifi yadda ya dace.​—Irmiya 30:11.

Ra’ayin karya game da dokar “ido a maimakon ido”

Ra’ayin karya: Dokar “ido a maimakon ido” yana da tsanani ainun.

Gaskiyar: Wannan dokar ba ta goyi bayan yin amfani da doka don cin zarafin mutum ba. A maimakon haka, idan aka yi amfani da wannan dokar yadda ya dace, alkalai za su yanke hukunci yadda ya dace bayan sun yi la’akari da dalilan da suka sa aka aikata laifin kuma suka bincika ko da gangan ne ko kuma a’a. (Fitowa 21:​28-30; Littafin Ƙidaya 35:​22-25) Dokar “ido a maimakon ido” tana sa a guji yanke hukuncin da ta wuce gona da iri.

Ra’yin karya: Dokar “ido a maimakon ido” ta ba mutane zarafi su yi ta rama laifin da aka yi musu.

Gaskiyar: Dokar da Allah ya ba da ta hannun Musa ta ce: “Ba za ka nemi hanyar ramuwa ko ka rike wani a zuciya ba.” (Littafin Firistoci 19:18) Maimakon karfafa mutane su rika rama abin da aka yi musu, dokar ta karfafa mutane su dogara ga Allah da kuma tsarin shari’a da ya kafa don magance matsaloli.​—Maimaitawar Shari’a 32:35.

Yesu ya daidaita ra’ayin da bai dace ba

Yesu ya san cewa wasu ba sa bin dokar “ido a maimakon ido” yadda ya dace. Ya yi musu gyara kuma ya ce: “Kun ji dai an fada cewa, ‘Ido a maimakon ido, hakori kuma a maimakon hakori.’ Amma abin da na fada muku shi ne, kada ku ki wanda ya yi muku laifi. Idan wani ya mare ka a kumatun dama, ka juya masa dayan ya mara.”​—Matiyu 5:​38, 39.

Ka yi la’akari da furucin Yesu cewa “kun ji dai an fada.” Watakila yana magana ne game da wasu shugabannin Yahudawa da suke koyarwa cewa ya kamata a rika ramako. Wani masanin Littafi Mai Tsarki mai suna Adam Clarke ya ce: “Kamar dai Yahudawan sun yi amfani da wannan dokar [ido a maimakon ido] . . . don su goyi bayan rike mutum a zuciya da kuma yin ramako.” Ta wajen karfafa yin ramako, wadannan shugabannin addinai sun bata manufar Dokar.​—Markus 7:13.

A maimakon haka, Yesu ya nanata cewa kauna ita ce dalilin kafa wannan Doka. Ya ce: “ ‘Ka kaunaci Ubangiji Allahnka . . . ’ Wannan ita ce doka ta farko, kuma mafi girma. Ta biyun ma kamar ta farkon take, ‘Ka kaunaci makwabcinka kamar yadda kake kaunar kanka.’ Dukan Koyarwar Musa da ta annabawa suna rataya a kan wadannan dokoki biyu.” (Matiyu 22:​37-40) Yesu ya koyar cewa kauna ce za ta sa a san mabiyansa na gaskiya ba yin ramako ba.​—Yohanna 13:​34, 35.

a Wasu yankuna a zamanin dā sun bi wannan dokar da a wasu lokuta ake kira lex talionis a yaren Latin.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba