Yaya Ƙarfin Dogararka Ga Allah?
“Ku fara biɗan mulkinsa.”—MATTA 6:33.
1, 2. Wane mataki ne wani saurayi ya ɗauka game da aiki, kuma me ya sa?
WANI saurayi yana so ya kasance da amfani ƙwarai a ikilisiya. Matsalarsa ita ce aikinsa yana hana shi halartar taro a kai a kai. Yaya ya magance matsalar? Ya sauƙaƙa rayuwarsa, ya yi murabus daga aikinsa, kuma daga baya ya sami aikin da ba zai hana shi ayyukansa na Kirista ba. A yau, ba ya samu kamar yadda yake samu a dā, amma har ila yana kula da iyalinsa kuma a yanzu ikilisiya tana iya amfani da shi.
2 Ka fahimci abin da ya sa wannan saurayin ya ɗauki wannan matakin kuwa? Kana gani za ka iya ɗaukan wannan mataki idan ka kasance a cikin yanayi irin nasa? Abin yabo ne, cewa Kiristoci da yawa sun yi haka, kuma abin da suka yi ya nuna dogararsu ga alkawarin Yesu: “Ku fara biɗan mulkinsa, da adalcinsa; waɗannan abu duka fa za a ƙara muku su.” (Matta 6:33) Sun dogara ga Jehobah domin kāriya ba ga duniya ba.—Misalai 3:23, 26.
3. Me ya sa wasu za su yi mamaki ko daidai ne a yau mutum ya fara biɗan Mulki?
3 Domin lokatai masu wuya da muke ciki, wasu za su yi mamaki ko matakin da wannan saurayin ya ɗauka daidai ne. A yau, wasu mutane suna rayuwa cikin matsanancin talauci sa’ad da wasu suna more dukiya mai yawa a duniya a dukan tarihi. Yawancin mutane a ƙasashe marasa arziki za su yi amfani da dukan wani zarafi da suka samu don su ɗan kyautata rayuwarsu. A wani ɓangare kuma, da yawa a ƙasashe masu arziki suna fuskantar matsi su adana irin rayuwa da suke yi a zamani da tattalin arziki ya raunana, yanayin ayyuka suna canjawa, shugabannin ma’aikata da suke bukatar ƙarin lokacin ma’aikatansu. Da irin wannan wahala wajen neman abinci, wasu za su yi mamaki, ‘Har yanzu daidai ne mutum ya fara biɗan Mulki?’ Domin mu amsa wannan tambayar, bari mu bincika waɗanne mutane ne Yesu yake yi wa magana.
“Kada Ku Yi Alhini”
4, 5. Ta yaya Yesu ya kwatanta cewa daidai ne kada mutanen Allah su yi alhini game da damuwa ta rayuwar yau da kullum?
4 Yesu yana Galili yana magana da mutane da suka fito daga wurare dabam dabam. (Matta 4:25) Kaɗan ne idan ma da akwai waɗanda suke da arziki tsakanin waɗannan mutane. Wataƙila, yawanci matalauta ne. Duk da haka Yesu ya aririce su kada su mai da hankali ga tara dukiya amma ga tara abin da ya fi muhimmanci, wato dukiya ta ruhaniya. (Matta 6:19-21, 24) Ya ce: “Kada ku yi alhini saboda ranku, abin da za ku ci, ko kuwa abin da za ku sha; ko saboda jikinku, abin da za ku yafa. Rai ba ya fi gaban abinci ba? jiki kuma ba ya fi tufafi ba?”—Matta 6:25.
5 Ga mutane da yawa da suka saurare shi, kalmomin Yesu za su kasance abu ne da ba zai yiwu ba. Sun sani cewa idan ba su yi fama ba iyalansu za su wahala. Amma kuma, Yesu ya tuna musu tsuntsaye. Tsuntsaye suna neman abinci da wurin kwana kowace rana, duk da haka, Jehobah Allah yana kula da su. Yesu kuma ya bayyana yadda Jehobah yake kula da furannin daji da kyaunsu ya wuce na Sulemanu a ɗaukakarsa. Idan Jehobah yana kula da tsuntsaye da furanni, ba zai fi ma kula da mu ba ne? (Matta 6:26-30) Yesu ya ce, rayuwarmu da kuma jikunanmu sun fi abincin da muke saya domin su rayar da ranmu muhimmanci da kuma kayaki da muke saya domin mu rufe jikinmu. Idan ƙoƙarinmu shi ne mu ciyar da kanmu mu yi wa kanmu sitira, ba tare da wani abin kirki da ya rage domin bauta wa Jehobah ba, ba mu fahimci ainihin dalilin rayuwa ba.—Mai-Wa’azi 12:13.
Ra’ayin da Ya Dace
6. (a) Menene hakkin Kiristoci? (b) Ga wa Kiristoci suke dogara matuƙa?
6 Hakika, Yesu bai ƙarfafa masu sauraronsa su daina aiki su jira Allah ya yi wa iyalansu tanadin abinci ba. Tsuntsaye ma dole ne su nemi abinci ga ’ya’yansu. Saboda haka, Kiristoci ma dole ne su yi aiki idan suna so su sami abinci. Dole ne su kula da hakkin iyalinsu. Kiristoci da suke yi wa wasu aiki da kuma bayi dole ne su yi wa iyayen gidansu aiki tuƙuru. (2 Tassalunikawa 3:10-12; 1 Timothawus 5:8; 1 Bitrus 2:18) Manzo Bulus sau da yawa ya yi aikin ɗinka tanti domin ya taimaki kansa. (Ayukan Manzanni 18:1-4; 1 Tassalunikawa 2:9) Duk da haka, waɗannan Kiristoci ba su dogara ga aikinsu ba domin tsaro. Sun dogara ga Jehobah. Domin haka, sun sami kwanciyar hankali da wasu ba su sani ba. Mai zabura ya ce: “Masu-dogara ga Ubangiji suna kama da dutse Sihiyona, wanda ba shi jijjiguwa, yana zaune har abada.”—Zabura 125:1.
7. Menene zai kasance ra’ayin wanda bai dogara ƙwarai ba ga Jehobah?
7 Dukan wanda bai dogara ba ƙwarai ga Jehobah zai yi tunani dabam. Yawancin ’yan adam suna ɗaukan dukiya ita ce ainihin dalilin tsaro. Saboda haka, iyaye suke ƙarfafa ’ya’yansu su ba da yawancin ƙuruciyarsu ga ƙarin ilimi, suna begen cewa wannan zai sa su sami aiki da za su riƙa samun kuɗi mai tsoka. Abin baƙin ciki, wasu iyalai Kiristoci sun ɗanɗana sun ga haka ba daɗi, sa’ad da ’ya’yansu suka yi hasarar ruhaniyarsu suka juya ga neman dukiya.
8. Wane daidaito ne Kiristoci suke yi?
8 Saboda haka, Kiristoci masu hikima sun fahimci cewa gargaɗin Kristi yana ci a yanzu kamar yadda ya yi a ƙarni na farko, kuma suna ƙoƙarin su kasance da daidaita. Ko da za su yi awoyi masu yawa a wurin aiki domin su cika hakkinsu na Nassosi, ba sa ƙyale bukatar samun kuɗi ta rufe musu ido daga batutuwa masu muhimmanci na ruhaniya.—Mai Wa’azi 7:12.
“Kada Ku Yi Alhini Fa”
9. Ta yaya Yesu ya ƙarfafa waɗanda suka dogara ga Jehobah ƙwarai?
9 A Hudubarsa ta kan Dutse, Yesu ya aririci masu sauraronsa: “Kada ku yi alhini fa, kuna cewa, Me za mu ci? ko kuwa, Me za mu sha? ko kuwa, Da menene za mu yi sutura? Gama waɗannan abu duka al’ummai suna ta biɗa; gama Ubanku na sama ya sani kuna bukatar waɗannan abu duka.” (Matta 6:31, 32) Hakika waɗannan kalmomi suna da ban ƙarfafa! Idan mun dogara ga Jehobah sosai, zai riƙa taimakonmu ko da yaushe. Duk da haka, kalmomin Yesu kuma suna sa a yi tunani. Sun kuma tuna mana cewa idan muka yi “ta biɗan” abin duniya, tunaninmu irin na “al’ummai” ne, mutane da ba Kiristoci na gaskiya ba.
10. Sa’ad da wani saurari ya nemi shawara a wurin Yesu, ta yaya Yesu ya nuna abin da saurayin ya fi ƙauna?
10 Akwai lokacin da wani saurayi mai arziki ya tambayi Yesu abin da zai yi domin ya sami rai madawwami. Yesu ya tuna masa abin da Doka take bukata, domin tana ci a lokacin. Saurayin ya gaya wa Yesu: “Dukan waɗannan na kiyaye su: me na rasa tukuna?” Yesu ya ce masa, “Idan kana so ka kamalta, sai ka tafi, ka sayarda abin da ka ke da shi, ka ba fakirai, za ka sami wadata a sama: ka zo kuma, ka biyo ni.” (Matta 19:16-21) Saurayin ya tafi yana baƙin ciki, domin ba ya son ya yi hasarar dukiyarsa. Ko da yaya yake ƙaunar Jehobah, ya fi ƙaunar dukiyarsa.
11, 12. (a) Wace magana ce mai sa tunani Yesu ya furta game da dukiya? (b) Ta yaya wadata za ta iya kasancewa mahani ga bauta wa Jehobah?
11 Wannan ya sa Yesu ya faɗi wani abin da ba a yi zato ba: “Yana da wuya ga mawadaci shi shiga cikin mulkin sama. . . . Ya fi sauƙi raƙumi ya shiga ta kafar allura, da mawadaci ya shiga cikin mulkin Allah. (Matta 19:23, 24) Yesu yana nufi ne cewa babu wani mai wadata da zai gaji Mulkin? A’a, domin ya ci gaba da cewa: “Ga Allah dukan abu ya yiwu.” (Matta 19:25, 26) Hakika, da taimakon Jehobah wasu masu arziki a wancan zamani sun zama Kiristoci shafaffu. (1 Timothawus 6:17) Duk da haka, Yesu ya furta wannan furci da dalili mai kyau. Yana ba da kashedi ne.
12 Idan mutum ya manne wa abin duniya da tara dukiya kamar yadda wannan saurayin ya yi, suna iya kasancewa abin da za su hana shi bauta wa Jehobah da zuciya ɗaya. Hakan zai kasance gaskiya ga wanda yake da arziki da kuma wanda yake ‘so ya zama mawadaci.’ (1 Timothawus 6:9, 10) Dogara ga abin duniya za ta iya hana mutum damuwa da bukata ta ruhaniya. (Matta 5:3) Saboda haka, ba zai ji yana bukatar taimakon Jehobah ba. (Kubawar Shari’a 6:10-12) Sai ya fara ganin ya kamata a ba shi daraja na musamman a ikilisiya. (Yaƙub 2:1-4) Sai ya ba da yawancin lokacinsa wajen more dukiyarsa maimakon bauta wa Jehobah.
Ku Karɓi Ra’ayin da Ya Dace
13. Wane ra’ayi ne da bai dace ba Lawidikiyawa suke da shi?
13 Wani rukuni da ya kasance da ra’ayi da bai dace ba na dukiya shi ne ikilisiyar Lawudikiya a ƙarni na farko. Yesu ya ce musu: ‘Kuna cewa, mun wadata, mun sami dukiya, ba mu bukaci kome ba; ba ku sani ba malalata na ne ku, abin tausayi, matalauta, makafi, tsiraru.’ Ba dukiyarsu ba ce ta sa Lawudikiyawan suka kasance cikin irin wannan yanayi na taƙaici a ruhaniya. Domin sun dogara ga dukiya ne maimakon ga Jehobah. A sakamakon haka, suka kasance ba su da sanyi ba su da zafi a ruhaniya, kusan Yesu ya tofar da su daga bakinsa.—Ru’ya ta Yohanna 3:14-17.
14. Me ya sa Kiristoci Yahudawa suka cancanci yabonsu da Bulus ya yi?
14 A wani ɓangare kuma, Bulus ya yabi Yahudawa Kiristoci domin halinsu a lokacin tsanani. Ya ce: “Gama kuka yi juyayin waɗanda ke cikin sarƙa, har kuma da farin ciki kuka sha wason dukiyarku, kuna sane ku da kanku kuna da dukiya mafiya kyau, matabbaciya kuwa.” (Ibraniyawa 10:34) Waɗannan Kiristoci hasarar dukiyarsu ba ta kashe musu jiki ba. Sun kasance da farin ciki domin suna riƙe da dukiyarsu “mafiya kyau, matabbaciya kuwa.” Kamar attajirin almarar Yesu wanda ya sadaukar da dukan abin da ya mallaka domin lu’ulu’u mai daraja, sun ƙuduri aniyar ba za su ƙyale begensu ba na Mulki, ko da menene za su sadaukar. (Matta 13:45, 46) Wannan hali ne mai kyau!
15. Ta yaya wata mace Kirista a Liberiya ta saka Mulki farko?
15 A yau mutane da yawa sun koyi irin wannan halin kirki. Alal misali, a Liberiya an ba wa wata matashiya Kirista zarafin zuwa jami’a. A wannan ƙasar ana ɗaukar irin wannan zarafin hanyar samun dukiya ne. Amma, ita majagaba ce, mai wa’azi ce ta cikakken lokaci, kuma an gayyace ta ta je hidimar majagaba na musamman na ɗan lokaci. Ta zaɓi ta saka Mulkin farko ta ci gaba da hidimarta na cikakken lokaci. Ta je inda aka turata, ta fara nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane 21 cikin watanni uku. Wannan matashiya da kuma dubbai kamanta suna saka Mulki farko, ko da za su saɗaukar da dukiya. Ta yaya za su ci gaba da kasancewa da irin wannan hali a duniya da ta cika da neman abin duniya? Sun riga sun koyi halaye masu kyau. Bari mu tattauna wasunsu.
16, 17. (a) Me ya sa filako yake da muhimmanci idan za mu dogara ga Jehobah? (b) Me ya sa ya kamata mu dogara ga alkawuran Allah?
16 Filako: Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka, kada ka jingina ga naka fahimi: A cikin dukan al’amuranka ka shaida shi, shi kuma za ya daidaita hanyoyinka. Kada ka ga kanka mai-hikima ne.” (Misalai 3:5-7) A wani lokaci, wani tafarki zai kasance kamar shi ya fi daga ra’ayin duniya. (Irmiya 17:9) Duk da haka, Kirista mai gaskiya zai dogara ga Jehobah domin ja-gora. (Zabura 48:14) ‘A dukan al’amuransa,’ a cikin ikilisiya, wajen batun ilimi ko kuma aiki, wajen shakatawa, ko kuma dukan wani abu, zai nemi shawarar Jehobah cikin filako.—Zabura 73:24.
17 Dogara ga alkawuran Jehobah: Bulus ya ce: “Mai-zuwa wurin Allah sai shi bada gaskiya akwai shi, kuma shi mai-sākawa ne ga waɗanda ke biɗarsa.” (Ibraniyawa 11:6) Idan muka yi shakkar cewa Jehobah zai cika alkawuransa, ‘morar wannan duniya’ za ta kasance ita ta fi. (1 Korantiyawa 7:31) A wani ɓangare kuma, idan bangaskiyarmu tana da ƙarfi, za mu ƙuduri aniyar fara biɗan Mulki. Ta yaya za ka gina bangaskiya mai ƙarfi? Ta wajen kusantar Jehobah cikin addu’a da kuma nazari na kai. (Zabura 1:1-3; Filibiyawa 4:6, 7; Yaƙub 4:8) Kamar Sarki Dauda, za mu iya addu’a: “Amma na dogara gareka, ya Ubangiji: Na ce, Kai ne Allahna. Ina misalin girman alherinka!”—Zabura 31:14, 19.
18, 19. (a) Ta yaya ƙwazo yake ƙarfafa dogararmu ga Jehobah? (b) Me ya sa ya kamata Kirista ya kasance mai son sadaukarwa ne da son rai?
18 Himma a hidimar Jehobah: Bulus ya haɗa dogara ga alkawuran Jehobah da ƙwazo sa’ad da ya rubuta: “Muna kuwa so kowane ɗayanku shi nuna wannan ƙwazo zuwa ga tabbatawar bege har ƙarshe.” (Ibraniyawa 6:11) Idan muka kasance da himma a hidimarsa, Jehobah zai tallafa mana. Duk lokacin da muka ga tabbacin wannan taimakon, dogaranmu a gare shi sai ya ƙarfafa, sai mu ‘mu kafu yadda ba mu kawuwa.’ (1 Korantiyawa 15:58) Bangaskiyarmu sai ta sabonta, begenmu kuma ya tabbata.—Afisawa 3:16-19.
19 Sadaukar da kai da son rai: Bulus ya sadaukar da aiki mai ba da arziki domin ya bi Yesu. A bayyane yake cewa abin da ya zaɓa daidai ne, ko da yake wani lokaci rayuwarsa tana da wuya idan aka dube ta ta fuskar abin duniya. (1 Korantiyawa 4:11-13) Jehobah bai yi alkawarin rayuwar sukuni ba, kuma a wasu lokatai bayinsa suna jimre wahala. Sauƙaƙa rayuwarmu da son ranmu yana tabbatar da ƙarfin ƙudurinmu mu bauta wa Jehobah.—1 Timothawus 6:6-8.
20. Me ya sa haƙuri yake da muhimmanci ga wanda ya saka Mulki farko?
20 Haƙuri: Almajiri Yaƙub ya aririci ’yan’uwansa Kiristoci: “Ku yi haƙuri fa, ’yan’uwa, har zuwan Ubangiji.” (Yaƙub 5:7) A wannan duniya mai wuya, yin haƙuri zai yi wuya. Muna bukatar abubuwa su faru da wuri. Amma Bulus ya aririce mu mu yi koyi da waɗanda ‘suka gāda alkawarai ta wurin bangaskiya da haƙuri.’ (Ibraniyawa 6:12) Ka saurari Jehobah da son rai. Rai madawwami a aljanna a duniya, ta isa a saurare ta!
21. (a) Menene muke nunawa idan muka saka Mulkin farko? (b) Menene za a tattauna a talifi na gaba?
21 Hakika, gargaɗin Yesu mu saka Mulki farko daidai ne. Idan muka yi haka, muna tabbatar da cewa da gaske mun dogara ga Jehobah, kuma mun zaɓi hanya marar haɗari da Kirista ya kamata ya bi. Amma kuma, Yesu ya yi mana gargaɗi mu “fara biɗan . . . adalcinsa [Allah].” A talifi na gaba, za mu ga abin da ya sa wannan gargaɗi yake da muhimmanci musamman a yau.
Za Ka Iya Ba da Bayani?
• Game da abin duniya wane daidaito ne Yesu ya ƙarfafa mu mu yi?
• Menene muka koya daga kwatancin Yesu na raƙumi da kafar allura?
• Waɗanne halaye ne na Kirista suke taimakonmu mu saka Mulkin Allah farko?
[Hoto a shafi na 23]
Mutane da yawa da suka saurari Yesu matalauta ne
[Hoto a shafi na 25]
Saurayi mai arziki ya ƙaunaci dukiyarsa fiye da yadda ya ƙaunaci Allah
[Hoto a shafi na 25]
Attajirin almarar Yesu ya sadaukar da dukan abin da ya mallaka domin lu’ulu’u mai daraja
[Hoto a shafi na 26]
Idan muna fama a hidimarsa, Jehobah zai taimake mu