Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w14 6/15 pp. 17-21
  • Ka ‘Ƙaunaci Maƙwabcinka Kamar Ranka’

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka ‘Ƙaunaci Maƙwabcinka Kamar Ranka’
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • WANE NE MAƘWABCINMU?
  • YADDA ZA MU NUNA CEWA MUNA ƘAUNAR MAƘWABCINMU
  • HANYA TA MUSAMMAN TA ƘAUNAR MAƘWABTANMU
  • MISALI MAI KYAU NA NUNA ƘAUNA
  • KA CI GABA DA ƘAUNAR MAƘWABCINKA KAMAR RANKA
  • Abin Da Ake Nufi Da Mu Ƙaunaci Makwabcinmu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Kana “Kaunar Makwabcinka Kamar Ranka” Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • A Ina Ƙaunarka Ta Tsaya?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Yadda Za Mu Kaunaci Kanmu?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
w14 6/15 pp. 17-21

Ka ‘Ƙaunaci Maƙwabcinka Kamar Ranka’

“[Doka] ta biyu . . . ita ce, Ka yi ƙaunar maƙwabcinka kamar ranka.”—MAT. 22:39.

MECE CE AMSARKA?

  • Wane ne maƙwabcinmu?

  • Me ya sa ya kamata mu nuna ƙauna ga maƙwabtanmu?

  • Ta yaya za mu iya nuna ƙauna ta wajen bin shawarar da ke 1 Korintiyawa 13:4-8?

1, 2. (a) Wace doka ce mafi girma ta biyu da Yesu ya ambata? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna?

SA’AD DA wani Ba-farisi ya tambayi Yesu wace doka ce mafi girma a cikin Attaura, Yesu ya ce: “Ka yi ƙaunar Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan azancinka.” (Mat. 22:37) Mun tattauna abin da hakan yake nufi a talifin da ya gabata. Yesu ya kuma ambaci doka mafi girma ta biyu sa’ad da ya ce: “Wata kuma ta biyu mai kamaninta ita ce, Ka yi ƙaunar maƙwabcinka kamar ranka.”—Mat. 22:34-39.

2 Yesu ya ce wajibi ne mu ƙaunaci maƙwabtanmu kamar ranmu. Don haka, ya kamata mu tambayi kanmu: Wane ne maƙwabcina? Ta yaya za mu nuna ƙauna ga maƙwabtanmu?

WANE NE MAƘWABCINMU?

3, 4. (a) Da wane kwatanci ne Yesu ya ba da amsa ga wannan tambayar: “Wane ne maƙwabcina”? (b) Ta yaya Basamariyen ya taimaka wa mutumin nan da mafasa suka yi masa dukan tsiya kuma suka bar shi tsakanin rai da mutuwa? (Ka duba hoton da ke wannan shafi.)

3 Za mu iya tunani cewa maƙwabci shi ne wanda yake zama kusa da mu. (Mis. 27:10) Amma sa’ad da wani mutum ya tambayi Yesu: “Wane ne maƙwabcina?” Yesu ya yi kwatancin wani Basamariye mai kirki don ya ba da amsar. (Karanta Luka 10:29-37.) Mafasa sun tare wani Bayahude kuma suka yi masa dukan tsiya suka ƙyale shi a kan hanya. Ya kamata firist Ba’isra’ile da Balawi da ke wucewa su taimaka masa da yake ɗan’uwansu ne. Amma suka wuce suka bar shi a wurin. Sai wani Basamariye ya zo ya taimaka wa wannan Bayahuden duk da cewa a lokacin, Yahudawa da ba sa shiri da Samariyawa.—Yoh. 4:9.

4 Wannan Basamariye mai kirki ya zuba mai da ruwan anab a ciwon da aka ji ma wannan Bayahuden don su warke. Sai ya kai shi wani masauki kuma ya ba mai masaukin sule biyu, wato kuɗin aikin kwana biyu don ya kula da majiyyacin. Yadda Basamariyen ya kula da Bayahude da ya faɗa a hannun mafasa ya nuna cewa yana ƙaunar maƙwabcinsa da gaske. Za mu iya zama kamar wannan Basamariyen idan muna ƙaunar mutane kuma muna tausayinsu.

5. Ta yaya Shaidun Jehobah suka nuna cewa suna ƙaunar maƙwabtansu sa’ad da wani bala’i ya auku?

5 A yau, ba a yawan samun mutane masu tausayi kamar wannan Basamariye mai kirki. Musamman ma idan muka tuna cewa muna rayuwa ne a “kwanaki na ƙarshe” da babu ƙauna, a maimakon haka, mutane da yawa suna da zafin hali kuma ba sa son nagarta. (2 Tim. 3:1-3) Alal misali, sa’ad da wata guguwar ruwa da iska mai suna Hurricane Sandy ta addabi wani yanki a Birnin New York a watan Oktoba ta shekara 2012, mutanen yankin sun yi rashin wutar lantarki da tanadin ɗumama ɗaki da wasu abubuwa na kyautata rayuwa. Ƙari ga haka, ɓarayi suka riƙa satar kayayyakin waɗannan mutanen da bala’i ya addaba. Amma Shaidun Jehobah sun tsara wani shiri don taimaka wa ’yan’uwansu da kuma wasu da ke wannan yankin. Sun yi hakan ne don Kiristoci na gaske suna ƙaunar maƙwabtansu. A waɗanne hanyoyi ne kuma za mu iya nuna ƙauna ga maƙwabtanmu?

YADDA ZA MU NUNA CEWA MUNA ƘAUNAR MAƘWABCINMU

6. Ta yaya aikin wa’azin da muke yi yake nuna cewa muna ƙaunar maƙwabtanmu?

6 Ka taimaka wa mutane su ƙulla dangantaka da Allah. Idan muka fita wa’azi, muna yi wa mutane ‘ta’aziya’ daga Littafi Mai Tsarki. (Rom. 15:4) Sa’ad da muka taimaka wa mutane su san gaskiyar Littafi Mai Tsarki, muna nuna cewa mu maƙwabtan kirki ne. (Mat. 24:14) Babu shakka, sanar da mutane game da saƙon Mulkin “Allah . . . na bege” babban gata ne!—Rom. 15:13.

7. Wane umurni ne Yesu ya bayar kuma ta yaya muke samun albarka idan muka bi shi?

7 Ka bi da mutane yadda za ka so su bi da kai. Yesu ya ce: “Dukan abu fa iyakar abin da ku ke so mutane su yi maku, ku yi musu hakanan kuma: gama Attaurat ke nan da Annabawa.” (Mat. 7:12) “Attaurat” shi ne littattafan Farawa zuwa Kubawar Shari’a. Jehobah ya ƙaunaci Isra’ilawa kuma yana so su ƙaunaci juna shi ya sa ya ba su “Attaurat” da kuma littattafan “Annabawa.” Hakazalika, Jehobah yana so mu ƙaunaci maƙwabtanmu. A littafin Ishaya, Jehobah ya ce: “Ku kiyaye shari’a, ku yi adalci . . . Mai-albarka ne mutum wanda ya ke aika wannan.” (Isha. 56:1, 2) Hakika, idan muka ƙaunaci maƙwabcinmu kuma muka bi da su kamar yadda muke so su bi da mu, za mu sami albarka ƙwarai.

8. Me ya sa ya kamata mu ƙaunaci maƙiyanmu, kuma mene ne sakamakon haka?

8 Ka ƙaunaci maƙiyanka. Yesu ya ce: “Kun ji aka faɗi, Ka yi ƙaunar maƙwabcinka, ka ƙi magabcinka: amma ni ina ce muku, Ku yi ƙaunar magabtanku, kuma waɗanda su kan tsananta muku, ku yi musu addu’a; domin ku zama ’ya’yan Ubanku wanda ke cikin sama.” (Mat. 5:43-45) Manzo Bulus ma ya ce: “Idan maƙiyinka yana jin yunwa, ka cishe shi; idan yana ƙishi, ka ba shi sha.” (Rom. 12:20; Mis. 25:21) Jehobah ya ba Isra’ilawa ta dā doka da ta bukace su su taimaka wa maƙiyansu ko kuma dabbar maƙiyan. (Fit. 23:5) Idan Isra’ilawa suka bi wannan dokar, wataƙila za su zama abokai da maƙiyansu. Da yake Kiristoci suna nuna irin wannan ƙaunar ga maƙiyansu, hakan yana sa maƙiyan su canja halinsu. Har ma wasu daga cikin su sun soma bauta wa Jehobah!

9. Mene ne Yesu ya ce game da yin sulhu da ’yan’uwanmu?

9 Ka yi “zaman lafiya da kowa.” (Ibran. 12:14, Littafi Mai Tsarki) Da yake an bukace mu mu yi zaman lafiya da kowa, wajibi ne mu yi hakan da ’yan’uwanmu masu bi. Yesu ya ce: “Idan . . . kana cikin miƙa baikonka a wurin bagadi, can ka tuna ɗan’uwanka yana da wani abu game da kai, sai ka bar baikonka can a gaban bagadi, ka yi tafiyarka, a sulhuntu da ɗan’uwanka tukuna, kāna ka zo ka miƙa baikonka.” (Mat. 5:23, 24) Allah zai albarkace mu idan muka ƙaunaci ’yan’uwanmu kuma muka yi sulhu da su.

10. Me ya sa bai kamata mu riƙa yin sūkar mutane ba.

10 Ka guji sūkar mutane. Yesu ya ce: “Kada ku zartar, domin kada a zartar muku. Gama da irin shari’a da ku ke shar’antawa, da ita za a shar’anta muku: da mudun nan da ku ke aunawa kuma da shi za a auna muku. Don me kuwa ka ke duban ɗan hakin da ke cikin idon ɗan’uwanka, amma ba ka kula da gungumen da ke cikin ido naka ba? Ko kuwa ƙaƙa za ka ce ma ɗan’uwanka, Bari in cire ɗan hakin daga cikin idonka; ga shi kuwa, gungume yana cikin ido naka? Kai mai-riya, ka fara cire gungume daga cikin ido naka; kāna za ka gani sarai da za ka cire ɗan hakin daga cikin idon ɗan’uwanka.” (Mat. 7:1-5) Duk lokacin da saɓani ya shiga tsakaninmu da ɗan’uwanmu, ya kamata mu yi sulhu ba tare da ɓata lokaci ba. Idan muka yi hakan, za mu faranta wa Jehobah rai.

HANYA TA MUSAMMAN TA ƘAUNAR MAƘWABTANMU

11, 12. A wace hanya ta musamman ce muke nuna ƙauna ga maƙwabtanmu?

11 Za mu iya ƙaunar maƙwabtanmu a hanyoyi dabam-dabam. Amma Yesu ya ce hanya ta musamman ta yin haka ita ce ta yin wa’azin Mulkin Allah. (Luk 8:1) Yesu ya umurci mabiyansa su “almajirtar da dukan al’ummai.” (Mat. 28:19, 20) Idan muka bi wannan umurnin, za mu iya taimaka wa maƙwabtanmu su bar hanya mai faɗi kuma su bi matsatsiyar hanya da za ta sa su sami rai na har abada. Mun san cewa Jehobah zai albarkaci wannan ƙoƙarin da muke yi.

12 Yesu ya taimaka wa mutane da yawa su san cewa suna bukata su san Jehobah. (Mat. 5:3) Sa’ad da muka yi wa mutane wa’azin “bisharar Allah,” muna yin koyi da Yesu. (Rom. 1:1) Waɗanda suka saurari bishara suna ƙulla dangantaka da Jehobah ta wajen ba da gaskiya da hadayar Yesu Kristi. (2 Kor. 5:18, 19) Ta wajen yin wa’azin bishara, muna nuna cewa muna ƙaunar maƙwabtanmu a wata hanya mai muhimmanci sosai.

13. Yaya kake ji game da saka hannun a wa’azin shelar Mulkin Allah?

13 Sa’ad da muka yi shiri sosai muka koma mu ziyarci mutane don mu yi nazarin Littafi Mai Tsarki da su, muna taimaka musu su bi dokokin Jehobah kuma hakan yana gamsar da mu. Ƙari ga haka, hakan zai sa mutane da yawa su yi canje-canje a rayuwarsu. (1 Kor. 6:9-11) Muna farin ciki sa’ad da muka ga yadda Jehobah yake taimaka wa waɗanda suke da “zuciya ta samun rai na har abada” su canja salon rayuwarsu kuma su ƙulla dangantaka ta ƙud da ƙud da shi. (A. M. 13:48, NW) Hakika, waɗanda ba su da bege a dā sun zama masu farin ciki kuma su daina alhini su dogara ga Ubanmu na sama. Muna jin daɗi sa’ad da muka ga waɗannan mutanen suna ci gaba! Babu shakka, gata ne babba mu nuna ƙauna ga maƙwabtanmu ta saka hannu a wa’azin shelar Mulkin Allah.

MISALI MAI KYAU NA NUNA ƘAUNA

14. Yaya manzo Bulus ya kwatanta ƙauna a 1 Korintiyawa 13:4-8?

14 Idan muka bi shawarar nan da manzo Bulus ya bayar a yadda muke bi da maƙwabtanmu, za mu magance matsaloli da yawa kuma za mu yi farin ciki. Ƙari ga haka, Allah zai yi mana albarka ƙwarai. (Karanta 1 Korintiyawa 13:4-8.) Bari mu ɗan tattauna abin da Bulus ya rubuta game da ƙauna kuma mu ga yadda za mu bi wannan shawarar a sha’anin da muke yi da maƙwabtanmu.

15. (a) Me ya sa ya kamata mu riƙa yin alheri da haƙuri a sha’anin da muke yi da mutane? (b) Me ya sa bai dace mu riƙa kishi ko fahariya ba?

15 “Ƙauna tana da yawan haƙuri, tana da nasiha.” Jehobah yana haƙuri da ’yan Adam kuma yana musu alheri. Hakazalika, ya kamata mu riƙa haƙuri kuma mu riƙa yi wa mutane alheri sa’ad da suka yi mana abin da bai dace ba ko kuma suka ɓata mana rai. “Ƙauna ba ta jin kishi.” Wasu ’yan’uwa suna da gata fiye da mu a cikin ikilisiya kuma bai kamata mu yi kishin su ba idan muna ƙaunarsu da gaske. Ban da haka ma, bai kamata mu riƙa fahariya ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Girman kai da fariya ke bi da mugaye, wannan kuwa zunubi ne.”—Mis. 21:4, Littafi Mai Tsarki.

16, 17. Ta yaya za mu bi shawarar da ke 1 Korintiyawa 13:5, 6?

16 Idan muna ƙaunar maƙwabtanmu, ba za mu yi musu rashin hankali ba. Ba za mu yi musu ƙarya ba. Ba za mu saci kayansu ko kuma mu yi musu wani abin da ya saɓa wa ƙa’idodin Jehobah ba. Ƙari ga haka, ƙauna za ta sa mu damu da mutane kuma mu taimaka musu maimakon mu riƙa yin son kai.—Filib. 2:4.

17 Ƙauna ta gaske ba ta saurin fushi kuma ba “ta yin nukura,” wato riƙo a zuci. Abin nufi, ƙauna za ta hana mu lissafta laifuffukan da mutane suke yi mana. (1 Tas. 5:15) Idan wani ya ɓata mana rai kuma muka ƙi mantawa, ba za mu faranta wa Allah rai ba. Ƙari ga haka, ba za mu ji daɗi ba kuma hakan zai shafi yadda muke sha’ani da mutane. (Lev. 19:18) Ƙauna tana sa mu yi murna da gaskiya, amma ba ta yin “murna cikin rashin adalci,” wato ba za mu yi farin ciki ba don wanda ya yi mana rashin adalci ya faɗa a cikin wata matsala.—Karanta Misalai 24:17, 18.

18. Mene ne muka koya game ga ƙauna a 1 Korintiyawa 13:4-8?

18 Bulus ya ƙara bayyana cewa ƙauna tana “jimrewa da abu duka.” Idan wani ya ɓata mana rai kuma ya ce mu gafarce shi, ƙauna za ta motsa mu mu yi hakan. Ƙauna tana “gaskata da abu duka” da ke cikin Kalmar Allah kuma muna godiya saboda koyarwar littafi mai tsarki da muke samu. Ƙauna “tana kafa bege ga abu duka.” Muna da bege don muna gaskata da dukan alkawuran da Jehobah ya yi mana kuma muna iya ƙoƙarinmu mu gawa wa mutane game da wannan begen don muna ƙaunarsu. (1 Bit. 3:15) Sa’ad da muke fuskantar yanayi mai wuya, muna yin addu’a kuma mu kasance da bege cewa abubuwa za su gyaru. Ko da an yi mana mugunta ko an tsananta mana, ba ma damuwa don ƙauna tana “daurewa da abu duka.” Bulus ya ƙara da cewa “ƙauna ba ta ƙarewa daɗai,” wato hali ne da mutane masu biyayya za su ci gaba da nunawa har abada.

KA CI GABA DA ƘAUNAR MAƘWABCINKA KAMAR RANKA

19, 20. Wane umurnin Littafi Mai Tsarki ne za mu bi don mu ci gaba da nuna ƙauna ga maƙwabcinmu?

19 Ta wajen bin umurnin Littafi Mai Tsarki, za mu iya nuna ƙauna ga maƙwabtanmu a koyaushe. Irin wannan ƙaunar ba ta nuna bambancin launin fata ko yare amma tana sa mu so dukan mutane. Kada mu manta cewa Yesu ya ce wajibi ne mu ‘ƙaunaci maƙwabcinmu kamar ranmu.’ (Mat. 22:39) Jehobah da kuma Kristi suna so mu ƙaunaci maƙwabcinmu. Idan ba mu san wani abin da ya kamata mu yi a wani yanayi ba, mu yi addu’a ga Allah ya yi ja-gora da ruhu mai tsarki. Hakan zai sa Jehobah ya albarkace mu kuma mu riƙa yin abubuwa cikin ƙauna.—Rom. 8:26, 27.

20 Wannan doka ta yin ƙaunar maƙwabcinmu kamar ranmu tana da muhimmanci sosai har Littafi Mai Tsarki ya ce shi ne ‘shari’ar sarauta.’ (Yaƙ. 2:8) Bayan Bulus ya ambaci wasu dokoki da Allah ya ba wa Isra’ila, sai ya ce: “Idan da wata doka, an tarke ta cikin wannan magana, cewa, Sai ka yi ƙaunar maƙwabcinka kamar ranka. Ƙauna ba ta aika mugunta ga maƙwabcinta ba; ƙauna fa cikar shari’a ce.” (Rom. 13:8-10) Saboda haka, ya kamata mu ci gaba da nuna ƙauna ga maƙwabtanmu.

21, 22. Me ya sa ya kamata mu ƙaunaci Allah da kuma maƙwabtanmu?

21 Yayin da muke bimbini a kan dalilin da ya sa ya kamata mu nuna ƙauna ga maƙwabtanmu, zai dace mu yi tunani a kan furucin da Yesu ya yi game da Allah. Ya ce “ya kan sa ranatasa ta fito ma miyagu da nagargaru, ya kan aiko da ruwa bisa masu-adalci da marasa-adalci.” (Mat. 5:43-45) Ya kamata mu ƙaunaci maƙwabtanmu, wato dukan mutane, ko da suna da kirki ko ba su da kirki. Kamar yadda muka ambata ɗazu, wata hanya mai muhimmanci da za mu nuna musu ƙauna ita ce ta yi musu wa’azi game da Mulkin Allah. Idan suka saurari bishara da muke yi musu, za su sami albarka sosai!

22 Muna da dalilai da yawa na yin ƙaunar Jehobah da dukan zuciyarmu da dukan ranmu da kuma hankalinmu. Ƙari ga haka, mun tattauna hanyoyi da yawa da za mu nuna ƙauna ga maƙwabtanmu. Idan muka ƙaunaci Allah da maƙwabtanmu, hakan zai nuna cewa muna bin dokoki biyu da suka fi muhimmanci. Ban da haka, za mu faranta ran Jehobah, Ubanmu na sama.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba