Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • ijwbq talifi na 155
  • Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Bayarwa?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Bayarwa?
  • Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Amsar Littafi Mai Tsarki
  • A wane lokaci ne bayarwa ke sa Allah farin ciki?
  • Yaushe ne bayarwa ba ta dace ba?
  • “Allah Yana Son Mai Bayarwa da Daɗin Rai”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Albarkar da Ake Samu Don Bayarwa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2017
  • Masu Karimci Suna Farin Ciki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
  • Yadda Za Ka San Kyauta Mafi Tamani
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2017
Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
ijwbq talifi na 155
Wani mutum yana rike da kyauta da aka kunsa

Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Bayarwa?

Amsar Littafi Mai Tsarki

Littafi Mai Tsarki ya ce a rika bayarwa da son rai kuma a yi hakan don dalilin da ya dace. Ya nuna cewa wanda ya bayar da kuma wanda ya karba suna farin ciki. (Karin Magana 11:25; Luka 6:38) Yesu ya ce: “Ya fi albarka a bayar da a karɓa.”​—Ayyukan Manzanni 20:35.

  • A wane lokaci ne bayarwa ke sa Allah farin ciki?

  • Yaushe ne bayarwa ba ta dace ba?

  • Nassosin da suka ambata bayarwa

A wane lokaci ne bayarwa ke sa Allah farin ciki?

Bayarwa tana sa Allah farin ciki sa’ad da aka yi hakan da son rai. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kowa ya bayar kamar yadda ya yi niyya, ba tare da ɓacin rai ko tilas ba, domin Allah yana son mai bayarwa da daɗin rai.”​—2 Korintiyawa 9:7.

Allah yana amincewa da bayarwa da aka yi da zuciya daya. (Yakub 1:27) Mutumin da ke taimaka wa mabukaci yana faranta ran Allah, kuma Allah yana daukan irin wannan taimakon kamar ana ba shi rance ne. (Karin Magana 19:17) Littafi Mai Tsarki ya koyar cewa Allah zai biya mutumin.​—Luka 14:​12-14.

Yaushe ne bayarwa ba ta dace ba?

Idan ka yi hakan don son kai. Alal misali don:

  • Ka burge mutane.​​—Matiyu 6:2.

  • Ka sami wani abu.​​—Luka 14:​12-14.

  • Ka sami rai na har abada.​—Zabura 49:​6, 7.

Idan ka yi hakan don ka tallafa fa ma ayyuka ko halayen da Allah ya haramta. Alal misali, ba zai dace mu ba wani kudi don ya yi caca ko ya sha kwaya ko kuma ya sha giya ya bugu ba. (1 Korintiyawa 6:​9, 10; 2 Korintiyawa 7:1) Hakazalika, ba zai dace mu tallafa ma wani da zai iya biyan bukatunsa amma ya ki yin aiki ba.​—2 Tasalonikawa 3:10.

Idan kana ba mutane kyauta sosai har ka mance da iyalinka. Littafi Mai Tsarki ya koyar cewa wajibi ne magidanta su biya bukatun iyalinsu. (1 Timoti 5:8) Ba zai dace magidanci ya rika ba mutane kyauta sosai amma iyalinsa suna shan wahala. Hakazalika, Yesu ya koyar cewa bai dace mutane su ki kula da iyayensu da suka tsufa ta wajen da’awa cewa sun riga sun kebe dukiyarsu ga Allah ba.​—Markus 7:​9-13.

Nassosin da suka ambata bayarwa

Karin Magana 11:25: “Mai bayarwa hannu sake zai kara yalwata, mai taimaka wa waɗansu, shi kansa zai sami taimako.”

Ma’ana: Mai bayarwa da wanda aka ba suna amfana.

Karin Magana 19:17: “Mai yi wa masu talaka kirki, kamar ya ba Yahweh rance ne, Yahweh kuwa zai sāka masa.”

Ma’ana: Allah yana ganin cewa wadanda suke taimaka wa mabukata suna ba shi rance, kuma ya yi alkawari zai albarkace su.

Matiyu 6:2: “Idan za ka ba da sadaka, kada ka yi ta surutu a kai, yadda munafukai suke yi . . . domin mutane su yabe su.”

Ma’ana: Bai kamata mu rika bayarwa don mutane su yabe mu ba.

Ayyukan Manzanni 20:35: “Ya fi albarka a bayar da a karba.”

Ma’ana: Mutum zai yi farin ciki idan yana bayarwa da dukan zuciyarsa.

2 Korintiyawa 9:7: “Kowa ya bayar kamar yadda ya yi niyya, ba tare da bacin rai ko tilas ba, domin Allah yana son mai bayarwa da dadin rai.”

Ma’ana: Bayarwa da aka yi da son rai tana faranta ran Allah.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba