Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w23 Fabrairu pp. 8-13
  • Ka Amfana Sosai Daga Karatun Littafi Mai Tsarki

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Amfana Sosai Daga Karatun Littafi Mai Tsarki
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • MU YI KARATU YADDA ZA MU FAHIMTA
  • KA YI KARATU YADDA ZA KA KOYI DARUSSA
  • KA BARI KARATUN DA KAKE YI YA CANJA RAYUWARKA
  • KARANTA KALMAR ALLAH TANA SA MU FARIN CIKI
  • Hanyoyi Bakwai da Za a Amfana Daga Karatun Littafi Mai Tsarki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • “Ku Zama Masu Aikata Kalmar Allah”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Yadda Za Ka Amfana Daga Karanta Littafi Mai Tsarki
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Ka Riƙe Kalmar Allah Gam
    Ka Bauta wa Allah Maƙadaici na Gaskiya
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
w23 Fabrairu pp. 8-13

TALIFIN NAZARI NA 7

Ka Amfana Sosai Daga Karatun Littafi Mai Tsarki

“Yaya kuma kake fassarta ta?”​—LUK. 10:26.

WAƘA TA 97 Kalmar Allah Za Ta Sa Mu Rayu

ABIN DA ZA A TATTAUNAa

1. Mene ne ya nuna cewa Yesu ya ɗauki Nassosi da muhimmanci sosai?

KA ƊAUKA kana wajen saꞌad da Yesu yake koyarwa. Ya yi ƙaulin Nassosi sau da yawa kuma ya haddace su duka! Kalmomin da ya fara furtawa bayan ya yi baftisma, da kalmominsa na ƙarshe kafin ya mutu, ya yi ƙaulinsu ne daga Nassosi.b (M. Sha. 8:3; Zab. 31:5; Luk. 4:4; 23:46) Ƙari ga haka, a shekaru uku da rabi da Yesu ya yi hidima a duniya, yakan yi ƙaulin Littafi Mai Tsarki a gaban jamaꞌa kuma ya bayyana su.​—Mat. 5:​17, 18, 21, 22, 27, 28; Luk. 4: 16-20.

Hotuna: 1. Saꞌad da Yesu yake yaro, yana sauraran iyayensa yayin da suke masa magana. 2. Da Yesu ya zama matashi, shi da iyayensa suna saurarawa yayin da ake karanta Nassosi a haikali. 3. A lokacin da ya yi girma, Yesu yana karanta nadadden littafi.

Sa’ad da Yesu yake duniya, ya nuna cewa yana ƙaunar Nassosi kuma ya bar abubuwan da ya karanta su shafi rayuwarsa (Ka duba sakin layi na 2)

2. Da Yesu yake girma, mene ne ya taimaka masa ya san Nassosi sosai? (Ka duba hoton da ke shafin farko.)

2 Kafin Yesu ya soma hidimarsa, yakan karanta da sauraran Kalmar Allah a koyaushe. Ba shakka, yakan ji mahaifiyarsa Maryamu da Yusufu suna ƙaulin Nassosi saꞌad da suke tattaunawa a gida.c (M. Sha. 6:​6, 7) Muna da tabbacin cewa Yesu yakan bi iyayensa zuwa haikali kowace ranar Assabaci. (Luk. 4:16) Ba shakka, yakan saurara da kyau yayin da ake karanta Nassosi a wajen. Da shigewar lokaci, Yesu ya koyi yadda zai riƙa karanta Nassosin nan da kansa. Hakan ya sa Yesu ya san Nassosin nan, ya ƙaunace su sosai kuma ya bar abubuwan da yake koya su shafi rayuwarsa. Alal misali, ka tuna abin da ya faru a haikali saꞌad da Yesu yake shekara 12. Malaman da suka san Dokar Musa sosai sun yi “mamakin ganewar [Yesu] da yadda yake ba da amsoshi.”​—Luk. 2:​46, 47, 52.

3. Mene ne za mu tattauna a talifin nan?

3 Idan muna karanta Kalmar Allah a kai a kai, mu ma za mu san ta kuma mu ƙaunace ta sosai. Amma ta yaya za mu amfana sosai daga karatun Littafi Mai Tsarki? Za mu iya koyan darasi daga abin da Yesu ya gaya wa waɗanda suka san Dokar Musa har da marubuta da Farisiyawa da kuma Sadukiyawa. Ko da yake waɗannan malaman suna karanta Nassosi a kai a kai, ba sa bin abubuwan da suke karantawa. Yesu ya ambata abubuwa uku da malaman nan ba sa yi da zai taimaka musu su amfana daga karatun Littafi Mai Tsarki. Abubuwan da ya gaya musu za su taimaka mana mu inganta (1) yadda muke fahimtar abin da muke karantawa, (2) yadda za mu koyi darussa daga abin da muke karantawa (3) yadda za mu bar Kalmar Allah ta canja rayuwarmu.

MU YI KARATU YADDA ZA MU FAHIMTA

4. Mene ne Luka 10:​25-29 suka koya mana game da karanta Kalmar Allah?

4 Muna so mu fahimci abubuwan da muke karantawa a Kalmar Allah. In ba haka ba, abin da muka karanta ba zai amfane mu ba. Alal misali, ka ga tattaunawar da Yesu ya yi da wani “malamin Koyarwar Musa.” (Karanta Luka 10:​25-29.) Da malamin ya tambayi Yesu abin da zai yi don ya sami rai na har abada, Yesu ya taimaka masa ya sami amsar daga Kalmar Allah ta wajen cewa: ‘Me Koyarwar Musa ta ce? Yaya kuma kake fassarta ta?’ Mutumin ya ba da amsar da ta dace ta wajen ƙaulin Nassin da ya ce mu ƙaunaci Allahnmu da kuma maƙwabtanmu. (L. Fir. 19:18; M. Sha. 6:5) Amma ka lura da abin da mutumin ya ce bayan hakan. Ya ce: “Shin, wane ne maƙwabcina?” Ta wannan tambayar, mutumin ya nuna cewa bai fahimci abin da yake karantawa ba. Kuma hakan ya sa bai san yadda zai yi amfani da abin da yake koya a rayuwarsa ba.

Za mu iya koyan yadda za mu fahimci abin da muke karantawa a Littafi Mai Tsarki

5. Ta yaya yin adduꞌa da kuma karatu a hankali za su taimaka maka?

5 Za mu iya inganta yadda muke karanta Kalmar Allah, idan muna karatu da kyau. Ga wasu abubuwan da za su taimaka maka ka yi hakan. Ka yi adduꞌa kafin ka soma karatun. Muna bukatar taimakon Jehobah don mu iya fahimtar Kalmarsa. Don haka, mu roƙe shi ya ba mu ruhu mai tsarki don mu iya mai da hankali yayin da muke karatu. Bayan haka, ka yi karatun a hankali. Wannan zai taimaka maka ka fahimci abin da kake karantawa. Kana iya karantawa da babbar murya ko kuma ka yi karatun yayin da kake sauraran rekodin na Littafi Mai Tsarki. Yin hakan zai taimaka maka ka fahimci abin da kake karantawa, ka koyi darasi kuma ka tuna abin da ka koya. (Yosh. 1:8) Idan ka gama karatun, ka sake yin adduꞌa kuma ka gode wa Jehobah don kyautar Kalmarsa Littafi Mai Tsarki, sai ka roƙe shi ya taimaka maka ka yi abin da ka koya.

Hotuna: 1. Wata ꞌyar ꞌuwa tana rubuta abin da za ta makala a Littafi Mai Tsarkinta. 2. Wani danꞌuwa da yake nazarin wani talifi a wayarsa yana jan layi kuma yana rubuta darussan da ya koya. 3. Wata ꞌyarꞌuwa da take karanta Littafi Mai Tsarki a manhajar “JW Library” tana jan layi kuma tana rubuta darussan da ta koya.

Me ya sa rubuta abin da kake karantawa zai taimaka maka ka fahimci abin da kake karantawa kuma ka tuna da shi? (Ka duba sakin layi na 6)

6. Me ya sa yi wa kanka tambayoyi da kuma rubuta abubuwan da ka koya za su taimaka maka ka fahimci abin da kake karantawa? (Ka kuma duba hoton.)

6 Ga wasu ƙarin abubuwa guda biyu da za su taimaka maka ka fahimci Littafi Mai Tsarki. Ka yi wa kanka tambayoyi game da abin da kake karantawa. Yayin da kake karanta wani labari, ka tambayi kanka: ‘Su wane ne a labarin nan? Wane ne yake magana? Da wa yake magana, kuma me ya sa? A ina ne abubuwan suke faruwa kuma yaushe ne suka faru?’ Irin waɗannan tambayoyin za su sa ka yi tunani kuma su sa ka fahimci abin da kake karantawa. Ƙari ga haka, idan kana karatun, ka riƙa rubuta abubuwan da kake koya. Idan kana rubuta abubuwan da kake koya, hakan zai taimaka maka ka yi tunani a kansu kuma ka fahimci labarin da kyau. Ban da haka ma, zai taimaka maka ka tuna abin da ka karanta. Kana iya rubuta tambayoyi ko ka rubuta abubuwan da ka koya daga binciken da ka yi ko kuma ka takaita muhimman batutuwa. Kana iya rubuta yadda za ka bi abin da ka karanta, ko ka rubuta yadda ka ji game da abin da ka karanta. Rubuta irin abubuwan nan za su taimaka maka ka ga cewa Kalmar Allah saƙo ne daga Allah gare ka.

7. Wane abu ne muke bukata yayin da muke karatu kuma me ya sa? (Matiyu 24:15)

7 Yesu ya ambata wani abu mai muhimmanci da muke bukata don mu fahimci Kalmar Allah, wato ganewa. (Karanta Matiyu 24:15.) Mece ce ganewa? Ganewa ce take taimaka mana mu ga yadda abubuwa suke da alaƙa da juna da yadda suka bambanta da kuma yadda za mu fahimci abin da ba a bayyana dalla-dalla ba. Ƙari ga haka, kamar yadda Yesu ya faɗa, muna bukatar ganewa don mu fahimci annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki da suke cika. Muna kuma bukatar ganewa don mu amfana sosai daga abubuwan da muke karantawa daga Littafi Mai Tsarki.

8. Ta yaya za mu yi karatu yadda za mu gane?

8 Jehobah yana ba wa bayinsa ganewa. Don haka, ka yi adduꞌa kuma ka roƙe shi ya sa ka kasance da wannan halin. (K. Mag. 2:6) Ta yaya za ka yi abubuwan da suka jitu da adduꞌarka? Ka riƙa bincika abubuwan da ka karanta kuma ka ga yadda suke da alaƙa da abubuwan da ka sani. Wani abin da zai taimaka maka ka yi hakan shi ne, Littafin Bincike Don Shaidun Jehobah. Wannan littafin binciken zai taimaka maka ka fahimci abin da kake karantawa a Littafi Mai Tsarki kuma za ka ga yadda za ka bi shawarar a rayuwarka. (Ibran. 5:14) Idan kana karatu yadda za ka gane, hakan zai sa ka ƙara fahimtar Littafi Mai Tsarki.

KA YI KARATU YADDA ZA KA KOYI DARUSSA

9. Wace koyarwa mai muhimmanci ce Sadukiyawan ba su mai da hankali a kai ba?

9 Sadukiyawa sun san littattafai biyar na farko na Nassosin Ibrananci, amma ba su amince da koyarwa masu muhimmanci da ke littattafan nan ba. Alal misali, ka ga abin da Yesu ya ce saꞌad da wasu Sadukiyawa suka yi masa tambaya game da tashin matattu. Yesu ya tambaye su: ‘Ba ku taɓa karanta wannan a littafin Musa ba, don an rubuta cikin labarin ƙaramin itacen da ya ci wuta, cewa, “Ni ne Allah na Ibrahim, da na Ishaku, da kuma na Yakub?” ’ (Mar. 12:​18, 26) Ko da yake Sadukiyawan sun sha karanta wannan Nassin, amma tambayar da Yesu ya yi musu ta nuna cewa ba su mai da hankali ga koyarwar tashin matattu ba, wadda koyarwa ce mai muhimmanci.​—Mar. 12:27; Luk. 20:38.d

10. Mene ne muke bukatar mu mai da hankali a kai saꞌad da muke karatu?

10 Wane darasi ne muka koya daga hakan? Idan muna karanta Littafi Mai Tsarki, mu mai da hankali ga abin da ayar ko kuma labarin yake koya mana. Ba abubuwa masu sauƙi ne za mu fi mai da hankali a kai ba, amma muna bukatar mu fahimci koyarwa da ƙaꞌidodi masu zurfi. Waɗannan abubuwan suna kama da arzikin da ke cikin ƙasa domin da wuya ake samun su.

11. Bisa ga abin da ke 2 Timoti 3:​16, 17, ta yaya za ka koyi darussa daga karatun Littafi Mai Tsarki?

11 Ta yaya za ka koyi darussa saꞌad da kake karanta Littafi Mai Tsarki? Ka ga abin da 2 Timoti 3:​16, 17 suka ce. (Karanta.) Ayar ta ce ‘duk Rubutacciyar Maganar Allah . . . tana kuma da amfani’ wajen (1) koyarwa, (2) tsawatarwa, (3) gyaran hali da (4) horarwa. Ko Nassosin da ba ka yawan karantawa ma za su iya amfanar ka a hanyoyi huɗun nan. Ka bincika abin da kake karantawa don ka ga abin da yake koya maka game da Jehobah da nufinsa da kuma ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki. Ka ga yadda yake da amfani wajen tsawatarwa. Za ka iya yin hakan ta wajen yin laꞌakari da ayoyin da za su taimaka maka ka san halaye marasa kyau da yadda za ka guje musu da kuma yadda za ka riƙe aminci ga Jehobah. Ka ga yadda za ka iya yin amfani da abin da ka karanta don ka gyara raꞌayi marar kyau na wani da ka haɗu da shi a waꞌazi. Ka lura da horarwar da ke ayoyin don ta taimaka maka ka ga abubuwa yadda Jehobah yake yi. Idan kana mai da hankali a kan abubuwa huɗun nan, za ka ga darussa masu muhimmanci da za su inganta yadda kake karanta Littafi Mai Tsarki.

KA BARI KARATUN DA KAKE YI YA CANJA RAYUWARKA

12. Me ya sa Yesu ya yi wa Farisawan tambayar nan “Ko ba ku karanta” ba?

12 Yesu ya yi tambayar nan ‘Ko ba ku karanta ba?’ don ya nuna raꞌayi marar kyau da Farisawan suke da shi game da Nassosi. (Mat. 12:​1-7)e Yesu ya yi tambayar nan ne saꞌad da Farisawan suka ce mabiyansa sun taka Dokar Assabaci. Da Yesu yake mai da martani, ya yi ƙaulin Nassosi guda biyu da kuma wata aya daga littafin Hosiya don ya nuna cewa Farisawan ba sa nuna jinƙai kuma ba su fahimci dalilin da ya sa aka kafa Dokar Assabaci ba. Me ya sa mutanen nan ba su bar abin da suke karantawa a Kalmar Allah ya canja su ba? Domin suna karantawa ne ba don kansu ba amma don su ga kurakuren wasu. Halinsu ya hana su fahimtar abin da suke karantawa.​—Mat. 23:23; Yoh. 5:​39, 40.

13. Wane raꞌayi ne ya kamata mu kasance da shi saꞌad da muke karanta Littafi Mai Tsarki, kuma me ya sa?

13 Abubuwan da Yesu ya faɗa sun nuna mana cewa muna bukatar mu kasance da raꞌayin da ya dace saꞌad da muke karanta Littafi Mai Tsarki. Muna bukatar mu kasance da sauƙin kai kuma mu so koyan sabon abu, ba kamar Farisawan ba. Dole ne mu kasance da ‘sauƙin kai’ don mu ‘karɓi kalmar da aka shuka a zuciyarmu.’ (Yak. 1:21) Idan muna da sauƙin kai, za mu bar Kalmar Allah ta canja rayuwarmu. Idan ba ma karanta Littafi Mai Tsarki don mu ga kurakuren wasu, hakan zai sa mu bi shawarwarin da ya bayar game da jinƙai da tausayi da kuma ƙauna a rayuwarmu.

Ta yaya za mu san ko muna barin Kalmar Allah ta canja mu? (Ka duba sakin layi na 14)f

14. Ta yaya za mu san ko muna barin Kalmar Allah ta canja mu? (Ka kuma duba hoton.)

14 Yadda muke shaꞌani da mutane zai nuna ko muna barin Kalmar Allah ta canja mu ko aꞌa. Farisawan sun ƙi su bar Kalmar Allah ta ratsa zuciyarsu kuma hakan ya sa suna ganin “marasa laifi da laifi.” (Mat. 12:7) Hakazalika, yadda muke ganin mutane zai nuna ko muna barin Kalmar Allah ta shafi rayuwarmu ko aꞌa. Alal misali, muna saurin ganin halaye masu kyau na mutane ko dai muna saurin ganin kurakurensu? Shin muna nuna wa mutane jinƙai kuma muna a shirye mu gafarta musu ko dai muna saurin sūkar mutane da kuma riƙe su a zuci? Amsoshinmu ga tambayoyin nan za su nuna ko muna barin abin da muke karantawa ya canja tunaninmu da ayyukanmu da kuma yadda muke ji.​—1 Tim. 4:​12, 15; Ibran. 4:12.

KARANTA KALMAR ALLAH TANA SA MU FARIN CIKI

15. Yaya Yesu ya ji game da Nassosi?

15 Yesu yana ƙaunar Nassosi sosai kuma an annabta yadda yake ji a cikin littafin Zabura 40:​8, da ta ce: “Ina marmari in aikata nufinka, ya Allahna, gama Koyarwarka a rubuce take a zuciyata.” A sakamakon haka, Yesu ya yi farin ciki kuma ya yi nasara a hidimarsa ga Jehobah. Mu ma za mu yi farin ciki kuma mu yi nasara idan muna barin Kalmar Allah ta ratsa zuciyarmu.​—Zab. 1:​1-3.

16. Mene ne za ka iya yi don ka amfana sosai daga karatun Littafi Mai Tsarki? (Ka duba akwatin nan “Kalaman Yesu Za Su Iya Taimaka Maka Ka Fahimci Abin da Ka Karanta.”)

16 Bisa ga kalaman Yesu da kuma misalin da ya kafa mana, zai dace mu inganta yadda muke karanta Littafi Mai Tsarki. Za mu iya yin hakan ta wajen yin adduꞌa da yin karatu a hankali da yin tambayoyi da kuma rubuta abubuwan da muka koya. Za mu iya gane abin da muke karantawa ta wajen yin amfani da littattafanmu don mu yi bincike. Za mu iya koyan yadda za mu yi amfani da Kalmar Allah da kyau ta wajen neman muhimman darussan da suke da wuyar ganewa. Ƙari ga haka, za mu iya barin Kalmar Allah ta canja rayuwarmu idan muna karanta ta da raꞌayin da ya dace. Idan muna iya ƙoƙarinmu don mu bi shawarwarin nan, za mu amfana sosai daga karatun Littafi Mai Tsarki kuma za mu ƙara kusantar Jehobah.​—Zab. 119:​17, 18; Yak. 4:8.

Kalaman Yesu Za Su Iya Taimaka Maka Ka Fahimci Abin da Ka Karanta

  • Ka yi ƙoƙari ka fahimci abin da kake karantawa kuma ka zama mai ganewa don ka san yadda za ka yi amfani da abin da ka koya.​—Mat. 24:15; Luk. 10:​25-37.

  • Ka yi bincike a kan nassin da ka karanta don ka iya samun muhimman darussan da suke da wuyar samuwa.​—Mar. 12:​18-27.

  • Ka bar Kalmar Allah ta canja ka kuma ta shafi yadda kake sha’ani da mutane.​—Mat. 12:​1-8.

YAYIN DA KAKE KARANTA LITTAFI MAI TSARKI, MENE NE ZAI IYA TAIMAKA MAKA KA . . .

  • fahimci abin da kake karantawa?

  • nemi darussa masu muhimmanci?

  • bar Kalmar Allah ta canja ka?

WAƘA TA 95 Muna Samun Ƙarin Haske

a Dukanmu da ke bauta wa Jehobah, muna duk ƙoƙarinmu don mu karanta Kalmarsa koyaushe. Ban da bayin Jehobah, akwai mutane da yawa da suke karanta Littafi Mai Tsarki, amma ba sa fahimtar abin da suke karantawa. Abin da ya faru da mutane ke nan a zamanin Yesu. Idan muka bincika abin da Yesu ya gaya wa waɗanda suke karanta Kalmar Allah, za mu koyi darasi a kan yadda za mu inganta karatunmu na Littafi Mai Tsarki.

b A lokacin da Yesu ya yi baftisma kuma aka shafe shi da ruhu mai tsarki, ya tuna rayuwarsa a sama kafin ya zo duniya.​—Mat. 3:16.

c Maryamu ta san Nassosi sosai kuma takan yi ƙaulin su. (Luk. 1:​46-55) Mai yiwuwa Yusufu da Maryamu ba su da isashen kuɗin da za su sayi Littafi Mai Tsarki. Saboda haka, sukan saurara da kyau saꞌad da ake karanta Kalmar Allah a haikali don su iya tunawa da ita.

d Ka duba talifin nan mai jigo “Ka Kusaci Allah​—Shi ‘Allah na . . . Masu Rai’ Ne” a Hasumiyar Tsaro 1 ga Maris, 2013.

e Ka kuma duba Matiyu 19:​4-6 inda Yesu ya yi wa Farisawan irin tambayar nan: “Ashe, ba ku karanta ba?” Ko da yake sun karanta game da lokacin da Allah ya halicci abubuwa, amma sun ƙi su mai da hankali ga abin da hakan yake koya mana game da raꞌayin Allah a kan aure.

f BAYANI A KAN HOTUNA: Saꞌad da ake taro a Majamiꞌar Mulki, wani ɗanꞌuwa da yake kula da bidiyo da sauti ya yi kurakurai da yawa. Duk da haka, bayan taro ꞌyanꞌuwan da suke tare da shi ba su mai da hankali ga kurakurensa ba amma sun yaba masa don ƙoƙarin da yake yi.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba