Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w02 9/1 pp. 15-20
  • “Babu Mutumin Da Ya Taɓa Yin Magana Haka”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Babu Mutumin Da Ya Taɓa Yin Magana Haka”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Tana da Sauƙi Kuma Tana Fita Sarai
  • Yin Amfani da Tambayoyi
  • Zuguguntawa don Koyar da Darasi
  • Magana da Makamar Hujja
  • Yesu Ya Bayyana ‘Hikima Daga Allah’
    Ka Kusaci Jehobah
  • “Na Yi Muku Kwatanci”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • “Lokaci Ya Yi”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Ka Yi Koyi Da Babban Malami
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
w02 9/1 pp. 15-20

“Babu Mutumin Da Ya Taɓa Yin Magana Haka”

“Dukansu suka shaida shi, suna mamaki da zantattukan alheri da suka fito bakinsa.”—LUKA 4:22.

1, 2. (a) Me ya sa dogarai da aka aike su su kama Yesu suka koma hannu goma? (b) Menene ya nuna cewa ba dogaran ne kawai koyarwar Yesu ta burge su ba?

DOGARAI sun kasa cika aikinsu. An aike su su kama Yesu Kristi, amma suka koma hannu goma. Firistoci da Farisawa suka tambaye su dalilin haka: “Don me ba ku kawo shi ba?” To, me ya sa dogaran ba su kama mutumin da ba zai yi kome ba don ya kāre kansa? Dogaran suka ce: “Babu mutumin da ya taɓa yin magana haka.” Koyarwar Yesu ta burge su ƙwarai har ba su iya ɗaga hannu su kama wannan mutumi mai salama ba.a—Yohanna 7:32, 45, 46.

2 Ba dogaran ne kawai koyarwar Yesu ta burge su ba. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa mutane masu yawa sun fito su ji maganarsa. Mutanen garinsu suka yi mamaki “da zantattukan alheri da suka fito bakinsa.” (Luka 4:22) Ya yi magana yana cikin kwalekwale ga taro mai girma da suka taru a bakin Tekun Galili fiye da sau ɗaya. (Markus 3:9; 4:1; Luka 5:1-3) A wani lokaci kuma, “taro mai-yawa” ya kasance tare da shi na kwanaki, ba tare da ci ba.—Markus 8:1, 2.

3. Wane dalili ne na musamman ya sa Yesu ya zama malami na musamman?

3 Me ya sa Yesu malami ne na musamman? Ƙauna ce muhimmiyar dalilin haka. Yesu ya ƙaunaci gaskiyar da ya koyar, kuma ya ƙaunaci mutanen da ya koyar da su. Amma kuma Yesu yana da fahimi ƙwarai game da hanyoyin koyarwa. A cikin talifofi na gaba za mu tattauna wasu hanyoyi masu muhimmanci da ya yi amfani da su da kuma yadda za mu koye su.

Tana da Sauƙi Kuma Tana Fita Sarai

4, 5. (a) Me ya sa Yesu ya yi amfani da kalmomi masu sauƙi a koyarwarsa, kuma menene ya kamata a lura game da yadda ya yi amfani da su? (b) Ta yaya ne Huɗuba Bisa Dutse ta kasance misali mai sauƙi na yadda Yesu ya koyar?

4 Ba sabon abu ba ne masu ilimi su yi amfani da kalmomin da masu sauraronsu ba su sani ba. Idan ba mu faɗi abin da wasu za su fahimta ba, ta yaya za su amfana daga iliminmu? Ko da yake malami ne, Yesu bai taɓa amfani da kalmomin da wasu ba su sani ba. Ka yi tunanin yawan kalmomin da ya sani. Amma duk da yawan iliminsa, ya yi tunanin masu sauraronsa, ba tunanin kansa ba. Ya sani cewa yawancinsu “marasa-karatu ne, talakawa.” (Ayukan Manzanni 4:13) Domin ya taɓa zuciyarsu, ya yi amfani da kalmomi da waɗannan mutane za su iya fahimta. Mai yiwuwa ne kalmomin masu sauƙi ne, amma gaskiyar da suka koyar mai girma ce.

5 Alal misali, Huɗuba Bisa Dutse, da ke rubuce a Matta 5:3–7:27. Wataƙila Yesu ya yi amfani da minti 20 ne kawai wajen gabatar da ita. Amma koyarwar tana da zurfi, ta yi magana a kan batutuwa na musamman kamar su zina, kisan aure, da kuma son abin duniya. (Matta 5:27-32; 6:19-34) Babu manyan kalmomi ko kuma na fahariya da ba a fahimta ba. Kai, babu wata kalma ma da yaro ba zai fahimta ba! Shi ya sa, yayin da ya gama, taron—da ƙila sun haɗa da manoma da yawa, makiyaya, da kuma masunta—“suka yi mamaki da koyarwansa”!—Matta 7:28.

6. Ka ba da misalin yadda Yesu ya faɗi maganganu da suke da sauƙi amma suna cike da ma’ana.

6 Sau da yawa, Yesu yana amfani da gajerun maganganu, da suke fita sarai, don ya idar da saƙo cikin sauƙi wanda ke cike da ma’ana. A cikin tsararraki kafin a soma buga littattafai, ya sahinta saƙonsa a azantai da kuma zukatan masu sauraronsa yadda ba za su manta ba. Ga wasu misalai: “Ba wanda ke da iko shi bauta ma ubangiji biyu: . . . ba ku da iko ku bauta ma Allah da [Arziki] ba.” “Kada ku zartar, domin kada a zartar muku.” “Bisa ga ’ya’yansu fa za ku sansance su.” “Lafiyayyu ba su da bukatar mai-magani, sai masu-ciwo.” “Dukan waɗanda suka ɗauki takobi, da takobi za su lalace.” “Ku ba Kaisar abin da ke na Kaisar, Allah kuma abin da ke na Allah.” “Bayarwa ta fi karɓa albarka.”b (Matta 6:24; 7:1, 20; 9:12; 26:52; Markus 12:17; Ayukan Manzanni 20:35) Har wa yau, kusan shekara 2,000 bayan Yesu ya faɗe su, ana tuna waɗannan maganganu masu muhimmanci.

Yin Amfani da Tambayoyi

7. Me ya sa Yesu yake tambayoyi?

7 Yesu ya yi tambayoyi. Sau da yawa ya yi hakan ko da zai ci masa lokacin koya wa masu sauraronsa darasi. To, me ya sa yake tambayoyi? A wasu lokatai, yakan yi amfani da tambayoyi na sa tunani ya fallasa burin masu hamayya da shi, da haka ya rufe musu baki. (Matta 12:24-30; 21:23-27; 22:41-46) Amma a yanayi da yawa, Yesu ya yi tambayoyi domin ya idar da gaskiya, ya sa masu sauraronsa su furta abin da ke zukatansu, kuma domin ya motsa ya koyar da tunanin almajiransa ne. Bari mu bincika misalai biyu, da sun shafi manzo Bitrus.

8, 9. Ta yaya Yesu ya yi amfani da tambayoyi ya taimaki Bitrus ya sami amsa da ta dace game da batun biyan harajin haikali?

8 Na farko, ka tuna da lokacin da masu karɓan haraji suka tambayi Bitrus ko Yesu ya biya harajin haikali.c Bitrus, da wani lokaci yana aikata abu bisa motsin rai, ya amsa, ‘E.’ Amma, bayan haka, Yesu ya sa shi ya yi tunani: “Ƙaƙa ka aza a ranka, Siman? daga wurin wa sarakunan duniya su ke karɓan garama ko gandu? daga wurin ’ya’yansu, ko kuwa daga wurin baƙi? Ya ce, Daga baƙi ne; kāna Yesu ya ce masa, ’Ya’ya fa sun kuɓuta.” (Matta 17:24-27) Lallai Bitrus ya fahimci darasin da tambayar Yesu ta koyar. Me ya sa?

9 A zamanin Yesu, ’ya’yan sarki ba sa biyan haraji. Saboda haka, da yake shi makaɗaicin Ɗan Sarki ne na samaniya da ake bauta wa a haikalin, ba za a bukaci Yesu ya biya haraji ba. Ka lura cewa maimakon ya bai wa Bitrus amsa kai tsaye, cikin gwaninta kuma a hankali Yesu ya yi amfani da tambayoyi ya taimaki Bitrus ya fahimci amsar da ta dace—ko kuma ƙila domin ya taimake shi ya ga ya dace ya yi tunani kafin ya yi magana.

10, 11. Me Yesu ya yi sa’ad da Bitrus ya yanke kunnen wani mutum a daren Faska ta shekara ta 33 A.Z., kuma yaya wannan ya nuna cewa Yesu ya san darajar amfani da tambayoyi?

10 Misali na biyu game da abin da ya faru ne a daren Faska ta shekara ta 33 A.Z., sa’ad da taron ’yan iska suka zo su kama Yesu. Almajiran suka tambayi Yesu ko su yi faɗā don su kāre shi. (Luka 22:49) Bai ma jira ya ba da amsa ba, Bitrus ya yanke kunnen wani mutum da takobi (kamar dai Bitrus yana da nufin ya ji wa mutumin rauni ne sosai). Bitrus ya yi abin da ubangijinsa ba ya so, domin Yesu a shirye yake ya ba da kansa. Me Yesu ya yi? Da yake uban haƙuri ne, ya yi wa Bitrus tambayoyi uku: “Ƙoƙo wanda Uba ya ba ni, ba zan sha ba?” “Kuna tsammani ba ni da iko in roƙi Ubana, ko yanzu ma shi aiko mini rundunan mala’iku ya fi goma sha biyu? Ƙaƙa fa littattafai za su cika da sun ce dole ya zama haka?”—Yohanna 18:11; Matta 26:52-54.

11 Ka ɗan yi tunani a kan wannan labarin. Yesu, da taron ’yan iska suka kewaye shi, ya sani mutuwarsa ta zo dab da dab, kuma ya sani cewa tsarkake sunan Ubansa da ceton dukan iyalin ’yan Adam na hannunsa. Duk da haka, ya ba da lokaci a take a wurin ya sahinta a zuciyar Bitrus muhimman gaskiya ta yin amfani da tambayoyi. Ba a bayyane yake ba cewa Yesu ya san darajar yin amfani da tambayoyi?

Zuguguntawa don Koyar da Darasi

12, 13. (a) Menene zuguguntawa? (b) Ta yaya Yesu ya yi amfani da zuguguntawa a nuna wautar yi wa ’yan’uwanmu gyara a ƙananan laifuffuka?

12 A hidimarsa, sau da yawa Yesu ya yi amfani da wani fannin koyarwa mai muhimmanci—zuguguntawa. Wannan zuguguntawa da ganga ne don nanata wani abu. Ta wurin zuguguntawa, Yesu ya yi kwatanci da ya zama da wuya a manta. Bari mu bincika misalai kalilan.

13 A Huɗuba Bisa Dutse, sa’ad da yake nanata dalilin “kada ku zartar” da wasu, Yesu ya ce: “Don me kuwa ka ke duban ɗan hakin da ke cikin idon ɗan’uwanka, amma ba ka kula da gungumen da ke cikin ido naka ba?” (Matta 7:1-3) Za ka iya ƙaga yanayin? Wani da yake yawan sukan wasu yana neman ya cire ɗan haki da ke “idon” ɗan’uwansa. Mai sukan zai iya cewa ɗan’uwansa bai fahimci batun yadda ya dace don a yi shari’ar da ta dace ba. Amma kuma “gungume” ne ya ɓata iyawar mai sukan ya yi gyara—katako ko kuma itace da ake amfani da shi a toƙare jinka. Lallai hanya ce da ba za a manta ba ta nuna wautar yi wa ’yan’uwanmu gyara a ƙananan laifuffuka yayin nan kuwa mu muke da manyan laifuffuka!

14. Me ya sa kalmomin Yesu game da tace ƙwaro da kuma haɗiye raƙumi zugugunci ne mai kyau?

14 A wani lokaci kuma, Yesu ya zartar da Farisawa cewa su “majayan hanya, makafi, [su] kan tace [ƙwaro, su] haɗiye raƙumi.” (Matta 23:24) Wannan yin amfani ne da kyau da zuguguntawa. Me ya sa? Masu sauraron Yesu sun san bambancin da ke tsakanin ƙwaro da raƙumi, raƙumi yana cikin dabbobi masu girma, kwatanci ne mai burgewa. An kimanta cewa don ƙwari su kai matsakaicin raƙumi guda, sai sun kai miliyan 70! Ban da haka ma, Yesu ya san cewa Farisawa suna tace giya da mararaki. Waɗannan mutane masu manne wa doka suna yin haka ne domin kada su haɗiye ƙwaro, su ƙazantu. Amma a alamance suna haɗiye raƙumi, wanda shi ma marar tsarki ne. (Leviticus 11:4, 21-24) Darasin Yesu ya fita sarai. Farisawan suna manne wa mafi ƙanƙanta na farillan Dokar, amma suna ƙyale batutuwa masu girma—“shari’a, da jinƙai da bangaskiya.” (Matta 23:23) Dubi yadda Yesu ya fallasa abin da suke yi sarai!

15. Ina waɗansu darussa da Yesu ya koyar ta yin amfani da zuguguntawa?

15 Duk cikin hidimarsa, sau da yawa Yesu ya yi amfani da zuguguntawa. Ga wasu misalai. “Bangaskiya kwatancin [ƙaramar] ƙwayar mastad” da za ta iya kawar da dutse—lallai babu wata hanya da Yesu zai bayyana cewa ƙaramar bangaskiya tana aikata abu mai girma dalla-dalla fiye da haka. (Matta 17:20) Babban raƙumi da yake fama ya shiga kan allurar ɗinki—ya bayyana wahalar mai arziki da yake ƙoƙarin ya bauta wa Allah kuma ya bi salon rayuwa na son abin duniya! (Matta 19:24) Bai burge ka ba yadda Yesu yake ƙaga zance da kuma iyawarsa na yin amfani da kalmomi kalilan don cim ma ma’ana mai zurfi?

Magana da Makamar Hujja

16. A wace hanya ce Yesu kullum yake amfani da iyawarsa mai kyau?

16 Domin shi kamili ne, Yesu gwani ne wajen saka mutane su yi tunani ta wajen magana da hujja. Duk da haka, bai ɓata wannan iyawar ba. Kuma ko da yaushe cikin koyarwarsa, yana amfani da wannan iyawarsa don gabatar da gaskiya. A wasu lokatai, ya yi magana da hujja don ya tsayayya wa cajin ƙarya na ’yan addini masu hamayyarsa. A yanayi da yawa, yana amfani da tushen magana don ya koyar wa almajiransa muhimman darussa. Bari mu bincika iyawar Yesu na yin magana da hujja.

17, 18. Wace irin magana da makamar hujja Yesu ya yi amfani da ita ya rushe zargin ƙarya na Farisawan?

17 Ka yi la’akari da wani lokaci da Yesu ya warkar da wani mutum bebe kuma makaho mai aljanu. Da suka ji game da shi, Farisawa suka ce: “Wannan mutum ba ya fitarda aljanu ba, sai ta wurin Ba’alazabula [Shaiɗan] sarkin aljanu.” Ka lura da cewa Farisawa sun yarda sai da iko da ya fi na mutum ake iya fitar da aljanun Shaiɗan. Amma, don su sa mutane su ƙi gaskata Yesu, suka ce ikon na Shaiɗan ne. A nuna cewa ba su yi tunani ba a kammalawarsu, Yesu ya amsa: “Kowanne mulkin da ya rabu biyu gāba da kansa, ya risbe; kowanne birni kuma ko kuwa gida wanda ya rabu biyu gāba da kansa, ba shi tsayawa: idan kuwa Shaiɗan yana fitarda Shaiɗan, ya rabu biyu gāba da kansa ke nan; ƙaƙa mulkinsa fa za ya tsaya?” (Matta 12:22-26) Yesu cewa yake: ‘Idan kuwa kun ce ni ma’aikacin Shaiɗan ne, da nake hana abin da Shaiɗan yake yi, to, ai Shaiɗan yana yaƙi da kansa ke nan kuma ba da daɗewa ba zai faɗi.’ Lallai kuwa, magana ce da hujja, ko ba haka ba?

18 Sai kuma Yesu ya ci gaba da sa tunani cikin batun nan. Ya tuna cewa wasu cikin mabiyan Farisawan sun fitar da aljanu. Saboda haka, ya yi tambaya da ta sha kansu: “Idan ni kuma ta wurin Ba’alazabula ni ke fitarda aljanu, ta wurin wa ’ya’yanku su ke fitarda su?” (Matta 12:27) Ga abin da Yesu yake nufi: ‘Idan ni ina fitar da aljanu da ikon Shaiɗan, to ai almajiranku ma suna ƙarƙashin wannan ikon ne.’ Me Farisawan za su ce? Ba za su taɓa yarda da cewa almajiransu suna ƙarƙashin ikon Shaiɗan ba. Ta wurin magana da hujja, Yesu ya rushe zargin da suka yi masa.

19, 20. (a) A wace hanya ce mai kyau Yesu ya yi amfani da magana da hujja? (b) Ta yaya Yesu ya yi amfani da hanyar sa tunani na “balle fa” yayin da yake amsa wa almajiransa roƙonsu ya koya musu yadda ake addu’a?

19 Wajen yin amfani da magana da hujja ya rufe bakin masu hamayya da shi, Yesu kuma ya yi amfani da hujjar rinjaya don ya koyar da gaskiya da kyau, mai daɗaɗawa game da Jehovah. Sau da yawa ya yi amfani da hanyar sa tunani na abin da ake iya ce da shi “balle fa” don ya taimaki masu sauraronsa su samu ƙarin fahimtar gaskiya zuwa tabbacinta. Bari mu bincika misalai biyu.

20 Sa’anda yake amsa roƙon almajiransa ya koya musu yadda ake addu’a, Yesu ya ba da wata almara game da wani mutum da ‘ya yi naciya,’ a ƙarshe abokinsa ya rinjayu, ya ba shi abin da ya roƙa. Yesu ma ya kwatanta yardar rai na iyaye su ‘yi alherai’ ga ’ya’yansu. Sai kuma ya kammala da cewa: “Idan ku fa da ku ke miyagu, kun san yadda za ku ba ’ya’yanku alherai, balle fa Ubanku na sama za ya bada Ruhu Mai-tsarki ga waɗanda su ke roƙonsa?” (Tafiyar tsutsa tamu ce; Luka 11:1-13) Darasin Yesu a nan ba nuna kamani ba ne amma nuna akasin zance ne. Idan wani aboki da yake da wuya a gamsar da shi ya iya gamsar da bukatar maƙwabcinsa, kuma idan iyaye ajizai sun iya cika bukatar ’ya’yansu, balle kuma Ubanmu mai ƙauna na samaniya ya ba da ruhu mai tsarki ga bayinsa masu aminci da suke zuwa gare shi cikin addu’a ba!

21, 22. (a) Wace hanyar sa tunani ce Yesu ya yi amfani da ita da yake ba da gargaɗi a kan alhini game da abin duniya? (b) Bayan maimaita kalilan cikin hanyoyin koyarwa na Yesu, me muka kammala?

21 Yesu ya yi amfani da hanyar sa tunani ɗaya yayin da yake gargaɗi a kan alhini game da abin duniya. Ya ce: “Ku lura da hankaki, ba su kan shuka ba, ba su kan yi girbi ba; ba su da wurin ajiya, ba su da rumbu; Allah ke ciyadda su: darajarku ga tsuntsaye fa, ina misalin fikonta! Ku lura da fure fa, girman da su ke yi: ba su kan yi wahala, ba su kan yi kaɗi ba . . . Amma idan Allah ya kan yi ma ganyaye cikin saura sitira haka, abin da ke rayuwa yau, gobe ana jefawa cikin tanderu; balle ku, ku masu-ƙanƙantan bangaskiya?” (Tafiyar tsutsa tamu ce; Luka 12:24, 27, 28) Hakika, idan Jehovah yana kula da tsuntsaye da furanni, balle kuma a ce ba zai kula da bayinsa ba! Babu shakka irin wannan hanyar ta sa tunani, ta motsa zuciyar masu sauraron Yesu.

22 Bayan mun maimaita hanyoyin koyarwa na Yesu, yana da sauƙi mu kammala cewa waɗancan dogarai da suka kasa kama shi lallai ba zugugunci ba ne da suka ce: “Babu mutumin da ya taɓa yin magana haka.” Amma hanyar koyarwa da aka fi sanin Yesu ita ce yin amfani da misalai ko kuma almara. Me ya sa ya yi amfani da waɗannan? Kuma me ya sa misalansa suke da kaifi haka? Za a tattauna waɗannan tambayoyi cikin talifi na gaba.

[Hasiya]

a Lallai dogaran ma’aikatan Majalisa ne kuma suna ƙarƙashin ikon manyan firistocin.

b Ƙauli na ƙarshe da ke Ayukan Manzanni 20:35, manzo Bulus ne kaɗai ya ɗauko shi, ko da yake ma’anarsu tana cikin Linjila. Mai yiwuwa ne Bulus ya samo su ta maganar baka (ƙila daga wani almajiri ne da ya ji Yesu ya faɗe shi kafin ko kuma bayan an ta da shi daga matattu) ko kuma ta wurin wahayin Allah.—Ayukan Manzanni 22:6-15; 1 Korinthiyawa 15:6, 8.

c An bukaci Yahudawa su biya harajin haikali kowacce shekara na drachma biyu (kuɗin yini biyu). Ana amfani da kuɗin harajin don a yi gyaran haikalin da shi, hidimomi da ake yi a ciki, da kuma hadayu da ake yi kullum domin al’ummar gabaki ɗayanta.

Ka Tuna?

• Waɗanne misalai suka nuna cewa Yesu ya koyar da sauƙi kuma koyarwar ta fita sarai?

• Me ya sa Yesu ya yi amfani da tambayoyi a koyarwarsa?

• Menene zugugu, kuma ta yaya Yesu ya yi amfani da wannan hanyar koyarwa?

• Ta yaya Yesu ya yi amfani da magana da makama ya koyar da almajiransa gaskiya mai kyau kuma mai daɗaɗa rai game da Jehovah?

[Hoto a shafi na 16]

Yesu ya yi amfani da kalmomin da talakawa za su fahimta

[Hoto a shafi na 17]

Farisawa suna ‘tace ƙwaro amma suna haɗiye raƙumi’

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba