Ka Yi Koyi Da Babban Malami Mai Almajirantarwa
“Ku yi lura fa yadda ku ke ji.”—LUKA 8:18.
1, 2. Me ya sa ya kamata ka mai da hankali ga yadda Yesu ya bi da mutane a lokacin hidimarsa?
YESU KRISTI yana cika aikinsa ne na Babban Malami da kuma Mai Almajirantarwa sa’ad da ya gaya wa mabiyansa: “Ku yi lura fa yadda ku ke ji.” (Luka 8:16-18) A matsayin ka na Kirista, wannan mizanin ya shafi hidimarka. Idan ka mai da hankali ga umurni na ruhaniya, za ka yi amfani da shi kuma za ka zama ƙwararren mai shelar Mulki. Babu shakka, ba za ka iya jin muryar Yesu ba a yau, amma za ka iya karanta abubuwan da ya ce da kuma waɗanda ya yi, kamar yadda aka bayyana a cikin Nassosi. Menene suka bayyana game da yadda Yesu ya bi da mutane a lokacin hidimarsa?
2 Yesu ƙwararren mai wa’azin bishara ne kuma fitaccen malamin Nassosi ne. (Luka 8:1; Yohanna 8:28) Aikin yin almajirantarwa ya ƙunshi yin wa’azi da kuma koyarwa, duk da haka, wasu Kiristoci waɗanda suka ƙware wajen yin wa’azi yana yi masu wuya su koyar da mutane sosai. Ko da yake yin wa’azi ya ƙunshi sanar da saƙo, koyar da mutane game da Jehobah da nufe-nufensa yana bukatar mai almajirantar da mutane ya kasance da dangantaka mai kyau da su. (Matta 28:19, 20) Za a iya yin hakan ta wajen yin koyi da Yesu Kristi, Babban Malami kuma Mai Almajirantarwa.—Yohanna 13:13.
3. Ta yaya ne yin koyi da Yesu zai iya shafan yadda kake yin almajirantarwa?
3 Idan ka yi koyi da yadda Yesu ya koyar da mutane, hakan na nufin cewa kana bin umurnin da manzo Bulus ya bayar: “Ku yi tafiya cikin hikima wajen waɗanda ke waje, kuna rifta zarafi. Bari zancenku kullum ya kasance tare da alheri, gyartace da gishiri, domin ku sani yadda za ku amsa tambayar kowa.” (Kolossiyawa 4:5, 6) Yin koyi da Yesu a aikin almajirantarwa yana bukatar ƙoƙari, amma hakan zai sa koyarwarka ta zama mai amfani domin hakan zai taimake ka ka san ‘yadda za ka amsa tambayar kowa’ bisa ga bukatun kowannensu.
Yesu Ya Ƙarfafa Mutane su Faɗi Ra’ayinsu
4. Me ya sa za a iya cewa Yesu yana saurarawa sosai?
4 Tun yana ƙaramin yaro, Yesu yake sauraron mutane kuma yake ƙarfafa su su faɗi ra’ayoyinsu. Alal misali, sa’ad da yake ɗan shekara 12, iyayensa sun gan shi a tsakiyar malamai a cikin haikali, “yana jinsu, yana kuwa yi masu tantambaya.” (Luka 2:46) Yesu bai je haikali don ya kunyatar da malaman da iliminsa ba. Ko da yake ya yi tambayoyi, ya je wurin ne don ya saurari abin da suke cewa. Wataƙila dalili ɗaya da ya sa ya sami tagomashin Allah da mutane shi ne domin yana saurarawa sosai.—Luka 2:52.
5, 6. Ta yaya ne muka san cewa Yesu ya saurari furcin waɗanda ya koyar?
5 Bayan baftismarsa da kuma sa’ad da ya zama Almasihu, Yesu ya ci gaba da sauraran mutane. Bai shagaltu sosai da abin da yake koyarwa ba har ya mance da masu sauraronsa. A yawancin lokaci yana dakatawa, ya tambaye su ra’ayinsu, kuma ya saurari amsarsu. (Matta 16:13-15) Alal misali, bayan mutuwar Li’azaru, ɗan’uwan Martha, Yesu ya gaya mata: “Dukan wanda yana da rai, yana kuwa bada gaskiya gareni, ba shi mutuwa ba har abada.” Sai ya tambaye ta: “Kin gaskanta wannan?” Babu shakka, Yesu ya saurara sa’ad da Martha ta ce: “I, Ubangiji; na rigaya na bada gaskiya kai ne Kristi, Ɗan Allah.” (Yohanna 11:26, 27) Yesu ya gamsu sa’ad da ya ji Martha ta furta bangaskiyarta!
6 Sa’ad da yawancin almajiran Yesu suka ƙyale shi, ya nemi ya ji ra’ayin manzanninsa. Sai ya tambaye su: “Ku kuma kuna so ku tafi? Siman Bitrus ya amsa masa, ya ce, Ubangiji, a wurin wa za mu tafi? kai ne da maganar rai na har abada. Mu kuwa mun rigaya mun bada gaskiya, kuma mun sani kai ne Mai-tsarki na Allah.” (Yohanna 6:66-69) Waɗannan kalaman sun faranta wa Yesu rai! Idan ɗalibi na Littafi Mai Tsarki ya furta bangaskiyarsa kamar haka, hakan zai faranta maka rai.
Yesu Ya Saurara Cikin Ladabi
7. Me ya sa Samariyawa da yawa suka ba da gaskiya ga Yesu?
7 Wani dalilin kuma da ya sa Yesu ya zama ƙwararren mai almajirantarwa shi ne, ya kula da mutane kuma ya saurari abin da suke cewa cikin ladabi. Alal misali, akwai lokacin da Yesu ya yi wa wata mata ’yar Samariya wa’azi a kusa da rijiyar Yakubu a Sukar. A lokacin da suke tattaunawa, Yesu bai yi magana shi kaɗai ba, ya saurari abin da matar ta ce. Sa’ad da yake sauraronta, Yesu ya lura cewa tana son bauta ta gaskiya kuma ya gaya mata cewa Allah yana neman waɗanda za su bauta masa cikin ruhu da gaskiya. Yesu ya kula da wannan matar kuma ya daraja ta, nan da nan ta gaya wa mutane game da shi, kuma “Samariyawa dayawa suka bada gaskiya gareshi sabada maganar mace.”—Yohanna 4:5-29, 39-42.
8. Ta yaya ne yadda mutane suke faɗin ra’ayoyinsu zai taimake ka ka soma tattaunawa a hidima?
8 Mutane suna jin daɗin faɗin ra’ayoyinsu. Alal misali, mazauna Atina na dā suna jin daɗin faɗin ra’ayoyinsu da kuma sauraron abin da ba su sani ba. Hakan ya sa manzo Bulus ya ba da jawabi mai kyau a Tudun Arasa da ke birnin. (Ayukan Manzanni 17:18-34) Sa’ad da kake son ka soma tattaunawa da wani maigida a hidimarka a yau, kana iya cewa: “Na ziyarce ka ne domin ina son in san ra’ayinka game da [batun].” Ka saurari ra’ayin mutumin, ka yi magana a kan abin da ya ce, ko kuma ka yi tambaya game da batun. Bayan haka, ka nuna abin da Littafi Mai Tsarki ya ce a kan batun.
Yesu Ya san Abin da Zai Ce
9. Menene Yesu ya yi kafin ya bayyana “dukan littattafai” ga Kilyobas da abokinsa?
9 Yesu bai taɓa rasa abin da zai ce ba. Ban da kasancewa mai saurarawa sosai, a yawancin lokaci ya san abin da ke zuciyar mutane, kuma ya san ainihin abin da zai ce. (Matta 9:4; 12:22-30; Luka 9:46, 47) Alal misali: Jim kaɗan bayan an ta da Yesu daga matattu, almajiransa guda biyu suna kan hanyarsu ta zuwa Imwasu daga Urushalima. “Suna cikin zance suna bincike tare da juna,” in ji labarin Linjilar, “sai Yesu da kansa ya kusance su, ya tafi tare da su. Amma idanunsu a kame su ke da ba za su sansance shi ba. Ya kuwa ce masu, Wane irin zance ke nan da ku ke yi da juna, kuna cikin tafiya? Suka tsaya, da fuskoki a ƙwansare. Ɗayansu, wanda ana ce da shi Kilyobas, ya amsa ya ce masa, Kai kaɗai kana baƙonta cikin Urushalima, ba ka san al’amuran da suka faru a nan cikin waɗannan kwanaki ba? Ya ce masu, Waɗanne al’amura?” Babban Malami ya saurara yayin da suke faɗin cewa Yesu Banazare ya koyar da mutane, ya yi mu’ujizai, kuma an kashe shi. Kuma a yanzu wasu suna cewa an ta da shi daga matattu. Yesu ya ƙyale Kilyobas da abokinsa su faɗi abin da ke zuciyarsu. Bayan haka, ya bayyana masu abin da suke bukatar su sani, “cikin dukan littattafai.”—Luka 24:13-27, 32.
10. Ta yaya za ka iya sanin ra’ayin addinin mutumin da ka sadu da shi a hidimarka?
10 Wataƙila ba ka san komi game da addinin wani maigida ba. Domin ka san ra’ayinsa, kana iya cewa kana jin daɗin sauraron ra’ayin mutane game da addu’a. Bayan haka kana iya tambayarsa: “Kana ganin cewa akwai ainihin wanda yake jin addu’o’i?” Amsar tana iya bayyana abubuwa masu yawa game da ra’ayin mutumin da kuma addininsa. Idan mai son addini ne, kana iya sanin ra’ayinsa ta wajen tambayarsa, “Kana tunanin cewa Allah yana jin dukan addu’o’i, ko kuwa akwai wasu addu’o’in da ba ya ji?” Irin waɗannan tambayoyin suna iya sa ka tattauna sosai da mutumin. Idan kana son ka nuna masa abin da Nassosi ya ce game da batun, ya kamata ka yi hakan cikin dabara, ban da ƙaryata imanin mutumin. Idan ya ji daɗin abin da ka ce, zai iya cewa ka sake dawowa. Amma, a ce ya yi wata tambayar da ba ka san amsarta ba fa? Kana iya yin bincike kuma ka koma a shirye don ka ‘amsa dalilin begen ka, cikin ladabi da tawali’u.’—1 Bitrus 3:15.
Yesu Ya Koyar da Waɗanda Suka Cancanta
11. Menene zai taimaka maka ka sami waɗanda suka cancanci a koyar da su?
11 Yesu kamiltaccen mutumi ne wanda yake da fahimin da ke taimaka masa ya gano waɗanda suka cancanci samun koyarwa. Yana yi mana wuya mu sami “waɗanda aka ƙadara su ga rai na har abada.” (Ayukan Manzanni 13:48) Haka ma manzannin da Yesu ya gaya wa: “Kowane birni ko ƙauye inda kuka shiga, a cikinsa ku nemi wanda ya cancanta.” (Matta 10:11) Kamar manzannin Yesu, dole ne ka nemi mutanen da suke son su saurara kuma su koyi gaskiyar da ke cikin Nassi. Kana iya samun waɗanda suka cancanta ta wajen sauraron dukan mutanen da ka tattauna da su, kuma ka lura da halin kowannensu.
12. Ta yaya za ka iya ci gaba da taimaka wa mutumin da ke son gaskiya?
12 Bayan ka bar mutumin da ya nuna cewa yana son saƙon Mulki, ya kamata ka ci gaba da yin tunani game da bukatunsa na ruhaniya. Idan ka rubuta abin da ka tattauna da mutum game da bishara, hakan zai sa ka ci gaba da taimaka wa mutumin a ruhaniya. A lokacin da ka koma ziyara, kana bukatar ka saurara sosai idan kana son ka ƙara sanin imanin mutumin, halinsa, ko kuma yanayinsa.
13. Menene zai iya taimaka maka ka gane ra’ayin mutum game da Littafi Mai Tsarki?
13 Ta yaya ne za ka iya ƙarfafa mutane su gaya maka ra’ayinsu game da Kalmar Allah? A wasu wurare, zai dace ka yi wannan tambayar, “Ka taɓa ƙoƙarin ka fahimci Littafi Mai Tsarki?” A yawancin lokaci, amsar da mutumin zai bayar za ta nuna ra’ayinsa game da batutuwa na ruhaniya. Wata hanyar kuma ita ce, ka karanta wata nassi kuma ka tambaye shi, “Ka gaskata da hakan?” Kamar Yesu, za ka iya cim ma abubuwa masu yawa a hidimarka ta wajen yin amfani da tambayoyi masu kyau. Amma fa, ya kamata a mai da hankali sosai.
Yesu Ya Yi Amfani da Tambayoyi Yadda Ya Kamata
14. Ba tare da tuhumar mutane ba, ta yaya za ka nuna cewa kana son ra’ayinsu?
14 Ka nuna kana son ra’ayin mutane ba tare da kunyatar da su ba. Ka bi misalin Yesu. Shi ba ya tambayoyin da ke ba mutane haushi, sai dai masu sa tunani. Yesu mutumi ne mai sauraro, ya wartsakar da mutanen da suke son gaskiya kuma ya kwantar da hankalinsu. (Matta 11:28) Mutane iri-iri sun gaya masa matsalolinsu. (Markus 1:40; 5:35, 36; 10:13, 17, 46, 47) Idan kana son mutane su saki jiki su gaya maka ra’ayinsu game da Littafi Mai Tsarki da kuma koyarwar da ke cikinsa, kana bukatar ka guje wa tuhumarsu.
15, 16. Ta yaya za ka iya soma tattaunawa da mutane game da batutuwan da suka shafi addini?
15 Ƙari ga yin amfani da tambayoyi yadda ya kamata, kana iya sa mutane su yi magana ta wajen faɗin wani abu da suke so kuma ka saurari abin da za su ce. Alal misali, Yesu ya gaya wa Nikodimu: “In ba a haifi mutum daga bisa ba, ba shi da iko shi ga mulkin Allah ba.” (Yohanna 3:3) Waɗannan kalaman suna da ban sha’awa wanda hakan ya sa Nikodimu ya yi kalami kuma ya saurari Yesu. (Yohanna 3:4-20) Kai ma kana iya soma tattaunawa da mutane a wannan hanyar.
16 Addinai masu yawa da ake kafawa a yau sun zama zancen da mutane suke yi a wurare kamarsu Afirka, Gabashin Turai, da kuma Amirka ta Tsakiya zuwa Yamma. A irin waɗannan wuraren kana iya soma tattaunawa ta wajen cewa: “Na damu cewa akwai addinai masu yawa. Amma ina da begen cewa nan ba da daɗewa ba mutane daga dukan al’ummai za su haɗa kai a bauta ta gaskiya. Za ka so ka ga hakan ya faru?” Ta wajen faɗin wani abu mai ban mamaki game da begenka, za ka iya motsa mutane su faɗi ra’ayinsu. Tambayoyi suna da sauƙin amsawa idan amsoshin suka kasu gida biyu. (Matta 17:25) Bayan maigidan ya amsa tambayarka, ka amsa tambayar da kanka ta wajen yin amfani da nassi ɗaya ko biyu. (Ishaya 11:9; Zephaniah 3:9) Idan ka saurara sosai kuma ka lura da amsar da mutumin ya bayar, hakan zai taimaka maka ka san abin da za ka tattauna sa’ad da ka sake dawowa.
Yesu Ya Saurari Yara
17. Menene ya nuna cewa Yesu yana son yara?
17 Yesu yana son yara ba manya kaɗai ba. Ya san irin wasannin da yara suke yi da kuma abubuwan da suke cewa. A wasu lokatai yana gayyatar yara su zo wurinsa. (Luka 7:31, 32; 18:15-17) Yara masu yawa suna cikin jama’ar da suka saurari Yesu. Sa’ad da yara maza suka yabi Almasihu, Yesu ya lura da hakan kuma ya nuna cewa Nassosin ya annabta hakan. (Matta 14:21; 15:38; 21:15, 16) A yau, yara da yawa suna zama almajiran Yesu. Saboda haka, ta yaya za ka taimake su?
18, 19. Ta yaya za ka iya taimaka wa yaronka a ruhaniya?
18 Domin ka taimaka wa yaronka a ruhaniya, dole ne ka saurare shi. Kana bukatar ka san ra’ayoyin da yake da shi da ba su jitu da tunanin Jehobah ba. Ko da menene yaronka ya ce, zai dace ka fara yaba ma shi. Bayan haka, kana iya yin amfani da nassosin da suka dace don ka taimaka wa yaronka ya fahinci ra’ayin Jehobah game da batutuwan.
19 Tambayoyi suna da na su amfanin. Amma kamar manyan mutane, yara ba sa son a dinga tuhumarsu. Maimakon ka ɗaura wa yaronka nauyin amsa tambayoyi masu wuya, me ya sa ba za ka yi ɗan gajeren furci ba game da kanka? Bisa ga batun da kuke tattaunawa, kana iya cewa a dā akwai yadda kake ji game da wani abu kuma ka faɗi dalilin hakan. Bayan haka, kana iya tambayarsa, “Kai ma kana jin hakan?” Amsar da yaronka ya bayar za ta iya sa ku tattauna Nassosin da zai taimake shi kuma ya ƙarfafa shi..
Ka Ci Gaba da Yin Koyi da Babban Mai Almajirantarwa
20, 21. Me ya sa ya kamata ka zama mai saurarawa sosai a aikinka na almajirantarwa?
20 Ko da kana tattauna wani batu ne da yaronka ko kuma wani mutumin dabam, saurarawa sosai yana da muhimmanci. Hakika, wannan nuna ƙauna ce. Ta wajen saurarawa, kana nuna tawali’u, kuma kana daraja wanda yake magana kuma kana la’akari da ra’ayinsa. Hakika, sauraro yana nufin ka mai da hankali ga abin da mutumin yake cewa.
21 Sa’ad da ka fita hidimar Kirista, ka ci gaba da sauraron abin da masu gida suke cewa sosai. Idan ka mai da hankali sosai ga abin da suke cewa, za ka iya sanin fasalolin gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki da za su so. Bayan haka, ka taimake su ta wajen yin amfani da hanyoyin koyarwa da Yesu ya yi amfani da su. Idan ka yi haka, za ka sami farin ciki da gamsuwa domin kana koyi da Babban Mai Almajirantarwa.
Ta Yaya Za Ka Amsa?
• Ta yaya ne Yesu ya ƙarfafa mutane su faɗi ra’ayoyinsu?
• Me ya sa Yesu ya saurari waɗanda ya koyar?
• Ta yaya za ka iya yin amfani da tambayoyi a hidimarka?
• Menene za ka iya yi don ka taimaka wa yara a ruhaniya?
[Hoto a shafi na 27]
Sa’ad da kake yin wa’azi, ka saurara sosai
[Hoto a shafi na 29]
Muna koyi da Yesu sa’ad da muka taimaka wa yara a ruhaniya