Ka Ci Gaba Da Yin Nagarta
“Ku yi . . . nagarta.”—LUKA 6:35.
1, 2. Me ya sa yin nagarta ga wasu sau da yawa yake zama ƙalubale?
YIN nagarta ga wasu ya kan iya zama ƙalubale. Waɗanda muka nuna wa ƙauna suna iya ƙin nuna mana ƙauna. Ko da yake muna iya ƙoƙarinmu mu taimaka wa mutane a ruhaniya ta wajen gaya musu “bishara ta darajar Allah mai-albarka” da kuma Ɗansa, suna iya ƙin saurarawa ko kuma su nuna rashin godiya. (1 Tim. 1:11) Wasu sun zama “maƙiyan [gungumen azaba na] Kristi.” (Filib. 3:18) A matsayinmu na Kiristoci, ta yaya ya kamata mu bi da su?
2 Yesu Kristi ya gaya wa almajiransa: “Ku yi ƙaunar magabtanku, ku yi masu nagarta.” (Luk 6:35) Bari mu bincika wannan umurnin sosai. Za mu amfana daga wasu darussa da Yesu ya koyar game da yin nagarta ga wasu.
“Ku Yi Ƙaunar Magabtanku”
3. (a) Da naka kalmomin, ka taƙaita furcin Yesu da ke rubuce a Matta 5:43-45. (b) Wane ra’ayi ne Shugabannin addinan Yahudawa na ƙarni na farko suke da shi game da Yahudawa da waɗanda ba Yahudawa ba?
3 A sananne Huɗubarsa a kan Dutse, Yesu ya gaya wa masu sauraronsa su ƙaunaci magabtansu kuma su yi wa waɗanda suke tsananta musu addu’a. (Ka karanta Matta 5:43-45.) Yahudawa ne suke wajen a wannan lokacin, kuma sun san dokar Allah da ta ce: “Ba za ka ɗauka ma kanka fansa, ba kuwa za ka yi nukuran ’ya’yan jama’arka; amma sai ka yi ƙaunar maƙwabcinka kamar ranka.” (Lev. 19:18) Shugabannin addinan Yahudawa na ƙarni na farko sun gaskata cewa “’ya’yan jama’arka” da “maƙwabcinka” yana nufin Yahudawa ne kawai. Dokar Musa ta ce Isra’ilawa su ware kansu daga sauran al’ummai, amma sun gaskata cewa dukan waɗanda ba Yahudawa ba ne maƙiya ne da za su tsana.
4. Ta yaya almajiran Yesu za su aikata ga maƙiyansu?
4 Akasin haka, Yesu ya ce: “Ku yi ƙaunar magabtanku, kuma waɗanda su kan tsananta muku, ku yi musu addu’a.” (Mat. 5:44) Almajiransa suna bukatar su nuna ƙauna ga dukan waɗanda suke nuna musu ƙiyayya. In ji Luka marubucin Linjila, Yesu ya ce: “Ku masu-ji, ina ce maku, Ku yi ƙaunar magabtanku, ku yi ma maƙiyanku nagarta, ku albarkaci masu-zaginku; waɗanda su ke wulakanta.” (Luka 6:27, 28) Kamar mutanen ƙarni na farko waɗanda suka yi amfani da abin da Yesu ya koyar, muna yi wa “maƙiyanku nagarta” ta wajen rama ƙiyayyarsu da ayyukan alheri. Muna yi wa ‘masu-zaginmu’ albarka ta wajen yi musu magana da kalamai masu daɗin ji. Kuma muna yin addu’a ga “waɗanda su kan tsananta” mana ta wajen yi mana mugunta ko kuma wasu ayyukan ‘wulakanci.’ Irin waɗannan roƙe-roƙen suna nuna cewa muna son masu tsananta mana su canja zuciyarsu kuma su yi abubuwa da za su sa su sami amincewar Jehobah.
5, 6. Me ya sa za mu ƙaunaci maƙiyanmu?
5 Me ya sa za mu nuna wa maƙiyanmu ƙauna? “Domin ku zama ’ya’yan Ubanku wanda ke cikin sama,” in ji Yesu. (Mat. 5:45) Idan muka yi biyayya ga wannan umurnin, za mu zama “’ya’yan” Allah da yake muna koyi da Jehobah wanda “ya kan sa ranatasa ta fito ma miyagu da nagargaru, ya kan aiko da ruwa bisa masu-adalci da marasa-adalci.” Kamar yadda labarin Luka ya faɗa, Allah “mai-alheri ne ga marasa-godiya da miyagu.”—Luka 6:35.
6 Da yake nanata yadda yake da muhimmanci almajiransa su ci gaba da ‘ƙaunar magabtansu,’ Yesu ya ce: “Idan kuna ƙaunar waɗanda ke ƙaunarku, wace lada ke gareku? ko masu-karɓan haraji ba haka su ke yi ba? Idan kuwa kuna gaida ’yan’uwanku kaɗai, ina kun fi waɗansu? ko Al’ummai ba haka su ke yi ba?” (Mat. 5:46, 47) Idan muna ƙaunar waɗanda suke ƙaunarmu ne kawai, hakan ba zai sa mu sami “lada” ko kuma tagomashin Allah ba. Masu karɓan haraji ma da mutane suke renawa suna ƙaunar waɗanda suke ƙaunarsu.—Luka 5:30; 7:34.
7. Me ya sa ba zai zama wani abin al’ajabi ba idan ‘’yan’uwanmu’ kaɗai ne muke gai da wa?
7 Gaisuwar Yahudawa ta haɗa da kalmar nan “salama.” (Alƙa. 19:20; Yoh. 20:19) Wannan na nufin cewa ana yi wa wanda aka gai da fatar alheri, samun lafiya da arziki. Ba za mu “fi waɗansu ba” idan muna gai da waɗanda muke ɗaukansu ‘’yan’uwanmu’ ne kawai. Kamar yadda Yesu ya ambata, mutanen “Al’ummai” ma suna yin hakan.
8. Menene Yesu yake ƙarfafawa masu sauraransa su yi sa’ad da ya ce: “Ku zama cikakku”?
8 Zunubin da almajiran Kristi suka gāda ne ya sa suka zama ajizai. (Rom. 5:12) Duk da haka, Yesu ya kammala wannan sashen jawabinsa da cewa: “Za ku zama cikakku, kamar yadda Ubanku na sama cikakke ne.” (Mat. 5:48) Ta hakan, yana ƙarfafa masu sauraronsa ne su yi koyi da Jehobah ‘Ubansu na sama,’ ta wajen sa ƙaunarsu ta zama cikakkiya, wato, ta wajen nuna ƙauna ga maƙiyansu. Mu ma muna bukatar mu yi hakan.
Me Ya Sa Za Mu Riƙa Gafartawa?
9. Menene ma’anar kalmomin nan: “Ka gafarta mana basussuwanmu”?
9 Muna yin nagarta sa’ad da muka gafarta wa wanda ya yi mana zunubi. Wani sashe na addu’ar misali na Yesu yana ɗauke da waɗannan kalmomin: “Ka gafarta mana basussuwanmu, kamar yadda mu kuma mun gafarta ma mabartanmu.” (Mat. 6:12) Hakika wannan ba ya nufin yafe bashin kuɗi. Linjilar Luka ta nuna cewa “basussuwa” da Yesu yake maganarsa a nan zunubai ne domin ta ce: “Ka gafarta mana zunubanmu; gama mu da kanmu kuma muna gafarta ma dukan wanda ya ke mabarcinmu.”—Luka 11:4.
10. Ta yaya za mu yi koyi da Allah a batun gafartawa?
10 Muna bukatar mu yi koyi da Allah, wanda yake gafarta wa masu zunubi da suka tuba. Manzo Bulus ya rubuta: “Ku kasance da nasiha zuwa ga junanku, masu-tabshin zuciya, kuna yi ma junanku gafara, kamar yadda Allah kuma cikin Kristi ya gafarta maku.” (Afis. 4:32) Mai zabura Dauda ya rera waƙa: “Ubangiji cike da tausayi ya ke, mai-nasiha, mai-jinkirin fushi, mai-yalwar jinƙai kuma. . . . Ba ya aika mamu gwalgwadon zunubanmu ba, Ba ya sāka mamu gwalgwadon laifofinmu ba. . . . Kamar nisan gabas da yamma, hakanan ya kawar da saɓe saɓenmu, ya nisantadda su. Kamar yadda uba ya kan yi juyayin ’ya’yansa, hakanan Ubangiji yana juyayin masu-tsoronsa. Gama ya san tabi’ammu; Ya kan tuna mu turɓaya ne.”—Zab. 103:8-14.
11. Waɗanne mutane ne Allah yake gafarta ma wa?
11 Allah zai gafarta wa mutane ne kawai idan sun riga sun gafarta wa waɗanda suka yi musu laifi. (Mar. 11:25) Da yake nanata wannan darasin, Yesu ya daɗa: “Gama idan kuna gafarta ma mutane laifofinsu, Ubanku na sama kuma za ya gafarta muku. Amma idan ba ku gafarta ma mutane laifofinsu, Ubanku kuma ba za shi gafarta naku laifofi ba.” (Mat. 6:14, 15) Hakika, Allah yana gafarta wa waɗanda suke gafarta wa mutane ne kawai. Hanya ɗaya da za ta taimaka mana mu ci gaba da yin nagarta ita ce ta bin shawarar Bulus: “Kamar yadda Ubangiji ya gafarta muku, hakanan kuma sai ku yi.”—Kol. 3:13.
Ku Daina ‘Zartar’
12. Wane gargaɗi ne Yesu ya ba da game da ganin laifin mutane?
12 An ambata wata hanyar da za a yi nagarta a cikin Huɗuba a kan Dutse sa’ad da Yesu ya gaya wa masu sauraronsa su daina zartar wa mutane kuma ya yi amfani da kwatanci mai kyau don ya nanata wannan darassin. (Ka karanta Matta 7:1-5.) Bari mu bincika abin da Yesu yake nufi sa’ad da ya ce: “Ku [daina] zartar.”
13. Ta yaya ne waɗanda suka saurari Yesu za su ci gaba da ‘kwancewa’?
13 Linjilar Matta ta yi ƙaulin Yesu yana cewa: “Ku [daina] zartar, domin kada a zartar muku.” (Mat. 7:1) In ji Luka, Yesu ya ce: “Kada ku zartas, ku kuma ba za a zartas maku ba: kada ku kayas, ku kuwa ba za a kāshe ku ba: ku kwance, za a kwance ku kuma.” (Luka 6:37) Farisawa na ƙarni na farko sun yi mugun shar’anta mutane, domin bin al’adu da ba sa bisa Nassi. Duk wani cikin masu sauraron Yesu da yake yin hakan ya kamata ya daina ‘zartarwa.’ Maimakon haka, za su ci gaba da ‘kwancewa,’ wato, za su ci gaba da gafarta wa mutane laifofinsu. Shi ma manzo Bulus ya ba da irin wannan gargaɗin game da gafartawa, kamar yadda aka ambata a baya.
14. Ta wajen gafartawa, menene almajiran Yesu za su motsa mutane su yi?
14 Ta wajen gafarta wa mutane, almajiran Yesu za su motsa mutane su riƙa gafartawa. Yesu ya ce: “Irin shari’a da ku ke shar’antawa, da shi za a shar’anta muku: da mudun nan da ku ke aunawa kuma da shi za a auna muku.” (Mat. 7:2) Za mu girbe abin da muka shuka dangane da yadda muka bi da mutane.—Gal. 6:7.
15. Ta yaya Yesu ya nuna cewa ba shi da kyau ana yawan sūka?
15 Domin ya nuna yadda ba shi da kyau a riƙa yawan sūkan mutane, Yesu ya yi tambaya: “Don me kuwa ka ke duban ɗan hakin da ke cikin idon ɗan’uwanka, amma ba ka kula da gungumen da ke cikin ido naka ba? Ko kuwa ƙaƙa za ka ce ma ɗan’uwanka, Bari in cire ɗan hakin daga cikin idonka; ga shi kuwa, gungume yana cikin ido naka?” (Mat. 7:3, 4) Mutumin da yake yawan sūkan wani yana lura da ɗan hakin da ke “idon” ɗan’uwansa. Mai sūkan yana cewa ɗan’uwansa ba ya ganin abubuwa sosai. Ko da yake laifin kaɗan ne kamar ɗan haki, mai sūkan yana son ya “cire ɗan hakin.” A munafunce ya ba da kansa don ya taimaki ɗan’uwan ya ga abubuwa sosai.
16. Me ya sa za a iya cewa Farisawa suna da “gungume” a idonsu?
16 Shugabannin addinan Yahudawa sun fi sūkan mutane. Alal misali: Sa’ad da wani makaho da Kristi ya warkar ya sanar cewa Yesu ya fito ne daga wurin Allah, Farisawa suka amsa cikin fushi: “Aka haife ka a cikin zunubai sarai, kana fa koya mamu?” (Yoh. 9:30-34) A batun fahimi na ruhaniya da iya zartar da mutane da kyau, Farisawa suna da “gungume” a idonsu kuma ba sa gani gabaki ɗaya. Saboda haka, Yesu ya ce: “Kai mai-riya, ka fara cire gungume daga cikin ido naka; kāna za ka gani sarai da za ka cire ɗan hakin daga cikin idon ɗan’uwanka.” (Mat. 7:5; Luka 6:42) Idan muka ƙudurta yin nagarta kuma muka bi da mutane yadda ya kamata, ba za mu zama masu sūka ba kuma ba za mu riƙa neman ɗan haki na alama a idon ɗan’uwanmu ba. Maimakon haka, za mu fahimci cewa mu ajizai ne saboda haka ya kamata mu guji zartar da kuma sūkan ’yan’uwanmu masu bi.
Yadda Ya Kamata Mu Bi da Mutane
17. Domin abin da ke cikin Matta 7:12, yaya ya kamata mu bi da mutane?
17 A cikin Huɗuba a Kan Dutse, Yesu ya nuna cewa Allah yana yi kamar uba ga bayinsa ta wajen amsa addu’o’insu. (Ka karanta Matta 7:7-12.) Abu ne mai muhimmanci cewa Yesu ya kafa wannan ƙa’idar hali: “Dukan abu fa iyakar abin da ku ke so mutane su yi maku, ku yi musu hakanan kuma.” (Mat. 7:12) Idan muka bi da mutane a wannan hanya ce kawai za mu nuna cewa mu mabiyan Yesu Kristi ne na gaske.
18. Ta yaya “Attaurat” ta nuna cewa ya kamata mu bi da mutane yadda muke son su bi da mu?
18 Bayan ya faɗi cewa ya kamata mu bi da mutane yadda muke son su bi da mu, Yesu ya daɗa: “Gama Attaurat ke nan da Annabawa.” Sa’ad da muka bi da mutane yadda Yesu ya faɗa, muna yin abin da “Attaurat” ya ce, wato, abubuwan da ke cikin littattafan Farawa zuwa Kubawar Shari’a na Littafi Mai Tsarki. Ban da bayyana nufin Jehobah na haifan zuriyar da za ta kawar da mugunta, waɗannan littattafan suna ɗauke da Dokar da Allah ya ba al’ummar Isra’ila ta bakin Musa a shekara ta 1513 K.Z. (Far. 3:15) Ban da wannan, Dokar ta nuna sarai cewa ya kamata Isra’ilawa su kasance masu adalci, ba za su nuna son kai ba, kuma za su yi wa talakawa da baƙin da ke zaune a ƙasar nagarta.—Lev. 19:9, 10, 15, 34.
19. Ta yaya “Annabawa” suka nuna cewa ya kamata mu yi nagarta?
19 Ta wajen ambata “Annabawa,” Yesu yana maganar littattafan annabawa na Nassosin Ibraniyawa ne. Sun ƙunshi annabce-annabcen Almasihu da suka cika don Kristi. Irin waɗannan rubuce-rubucen sun nuna cewa Allah yana yi wa mutanensa albarka sa’ad da suka yi abin da yake da kyau a gabansa kuma suka bi da mutane yadda ya kamata. Alal misali, annabcin Ishaya ya yi wa Isra’ilawa wannan gargaɗin: “Haka Ubangiji ya faɗi, Ku kiyaye shari’a, ku yi adilci, . . . Mai-albarka ne mutum wanda ya ke aika wannan, ɗan mutum kuma wanda ya lizimce shi, . . . yana kuwa tsare hannunsa ga barin yin mugunta.” (Isha. 56:1, 2) Hakika, Allah yana bukatar mutanensa su ci gaba da yin nagarta.
Ka Riƙa Yi wa Mutane Nagarta a Koyaushe
20, 21. Ta yaya mutane suka aikata ga Huɗubar Yesu a kan Dutse, kuma me ya sa ya kamata ka yi bimbini a kai?
20 Mun tattauna kaɗan kawai cikin darussa masu muhimmanci da Yesu ya yi a Huɗubarsa a kan Dutse da babu kamarsa. Duk da haka, muna iya fahimtar yadda waɗanda suka ji abin da ya faɗa a wannan lokacin suka aikata. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Sa’anda Yesu ya gama waɗannan zantattuka, taron mutane suka yi mamaki da koyarwansa: gama ya koya masu kamar mai-hukunci, ba kamar marubutansu ba.”—Mat. 7:28, 29.
21 Babu shakka Yesu Kristi ne ya zama “Al’ajabi, Mai-shawara” da aka annabta. (Isha. 9:6) Huɗuba a kan Dutse misali ne na musamman da ya nuna cewa Yesu ya san ra’ayin Ubansa na samaniya game da abubuwa. Ƙari ga batutuwan da muka tattauna, wannan jawabin ya faɗi abubuwa da yawa game da farin ciki na gaske, yadda za a guji lalata, yadda za a yi adalci, abin da dole ne mu yi don mu more kwanciyar rai da farin ciki a nan gaba, da sauransu. Me ya sa ba za ka sake karanta Matta sura 5 zuwa 7 ba sosai tare da addu’a? Ka yi bimbini a kan gargaɗin Yesu mai ban al’ajabi da aka rubuta a ciki. Ka yi amfani da abin da Kristi ya faɗa a cikin Huɗubarsa a kan Dutse a rayuwarka. Ta hakan, za ka faranta wa Jehobah rai sosai, za ka bi da mutane yadda ya kamata, kuma za ka ci gaba da yin nagarta.
Yaya Za Ka Amsa?
• Ta yaya za mu bi da maƙiyanmu?
• Me ya sa ya kamata mu riƙa gafartawa?
• Menene Yesu ya ce game da zartar da mutane?
• In ji Matta 7:12, yaya ya kamata mu bi da mutane?
[Bayanin da ke shafi na 10]
Ka san abin da ya sa Yesu ya ce: “Ku [daina] zartar”?
[Hoto a shafi na 8]
Me ya sa ya kamata mu yi wa waɗanda suke tsananta mana addu’a?
[Hoto a shafi na 10]
Kana bi da mutane a koyaushe yadda za ka so su bi da kai?