Roƙo da Ake Yi A Dukan Duniya
KA YI tunani, miliyoyi ko ma biliyoyin mutane duka suna roƙon abu ɗaya. Suna roƙon mai iko duka wani abu takamaimai. Duk da haka, mutane kalilan ne kawai cikinsu suka san ainihin abin da suke roƙa. Irin wannan abin yana iya faruwa kuwa? Hakika, yana faruwa kowace rana. Menene dukan waɗannan mutane suke roƙa? Zuwan Mulkin Allah ne!
An kimanta cewa da addinai 37,000 da suke kiran kansu Kiristoci, kuma suke da’awar Yesu Kristi ne Shugabansu. Mabiyan waɗannan addinai sun wuce biliyan biyu. Yawancinsu kuma suna addu’a da sau da yawa ake kira Ubanmu wanda ke sama ko kuma Addu’ar Ubangiji. Ka san wannan addu’ar? Kamar yadda Yesu ya koyar da mabiyansa, addu’ar ta fara ne da: “Ubanmu wanda ke cikin sama, A tsarkake sunanka. Mulkinka shi zo. kAbin da ka ke so, a yi shi, cikin duniya, kamar yadda a ke yinsa cikin sama.”—Matta 6:9, 10.
Shekaru ɗarurruwa yanzu, masu bauta suna maimaita waɗannan kalmomi a coci cocinsu. Suna kuma furta su a lokacin da suka kaɗaita da kuma a lokacin da iyalansu suka taru wuri ɗaya, a lokacin farin ciki da lokacin baƙin ciki. Suna furta waɗannan kalmomin da gaskiya da kuma aniya. Wasu kuma sun haddace su, suna furta su ba tare da tunanin ma’anarsu ba. Ba waɗannan ’yan Kiristandam ne kawai suke bege kuma suke addu’a Mulkin Allah ya zo ba.
Roƙo da Ba a Addini Ɗaya Kawai Ake Yi Ba
Wata addu’a da aka sani sosai a addinin Yahudawa ita ce addu’ar masu makoki. Ko da yake ba game da mutuwa ba ne ko kuma makoki, ana yawan furta wa a lokacin jana’iza. Addu’ar ta ce: “Muna fata Allah ya kafa Mulkinsa sa’ad da kake raye . . . , a hanzarce.”a Wata addu’a kuma da ake yi a dā a wajen bauta ta Yahudawa nuna bege ne na Mulkin Almasihu ɗan gidan Dauda.
Wasu addinai ma da ba Kiristoci ba ra’ayi na Mulkin Allah ya kasance da sha’awa a gare su. In ji The Times of India, wani babban shugaban addini na Indiya, wanda yake so ya ga haɗewar addinan Hindunci, Musulinci, da Kiristanci, ya ce: “Mulkin Allah na gaskiya ba zai kasance ba har sai gabas da yamma sun haɗa kai.” Kuma wani shugaban makarantar Musulinci a Strathfield ta Austireliya ya rubuta ba da daɗewa ba a jarida: “Kamar sauran Musulmai, ni ma na gaskata cewa Yesu zai dawo ya kafa Mulkin Allah na gaskiya.”
Ba tare da wata shakka ba, yawan dukan waɗanda suke bege da roƙon zuwan Mulkin Allah ya kai biliyoyi. Amma ka yi la’akari da wani abin ban mamaki.
Wataƙila ka sani cewa mu Shaidun Jehobah waɗanda muke buga wannan mujallar, muna bi gida gida a unguwarku muna tattaunawa game da Littafi Mai Tsarki. Muna wannan aikin a dukan duniya, a ƙasashe 236 a kuma harsuna fiye da 400. Kuma ainihin jigon wa’azinmu shine Mulkin Allah. Hakika ka lura cewa cikakken jigon wannan mujallar shi ne Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah. Muna yawan tambayar mutane ko suna addu’a domin zuwan wannan Mulkin. Yawancin mutane suna cewa e. Amma, sa’ad da muka yi tambaya menene Mulkin, abin da yawancin mutane suke cewa shi ne “ban sani ba.” Ko kuma amsarsu ba cikakkiya ba ce kuma marar tabbaci.
Me ya sa mutane da yawa suke roƙon abin da ba za su iya bayani a kai ba? Shin domin Mulkin Allah wani abu ne mai wuyar fahimta? A’a. An ba da cikakken bayani a kan Mulkin a cikin Littafi Mai Tsarki. Ƙari ga haka, saƙon Littafi Mai Tsarki game da Mulkin zai ba ku bege na gaskiya a cikin wannan lokatai masu wuya. A talifi na gaba, za mu ga yadda Littafi Mai Tsarki ya yi bayani game da wannan begen. Kuma za mu ga lokacin da za a amsa addu’ar Yesu game da zuwan Mulkin.
[Hasiya]
a Kamar addu’ar da Yesu ya koyar, addu’ar makoki ta Yahudawa ma ta roƙa a tsarkake sunan Allah. Ana jayayya a kan lokacin da aka fara addu’ar makokin ko a lokacin Kristi ne ko kuma kafin lokacinsa, ko yaya dai kada kamanin addu’o’in ya ba mu mamaki. Addu’ar Yesu ba domin ya kawo sabon abu ba ne. Dukan wani roƙo yana bisa Nassosi ne da dukan Yahudawa suke da shi a lokacin. Yesu yana ƙarfafa ’yan’uwansa Yahudawa ne su yi addu’a game da abubuwan da ya kamata su yi addu’a a kan su.