Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 2/15 pp. 24-28
  • Ka Yi Ƙaunar Adalci Da Dukan Zuciyarka

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Yi Ƙaunar Adalci Da Dukan Zuciyarka
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ku Biɗi Adalcin Allah
  • Ka Bincika Makamanka na Ruhaniya
  • Ka Kasance da Kyakkyawan Lamiri
  • Yunwa da Ƙishi don Adalci
  • Samun Amfani ta Wurin Ƙaunar Nagarta
  • Bayin Jehobah Suna Son Adalci
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • Ka Yi Murna Cikin Adalcin Jehovah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Biɗan Adalci Zai Kāre Mu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ka Ci Gaba Da Biɗan “Adalcinsa” Da Farko
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 2/15 pp. 24-28

Ka Yi Ƙaunar Adalci Da Dukan Zuciyarka

“Ka yi ƙaunar adalci.”—ZAB. 45:7.

1. Mene ne zai taimake mu mu yi tafiya bisa “hanyoyin adalci”?

JEHOBAH yana yi wa mutanensa ja-gora bisa “hanyoyin adalci,” ta kalmarsa da ruhunsa mai tsarki. (Zab. 23:3) Tun da mu ajizai ne, mukan kauce daga wannan hanya. Koma ga yin abin da ya dace yana bukatar ƙoƙari. Mene ne zai taimake mu mu yi nasara? Kamar Yesu, wajibi ne mu yi ƙaunar adalci.—Karanta Zabura 45:7.

2. Mene ne “hanyoyin adalci”?

2 Mene ne “hanyoyin adalci”? Ana sanin waɗannan “hanyoyin” ta mizanin Jehobah na adalci. A Ibrananci da Helenanci, “adalci” yana nufin a manne wa mizanai na ɗabi’a. Tun da Jehobah “mazaunin adalci” ne, waɗanda suke bauta masa suna farin cikin bincika tafarkin adalci da ya kamata su bi.—Irm. 50:7.

3. Ta yaya za mu iya daɗa koyo game da adalcin Allah?

3 Sai idan mun ƙoƙarta da dukan zuciyarmu don mu yi biyayya ga mizanan Allah masu adalci ne kaɗai za mu faranta masa rai sosai. (K. Sha 32:4) Hakan yana somawa ta koyon dukan abin da za mu iya game da Jehobah Allah daga Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki. Yayin da muke koyo game da shi, muna kusantarsa kowacce rana, ƙaunarmu ga adalcinsa za ta ƙaru sosai. (Yaƙ. 4:8) Wajibi ne kuma mu amince da ja-gorancin hurarriyar Kalmar Allah sa’ad da muke bukatar tsai da muhimmiyar shawara a rayuwa.

Ku Biɗi Adalcin Allah

4. Biɗin adalcin Allah ya ƙunshi me?

4 Karanta Matta 6:33. Biɗan adalcin Allah ya ƙunshi fiye da yin wa’azin bisharar Mulki sa’o’i da yawa. Don Allah ya amince da tsarkakkar hidimarmu, wajibi ne halinmu na kullum ya jitu da mizanansa masu kyau. Dukan waɗanda suke biɗin adalcin Jehobah suna bukatar yin me? Wajibi ne su “yafa sabon mutum, wanda an halitta shi bisa ga Allah cikin adalci da tsarkin gaskiya.”—Afis. 4:24.

5. Mene ne zai taimaka mana mu sha kan sanyin gwiwa?

5 Yayin da muke ƙoƙari mu yi biyayya ga mizanan adalci na Allah, za mu iya sanyin gwiwa a wasu lokatai saboda kurakuranmu. Mene ne zai iya taimaka mana mu sha kan sanyin gwiwa mai raunana mu kuma mu koya ƙauna da kuma yin adalci? (Mis. 24:10) Dole ne mu kusaci Jehobah ta addu’a a kai a kai “da zuciya mai-gaskiya da sakankancewar bangaskiya.” (Ibran. 10:19-22) Ko mu shafaffu Kiristoci ne ko kuma muna da begen zama a duniya, muna ba da gaskiya ga hadayar fansa na Yesu Kristi da kuma hidimominsa a matsayin Babban Firist. (Rom. 5:8; Ibran. 4:14-16) Manzo Yohanna ya rubuta: “Jinin Yesu . . . yana tsarkake mu kuma daga zunubi duka.” (1 Yoh. 1:6, 7) Ko da zunubanmu “sun yi baƙi kamar mulufi, za su yi fari kamar kankara” in ji Littafi Mai Tsarki. Jehobah ya yi mana tanadi mai girma ta wurin hadayar fansa na Ɗansa ƙaunatacce!—Isha. 1:18.

Ka Bincika Makamanka na Ruhaniya

6. Me ya sa yake da muhimmanci mu riƙa bincika makamanmu na ruhaniya?

6 A kowane lokaci, muna bukatar mu yafa “sulke na adalci” don sashe ne mai muhimmanci na makami na ruhaniya daga wurin Allah. (Afis. 6:11, 14) Ko bai daɗe ba da muka keɓe kanmu ga Jehobah ko idan muna bauta masa da daɗewa, yana da muhimmanci mu riƙa bincika makamanmu na ruhaniya a kowace rana. Me ya sa? Domin an jefo Iblis da aljannunsa zuwa duniya. (R. Yoh. 12:7-12) Shaiɗan yana fushi, kuma ya san cewa lokacinsa saura kaɗan. Saboda haka, yana daɗa kai wa mutanen Allah farmaki. Shin mun san muhimmancin yafa “sulke na adalci”?

7. Ta yaya za mu aikata idan muka san bukatarmu na “sulke na adalci”?

7 Sulke yana kāre zuciya ta zahiri. Domin yanayinmu na ajizanci, zuciyarmu ta alama takan kasance da rikici kuma tana cutarmu. (Irm. 17:9) Tun da yake zuciyarmu takan yi abin da ba shi da kyau, yana da muhimmanci mu koyar da ita kuma mu kame ta. (Far. 8:21) Idan muka san cewa muna bukatar “sulke na adalci” ba za mu cire shi na ɗan lokaci ba ta wurin zaɓan nishaɗi da Allah ba ya so; ko kuma mu ƙyale kanmu muna wasiƙar jaki game da yin laifi. Ba za mu ɓata lokaci da yawa wajen kallon talabijin ba. Maimakon haka, za mu ci gaba da yin ƙoƙari don mu yi abin da ke faranta wa Jehobah rai. Ko idan mun yi tuntuɓe ta wajen yin tunanin abubuwa na jiki na ɗan lokaci, za mu tashi kuma da taimakon Jehobah.—Karanta Misalai 24:16.

8. Me ya sa muke bukatar “garkuwa ta bangaskiya”?

8 Wani sashe na makamanmu na ruhaniya shi ne “garkuwa ta bangaskiya.” Tana taimaka mana mu “ɓice dukan jefejefe masu-wuta na Mugun.” (Afis. 6:16) Kuma bangaskiya da ƙaunar Jehobah da dukan zuciyarmu za su taimaka mana mu yi adalci kuma mu kasance a kan hanyar rai madawwami. Yayin da muke ƙara ƙaunar Jehobah, za mu ƙara ɗaukan adalcinsa da tamani. Lamirinmu kuma fa? Ta yaya yake taimakonmu a ƙoƙarce-ƙoƙarcenmu don mu ƙaunaci adalci?

Ka Kasance da Kyakkyawan Lamiri

9. Ta yaya za mu amfana ta wajen kasancewa da kyakkyawan lamiri?

9 A lokacin da muka yi baftisma, mun roƙi Jehobah ya ba mu “kyakkyawan lamiri.” (1 Bit. 3:21) Domin muna ba da gaskiya ga fansa, jinin Yesu yana rufe zunubanmu kuma saboda haka muna more dangantaka na kud da kud da Allah. Amma, don mu ci gaba da wannan dangantakar, muna bukatar mu kasance da kyakkyawan lamiri. Idan lamirinmu a wani lokaci yana damunmu da kuma yi mana gargaɗi, ya kamata mu yi farin ciki cewa yana aiki da kyau. Irin wannan gargaɗin yana nuna cewa lamirinmu yana aiki daidai wa daida game da hanyoyin adalci na Jehobah. (1 Tim. 4:2) Amma lamiri zai iya taimaka wa mutane da suke ƙaunar adalci a wata hanya.

10, 11. (a) Ka ba da labarin da ya nuna abin da ya sa za mu yi biyayya da lamirinmu da aka koyar da Littafi Mai Tsarki. (b) Me ya sa yin ƙaunar adalci za ta sa mu farin ciki sosai?

10 Sa’ad da muka yi abin da ba shi da kyau, lamirinmu zai iya hukunta mu ko kuma ya riƙa damunmu. Wani matashi ya bijire daga “hanyoyin adalci.” Ya faɗa jarrabar kallon hotunan batsa kuma ya soma shan wi-wi. Ba ya sakin jiki sa’ad da ya halarci taro kuma ya ji kamar munafuki sa’ad da ya fita hidimar fage, saboda haka sai ya daina yin waɗannan ayyukan Kirista. Ya ce: “Amma ban san cewa lamirina zai riƙa damu na don ayyukan da nake yi ba.” Ya daɗa, “Na yi shekaru huɗu ina wannan salon rayuwa na wauta.” Sai ya soma tunanin ya dawo ƙungiyar. Ko da yake yana tunanin cewa Jehobah ba zai saurari addu’arsa ba, ya yi addu’a kuma ya roƙi gafara. Bai kai minti goma ba sai mahaifiyarsa ta ziyarce shi kuma ta ƙarfafa shi ya soma halartan taro kuma. Ya tafi Majami’ar Mulki kuma ya gaya wa wani dattijo ya yi nazari da shi. Da shigewar lokaci, sai ya yi baftisma kuma ya yi godiya ga Jehobah don ceton ransa.

11 Babu shakka muna amfana ta yin abin da yake da kyau. Yayin da muke koyo mu yi ƙaunar adalci kuma mu yi hakan sosai, za mu ƙara yin farin ciki ta yin abin da ke faranta wa Ubanmu na samaniya rai. Kuma ka yi tunanin wannan, rana tana zuwa da dukan ’yan Adam za su riƙa jin daɗin lamirinsu; za su nuna halin Allah sosai a rayuwarsu. Saboda haka, bari mu yi ƙaunar adalci da dukan zuciyarmu kuma mu sa Jehobah farin ciki.—Mis. 23:15, 16.

12, 13. Ta yaya za mu koyar da lamirinmu?

12 Mene ne za mu iya yi don mu koyar da lamirinmu? Sa’ad da muka yi nazarin Nassosi da littattafanmu da suke bayyana Littafi Mai Tsarki, yana da muhimmanci mu tuna cewa “zuciyar mai-adalci ta kan yi tunanin abin da za ta amsa.” (Mis. 15:28) Ka yi la’akari yadda wannan yake da amfani sa’ad da muke son mu tsai da shawara game da aiki. Idan wani aiki ya saɓa wa bukatu na Nassi, yawancinmu da sauri za mu bi ja-gorar da rukunin bawan nan mai aminci mai hikima ya ba da. Amma, sa’ad da ba a faɗa dalla-dalla ba cewa wani aiki bai dace ba ko ya dace, muna bukatar mu nemi ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da sun yi daidai da wannan yanayin kuma mu yi tunani da kuma addu’a a kan waɗannan ƙa’idodin.a Wannan ya shafi ƙa’idodi kamar su guje wa ɓata lamirin wasu mutane. (1 Kor. 10:31-33) Ya kamata mu damu musamman game da ƙa’idodin da suka shafi dangantakarmu da Allah. Idan Jehobah ya kasance da gaske a gare mu, za mu tambayi kanmu, ‘Yin wannan aikin zai ɓata wa Jehobah rai ne?’—Zab. 78:40, 41.

13 Sa’ad da muke shiri don Nazarin Hasumiyar Tsaro ko kuma Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya, ya kamata mu tuna cewa muna bukatar mu yi bimbini a kan bayanin da aka ba da. Muna saurin jan layi ga amsa na tambayar nazarin kuma mu wuce zuwa sakin layi na gaba? Yin nazari hakan ba zai zurfafa ƙaunarmu ta adalci ba ko kuma ya sa mu sami lamiri da zai riƙa yi mana gargaɗi ba. Idan za mu ƙaunaci adalci, muna bukata mu yi nazari sosai da bimbini a kan abin da muka karanta a cikin Kalmar Allah. Koyon ƙaunar adalci da dukan zuciyarmu yana bukatar ƙoƙari sosai!

Yunwa da Ƙishi don Adalci

14. Yaya Jehobah Allah da Yesu Kristi suke son mu ji game da tsarkakkiyar hidimarmu?

14 Jehobah Allah da kuma Yesu Kristi suna son mu kasance da farin ciki a yin tsarkakkar hidima. Mene ne zai sa mu farin ciki sa’ad da muke hakan? Ƙaunar adalci! A Huɗubarsa a kan Dutse, Yesu ya ce: “Masu-albarka ne waɗanda suke yunwata suna ƙishirta zuwa adalci: gama za a ƙosadda su.” (Mat. 5:6) Waɗannan kalmomi suna da waɗanne muhimmanci ga waɗanda suke da muradin yin ƙaunar adalci?

15, 16. A waɗanne hanyoyi ne za a iya ƙosar da yunwa da ƙishirwa na ruhaniya?

15 Shaiɗan ne yake sarautar duniyar da muke zama a ciki. (1 Yoh. 5:19) Idan muka karanta jarida a kowace ƙasa, za mu ga labaran zalunci da mugunta da ya zama gama gari. Yana damun mai adalci ya yi tunanin yadda ’yan Adam suke zalunta juna. (M. Wa. 8:9) A matsayin waɗanda suke ƙaunar Jehobah, mun san cewa shi kaɗai ne zai ƙosar da yunwa na ruhaniya da ƙishirwar waɗanda suke son su koya adalci. Ba da daɗewa ba, za a kawar da marasa adalci, kuma masu ƙaunar adalci ba za su ƙara fuskantar matsala da masu mugunta da mugayen ayyukansu suke jawowa ba. (2 Bit. 2:7, 8) Babu shakka wannan zai kawo sauƙi!

16 A matsayin bayin Jehobah da mabiyan Yesu Kristi, mun fahimci cewa “za a ƙosadda” dukan waɗanda suke yunwa da ƙishirwa don adalci. Za a ƙosar da su sosai ta wurin tsarin Allah na sababbin sammai da sabuwar duniya “inda adalci yake zaune.” (2 Pet. 3:13) Saboda haka kada mu yi sanyin gwiwa ko kuma mu yi mamaki cewa zalunci da mugunta sun ɗauke adalci daga wannan duniya na Shaiɗan. (M. Wa. 5:8) Jehobah, Maɗaukaki Duka ya san abin da yake faruwa kuma ba da daɗewa ba zai ceci masu ƙaunar adalci.

Samun Amfani ta Wurin Ƙaunar Nagarta

17. Waɗanne amfani ne ake samu ta wurin ƙaunar adalci?

17 Zabura 146:8 ya nanata amfani na musamman na bin tafarkin adalci. Marubucin wannan zabura ya rera waƙa: “Ubangiji yana ƙaunar masu-adalci.” Ka yi tunanin wannan! Mamallakin dukan sararin samaniya yana ƙaunarmu don muna ƙaunar adalci! Domin Jehobah yana ƙaunarmu, zai tabbata cewa muna da abin biyan bukata yayin da muke saka al’amura na Mulkin farko a rayuwarmu. (Karanta Zabura 37:25; Misalai 10:3.) Ba da daɗewa ba, masu ƙaunar adalci za su more dukan wannan duniya. (Mis. 13:22) Ga yawancin mutanen Allah, ladar yin adalci zai zama farin ciki matuƙa da rayuwa na dindindin a cikin kyakkyawar aljanna a duniya. A yanzu ma, waɗanda suke ƙaunar adalcin Allah suna samun ladar kwanciyar hankali da ke kawo haɗin kai cikin iyalansu da kuma ikilisiyoyinsu.—Filib. 4:6, 7.

18. Waɗanne abubuwa masu kyau ne za mu iya yi yayin da muke jiran ranar Jehobah?

18 Yayin da muke jiran zuwan wannan babbar ranar Jehobah, dole ne mu ci gaba da biɗan adalcinsa. (Zaf. 2:2, 3) Saboda haka, bari mu nuna tabbataciyar ƙauna ga hanyoyin adalci na Jehobah Allah. Hakan ya ƙunshi yafa “sulke na adalci” sosai don mu kāre zuciyarmu ta alama. Muna bukatar mu kasance da kyakkyawan lamiri, wanda zai kawo mana farin ciki kuma ya faranta zuciyar Allahnmu.—Mis. 27:11.

19. Mene ne ya kamata mu ƙuduri aniyar yi, kuma mene ne za a tattauna a talifi na gaba?

19 Idanun Jehobah “suna kai da kawowa a cikin dukan duniya, domin ya bayyana kansa mai ƙarfi sabili da waɗanda zuciyarsu ta kamalta gareshi.” (2 Laba. 16:9) Waɗannan kalmomi suna da ban ƙarfafa a gare mu yayin muke yin abu mai kyau sa’ad da muke fuskantar rashin kwanciyar hankali, aika laifi, da mugunta a wannan duniya mai cike da wahala! Hakika, ’yan Adam da yawa da suke a bāre daga Allah suna iya yin mamaki game da hanyoyinmu na adalci. Amma muna amfane kanmu sosai ta wajen manne wa adalcin Jehobah. (Isha. 48:17; 1 Bit. 4:4) Saboda haka, bari mu ƙuduri aniya mu ci gaba da yin farin ciki wajen yin ƙauna da kuma nuna adalci da dukan zuciyarmu. Amma, yin hakan da dukan zuciyarmu ta ƙunshi ƙin mugunta. Talifi na gaba zai nuna abin da wannan yake nufi.

[Hasiya]

a Don samun bayani a kan ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da suka yi magana a kan zaɓan aikin, ka duba lv babi na 15 sakin layi na 14 zuwa 17.

Yaya Za Ka Amsa?

• Me ya sa nuna godiya don fansa yake da muhimmanci don yin ƙaunar adalci?

• Me ya sa yake da muhimmanci mu yafa “sulke na adalci”?

• Ta yaya za mu koyar da lamirinmu?

[Hoton da ke shafi na 26]

Lamiri da aka koyar yana taimaka mana mu magance shawarwarin zaɓan aiki da za mu yi

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba