Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • ijwbq talifi na 159
  • Dabbobi Suna Zuwa Sama Ne?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Dabbobi Suna Zuwa Sama Ne?
  • Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Amsar Littafi Mai Tsarki
  • Dabbobi suna da kurwa ne?
  • Kurwa tana iya mutuwa kuwa?
  • Dabbobi suna iya yin zunubi?
  • Zai dace a rika cin zalin dabbobi ne?
  • Tambayoyi Daga Masu Karatu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Wadanda Ba Sa Cin Nama​—Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?
    Karin Batutuwa
  • “Kurwa” da Kuma “Ruhu”—Menene Ainihi Ma’anar Waɗannan Kalmomi?
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
ijwbq talifi na 159
Kare

Dabbobi Suna Zuwa Sama Ne?

Amsar Littafi Mai Tsarki

Littafi Mai Tsarki ya koyar cewa a dukan halittun da ke duniya, mutane ne kadan za su je sama. (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 14:​1, 3) Za su je ne su yi hidimar firistoci da kuma sarakuna tare da Yesu. (Luka 22:​28-30; Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 5:​9, 10) Yawanci mutane kuma da za a ta da daga mutuwa za su yi rayuwa a aljanna a duniya.​—Zabura 37:​11, 29.

A Littafi Mai Tsarki ba a ambata cewa dabbobi za su je sama ba. Me ya sa? Dabbobi ba za su iya daukan matakan samun “kiran nan na sama” ba. (Ibraniyawa 3:1) Wadannan matakan sun kunshi koyo game da Allah da yin imani da shi da kuma bin umurnansa. (Matiyu 19:17; Yohanna 3:16; 17:3) Mutane ne kadai aka halitta don yin rayuwa na har abada.​—Farawa 2:​16, 17; 3:​22, 23.

Kafin halittun duniya su je sama, ana bukatar a ta da su daga mutuwa. (1 Korintiyawa 15:42) Littafi Mai Tsarki ya ambata wasu tashin matattu da aka yi. (1 Sarakuna 17:​17-24; 2 Sarakuna 4:​32-37; 13:​20, 21; Luka 7:​11-15; 8:​41, 42, 49-56; Yohanna 11:​38-44; Ayyukan Manzanni 9:​36-42; 20:​7-12) Amma dukansu mutane ne aka ta da.

  • Dabbobi suna da kurwa ne?

  • Kurwa tana iya mutuwa kuwa?

  • Dabbobi suna iya yin zunubi?

  • Zai dace a rika cin zalin dabbobi ne?

Dabbobi suna da kurwa ne?

A’a. Littafi Mai Tsarki ya ce dabbobi da ’yan Adam dukansu kurwa ne. (Littafin Ƙidaya 31:28) Sa’ad da aka halicci mutum na farko, wato Adamu, Allah bai saka masa kurwa ba amma ‘mutum ya zama mai rai.’ (Farawa 2:7) Kurwa tana dauke da abubuwa biyu: “Ƙurar ƙasa” da kuma “numfashin rai.”

Kurwa tana iya mutuwa kuwa?

E, Littafi Mai Tsarki ya koyar cewa kurwa tana iya mutuwa. (Littafin Firistoci 21:11; Ezekiyel 18:20) Sa’ad da dabbobi da kuma ’yan Adam suka mutu, dukansu suna zama ƙurar ƙasa. (Mai-Wa’azi 3:​19, 20) Wato za su daina wanzuwa.a

Dabbobi suna iya yin zunubi?

A’a. Yin zunubi yana nufin tunani ko kuma yin abin da ya saba wa ka’idodin Allah. Kafin halittu su iya yin zunubi, suna bukatar su san abu mai kyau da marar kyau, amma dabbobi ba za su iya yin hakan ba. A dan gajeriyar rayuwa da suke da ita suna yin abubuwa ne bisa iliminsu. (2 Bitrus 2:12) Idan kwanakinsu ya kare sai su mutu duk da cewa ba su yi zunubi ba.

Zai dace a rika cin zalin dabbobi ne?

A’a. Allah ya ba ’yan Adam iko a kan dabbobi amma ba don su rika cin zalinsu ba. (Farawa 1:28; Zabura 8:​6-8) Allah ya damu da dukan dabbobi har da kananan tsuntsaye. (Yona 4:11; Matiyu 10:29) Ya umurci bayinsa su rika bi da dabbobi yadda ya dace.​—Fitowa 23:12; Maimaitawar Shari’a 25:4; Karin Magana 12:10.

Ayoyin da suka yi magana a kan dabbobi

Farawa 1:28 ta ce: “Allah ya sa musu [mutane na farko] albarka ya ce, ‘Ku yi ta haifuwa sosai ku yalwata, ku ciccika duniya ku kuma sha ƙarfinta. Ku yi mulkin kifayen teku, da tsuntsayen sararin sama, da kowane abu mai rai mai kai da kawowa cikin duniya.’”

Ma’ana: Allah ya ba ’yan Adam iko a kan dabbobi

Littafin Ƙidaya 31:28 ta ce: “Daga . . . , sojojin da suka tafi yaƙi, sai ka keɓe kashi na musamman ya zama haraji ga Yahweh. Ka ɗauki abu ɗaya daga cikin kowane ɗari biyar domin harajin, ko na mutane, ko na shanu, ko na jakuna, ko na awaki.”

Ma’ana: ’Yan Adam da kuma dabbobi dukansu kurwa ne.

Karin Magana 12:10: “Mai adalci yana kula da lafiyar dabbobinsa.”

Ma’ana: Mutane masu halin kirki suna kula da dabbobi har da nasu.

Matiyu 10:29: “Ba ana tsayar da dan tsuntsu guda biyu kobo daya ba? To, ba dayansu wanda zai fadi a kasa ba tare da sanin Ubanku ba.”

Ma’ana: Allah yana lura da kuma kula da dabbobi har da tsuntsaye.

a Don samun karin bayani, ka duba babi na 6 a littafin nan Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba