Ka Kau Da Idanunka Daga Abubuwa Marasa Amfani!
“Ka kawar da idanuna ga barin duban abin banza, kuma ka rayar da ni cikin tafarkunka.”—ZAB. 119:37.
1. Menene muhimmancin baiwar idanu?
IDANUNMU abu mai tamani ne! Da su, za mu iya ganin abin da ke faruwa a kewayenmu farat ɗaya, kuma mu ga kala. Idanunmu suna sa mu ga abokai ƙaunatattu ko kuma abubuwa da za su jawo mana haɗari. Da su, muna ganin kyawawan abubuwa, mu more al’ajabi na halitta, kuma mu ga alamar wanzuwar Allah da ɗaukakarsa. (Zab. 8:3, 4; 19:1, 2; 104:24; Rom. 1:20) Kuma a matsayin hanya mai muhimmanci na sadawa da tunani, idanunmu suna da matsayi na musamman na sanin Jehobah da kuma ba da gaskiya a gare shi.—Josh. 1:8; Zab. 1:2, 3.
2. Me ya sa ya kamata mu damu da abin da muka gani, kuma menene za mu koya daga roƙon mai zabura?
2 Amma, abin da muka kalla, yana iya jawo mana la’ani. Idanunmu da tunaninmu suna da nasaba sosai domin abin da muka gani zai iya ta da sha’awa mai ƙarfi a zuciyarmu. Kuma domin muna zaune a duniya wadda Shaiɗan Iblis yake sarauta, mai cike da lalata da kuma mutane masu gamsar da kansu, ana cika mu da hotuna da kuma ƙaryace-ƙaryace da za su iya sa mu bijire, ko da za mu kalle su ne na ɗan lokaci. (1 Yoh. 5:19) Shi ya sa mai zabura ya roƙi Allah: “Ka kawar da idanuna ga barin duban abin banza, kuma ka rayar da ni cikin tafarkunka.”—Zab. 119:37.
Yadda Idanunmu Za Su Iya Yaudararmu
3-5. Wane labarin Littafi Mai Tsarki ne ya kwatanta haɗarin ƙyale idanunmu su rinjaye mu?
3 Ka yi la’akari da abin da ya faru da Hauwa’u, mace ta farko. Shaiɗan ya shawarce ta cewa idanunta lallai “za su buɗe,” idan ta ci ’ya’yan “itace na sanin nagarta da mugunta.” Babu shakka, sanin cewa idanunta za su “buɗe” ya ba Hauwa’u sha’awa sosai. Marmarinta na cin haramtaccen ’ya’yan itacen ya daɗu sa’ad da ta ga cewa “itacen yana da kyau domin ci, abin sha’awa ne kuma ga idanu, itacen kuma abin marmari ne domin bada hikima.” Kallon itacen da sha’awa ne ya sa Hauwa’u ta karya dokar Allah. Mijinta, Adamu ma ya yi rashin biyayya, da mugun sakamako ga dukan ’yan Adam.—Far. 2:17; 3:2-6; Rom. 5:12; Yaƙ. 1:14, 15.
4 A zamanin Nuhu, an rinjaye wasu mala’iku ma saboda abin da suka gani. Game da su, Farawa 6:2 ya ce: “’Ya’yan Allah suka ga ’yan mata na mutane kyawawa ne; suka ɗauko wa kansu mata dukan waɗanda suka zaɓa.” Kallon ’yan matan mutane da sha’awa ya ta da sha’awar da ba ta dace ba na yin jima’i da ’yan Adam a zukatan waɗannan mala’iku masu tawaye, kuma suka haifi ’ya’ya masu mugunta sosai. Muguntar mutane a lokacin ya kai ga halakar dukan ’yan Adam, ban da Nuhu da kuma iyalinsa.—Far. 6:4-7, 11, 12.
5 Ƙarnuka bayan hakan, idanun Ba’isra’ila Achan sun rinjaye shi ya sato wasu kayayyaki daga birnin Yariko. Allah ya ba da umurni cewa a halaka dukan abubuwa da ke cikin birnin, ban da wasu abubuwa da za a saka a cikin baitulmali na Jehobah. An gargaɗi Isra’ilawa: ‘Ku hanu daga keɓaɓen abin, domin kada ku yi sha’awarta’ kuma ku ɗiba wasu abubuwa daga birnin. Sa’ad da Achan ya yi rashin biyayya, birnin Ai ya ci mutanen Isra’ila a yaƙi, kuma da yawa cikinsu suka mutu. Achan bai amince cewa ya yi sata ba sai da aka tona shi. Achan ya ce: “Sa’anda na ga” kayayyakin “sa’annan na yi ƙyashinsa, na ɗauke su.” Sha’awar idanunsa ta kai ga halakarsa, tare da “dukan abin da ya ke da shi.” (Josh. 6:18, 19; 7:1-26) Achan ya yi sha’awar abin da aka haramta.
Amfanin Horar da Kanmu
6, 7. Wanne cikin ‘makiɗan’ Shaiɗan ne ake yawan amfani da shi don a rinjaye mu, kuma yaya masu talla suke amfani da shi?
6 Har yau, ana gwada ’yan Adam a hanyar da ta yi kama da abin da aka yi amfani da shi a batun Hauwa’u, mala’iku da suka yi rashin biyayya, da kuma Achan. A cikin dukan ‘makiɗan’ da Shaiɗan yake amfani da su don rinjayar ’yan Adam, “sha’awar idanu” ta fi ƙarfi. (2 Kor. 2:11; 1 Yoh. 2:16) Masu talla na zamani sun sani da daɗewa cewa abin da aka gani da idanu ya fi rinjaya. “Idanu sun fi rinjaya,” in ji wani gwani mai talla a Turai. “Sau da yawa sukan sha kan sauran azanci, kuma suna da ikon sa mutane kada su yi abin da suka san ya fi kyau.”
7 Shi ya sa masu talla suke nuna mana hotunan abubuwa da aka ƙera da basira don su yi kyau sosai ga idanunmu kuma su sa mu yi sha’awar kayayyakinsu ko kuma ayyukansu! Wani mai bincike a ƙasar Amirka, wanda ya yi nazarin yadda talla yake rinjayar mutane ya ce “an tsara shi ba don kawai ya idar da saƙo ba, amma mafi muhimmanci ya sa mai kallo ya aikata.” Hoton lalata mai ta da sha’awa ne ake yawan amfani da shi. Shi ya sa yake da muhimmanci mu ƙudura aniya mu sarrafa abin da muke kallo da abin da muke tunaninsa!
8. Yaya aka nanata bukatar tsare idanunmu a cikin Littafi Mai Tsarki?
8 Kiristoci na gaskiya ma suna sha’awar idanu da na jiki. Saboda haka, Kalmar Allah ta ƙarfafamu mu yi wa kanmu horo game da abin da muke kallo da abin da muke sha’awarsa. (1 Kor. 9:25, 27; karanta 1 Yoh. 2:15-17.) Ayuba mutum mai adalci ya fahimci cewa gani da sha’awa suna da alaƙa. Ya ce: “Na yi wa’adi da idanuna; ya’ya fa zan yi sha’awar budurwa?” (Ayu. 31:1) Ayuba ya ƙi taɓa mace ta hanyar lalata, kuma ba zai ma sa kansa ya yi irin wannan tunanin ba. Yesu ya nanata cewa dole ne a tsabtace zuciya ta wurin ƙin yin tunanin lalata sa’ad da ya ce: “Dukan wanda ya [kalli] mace har ya yi sha’awarta, ya rigaya ya yi zina da ita cikin zuciyatasa.”—Mat. 5:28.
Abubuwa Marasa Amfani da Ya Kamata Mu Guji
9. (a) Me ya sa za mu mai da hankali musamman sa’ad da muke amfani da Intane? (b) Menene zai iya faru ta wurin kallon hotunan batsa ko na ɗan lokaci?
9 A duniyar yau, ya zama abu na yau da kullum a dinga “kallon” hotunan batsa, musamman a cikin Intane. Yaya za mu kalli irin wannan duniyar gizo cikin kuskure, sa’ad da ba mu neme shi ba? Wani dandali da ke gabatar da hoto mai rinjaya yana iya fitowa a kan kwamfutar mutum farat ɗaya. Ko kuma saƙon kwamfuta da muddin aka buɗe zai iya zama hoton batsa da aka tsara a hanyar da za ta yi wuya mutum ya rufe shi. Ko da mutum ya ɗan kalla kafin ya goge shi, hoton ya riga ya kafu a zuciyarsa. Kallon hotunan batsa na ɗan lokaci yana iya kawo mummunan sakamako. Zai iya sa lamirin mutum ya dinga damunsa kuma ya riƙa faman kawar da hotunan lalata daga zuciyarsa. Mafi muni ma, wanda ya ci gaba da “kallo” da ganga yana bukatar ya matar da sha’awoyinsa.—Karanta Afisawa 5:3, 4, 12; Kol. 3:5, 6.
10. Me ya sa yara musamman ne suke fi faɗa wa kallon hotunan batsa, kuma menene zai zama sakamakon kallon ta?
10 Yara za su iya dinga kallon hotunan batsa saboda karambaninsu. Idan hakan ya faru, da daɗewa zai iya shafi yadda suke ɗaukan jima’i. Waɗannan sakamakon, in ji wani rahoto, sun ƙunshi ra’ayin da bai dace ba game da jima’i kuma “zai yi musu wuya su kasance da dangantaka mai kyau, za su samu ra’ayi da bai dace ba game da mata; da kuma yawan kallon hotunan batsa, da zai shafi aikinsu na makaranta, abuta da dangantaka na iyali.” Sakamako mafi muni zai taso a nan gaba a dangantakar aure.
11. Ka ba da misali da zai nuna haɗarin kallon hotunan batsa.
11 “A cikin dukan mummunan halaye da nake da su kafin na zama Mashaidi, wanda ya fi mini wuya na daina, shi ne kallon hotunan batsa,” in ji wani ɗan’uwa Kirista. “Har ila ina tuna da waɗannan hotuna a wani lokaci, tare da ƙamshi, wasu kaɗe-kaɗe, abin da na gani, ko kuma tunani suna sa na tuna da su. Kullum ina kokawa da wannan.” Wani ɗan’uwa ya kalli jaridun batsa na babansa da ba mai bi ba ne sa’ad da yake yaro a lokacin da iyayensa ba sa gida. Ya rubuta: “Waɗannan hotuna suna da mugun sakamako a gare ni sa’ad da nake yaro! Har yanzu, bayan shekaru 25 ban manta da waɗannan hotunan ba. Duk da kokawa da nake yi, har ila ina tunawa da su. Hakan yana sa na riƙa jin laifi, duk da cewa ina guje wa yin tunaninsa.” Yana da kyau mu guji irin wannan nauyin ta wurin ƙin kallon abubuwa marasa amfani! Ta yaya mutum zai cim ma hakan? Yana bukatar ya yi ƙoƙari ya komo “da kowane tunani cikin bauta ga biyayyar Kristi.”—2 Kor. 10:5.
12, 13. Kiristoci za su guji kallon waɗanne abubuwa marasa amfani, kuma me ya sa?
12 Wani “mummunan al’amari,” ko abubuwa marasa amfani da za a guji shi ne nishaɗi da ke gabatar da son abin duniya ko rukuni na asiri ko kuma aikata laifi, zubar da jini, da kuma kisa. (Karanta Zabura 101:3.) Iyaye Kirista suna da hakki a gaban Jehobah su riƙa zaɓan abin da za su yarda a kalla a gidansu. Hakika, babu Kirista na gaskiya da zai sa hannu da gangan a cikin sihiri. Duk da haka, iyaye suna bukatan su san cewa wasu fina-finai, tsarin talabijin, wasan bidiyo, har ma da wasanni da littattafan yara suna nuna ayyukan sihiri.—Mis. 22:5.
13 Ko mu yara ne ko manya, bai kamata mu kalli wasannin bidiyo da ake mugunta da kuma nuna kisa da ake azabtar da mutane ba. (Karanta Zabura 11:5.) Dole ne mu ƙi mai da hankali ga ayyuka da Jehobah ya haramta. Ka tuna, Shaiɗan yana son ya ɓata tunaninmu. (2 Kor. 11:3) Ko da nishaɗin ya dace, ba da lokaci ainun wajen nishaɗin zai sa ba za mu sami lokacin bauta ta iyali, karatun Littafi Mai Tsarki na kullum da kuma shirya taro.—Filib. 1:9, 10.
Ka Bi Misalin Yesu
14, 15. Menene za a lura da shi game da jarabar Shaiɗan na uku ga Kristi, kuma yaya Yesu ya iya jimre da shi?
14 Abin baƙin ciki, ba za mu iya guje wa ganin wasu abubuwa da ke marar amfani ba a cikin wannan muguwar duniya. Har ma Yesu ya ga irin waɗannan abubuwa. Sa’ad da Shaiɗan yake ƙoƙari ya sa Yesu kada ya yi nufin Allah, ‘Shaiɗan ya tafi da shi cikin wani dutse mai-tsawo ƙwarai, ya gwada masa dukan mulkokin duniya, da ɗaukakarsu.’ (Mat. 4:8) Me ya sa Shaiɗan ya yi hakan? Babu shakka, yana son ya yi amfani da mugun tasiri na idanu. Kallon ɗaukaka na dukan mulkokin duniya yana iya sa Yesu ya yi sha’awar zama babban mutum a duniya. Yaya Yesu ya aikata?
15 Yesu bai mai da hankali ga wannan abin da zai iya jan ra’ayinsa ba. Bai ƙyale zuciyarsa ya yi mummunan sha’awa ba. Kuma ba ya bukata ya yi tunanin abin da Iblis ya ba shi kafin ya ƙi su. Yesu ya ƙi babu ɓata lokaci. Ya ba shi umurni, “Rabu da ni, ya Shaiɗan!” (Mat. 4:10) Yesu ya mai da hankali ga dangantakarsa da Jehobah kuma ya ba da amsa da ta yi daidai da nufinsa a rayuwa, wato, yin nufin Allah. (Ibran. 10:7) A sakamako, Yesu ya yi nasara wajen ɓata dabarar Shaiɗan.
16. Waɗanne darussa za mu iya koya daga misalin Yesu wajen ƙi da gwajin Shaiɗan?
16 Za mu iya koyon abubuwa da yawa daga misalin Yesu. Na farko, babu wanda zai kuɓuce wa dabarun Shaiɗan. (Mat. 24:24) Na biyu, abin da muka kafa idanunmu zai iya ƙarfafa sha’awoyi na zuciyarmu, da kyau ko marar kyau. Na uku, Shaiɗan zai yi amfani da “sha’awar idanu” daidai yadda zai iya don ya sa mu bijire. (1 Bit. 5:8) Na huɗu, mu ma za mu iya yin tsayayya da Shaiɗan, musamman idan mun aikata babu ɓata lokaci.—Yaƙ. 4:7; 1 Bit. 2:21.
Ka Kafa Idonka “Sarai”
17. Me ya sa ba shi da kyau mu jira har sai mun ga abin da ke marar amfani kafin mu tsai da abin da za mu yi?
17 Keɓe kanmu ga Jehobah ya haɗa da alkawarin ƙin kallon abin da ke marar amfani. Sa’ad da muka yi alkawarin yin nufin Allah, mun bi mai zabura wajen cewa: “Na kawasda sawayena daga kowace hanyar mugunta, domin in lura da maganarka.” (Zab. 119:101) Yana da haɗari mu jira sai an jarabe mu kafin mu tsai da abin da za mu yi. An bayyana mana abubuwa da Nassosi suka hana sarai. Mun san dabarun Shaiɗan. A wane lokaci ne Shaiɗan ya jarabe Yesu ya canja duwatsu zuwa burodi? Bayan ya yi azumi yini arba’in kwana arba’in kuma “ya ji yunwa.” (Mat. 4:1-4) Shaiɗan yana iya sanin lokacin da ba mu da ƙarfi kuma muna iya faɗa wa gwaji. Saboda haka, yanzu ne lokacin da za mu mai da hankali ga waɗannan al’amura. Kada ka yi banza da wannan! Idan muna tuna da keɓe kai da muka yi ga Jehobah kullum, za mu ƙuduri aniya mu ƙi abubuwa marasa amfani.—Mis. 1:5; 19:20.
18, 19. (a) Ka nuna bambancin idon da ke “sarai” da mai “lahani.” (b) Me ya sa yake da muhimmanci mu ci gaba da bincika abin da ke da amfani, kuma wace shawara Filibiyawa 4:8 ya ba da game da wannan?
18 A kowace rana, muna ƙara fuskantar abubuwa masu ban sha’awa da ke jan hankali. Ya fi muhimmanci yanzu mu bi gargaɗin Yesu mu sa idonmu “sarai.” (Mat. 6:22, 23) Idon da ke “sarai” na mai da hankali ga nufi guda, wato, yin nufin Allah. Amma, ido mai “lahani” yana makirci, ƙyashi, kuma yana bin abubuwan marasa amfani.
19 Ka tuna, abin da idanunmu suka gani yana shafan zuciyarmu. Saboda haka, yana da muhimmanci mu ci gaba da bincika abu mai amfani. (Karanta Filibiyawa 4:8.) Hakika, bari mu ci gaba da maimaita addu’ar mai zabura: “Ka kawar da idanuna ga barin duban abin banza.” Sa’annan, yayin da muke ƙoƙari mu aikata daidai da wannan addu’a, za mu kasance da tabbaci cewa Jehobah zai ‘rayar da mu cikin tafarkunsa.’—Zab. 119:37; Ibran. 10:36.
Menene Ya Kamata Mu Tuna Game da . . .
• alaƙa tsakanin idanunmu, tunani, da zuciya?
• haɗarurrukan kallon hotunan batsa?
• muhimmancin kasancewa da idon da ke “sarai”?
[Hotuna da ke shafi na 23]
Dole Kiristoci su guji kallon waɗanne abubuwa marasa amfani?