Ka Sani?
Yaya darajar anini biyu na Gwauruwa?
A ƙarni na farko A.Z., harajin da Yahudawa suke biya a haikali kowace shekara “rabin shekel,” ne wato kuɗin aiki na kwana biyu ke nan. (Matta 17:24) Akasarin haka, Yesu ya ce ana sayar da gwarare biyu a bakin ‘anini guda,’ wato kuɗin aiki na minti 45 ke nan. Hakika, ana iya sayan gwarare biyar da anini biyu, ko kuma kuɗin aiki na minti 90.—Matta 10:29; Luka 12:6.
Abin da gwauruwa matalauciya ta bayar a haikali da Yesu ya gani bai ma kai wannan ba. Saba biyu da ta bayar ko kuma lefta, su ne ƙananan kuɗi na ƙarshe da ake amfani da su a Isra’ila a lokacin. Sun yi daidai da kashi 1 cikin 64 na kuɗin aiki na rana, ko kuma kasa da kuɗin aiki na minti 12 wato bisa ga aikin awa 12 ke nan a rana.
Yesu ya ɗauki abin da wannan gwauruwa ta bayar da daraja fiye da dukan kuɗi mai yawa da sauran mutanen suka bayar “cikin falalassu.” Me ya sa? Labarin ya ce tana da “anini biyu,” tana iya jefa ɗaya ta riƙe ɗaya. Duk da haka, ta bayar da “abin da ta ke da shi duka, iyakar abin zaman garinta ke nan.”—Markus 12:41-44; Luka 21:2-4.
Yaushe ne aka san Shawulu da suna Bulus?
An haifi Bulus Bayahude ne mai ’yancin Barome. (Ayukan Manzanni 22:27, 28; Filibbiyawa 3:5) To wataƙila tun yana yaro ne yake da sunayen nan Shawulu na Ibraniyawa da kuma Bulus na Romawa. Wasu cikin ’yan’uwan Bulus ma suna da sunaye na Romawa da na Helenawa. (Romawa 16:7, 21) Bugu da ƙari, ba abin mamaki ba ne ga Yahudawa na zamanin, musamman tsakanin waɗanda ba sa zama a cikin Isra’ila su kasance da sunaye biyu.—Ayukan Manzanni 12:12; 13:1.
Fiye da shekara 10 bayan ya zama Kirista, kamar dai an fi sanin wannan manzo da sunansa ne na Ibrananci, Shawulu. (Ayukan Manzanni 13:1, 2) Amma, a tafiyarsa ta wa’azi ta farko, a tsakanin shekara ta 47 ko 48 A.Z., wataƙila ya fi so ya yi amfani da sunansa na Romawa Bulus. An aike shi ya yi bishara ga waɗanda ba Yahudawa ba, wataƙila ya ga cewa sunansa na Romawa zai fi dacewa. (Ayukan Manzanni 9:15; 13:9; Galatiyawa 2:7, 8) Kuma wataƙila ya yi amfani da sunansa Bulus ne domin yadda ake furta sunansa na Ibrananci a Helenanci ya yi kusa da wata kalmar Helenanci da take da mummunar ma’ana. Ko menene dai dalilin da ya sa ya yi wannan canji, Bulus ya nuna cewa yana shirye ya ‘zama dukan abu ga dukan mutane, domin ko da ƙaƙa ya ceci waɗansu.’—1 Korinthiyawa 9:22.
[Hoto a shafi na 28]
Leftan, ainihinsa