Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w02 1/1 pp. 9-14
  • “Ku Koya Daga Wurina”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Ku Koya Daga Wurina”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Yadda Yesu Ya Bi da Mutane
  • Bambanci Tsakanin Yesu da Farisawa
  • Yadda Ra’ayin Yesu Yake
  • Yaya Yesu Ya Warware Matsaloli?
  • Sakamakon Koyarwar Yesu
  • ‘Ku Yi Hankali da Yisti na Farisawa’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Yesu Ya Yi Warkarwa a Ranar Assabaci
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • “Ku Zo Gare Ni, . . . Zan Ba Ku Hutawa”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
  • Ka Yi Koyi da Yadda Jehobah Yake Nuna Adalci da Jin Kai
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
w02 1/1 pp. 9-14

“Ku Koya Daga Wurina”

“Ku ɗauka ma kanku karkiyata, ku koya daga wurina; gama ni mai-tawali’u ne, mai-ƙasƙantar zuciya: za ku sami hutawa ga rayukanku.”—MATTA 11:29.

1. Me ya sa koya daga Yesu zai zama da daɗi kuma ya kyautata rayuwa?

YESU KRISTI koyaushe yana tunani, yana koyarwa, da kuma aikata abin da ya dace. Lokacinsa a duniya gajere ne, amma ya ji daɗin aiki mai sakayya kuma mai gamsarwa, ya kasance da farin ciki kuma. Ya tara almajirai kuma ya koya musu yadda za su bauta wa Allah, su ƙaunaci ’yan Adam, kuma su yi nasara da duniya. (Yohanna 16:33) Ya cika zuciyarsu da bege, kuma “ya haskaka rai da dawwama ta wurin bishara.” (2 Timothawus 1:10) Idan kana cikin almajiransa, menene kake tunani yake nufi a zama almajiri? Ta bincika abin da Yesu ya faɗa game da almajirai, za mu iya koyon yadda za mu kyautata rayuwarmu. Wannan ya ƙunshi amincewa da ra’ayinsa da kuma amfani da wasu ƙa’idodi.—Matta 10:24, 25; Luka 14:26, 27; Yohanna 8:31, 32; 13:35; 15:8.

2, 3. (a) Menene almajiri na Yesu? (b) Me ya sa yake da muhimmanci mu tambayi kanmu, ‘Almajirin waye na zama?’

2 A cikin Nassosin Kirista na Helenanci, kalma da aka fassara “almajiri” tana nufin wanda ke sa zuciyarsa a wani abu, ko wanda yake koyo. Irin wannan kalma ta bayyana cikin aya inda jigonmu ya fito, Matta 11:29: “Ku ɗauka ma kanku karkiyata, ku koya daga wurina; gama ni mai-tawali’u ne, mai-ƙasƙantar zuciya: za ku sami hutawa ga rayukanku.” Hakika, almajiri mai koyo ne. Lingila ta yi amfani da kalmar “almajiri” ga mabiyan Yesu na kurkusa, waɗanda suka yi tafiya da shi yayin da yake wa’azi kuma waɗanda ya koyar da su. Ƙila wasu mutane sun amince da koyarwar Yesu kawai, har suna yin haka a ɓoye. (Luka 6:17; Yohanna 19:38) Marubutan Lingila sun yi maganar “almajiran Yohanna [Mai Baftisma] da almajiran Farisawa.” (Markus 2:18) Tun da Yesu ya gargaɗi mabiyansa su “yi hankali da . . . koyarwa ta Farisawa,” za mu iya tambayar kanmu, ‘Almajirin wa na zama?’—Matta 16:12.

3 Idan mu almajiran Yesu ne, idan mun koya daga wurinsa, ya kamata wasu su sami wartsakewa ta ruhaniya a wajenmu. Ya kamata su fahimci mun ƙara zama masu tawali’u da masu ƙasƙantar zuciya. Idan muna da hakkin shugabanci wajen aikinmu, mu iyaye ne, ko muna ayyukan makiyayi cikin ikilisiyar Kirista, waɗanda muke kula da su suna ji muna bi da su yadda Yesu ya bi da waɗanda yake kula da su?

Yadda Yesu Ya Bi da Mutane

4, 5. (a) Me ya sa bai yi wuya ba a san yadda Yesu ya bi da mutane da suke da matsaloli? (b) Menene Yesu ya fuskanta yayin da yake ci a gidan wani Bafarisi?

4 Muna bukatar mu san yadda Yesu ya bi da mutane, musamman waɗanda suke da matsala mai tsanani. Wannan bai kamata ya yi wuyar koyarwa ba; Littafi Mai Tsarki na ɗauke da rahotanni da yawa na yadda Yesu ya yi sha’ani da mutane, wasu cikinsu matalauta ne. Bari mu bincika hanyar da shugabannan addinai, Farisawa musamman, suka bi da mutane da suke da irin matsalar nan. Bambancin zai koyar da mu.

5 A shekara ta 31 A.Z., yayin da Yesu yake wa’azi a Galili, “wani fa daga cikin Farisawa ya biɗe [Yesu] ya ci tare da shi.” Yesu ba ya so ya ƙi gayyatar. “Ya kuwa shiga gidan Bafarisin, ya zauna wurin ci. Sai ga wata mace, mai-zunubi, wadda tana cikin birni; sa’anda ta san yana zaune wurin ci cikin gidan Bafarisin, ta kawo tandun alabastar na man ƙamshi, tana tsaye a baya wajen ƙafafunsa, tana kuka, ta soma jiƙa ƙafafunsa da hawayenta, ta shafe su da gashin kanta, ta dinga sumbar ƙafafunsa, ta goge su da man ƙamshi.”—Luka 7:36-38.

6. Ƙila me ya sa mace “mai-zunubi” ta je gidan Bafarisi?

6 Za ka iya zana wannan a hoton zuci? Wani aikin bincike ya ce: “Matar (aya ta 37) ta yi amfani da zarafin al’adu na mutane da ya yarda wa mutane da suke bukata su ziyarci wurin bikin nan don su sami abinci da ya rage.” Wannan ya bayyana yadda mutum zai iya shiga ba a gayyace shi ba. Ƙila akwai wasu da suke so su yi kala a ƙarshen cin abincin. Amma, wannan matar ta yi abin mamaki. Ba ta lura da mutane da suke jira a gama dina ba. Ba ta da suna mai kyau, da shi ke ita “mai-zunubi” ce da aka sani, Yesu ya ce ya san “zunubanta da suke dayawa.”—Luka 7:47.

7, 8. (a) Yaya ƙila za mu aikata a cikin irin wannan yanayi kamar wanda aka ba da labarinsa a Luka 7:36-38? (b) Me Siman ya yi?

7 Ka yi tunani kana da rai a lokacin kuma kana matsayin Yesu. Da yaya za ka ji? Za ka ji kunya ne yayin da wannan matar ta zo wurinka? Yaya irin wannan yanayin zai shafe ka? (Luka 7:45) Da za ka firgita?

8 Da kana tsakanin sauran baƙin, da za ka yi tunani aƙalla kamar Siman Bafarisi? “Lokacinda Bafarisi wanda ya kira [Yesu] ya ga wannan, ya yi magana a ransa, ya ce, Wannan mutum, da annabi ne, da ya gāne ko wacce ce macen nan da ta ke taɓa shi, da ko irinta, mai-zunubi ce.” (Luka 7:39) Akasin haka, Yesu mutumi ne mai juyayi sosai. Ya fahimci yanayin matar kuma ya san baƙin cikinta. Ba a gaya mana yadda ta faɗa cikin rayuwa ta zunubi ba. Idan da gaske karuwa ce, mazan garin, Yahudawa da suka ba da kansu cikin addini, lallai ba su taimake ta ba.

9. Yaya Yesu ya amsa, mai yiwuwa da wane sakamako?

9 Amma Yesu yana son ya taimake ta. Ya ce mata: “An gafarta miki zunubanki.” Sai ya daɗa: “Bangaskiyarki ta cece ƙi; ki tafi lafiya.” (Luka 7:48-50) A nan ne labarin ya ƙare. Wani zai iya cewa Yesu bai yi mata abu mai yawa ba. Musamman, ya yi mata albarka. Kana tunani cewa wataƙila ta koma hanyar rayuwarta ta baƙin ciki? Ko da ba mu tabbata ba, ka lura da abin da Luka ya faɗa a gaba. Ya ce Yesu ya yi ta yawo “a cikin birane da ƙauyuka, yana wa’azi, yana kawo bishara ta mulkin.” Luka ya ba da rahoto cewa “waɗansu mata” na tare da Yesu da almajiransa, da “suke yi musu hidima daga cikin dukiyar [matan].” Mai yiwuwa ne cewa wannan matar da ta tuba kuma mai godiya tana cikinsu, ta soma rayuwa da ke faranta wa Allah rai da lamiri mai tsabta, sabon fahimi game da ƙuduri, da ƙauna mai zurfi ga Allah.—Luka 8:1-3.

Bambanci Tsakanin Yesu da Farisawa

10. Me ya sa yake da amfani mu bincika labarin Yesu da mace a gidan Siman?

10 Menene za mu iya koya daga wannan labarin da ya fita sarai? Yana taɓa zuciyarmu, ko ba haka ba? Ka yi tunani kana gidan Siman. Yaya za ka ji? Za ka yi yadda Yesu ya yi, ko za ka ɗan ji kamar magayyacin Bafarisi? Yesu Ɗan Allah ne, saboda haka ba za mu ji kuma mu aikata abu daidai yadda ya yi ba. A wata sassa, ƙila ba za mu yi saurin tunanin kanmu kamar Siman, Bafarisi ba. Kalilan ne za su yi fahariyar zama Bafarisi.

11. Me ya sa ba za mu so a lissafta mu da Farisawa ba?

11 Daga nazarin Littafi Mai Tsarki da abin da mutane suka gani, za mu kammala cewa Farisawa suna ɗaukan kansu da girma su masu ja-gorar ci gaban mutane da lafiyar ƙasa. Ba su ji daɗi ba cewa Dokar Allah tana bayyane kuma na da sauƙin fahimta. Inda kamar Dokar ba ta faɗa ainihin abin da za a yi ba, sai su saka tasu kuma su ba ta ma’ana da za ta kawar da bukatar yin amfani da lamiri. Waɗannan shugabannin addinai sun yi ƙoƙari su kafa ƙa’ida da za ta ja-goranci dukan batu, har ma da ƙananan abubuwa.a

12. Yaya Farisawa suke ɗaukan kansu?

12 Ɗan tarihi Bayahude Josephus na ƙarni na farko ya nuna cewa Farisawa na ɗaukan kansu masu alheri, masu kissa, masu gaskiya, kuma sun cancanta su yi aiki da suke yi. Babu shakka, wasu cikinsu sun kusa da haka. Za ka iya tuna da Nikodimu. (Yohanna 3:1, 2; 7:50, 51) A kwana a tashi, wasu cikinsu sun bi hanyar Kiristoci. (Ayukan Manzanni 15:5) Kirista manzo Bulus ya rubuta game da wasu Yahudawa, kamar Farisawa: “Suna da himma domin Allah, amma ba bisa ga sani ba.” (Romawa 10:2) Amma Lingila sun nuna su yadda talakawa suke ganin su—masu fahariya, masu girman kai, masu adalcin kansu, masu neman laifi, masu zargi, da kuma reni.

Yadda Ra’ayin Yesu Yake

13. Menene Yesu ya faɗa game da Farisawa?

13 Yesu ya tsauta wa marubuta da Farisawa cewa su masu riyya ne. “Su kan ɗaura kaya masu-nauyi, masu-wuyan ɗaukawa kuma, su ɗibiya ma mutane a kafaɗu; amma su da kansu ba su yarda su ko motsa su da yatsansu ba.” Hakika, kayan yana da nauyi, kuma karkiya da aka ɗaura wa mutanen ba ta da sauƙi. Yesu ya kira marubuta da Farisawa “wawaye.” Wawa haɗari ne ga jama’a. Yesu ya kuma kira marubuta da Farisawa ‘makafi masu ja-gora’ kuma ya ce sun “ƙyale matsaloli mafiya girma na Attaurat, shari’a, da jinƙai da bangaskiya.” Wanene zai so Yesu ya kira shi Bafarisi?—Matta 23:1-4, 16, 17, 23.

14, 15. (a) Yadda Yesu ya bi da Matta Lawi ya nuna menene game da hanyoyin Farisawa? (b) Waɗanne muhimman darussa ne za mu iya koya daga wannan labarin?

14 Kusan kowanne mai karatun labarin Lingila zai iya ganin halin yawancin Farisawa. Bayan Yesu ya gayyaci Matta Lawi, mai karɓan haraji, ya zama almajiri, Lawi ya yi masa babban biki. Labarin ya ce: “Amma Farisawa da marubutansu suka yi ma almajiransa gunaguni, suka ce, Don menene ku ke ci da sha tare da masu-haraji da masu-zunubi?” Yesu ya amsa ya ce musu: “Ni ban zo domin in kira masu-adalci ba, amma masu zunubi zuwa tuba.”—Luka 5:27-32.

15 Lawi kansa ya fahimci wani abu da Yesu ya faɗa a wannan lokacin: “Ku tafi ku koya azancin wannan, Ni, jinƙai ni ke so, ba hadaya ba.” (Matta 9:13) Ko da Farisawa suna da’awar sun gaskata rubutun annabawa Ibraniyawa, ba su amince da wannan magana daga Hosea 6:6 ba. Idan za su karya doka, sukan tabbata cewa zai zama ta wajen biyayya da al’ada. Kowannenmu za mu iya tambayar kanmu, ‘An san ni da nace wa wasu dokoki ne, irin waɗanda suke nuna nawa ra’ayi ko kuma yadda nike ɗaukar wani al’amari? Ko kuma wasu suna ɗauka, ni mai jinƙai da kirki ne?’

16. Menene halin Farisawa, kuma yaya za mu guje zama kamar su?

16 Neman laifi a ƙananan abubuwa. Halin Farisawa ke nan. Farisawa suna neman kowanne kuskure—na gaske ko wanda tsammani kawai suke. Suna sa mutane a yanayin kuma tunasar musu kasawarsu. Farisawa suna ɗaukaka kansu wai suna biyan ushirin ganye kamar su ɗanɗoya, anise, da algaru. Suna nuna ibadarsu ta tufafinsu kuma suna yin ƙoƙari su ja-goranci al’ummar. Hakika, idan ayyukanmu ba su jitu da misalin Yesu ba, dole mu guje wa halin ganin laifin wasu da kuma girmama kasawarsu.

Yaya Yesu Ya Warware Matsaloli?

17-19. (a) Ka ba da bayani yadda Yesu ya bi da yanayi da da ya jawo matsala mai tsanani. (b) Me ya sa yanayin ke da wuya kuma ba mai daɗi ba? (c) Da kana wajen lokacin da matar ta doshi Yesu, yaya za ka yi?

17 Yadda Yesu yake warware matsaloli ya bambanta sosai da na Farisawa. Yi la’akari da yadda Yesu ya warware wata matsala da ƙila za ta kasance da tsanani. Wata mata ce da tana zuban jini na shekara 12. Za ka iya karanta labarin a Luka 8:42-48.

18 Labarin Markus ya ce matar “tana jin tsoro, tana rawan jiki.” (Markus 5:33) Me ya sa? Babu shakka domin ta sani cewa ta karya Dokar Allah. Bisa ga Leviticus 15:25-28, mace mai zuban jini ba ta da tsarki a yanayin da take ciki, muddin ya wuce lokaci har da ƙarin mako guda. Duk abin da ta taɓa da kowa da ta sadu da shi za su ƙazanta. Don ta samu Yesu, wannan matar ta shiga cikin jama’ar. Yayin da muke karanta labarin bayan shekaru 2,000, mu kan ji tausayinta a wahalarta.

19 Da kana wajen ranar nan, yaya za ka ji game da yanayin? Da me za ka ce? Yesu ya bi da wannan matar da kirki, da ƙauna, da kula, bai ma yi maganar wata matsala da ta haddasa ba.—Markus 5:34.

20. Idan Leviticus 15:25-27 farilla ce a yau, wane ƙalubale ne za mu fuskanta?

20 Za mu iya koyan wani abu daga wannan aukuwa? A ce kai dattijo ne a cikin ikilisiyar Kirista a yau. Kuma a ce Leviticus 15:25-27 farilla ce ta Kirista a yau kuma mace Kirista ta karya dokar, tana jin tsoro kuma ba taimako. Yaya za ka yi? Za ka ba ta kunya a gaban jama’a da gargaɗi na nuna muhimmancin haka ne? “Kai,” in ji ka, “ba zan taɓa haka ba! A bin misalin Yesu, zan yi iyakar ƙoƙarina na kasance da kirki, ƙauna, tunanin kirki, da kula.” Da kyau! Amma damuwar ita ce a yi ta, a yi koyi da misalin Yesu.

21. Menene Yesu ya koya wa mutane game da Dokar?

21 Ainihi, Yesu ya wartsake mutane, ya ɗaukaka su kuma ƙarfafa su. Inda Dokar Allah ta faɗi abu, ta tabbata abin da ta faɗa. Idan dokar ta faɗi abu galibi, mutane za su yi amfani da lamirinsu sosai kuma za su nuna ƙaunarsu ga Allah ta shawarwarinsu. Dokar tana da sauƙi a bi ta. (Markus 2:27, 28) Allah yana ƙaunar mutanensa, yana aiki koyaushe domin amfaninsu, da yardan rai yana jinƙai in sun yi kuskure. Haka Yesu yake.—Yohanna 14:9.

Sakamakon Koyarwar Yesu

22. Koyo daga Yesu ya taimaki almajiransa su kasance da wane hali?

22 Waɗanda suka saurari Yesu kuma suka zama almajiransa sun daraja gaskiyar sanarwarsa: “Karkiyata mai-sauƙi ce, kayana kuma mara-nauyi.” (Matta 11:30) Ba su nawaita ba, bai gajiyar da su ba ko yi musu lacca. Sun fi ’yanci, sun fi farin ciki, kuma sun tabbata da dangantakarsu da Allah da kuma juna. (Matta 7:1-5; Luka 9:49, 50) Daga wurinsa sun koya cewa zama shugaba mai ruhaniya ta ƙunshi wartsake wasu, yana nuna tawali’u na azanci da zuciya.—1 Korinthiyawa 16:17, 18; Filibbiyawa 2:3.

23. Kasance tare da Yesu ya koya wa almajiran wane muhimmin darasi kuma ya taimake su su kai wace kammalawa?

23 Bugu da ƙari, muhimmancin zama cikin Kristi da ɗaukan halin da ya nuna ya burge mutane da yawa sosai. Ya gaya wa almajiransa: “Kamar yadda Ubana ya ƙaunace ni, ni kuma na ƙaunace ku; ku zauna cikin ƙaunata. Idan kun kiyaye dokokina, za ku zauna cikin ƙaunata: kamar yadda na kiyaye dokokin Ubana, ina zaune kuwa cikin ƙaunatasa.” (Yohanna 15:9, 10) Idan za su yi nasara na masu hidima kuma bayin Allah, za su yi amfani sosai da abin da suka koya daga Yesu, a wa’azi da koyarwar a fili game da bisharar Allah mai ban al’ajabi da yadda suke bi da iyali da abokanansu. Yayin da ’yan’uwancin yake girma ya zama ikilisiyoyi, a kai a kai za su bukaci su tunasar wa kansu cewa hanyarsa ce daidai. Abin da ya koyar gaskiya ne, kuma rayuwa da suka gani ya yi da gaske rayuwa ce da za a biɗa.—Yohanna 14:6; Afisawa 4:20, 21.

24. Waɗanne abubuwa ne ya kamata mu tuna daga misalin Yesu?

24 Yayin da ka yi bimbini a kan wasu abubuwa da muka tattauna, ka ga hanyoyi da za ka yi gyara? Ka yarda cewa koyaushe Yesu yana tunani, koyar da kuma aikata abubuwa daidai? Sai ka ƙarfafa. Ya ƙarfafa mu da waɗannan kalmomi: “Idan kun san waɗannan abu, masu-albarka ne idan kun yi su.”—Yohanna 13:17.

[Hasiya]

a “Bambanci na musamman [tsakanin Yesu da Farisawa] a bayyane yake ta bincika hanyoyi biyu na yadda aka fahimci Allah da suka saɓa wa kansu. In ji Farisawa, Allah wanda yake yawan biɗa ne; ga Yesu, Allah mai alheri ne da juyayi. Hakika, Bafarisin bai yi musu ba cewa Allah nagari ne kuma mai ƙauna, amma a gare shi an nuna wannan cikin kyautar [Dokar] Torah da yin abin da ake bukata a ciki in ya yiwu. . . . Manne wa al’adar da ba a rubuta ba, da dokokinta wajen fassara dokar, Bafarisin ya ga cewa hanyar cika Torah ce. . . . Ɗaukaka umurnin ƙauna baki biyu da Yesu ya yi a (Mat. 22:34-40) zuwa fassarar da aka amince da ita kuma da yadda ya ƙi hani na al’adar da ba a rubuta ba . . . ya sa bai yarda da ƙa’idodin neman hujja na Farisawa ba.”—The New International Dictionary of New Testament Theology.

Yaya Za Ka Amsa?

• Menene yake nufi a gare ka ka zama almajirin Yesu?

• Yaya Yesu ya bi da mutane?

• Menene za mu iya koya daga hanyar da Yesu ya koyar?

• Ta yaya Farisawa da Yesu suka bambanta?

[Hoto a shafi na 12]

Halin Yesu game da mutane dabam yake da na Farisawa!

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba