‘Ku Yi Ƙarfi Ku Yi Gaba Gaɗi!’
“Ku yi farinciki, na yi nasara da duniya.”—YOHANNA 16:33.
1. Domin abin da ke jiran Isra’ilawa a Kan’ana, wace ƙarfafa suka samu?
LOKACIN da Isra’ilawa suke bakin ƙetare Kogin Urdun zuwa Ƙasar Alkawari, Musa ya gaya musu: ‘Ku yi ƙarfi ku yi gaba gaɗi, kada ku ji tsoro, kada ku firgita dominsu: gama Ubangiji Allahnku, shi ne ya ke tafiya tare da ku.’ Sai Musa ya kira Joshua, wanda aka zaɓa ya shugabanci Isra’ilawa zuwa Kan’ana, kuma ya yi masa gargaɗi ya kasance da gaba gaɗi. (Kubawar Shari’a 31:6, 7) Daga baya, Jehovah ya ƙarfafa Joshua, yana cewa: “Ka ƙarfafa, ka yi ƙarfin zuciya . . . Sai dai ka ƙarfafa, ka yi ƙarfin zuciya ƙwarai.” (Joshua 1:6, 7, 9) Kalmomin sun dace. Isra’ilawa suna bukatar ƙarfin zuciya domin su fuskanci magabtansu masu ƙarfi da suke jiransu a ƙetaren Urdun.
2. Wane yanayi muka kasance ciki a yau, kuma menene muke bukata?
2 A yau, Kiristoci na gaskiya suna bakin ƙetarewa zuwa cikin sabuwar duniya da aka yi alkawarinta, kuma kamar Joshua, suna bukatar kasancewa da ƙarfin zuciya. (2 Bitrus 3:13; Ru’ya ta Yohanna 7:14) Amma, yanayinmu ya bambanta da na Joshua. Joshua ya yi yaƙi da takubba da masu. Mu muna yaƙi na ruhaniya kuma ba ma amfani da makamai na zahiri. (Ishaya 2:2-4; Afisawa 6:11-17) Ban da haka ma, Joshua ya bukaci ya yi yaƙe-yaƙe da yawa masu tsanani har ma bayan ya shiga Ƙasar Alkawari. Amma muna fuskantar namu yaƙi mafi tsanani a yanzu—kafin mu ƙetare zuwa cikin sabuwar duniya. Bari mu maimaita wasu yanayi da ke bukatar a kasance da ƙarfin zuciya.
Me Ya Sa Muke Bukatar Mu Yi Fama?
3. Menene Littafi Mai Tsarki ya bayyana game da uban hamayyarmu?
3 Manzo Yohanna ya rubuta: “Mun sani mu na Allah ne, duniya duka kuwa tana kwance cikin Shaiɗan.” (1 Yohanna 5:19) Waɗannan kalmomin sun nuna dalili na musamman da ya sa Kiristoci suke bukatar yin fama domin su riƙe bangaskiyarsu. Idan Kirista ya riƙe amincinsa, a wata hali nasara ce bisa Shaiɗan Iblis. Saboda haka ne, Shaiɗan yake yawo kamar “zaki mai-ruri” yana ƙoƙarin ya tsoratar kuma ya haɗiye Kiristoci masu aminci. (1 Bitrus 5:8) Hakika, yana yaƙi da Kiristoci shafaffu da kuma abokansu. (Ru’ya ta Yohanna 12:17) Yana amfani da mutane a cikin wannan yaƙi, waɗanda da saninsu ko kuma cikin rashin sani suka cika nufinsa. Yana bukatar ƙarfin zuciya domin a tsaya da ƙarfi gāba da Shaiɗan da dukan manzanninsa.
4. Wane gargaɗi ne Yesu ya bayar, amma wane hali Kiristoci na gaskiya suka nuna?
4 Da yake Yesu ya sani cewa Shaiɗan da manzanninsa za su yi hamayya ƙwarai da bisharar, Ya yi wa mabiyansa gargaɗi: “Za su miƙa ku ga ƙunci, za su kashe ku kuma: za ku zama abin ƙi ga dukan al’ummai sabili da sunana.” (Matta 24:9) Waɗannan kalmomin sun cika a ƙarni na farko, kuma suna cika a yau. Hakika, tsanantawa da wasu Shaidun Jehovah na zamanin yau suka jimre wa yana da tsanani sosai a duk cikin tarihi. Amma, Kiristoci na gaskiya suna da ƙarfin zuciya wajen fuskantar irin waɗannan matsi. Sun sani cewa “tsoron mutum ya kan kawo tarko,” kuma ba sa son tarko ya kama su.—Misalai 29:25.
5, 6. (a) Waɗanne yanayi ke bukatar ƙarfin zuciya a gare mu? (b) Menene Kiristoci masu aminci suka yi yayin da aka gwada ƙarfin zuciyarsu?
5 Da wasu ƙalubale ban da na tsanantawa da ake bukatar ƙarfin zuciya dominsu. Ga wasu masu shela, yin magana da baƙi game da bisharar yana musu wuya. Wasu ’yan makaranta ma suna fuskantar gwaji na ƙarfin zuciyarsu sa’ad da ya zo ga rera waƙar bautar ƙasa ko kuma ga tuta. Tun da yake waƙar nan furci na addini ne, yara Kiristoci suna ƙarfin zuciya su ƙudiri aniyar yi yadda zai faranta wa Allah rai, kuma lallai suna da sunan kirki a batun nan.
6 Muna kuma bukatar ƙarfin zuciya lokacin da ’yan hamayya suka rinjayi hanyoyin wasa labarai domin su wasa mugun labari game da bayin Allah ko kuma yayin da suka yi ƙoƙarin su hana bauta ta gaskiya ta wurin ƙulla “ƙeta a kan farilla.” (Zabura 94:20) Ga misali, yaya ya kamata mu ji yayin da jarida, rediyo, ko kuma telibijin ya ba da labari da ba daidai ba game da Shaidun Jehovah ko kuma ƙarya kai tsaye? Ya kamata ne mu yi mamaki? A’a. Muna tsammanin irin waɗannan. (Zabura 109:2) Kuma ba ma mamaki yayin da wasu suka gaskata ƙaryace-ƙaryace da aka yi, da yake “marar wayo yana gaskata kowacce magana.” (Misalai 14:15) Har ila, Kiristoci na gaskiya suna ƙin gaskata kowanne furci da ake yi game da ’yan’uwansu, kuma ba sa ƙyale yaɗuwar irin wannan ƙaryar ta sa su ƙi halartar taron Kirista, ta rage himmarsu a hidimar fage, ko kuma su raunana a bangaskiyarsu. Akasin haka, suna “koɗa [kansu] masu-hidimar Allah . . . ta wurin daraja da ƙanƙanci, ta wurin mugun ambato da kyakkyawan ambato kamar [’yan adawa] masu-ruɗi [da gaske] mu ke, masu gaskiya ne kuwa.”—2 Korinthiyawa 6:4, 8.
7. Waɗanne tambayoyi na bincike ya kamata mu tambayi kanmu?
7 Bulus da yake rubutu zuwa ga Timothawus ya ce: “Allah ba ya ba mu ruhun tsorata ba; amma na iko . . . Kada fa ka ji kunyar shaidar Ubangijinmu.” (2 Timothawus 1:7, 8; Markus 8:38) Bayan da mun karanta kalmomin nan za mu iya tambayar kanmu: ‘Ina jin kunyar imanina ne, ko kuma ina da ƙarfin zuciya? A inda nake aiki (ko kuma nake zuwa makaranta), na shaida wa mutane da suke wurin cewa ni Mashaidin Jehovah ne, ko kuma ɓoye kaina nake yi? Ina jin kunyar in bambanta ne da wasu, ko kuma ina farin ciki domin dangantakata da Jehovah?’ Idan wani yana jin tsoron yin wa’azin bishara ko kuma game da bambancin imaninsa, bari ya tuna da gargaɗin da Jehovah ya yi wa Joshua: “Ka yi ƙarfi ka yi gaba gaɗi.” Kada ku manta, ba ra’ayin abokan aikinmu ne ko kuma na abokan makaranta yake da muhimmanci ba amma ra’ayin Jehovah da kuma na Yesu Kristi ne yake da muhimmanci.—Galatiyawa 1:10.
Yadda Za Mu Daɗa Zama da Gaba Gaɗi
8, 9. (a) A wani lokaci, ta yaya aka gwada gaba gaɗi na Kiristoci na farko? (b) Yaya Bitrus da Yohanna suka yi sa’ad da aka yi musu barazana, kuma menene su da ’yan’uwansu suka fuskanta?
8 Yaya za mu iya gina irin gaba gaɗi da zai taimake mu mu riƙe amincinmu a lokatai masu wuya? To, yaya Kiristoci na farko suka gina gaba gaɗi? Ka tuna da abin da ya faru lokacin da manyan firistoci da dattawa a Urushalima suka gaya wa Bitrus da Yohanna su daina wa’azi cikin sunan Yesu. Almajiran suka ƙi aka yi musu barazana aka sake su. Bayan haka, sun haɗu da ’yan’uwansu, suka yi addu’a, suna cewa: “Ubangiji, ka dubi kashedinsu: ka ba bayinka kuma su faɗi maganarka da ƙarfinzuciya duka.” (Ayukan Manzanni 4:13-29) Jehovah ya amsa musu ya ƙarfafa su da ruhu mai tsarki, kuma kamar yadda shugabannan Yahudawa daga baya suka tabbatar, sun “gama Urushalima” da koyarwarsu.—Ayukan Manzanni 5:28.
9 Bari mu bincika abin da ya faru a lokacin. Yayin da shugabannan Yahudawa suka yi wa almajiran barazana, almajiran ba su yi tunanin daina aikinsu ba. Maimakon haka, almajiran suka yi addu’a domin ƙarfin zuciya su ci gaba da wa’azi. Sai suka bi daidai da addu’arsu, kuma Jehovah ya ƙarfafa su da ruhunsa. Abin da suka fuskanta ya nuna cewa abin da Bulus ya rubuta shekaru daga baya a wani matani dabam domin Kiristoci ne lokacin da suke shan tsanani. Bulus ya ce: “Na iya yin abu duka a cikin wannan da ya ke ƙarfafata.”—Filibbiyawa 4:13.
10. Ta yaya abin da ya faru wa Irmiya ya taimaki matsorata?
10 A ce mutum matsoraci ne fa? Zai iya ne ya bauta wa Jehovah da gaba gaɗi a lokacin hamayya? Shakka babu! Ka tuna da abin da Irmiya ya yi lokacin da Jehovah ya naɗa shi annabi. Matashin ya ce: “Ni yaro ne.” A bayyane yake, yana jin bai cancanci aikin ba. Duk da haka, Jehovah ya ƙarfafa shi da waɗannan kalmomi: “Kada ka ce, Ni yaro ne; gama za ka tafi wurin dukan wanda zan aike ka gareshi, iyakacin abin da zan umurce ka kuma za ka faɗi. Kada ka ji tsoronsu: gama ina tare da kai domin in cece ka.” (Irmiya 1:6-10) Irmiya ya dogara ga Jehovah, kuma domin haka, ta wurin ƙarfin Jehovah ya sha kan yadda yake ji game da wa’azi kuma ya zama mashaidi mai gaba gaɗi a Isra’ila.
11. Menene ke taimakon Kiristoci a yau su zama kamar Irmiya?
11 Shafaffun Kiristoci a yau suna da aiki irin na Irmiya, kuma “taro mai-girma” na “waɗansu tumaki” suna goya musu baya su ci gaba da shelar nufe-nufen Jehovah, har a lokacin rashin son saƙon, ba’a, da kuma tsanani. (Ru’ya ta Yohanna 7:9; Yohanna 10:16) Sun sami ƙarfafa daga kalmomin Jehovah ga Irmiya: “Kada ka ji tsoro.” Ba su taɓa manta cewa Allah ne ya aike su kuma wa’azin saƙonsa suke yi.—2 Korinthiyawa 2:17.
Misalai na Gaba Gaɗi da Sun Cancanci Yin Koyi
12. Wane misalin gaba gaɗi ne Yesu ya bari, kuma ta yaya ya ƙarfafa mabiyansa?
12 Za mu iya samun taimako a ƙoƙarce-ƙoƙarcenmu mu gina gaba gaɗi idan muka yi bimbini a kan misalai na waɗansu, kamar Irmiya, da ya aika cikin gaba gaɗi. (Zabura 77:12) Alal misali, lokacin da muke bincika hidimar Yesu, gaba gaɗinsa yayin da Shaiɗan ya gwada shi ya burge mu sai kuma lokacin da ya fuskanci hamayya daga wurin shugabannan Yahudawa. (Luka 4:1-13; 20:19-47) Da ƙarfin Jehovah, Yesu ya tsaya tsayin daka, kuma kafin mutuwarsa, ya gaya wa almajiransa: “A cikin duniya kuna da wahala; amma ku yi farinciki, na yi nasara da duniya.” (Yohanna 16:33; 17:16) Idan almajiran Yesu suka bi misalinsa, su ma za su yi nasara. (1 Yohanna 2:6; Ru’ya ta Yohanna 2:7, 11, 17, 26) Amma suna bukatar ‘gaba gaɗi.’
13. Wace ƙarfafa ce Bulus ya yi wa mutanen Filibbi?
13 Wasu shekaru bayan mutuwar Yesu, aka jefa Bulus da Sila cikin kurkuku a Filibbi. Daga baya, Bulus ya ƙarfafa ikilisiyar Filibbi su ci gaba da “tsayawa da ƙarfi cikin ruhu ɗaya, [s]una yaƙi gaba ɗaya domin imanin bishara; ba [s]u firgita ko kaɗan saboda [magabtansu] ba.” Don a ƙarfafa su su yi haka, Bulus ya ce: “Wannan kuwa a garesu [Kiristoci da ake tsananta musu] shaida ce a sarari ta halakarwa [ga masu tsanantawa], amma ta cetonku ce, daga wajen Allah ne kuwa; gama a gareku an bayar sabili da Kristi, ba bada gaskiya gareshi kaɗai ba, amma shan wahala kuma dominsa.”—Filibbiyawa 1:27-29.
14. Menene sakamakon gaba gaɗin Bulus a Roma?
14 Lokacin da Bulus ya yi rubutu zuwa ga ikilisiyar Filibbi, a kurkuku yake, amma wannan lokaci a Roma ce. Duk da haka, ya ci gaba da yin wa’azi wa wasu da gaba gaɗi. Menene sakamakon haka? Ya rubuta: “Sarƙoƙina suka zama bayyanannu cikin Kristi ga matsara na [Alƙali] duka, har ga saura duka kuma; yawancin ’yan’uwa kuma cikin Ubangiji suna ƙarfafawa ta wurin sarƙoƙina, har sun ƙara ƙarfin hali ƙwarai garin faɗin maganar Allah banda tsoro.”—Filibbiyawa 1:13, 14.
15. A ina ne za mu iya samun misalai masu kyau na bangaskiya da za su iya ƙarfafa ƙudurinmu mu kasance da gaba gaɗi?
15 Misalin Bulus yana ƙarfafa mu. Haka nan ma misalai masu kyau na Kiristoci na zamanin yau waɗanda suka jimre tsanani a ƙasashe da suke mulkin kama karya ko kuma na limaman addini. An ba da labarai irinsu da yawa cikin jaridun Hasumiyar Tsaro da Awake! da kuma a cikin Yearbooks of Jehovah’s Witnesses. Yayin da kake karanta labaran, ka tuna cewa waɗanda ake ba da labarinsu mutane ne halittu irinmu; amma lokacin da suke cikin yanayi mai wuya, Jehovah ya ba su ƙarfin hali ƙwarai domin su jimre. Mu tabbata cewa zai iya yi mana haka sa’ad da bukata ta kama.
Gaba Gaɗinmu Yana Faranta wa Jehovah Zuciya Kuma Yana Ɗaukaka Shi
16, 17. Ta yaya mu a yau za mu iya kasancewa da hali na gaba gaɗi?
16 Idan Kirista ya yi gaba gaɗi domin gaskiya da adalci, wannan shi ne ƙarfin hali. Idan mutum ya yi hakan lokacin da yake jin tsoro, wannan shi ne ƙarfin hali na ƙwarai. Hakika, kowanne Kirista zai iya kasancewa da ƙarfin hali idan yana son ya yi nufin Jehovah, kuma idan kowanne lokaci yana tuna cewa a dā Jehovah ya ƙarfafa mutane da yawa kamarsa. Ban da haka ma, idan muka fahimci cewa tsayawarmu da gaba gaɗi yana faranta zuciya kuma ɗaukaka Jehovah, za mu so mu ma mu daɗa tsayawa da ƙarfi. Za mu kasance a shirye mu jimre wa ba’a ko kuma abu mafi muni domin muna ƙaunarsa ƙwarai da gaske.—1 Yohanna 2:5; 4:18.
17 Kada ka manta cewa idan muna wahala domin bangaskiyarmu, ba ya nufin cewa mun yi wani mugun abu. (1 Bitrus 3:17) Muna wahala domin ɗaukaka ikon mallakar Jehovah, domin yin nagarta, da kuma domin kasancewa ba na duniya ba. Domin wannan manzo Bitrus ya ce: “Idan, sa’anda ku ke yin nagarta, kuna shan wuya dominta kuwa, kuka yi haƙuri, wannan abin karɓa ne wurin Allah.” Bitrus ma ya ce: “Bari waɗannan da ke shan wuya bisa ga nufin Allah su damƙa rayukansu cikin aika nagarta ga Mahalicci mai-aminci.” (1 Bitrus 2:20; 4:19) Hakika, bangaskiyarmu tana faranta wa Allahnmu mai ƙauna Jehovah zuciya, kuma tana ɗaukaka shi. Kyakkyawan dalili ne kuwa na kasancewa da gaba gaɗi!
Yin Magana da Masu Iko
18, 19. Yayin da muka yi gaba gaɗi a gaban alƙali, a taƙaice, wane saƙo muke bayarwa?
18 Lokacin da Yesu ya gaya wa mabiyansa cewa za a tsananta musu, ya daɗa cewa: “[Mutane] za su bashe ku ga majalisai, cikin majami’unsu kuma za su yi muku bulala; i, kuma a gaban mahukunta da sarakuna za a kawo ku sabili da ni, domin shaida garesu da Al’ummai kuma.” (Matta 10:17, 18) Domin a je gaban alƙali ko kuma wani masarauci domin tuhumar ƙarya na bukatar gaba gaɗi. Amma, idan muka yi gaba gaɗi a lokatan domin mu yi wa’azi ga mutanen, muna mai da yanayi mai wuya zuwa zarafi ne na yin wani muhimmin abu. Watau, muna gaya wa waɗanda suke shari’armu kalmomin Jehovah, yadda aka rubuta a Zabura ta biyu: “Ku yi hikima fa, ku sarakuna; ku horu da sani, ku alƙalan duniya. Ku bauta ma Ubangiji da tsoro.” (Zabura 2:10, 11) Sau da yawa, idan aka tuhumi Shaidun Jehovah a kotu, alƙalai sukan ba da ’yancin bauta, kuma muna godiya domin wannan. Amma wasu alƙalai, sun ƙyale ’yan hamayya sun rinjaye su. Ga irin waɗannan, Nassi ya ce: ‘Ku yi wa kanku gyara.’
19 Ya kamata alƙalai su fahimci cewa doka mafi girma ta Jehovah Allah ce. Ya kamata su tuna cewa dukan mutane, har da alƙalai, za su ba da lissafi ga Jehovah Allah da kuma Yesu Kristi. (Romawa 14:10) A gare mu, ko alƙalai sun yi mana shari’a ta gaskiya ko babu, ya kamata mu kasance da gaba gaɗi domin Jehovah yana goyon bayanmu. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Masu-albarka ne dukan waɗanda ke dogara gareshi.”—Zabura 2:12.
20. Me ya sa za mu yi farin ciki idan muka jimre wa tsanani da kuma tsegumi?
20 A Huɗuba Bisa Dutse, Yesu ya ce: “Masu-albarka ne ku lokacinda ana zarginku, ana tsananta muku, da ƙarya kuma ana ambatonku da kowacce irin mugunta, sabili da ni. Ku yi farinciki, ku yi murna ƙwarai: gama ladarku mai-girma ce cikin sama: gama hakanan suka tsananta ma annabawan da suka rigaye ku.” (Matta 5:11, 12) Hakika, tsanani kansa ba abin murna ba ne, amma dagewarmu duk da tsanani, da mugun labarai na hanyoyin wasa labarai dalilai ne na farin ciki. Yana nufin cewa muna faranta wa Jehovah rai kuma za mu sami lada. Tsayawarmu da ƙarfi yana nuna bangaskiyarmu ta gaske kuma yana tabbatar da cewa muna da tagomashin Allah. Hakika yana nuna cewa muna dogara ga Jehovah da zuciya ɗaya. Irin wannan dogarar tana da muhimmanci ga Kirista, yadda talifi na gaba zai nuna.
Me Ka Koya?
• Waɗanne yanayi ne a yau suke bukatar gaba gaɗi?
• Ta yaya za mu gina halin gaba gaɗi?
• Su waɗanne ne misalan kirki na gaba gaɗi?
• Me ya sa muke son mu riƙa aikatawa da gaba gaɗi?
[Hotuna a shafi na 21]
Simone Arnold (yanzu Liebster) a Jamus, Widdas Madona a Malawi, da Lydia da Oleksii Kurdas a Ukraine sun nuna gaba gaɗi kuma sun tsayayya wa mugun
[Hotuna a shafi na 22]
Ba ma kunyar bishara
[Hoto a shafi na 23]
Ƙarfin hali na Bulus cikin kurkuku ya sa bisharar ta cim ma abu da yawa
[Hoto a shafi na 24]
Idan muka bayyana matsayinmu na Nassi ga alƙali da gaba gaɗi, muna idar da muhimmin saƙo ne