Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • Ka Dogara Ga Jehovah Ƙwarai A Lokacin Wahala
    Hasumiyar Tsaro—2003 | 1 Satumba
    • 7, 8. (a) Ta yaya Yesu ya nuna ya san cewa ’yan Adam ajizai suna da halin damuwa game da abin duniya? (Duba hasiya.) (b) Wace shawara ta hikima Yesu ya bayar game da yadda za a guje wa yawan alhini?

      7 A cikin Huɗuba ta Bisa Dutse, Yesu ya yi gargaɗi: “Kada ku yi alhini saboda ranku, abin da za ku ci, ko kuwa abin da za ku sha; ko saboda jikinku, abin da za ku yafa.”b (Matta 6:25) Yesu ya sani cewa mutane ajizai dama suna damuwa da samun abubuwan biyan bukata. Amma, ta yaya za mu iya daina yin “alhini” game da irin waɗannan abubuwa? “Ku fara biɗan mulkin” in ji Yesu. Duk da irin matsalolin da muke fuskanta, dole mu ci gaba da bauta wa Jehovah abu na farko a rayuwarmu. Idan muka yi haka, Ubanmu na samaniya zai “ƙara” mana dukan abubuwan yau da kullum da muke bukata. A wata sassa, zai sa mu ci gaba da samun na ci da sha.—Matta 6:33.

  • Ka Dogara Ga Jehovah Ƙwarai A Lokacin Wahala
    Hasumiyar Tsaro—2003 | 1 Satumba
    • b Alhini da aka kwatanta a nan, an ce “damuwa da tsoro da ke hana farin ciki a rayuwa” ne. Wasu fassara suka ce “kada ku yi alhini” ko kuma “kada ku damu.” Amma irin juyin nan ‘kada ku yi alhini’ ko kuma ‘kada ku damu’ na nuna cewa kada ma a soma yin alhinin ko damuwar. Amma wata majiya ta ce: “Aikatau na Helenanci mai nuna sa’in da ake ciki, yana ba da umurnin da ke nuna cewa a daina wasu ayyukan da aka soma.”

Littattafan Hausa (1987-2025)
Fita
Shiga Ciki
  • Hausa
  • Raba
  • Wadda ka fi so
  • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
  • Ka'idojin Amfani
  • Tsarin Tsare Sirri
  • Saitin Tsare Sirri
  • JW.ORG
  • Shiga Ciki
Raba