-
Kana Rayuwa Bisa Addu’ar Misali Kuwa?—Sashe na IHasumiyar Tsaro—2015 | 15 Yuni
-
-
“UBANMU WANDA KE CIKIN SAMA”
4. Mene ne kalmar nan “Ubanmu” take tuna mana, kuma ta yaya Jehobah ya zama “Uba” ga waɗanda suke da begen yin rayuwa a aljanna a duniya?
4 Addu’ar nan da Yesu ya koya mana, addu’ar misali ce. Da yake ya ce mu kira Allah “Ubanmu,” hakan ya nuna cewa dukanmu ‘’yan’uwan’ juna ne kuma muna ƙaunar juna da gaske. (1 Bit. 2:17) Wannan ba ƙaramin gata ba ne! Jehobah ya ɗauke shafaffu a matsayin ’ya’yansa kuma ya ba su gatan zuwa sama, shi ya sa ya dace su kira Jehobah “Uba.” (Rom. 8:15-17) Kiristoci da suke da begen yin rayuwa a aljanna a duniya za su iya kiran Jehobah “Uba” don shi ne ya ba su rai kuma yana biyan bukatun dukan masu bauta masa da gaske. Waɗanda suke da begen zama a aljanna a duniya za su zama ’ya’yan Allah bayan sun zama kamilai kuma sun kasance da aminci a gwaji na ƙarshe.—Rom. 8:21; R. Yoh. 20:7, 8.
-
-
Kana Rayuwa Bisa Addu’ar Misali Kuwa?—Sashe na IHasumiyar Tsaro—2015 | 15 Yuni
-
-
“A TSARKAKE SUNANKA”
7. Wane gata ne mutanen Allah suke da shi, kuma wane hakki ne yake kanmu?
7 Muna da gatan sanin sunan Allah da kuma na kasancewa “jama’a . . . domin sunansa.” (A. M. 15:14; Isha. 43:10) Mukan yi addu’a ga Ubanmu na sama cewa: ‘A tsarkake sunansa.’ Yin wannan addu’ar zai sa mu roƙi Jehobah ya taimaka mana mu guji faɗin ko kuma yin duk wani abin da zai ɓata sunansa mai tsarki. Ba zai dace mu yi kamar wasu a ƙarni na farko da ba sa aikata abin da suke wa’azinsa ba. Manzo Bulus ya ce game da su: “Gama a wurin al’ummai ana saɓon sunan Allah saboda ku.”—Rom. 2:21-24.
8, 9. Ka ba da misali a kan yadda Jehobah yake taimaka wa waɗanda suke so su tsarkake sunansa.
8 Burinmu ne mu tsarkake sunan Allah. Wata ’yar’uwa a ƙasar Norway da mijinta ya rasu ya bar ta da yaro ɗan shekara biyu, ta ce: Wannan mawuyacin lokaci ne a rayuwata. Nakan yi addu’a kullum, kusan kowane sa’a don in sami ƙarfin kasancewa da aminci da kuma guje wa duk wani abin da zai sa Shaiɗan ya zargi Jehobah. Ina son in tsarkake sunan Allah, kuma ina son ɗana ya sake ganin mahaifinsa a Aljanna.”—Mis. 27:11.
9 Shin Jehobah ya amsa addu’ar ta ne? Hakika. ’Yar’uwar ta ci gaba da yin tarayya da ’yan’uwa masu bi kuma hakan ya ƙarfafa ta. Shekaru biyar bayan haka, sai ta auri wani dattijo. Yanzu, ɗanta yana da shekara 20 kuma ya yi baftisma. “Ina farin ciki cewa mijina ya taimaka wajen tarbiyyartar da shi.”
10. Ta yaya Allah zai tsarkake sunansa?
10 Jehobah zai tsarkake sunansa sa’ad da ya halaka duk waɗanda suke gāba da sarautarsa. (Karanta Ezekiyel 38:22, 23.) A hankali, ’yan Adam za su zama kamilai. Muna marmarin ganin lokacin da dukan ’yan Adam da mala’iku za su tsarkake sunan Jehobah! Bayan haka, Ubanmu na sama mai ƙauna zai zama “kome” ga kowa.—1 Kor. 15:28.
-