DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | MATTA 1-3
“Mulkin Sama Ya Kusa”
Tufafin Yohanna da shigarsa sun nuna cewa ya sauƙaƙa rayuwarsa don ya iya yin nufin Allah
Babban gatan da Yohanna ya samu na shirya wa Yesu hanya ya fi kowace irin sadaukarwa da ya yi muhimmanci
Idan muka sauƙaƙa rayuwarmu, hakan zai taimaka mana mu mai da hankali ga yin nufin Allah. Ƙari ga haka, zai sa mu yi farin ciki. Za mu iya sauƙaƙa rayuwarmu idan mun . . .
san ainihin bukatunmu
daina sayan abubuwan da ba ma bukata
rubuta abubuwan da muke bukata
kawar da abubuwan da ba ma amfani da su
biya bashin da ake bin mu
daina wasu ayyukan da suke ɗaukan lokaci sosai
Abincin Yohanna shi ne fari da zuma
Wane makasudi ne zan iya cim ma idan na sauƙaƙa rayuwata?