Kuna Shirye Ku Yi Wasu Canje-canje?
1. Waɗanne gyare-gyare ne muke bukatar yi saboda canje-canje da ke aukuwa a duniya?
1 A 1 Korintiyawa 7:31, Littafi Mai Tsarki ya kamanta duniya da dandali, inda akwai ’yan wasa da ke yawan canjawa. Yadda yanayin duniya yake canjawa zai sa mu riƙa canja yadda muke yin wa’azi da lokatan da muke fita wa’azi da kuma gabatarwarmu. Shin kuna shirye don ku yi waɗannan canje-canje?
2. Me ya sa ya dace mu yi gyara don mu bi tsarin ƙungiyar Jehobah?
2 Yadda Kuke Wa’azi: An san ikilisiyar Kiristoci da yin gyare-gyare tun da daɗewa. Sa’ad da Yesu ya aiki almajiransa su yi wa’azi, ya gaya musu kada su ɗauki jakar saka abinci ko kuɗi. (Mat. 10:9, 10) Amma daga baya ya sake canja wannan umurnin domin ya hango cewa za a yi wa almajiransa adawa kuma almajiran za su yi aikin wa’azi a wasu yankuna. (Luk 22:36) A ƙarnin da ya shige, ƙungiyar Jehobah ta yi amfani da hanyoyi dabam-dabam wajen yin wa’azin bishara. Alal misali, ƙungiyar ta yi amfani da katuna, gidajen rediyo da kuma motoci masu ɗauke da lasafika, bisa ga abin da ake bukata a lokacin. A yau, bayan wa’azi gida-gida, an fi mai da hankali ga yin wa’azi a fili da kuma duk inda aka sami zarafin yin hakan domin ba a cika samun mutane a gida a yankuna da yawa. An kuma ƙarfafa mu mu riƙa yin wa’azi gida-gida da yamma idan ba ma cika samun mutane a gida da rana. Yayin da ƙungiyar Jehobah take canja tsarinta, shin kana bin ja-gorancinta?—Ezek. 1:20, 21.
3. Ta yaya daidaita gabatarwarmu zai sa mutane a yankinmu su so saƙon bishara?
3 Gabatarwarku: Mene ne mutane a yankinku suka fi damuwa a kai? Tattalin arziki? Iyali? Tsaro? Yaƙi? Zai dace mu san abubuwan da suke faruwa a yankinmu da kuma yanayin mutane don mu daidaita yadda muke gabatar da saƙon bishara. (1 Kor. 9:20-23) Maimakon mu ba da gajeriyar amsa sa’ad da mutane suka bayyana ra’ayinsu kuma mu ci gaba da gabatarwa da muka shirya, zai dace mu daidaita gabatarwar don ta dace da batun da suka fi damuwa da shi.
4. Me ya sa ya kamata mu yi gyara ba tare da ɓata lokaci ba?
4 Ba da daɗewa ba, wannan yanayin duniyar da ta kusan ƙarewa za ta shuɗe, kuma za a soma ƙunci mai girma. Littafi Mai Tsarki ya ce: “An gajertar da kwanaki.” (1 Kor. 7:29) Saboda haka, yana da muhimmanci mu yi gyara kuma mu yi hakan ba tare da ɓata lokaci ba domin mu iya cim ma burinmu da kyau!