Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w03 7/1 pp. 26-31
  • “Allah Ƙauna Ne”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Allah Ƙauna Ne”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Nuna Ƙauna da ta Fice
  • Yadda Jehovah Ya Tabbatar Mana Ƙaunarsa
  • Allah Wanda Yake da “Hanzarin Gafartawa”
  • ‘Juyayi Mai-Taushi na Allahnmu’
  • “Yawan Jinƙai . . . na Allahnmu”
    Ka Kusaci Jehobah
  • “Ya Fara Kaunace Mu”
    Ka Kusaci Jehobah
  • Babu Abin da Zai Iya “Raba Mu da Ƙaunar Allah”
    Ka Kusaci Jehobah
  • Allah “Mai Yin Gafara”
    Ka Kusaci Jehobah
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
w03 7/1 pp. 26-31

“Allah Ƙauna Ne”

“Wanda ba ya yin ƙauna ba, ba ya san Allah ba; gama Allah ƙauna ne.” —1 YOHANNA 4:8.

1-3. (a) Menene Littafi Mai Tsarki ya faɗi game da halin Jehovah na ƙauna, kuma a waɗanne hanyoyi furcin ke da muhimmanci? (b) Me ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce “Allah ƙauna ne”?

DUKAN halayen Jehovah mafi kyau ne, kamilai, kuma na ban sha’awa. Amma mafi ban sha’awa a dukan halayen Jehovah ita ce ƙauna. Babu wani abin da ke jawo mu kusa da Jehovah da take da iko kamar ƙaunarsa. Abin farin ciki ne cewa ƙauna ce halinsa na musamman. Ta yaya muka san wannan?

2 Littafi Mai Tsarki ya faɗi wani abu game da ƙauna da bai taɓa faɗa ba game da wasu halayen Jehovah na musamman. Nassosi ba su ce Allah iko ne ko cewa Allah shari’a ne ko ma cewa Allah hikima ne ba. Yana da waɗannan halaye, kuma shi ne tushen su ukun duka. Ban da haka, an faɗi wani abu mafi iko a 1 Yohanna 4:8: “Allah ƙauna ne.” Hakika, ƙauna ce take cike cikin Jehovah. Ainihinsa ne, ko kuma halinsa ne. Galibi, za mu yi tunani game da shi a wannan hanyar: Ikon Jehovah yana sa shi ya aikata. Shari’arsa da kuma hikimarsa suna ja-gorar yadda yake aikatawa. Amma ƙaunar Jehovah take motsa shi ya aikata. Kuma wannan ƙauna tana bayyane a yadda yake amfani da wasu halayensa.

3 Sau da yawa a kan ce Jehovah ƙauna ne. Saboda haka, idan muna son mu koya game da ƙauna, dole ne mu koya game da Jehovah. Bari mu bincika wasu fannoni na ƙaunar Jehovah da babu na biyunta.

Nuna Ƙauna da ta Fice

4, 5. (a) Menene nuni na ƙauna da ta fice a dukan tarihi? (b) Me ya sa za mu iya ce Jehovah da Ɗansa suna da haɗin kai ta wurin gami mai ƙarfi na ƙauna?

4 Jehovah ya nuna ƙauna a hanyoyi da yawa, amma da akwai ɗaya da ta fice wa saura. Mecece wannan? Aiko da ɗansa ne ya wahala ya mutu dominmu. Hakika, za mu iya ce ita ce ƙauna da ta fice a dukan tarihi. Me ya sa?

5 Littafi Mai Tsarki ya kira Yesu “ɗan fari ne gaban dukan halitta.” (Kolossiyawa 1:15) Ka yi tunani—Ɗan Jehovah ya wanzu kafin sararin halitta da muke gani. Menene yawan tsawon lokaci da Uba da Ɗa suka kasance tare? Wasu ’yan kimiyya sun kimanta cewa sararin halitta ya wanzu na shekaru biliyan 13 yanzu. Duk da haka, idan kimantawar daidai ce, bai daɗe yadda zai yi daidai da rayuwar Ɗan fari na Jehovah ba! Me yake yi a duk shekarun nan? Cikin farin ciki Ɗan ya yi hidima ta “gwanin mai-aiki” da Ubansa. (Misalai 8:30; Yohanna 1:3) Jehovah da Ɗansa sun yi aiki tare su sa wasu halittu su wanzu. Lallai sun sha daɗin aiki tare! Waye cikinmu da zai iya fahimtar ikon gamin da ya kasance na tsawon lokacin da ya shige? A bayyane ne, Jehovah Allah da Ɗansa suna da haɗin kai ta wurin gami mai ƙarfi na ƙauna.

6. Lokacin da Yesu ya yi baftisma, yaya Jehovah ya furta yadda yake ji game da Ɗansa?

6 Duk da haka, Jehovah ya aiko da Ɗansa zuwa duniya a haife shi jaririn ɗan mutum. Yin haka na shekaru, yana nufin cewa Jehovah zai ƙyale tarayya na kurkusa da ƙaunatacen Ɗansa a sama. Domin yana so, Yana kallo daga sama yayin da Yesu yake girma ya zama kamilin mutum. A shekararsa ta 30, Yesu ya yi baftisma. A lokacin, Uban ya yi magana da kansa daga sama: “Wannan Ɗana ne, ƙaunatacena, wanda raina ya ji daɗinsa sarai.” (Matta 3:17) Da ganin cewa Yesu cikin aminci ya yi dukan abin da aka yi annabcinsa, dukan abin da aka biɗa daga gare shi, lallai Ubansa ya yi farin ciki!—Yohanna 5:36; 17:4.

7, 8. (a) Menene Yesu ya sha azabarsa a ranar 14 ga Nisan, 33 A.Z., kuma yaya wannan ya shafi Ubansa na samaniya? (b) Me ya sa Jehovah ya ƙyale Ɗansa ya wahala kuma ya mutu?

7 To, yaya Jehovah ya ji a ranar 14 ga Nisan, 33 A.Z., lokacin da aka ci amanar Yesu kuma taron ’yan banza suka kama shi? Lokacin da aka yi wa Yesu ba’a, tofa masa yau, kuma buge shi da dunƙulen hannu fa? Lokacin da aka dūke shi, bayansa ya yayyage fa? Da aka kafa shi, hannaye da ƙafafu, a kan itace kuma aka ƙyale shi ya rataye yayin da mutane suke masa zargi fa? Yaya Uban ya ji lokacin da Ɗansa ƙaunatacce yake kuka gare shi domin zafi? Yaya Jehovah ya ji yayin da Yesu ya ja numfashinsa na ƙarshe a lokaci na farko tun halitta, Ɗansa ƙaunatacce ya mutu?—Matta 26:14-16, 46, 47, 56, 59, 67; 27:26, 38-44, 46; Yohanna 19:1.

8 Tun da yake Jehovah yana da jiye-jiye, azabar da ya sha game da mutuwar Ɗansa kalmomi ba sa iya bayyanawa. Abin da za a iya faɗa shi ne nufin Jehovah na ƙyale wannan ya faru. Me ya sa Uban ya sa kansa ya sha azaba haka? Jehovah ya bayyana mana wani abin mamaki a Yohanna 3:16—ayar Littafi Mai Tsarki da take da muhimmanci ƙwarai da ake kiranta ƙaramar Lingila. Ta ce: “Allah ya yi ƙaunar duniya har ya bada Ɗansa, haifaffe shi kaɗai, domin dukan wanda yana bada gaskiya gareshi kada ya lalace, amma ya sami rai na har abada.” Saboda haka, dalilin Allah shi ne: ƙauna. Babu wata ƙauna da aka nuna da ta fi wannan.

Yadda Jehovah Ya Tabbatar Mana Ƙaunarsa

9. Menene Shaiɗan yake son mu gaskata game da yadda Jehovah yake ɗaukanmu, amma menene Jehovah ya tabbatar mana?

9 Amma, an yi muhimmiyar tambaya: Allah yana ƙaunarmu ɗai-ɗai kuwa? Wasu za su yarda cewa Allah yana ƙaunar mutane galibinsu, kamar yadda Yohanna 3:16 ta ce. Amma suna ji, kamar dai a ce, ‘Allah ba zai taɓa ƙaunata ba.’ Hakika Shaiɗan yana ɗokin ya sa mu yarda cewa Jehovah ba ya ƙaunarmu kuma ba ya ɗaukanmu da tamani. A wata sassa, ko yaya muke tunanin ba a ƙaunarmu ko kuma ba mu da wata daraja, Jehovah ya tabbatar mana cewa kowanne cikin bayinsa masu aminci yana ɗaukansu da tamani.

10, 11. Ta yaya misalin Yesu na gwarare ya nuna cewa muna da tamani a idanun Jehovah?

10 Alal misali, ka yi la’akari da kalmomin Yesu da suke rubuce a Matta 10:29-31. Da yake kwatanta tamanin almajiransa, Yesu ya ce: “Ba a kan sayarda gwarare biyu a bakin [kwabo] guda ba? Ko ɗaya a cikinsu kuwa ba shi fāɗuwa a ƙasa ba sai da sanin Ubanku: amma har da gasussuwan kanku dukansu an ƙididdige su. Kada ku ji tsoro fa; kun fi gwarare masu-yawa daraja.” Ka yi la’akari da abin da waɗannan kalmomin suke nufi ga masu sauraron Yesu na ƙarni na farko.

11 A zamanin Yesu gwara ita ce tsuntsuwa mafi araha da ake abinci da ita. Da kwabo ɗaya sai mai saya ya samu guda biyu. Amma, daga baya Yesu ya ce, in ji Luka 12:6, 7, idan mutum ya ba da kwabo biyu, sai ya sami gwarare ba huɗu ba amma biyar. Tsuntsuwa da aka ba da ita gyara kamar dai ba ta da tamani ko kaɗan. Wataƙila wannan tsuntsuwa ba ta da tamani a idanun mutane, amma yaya Mahalicci yake ɗaukanta? Yesu ya ce: “Ko ɗaya kuwa a cikinsu [har da wadda aka ba da ita gyara] ba a manta da shi wurin Allah ba.” Yanzu za mu fara fahimtar abin da Yesu yake nufi. Tun da Jehovah ya ɗauki gwara guda da tamani, to, lallai tamanin mutum yana da yawa! Kamar yadda Yesu ya ce, Jehovah ya san kome game da mu. Har gasun kanmu duka a ƙirge suke!

12. Me ya sa za mu tabbata cewa Yesu da gaske yake lokacin da yake magana game da ƙirgen gasussuwan kanmu?

12 Wasu za su yi tsammanin cewa Yesu zugugu yake yi a nan. Amma ka yi tunani, game da begen tashin matattu. Dole ne Jehovah ya san mu ƙwarai domin ya sake halittarmu! Yana ɗaukanmu da tamani sosai da har yana tuna da dukan wani abu game da mu, har da jinsinmu da dukan fahiminmu da abin da muka sani. Ƙirga gasussuwanmu—wanda matsakaicin kai yana ɗauke da guda 100,000—abu ne mai sauƙi idan aka gwada. Kalmomin Yesu sun tabbatar mana cewa Jehovah yana ƙaunar kowannenmu!

13. Ta yaya batu game da Sarki Jehoshaphat ya nuna cewa Jehovah yana neman abin kirki cikinmu ko da mu ajizai ne?

13 Littafi Mai Tsarki ya faɗi wani abu da ya tabbatar da mu game da ƙaunar Jehovah. Yana neman kuma daraja nagarin abu daga cikinmu. Ga misalin nagari Sarki Jehoshaphat. Lokacin da sarkin ya yi wata wauta, annabin Jehovah ya gaya masa: “Domin wannan fushi daga wurin Ubangiji yana bisa kanka.” Dubi abin taɓa zuciya! Amma saƙon Jehovah bai ƙare a wajen ba. Ya ci gaba: “Duk da wannan aka iske abubuwan kirki a cikinka.” (2 Labarbaru 19:1-3) Saboda haka, wannan fushin adalci na Jehovah bai makantar da shi ba ga “abubuwan kirki” game da Jehoshaphat. Ba abin tabbatarwa ne mu sani cewa Allahnmu yana neman abin kirki cikinmu ko da mu ajizai ne ba?

Allah Wanda Yake da “Hanzarin Gafartawa”

14. Sa’ad da muka yi zunubi, wane nauyi za mu ji, amma ta yaya za mu iya amfana daga gafarar Jehovah?

14 Sa’ad da muka yi zunubi, baƙin ciki, kunya, da nauyin lamiri mai ciwo zai sa mu ji ba mu cancanta bauta wa Jehovah ba. Amma, ka tuna cewa Jehovah “mai-hanzarin gafartawa” ne. (Zabura 86:5) Hakika, idan muka tuba daga zunubanmu kuma yi ƙoƙarin kada mu maimaita su, za mu iya amfana daga gafarar Jehovah. Ka yi la’akari da yadda Littafi Mai Tsarki ya kwatanta wannan fanni mai girma na ƙaunar Jehovah.

15. Yaya nisan yadda Jehovah yake kawar da zunubinmu daga gare mu yake?

15 Mai Zabura Dauda ya yi amfani da furci na sarai ya kwatanta gafartawa ta Jehovah: “Kamar nisan gabas da yamma, hakanan ya kawar da saɓe saɓenmu, ya nisantadda su.” (Tafiyar tsutsa tamu ce; Zabura 103:12.) Yaya nisan gabas daga yamma yake? Nisan gabas daga yamma ba ta da iyaka; waje biyun ba za su taɓa haɗuwa ba. Wani manazarci ya lura cewa wannan furcin yana nufin “yadda nisan ya yiwu; nisan da za mu iya tunaninsa.” Hurarrun kalmomin Dauda sun gaya mana cewa sa’ad da Jehovah ya gafarta, yana kawar da zunubanmu da nisa yadda ba za mu yi tsammani ba daga gare mu.

16. Sa’ad da Jehovah ya gafarta mana zunubanmu, me ya sa za mu tabbata cewa yana ɗaukanmu masu tsabta bayan haka?

16 Ka taɓa ƙoƙarin cire datti daga farar riga? Wataƙila duk da ƙoƙarinka dattin ya kasance ana gani. Ka lura yadda Jehovah ya kwatanta yawan yadda yake gafartawa: “Ko da zunubanku sun yi kamar mulufi, za su yi fari kamar [dusar ƙanƙara]; ko da suna ja wur kamar garura, za su zama kamar auduga.” (Tafiyar tsutsa tamu ce; Ishaya 1:18.) Kalmar nan “mulufi” tana nufin launi ja mai haske.a “Garura” tana nufin launi mai duhu na kayan rini. Ba za mu taɓa iya cire tabon zunubi ba ta wajen ƙoƙarinmu. Amma, Jehovah zai iya ɗaukar zunuban da suke kama da mulufi da garura ya mai da su fari fat kamar dusar ƙanƙara ko ulu da ba a rine ba. Sa’ad da Jehovah ya gafarta mana zunubanmu, ba ma bukatar jin cewa muna ɗauke da tabon wannan zunubi a duk rayuwarmu.

17. A wace hanya ce Jehovah yake yar da zunubi a bayansa?

17 A waƙar godiya da Hezekiya ya yi bayan an ceci ransa daga ciwon ajali, ya ce wa Jehovah: “Ka yarda zunubaina duka a bayanka.” (Tafiyar tsutsa tamu ce; Ishaya 38:17.) A nan an nuna cewa Jehovah yana ɗaukan zunuban masu laifi da suka tuba ya yar da su a bayansa inda ba zai gansu ba ko ya lura da su. In ji wata majiya, za a iya furta abin da ake nufi haka: “Ka mayar da [zunubai na] kamar ba su taɓa faruwa ba.” Wannan ba yana da ban ƙarfafa ba?

18. Yaya annabi Mikah ya nuna cewa sa’ad da Jehovah ya gafarta, Ya ɗauke zunubanmu dindindin?

18 A cikin alkawarin maidowa, annabi Mikah ya furta tabbacinsa cewa Jehovah zai gafarta wa mutanensa da suka tuba: “Wanene Allah makwatancinka, . . . wanda ya rufe laifi na ringin mutanen gadōnsa? . . . za ka zubarda zunubansu duka cikin zurfin teku.” (Tafiyar tsutsa tamu ce; Mikah 7:18, 19.) Ka yi tunanin abin da kalmomin nan suke nufi ga waɗanda suke a zamanin Littafi Mai Tsarki. Zai yiwu ne a maido da abin da aka riga aka jefa “cikin zurfin teku”? Saboda haka, kalmomin Mikah sun nuna cewa sa’ad da Jehovah ya gafarta, ya ɗauke zunubanmu dindindin.

‘Juyayi Mai-Taushi na Allahnmu’

19, 20. (a) Mecece ma’anar aikatau na Ibrananci da aka fassara “yi jinƙai” ko kuma “ji tausayi”? (b) Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya yi amfani da motsin rai da uwa take yi ga jaririnta ya koya mana game da jinƙan Jehovah?

19 Juyayi ne wani fannin ƙauna na Jehovah. Menene juyayi? A cikin Littafi Mai Tsarki, juyayi da jinƙai suna da nasaba ta kusa kusa. Kalmomin Ibrananci da na Helenanci da yawa sun ba da ma’ana ta juyayi mai taushi. Alal misali, aikatau na Ibrananci ra·chamʹ ana yawan fassara shi “yi jinƙai” ko kuma “ji tausayi.” Wannan kalmar Ibrananci, da Jehovah ya yi amfani da ita wa kansa, tana da nasaba da kalmar nan “mahaifa” kuma za a iya ce da ita “juyayi na uwa.”

20 Littafi Mai Tsarki ya yi amfani da wannan motsin rai da uwa take da shi ga jaririnta ya koya mana game da jinƙai na Jehovah. A Ishaya 49:15 ta ce: “Ya yiwu mace ta manta da ɗanta mai-shan mama, har da ba za ta yi juyayin [ra·chamʹ] ɗan cikinta ba? i, ya yiwu waɗannan su manta, amma ni ba ni manta da ke ba.” Yana da wuya a yi tunanin cewa uwa za ta manta ta ciyar da jaririnta kuma ta kula da shi. Ban da haka ma, jariri ba shi da na kansa; dare da rana jariri yana bukatar ƙaunar uwar da kuma hankalinta. Abin taƙaici, ƙyaliya ta uwaye ba sabon abu ba ne, musamman ma a wannan “miyagun zamanu.” (2 Timothawus 3:1, 3) “Amma,” Jehovah ya ce, “ni ba ni manta da ke ba.” Jinƙai mai taushi da Jehovah yake da shi ga bayinsa ya fi motsin rai mafi taushi da za mu iya tunaninsa—juyayi da uwa take yi wa jaririnta.

21, 22. Menene Isra’ilawa suka shaida a ƙasar Masar ta dā, kuma ta yaya ne Jehovah ya amsa kukarsu?

21 Ta yaya Jehovah, kamar mahaifi mai ƙauna, yake nuna jinƙai? Wannan halin yana bayyana sarai a hanyar da ya bi da al’ummar Isra’ila ta dā. A ƙarshen ƙarni na 16 K.Z., miliyoyin Isra’ilawa suna bauta a ƙasar Masar, inda aka ci zalinsu ƙwarai. (Fitowa 1:11, 14) A cikin wahalarsu Isra’ilawa suka yi kuka ga Jehovah. Yaya Allah mai jinƙai mai taushi ya amsa?

22 Ta taɓa zuciyar Jehovah. Ya ce: “Na ga ƙuncin mutanena waɗanda ke cikin Masar, na kuwa ji kukarsu . . . gama na san baƙinzuciyarsu.” (Fitowa 3:7) Ba zai yiwu ba Jehovah ya ga wahalar mutanensa ko kuma ya ji kukarsu bai yi juyayinsu ba. Jehovah, Allah ne mai tausayi. Kuma tausayi—iya fahimtar wahalar wasu ne—ɗan’uwan juyayi ne. Amma Jehovah bai yi juyayin mutanensa kawai ba, ya motsa ya aikata dominsu. Ishaya 63:9 ta ce: “Cikin ƙaunarsa da cikin tausayinsa ya fanshe su.” Da “hannu mai-ƙarfi,” ya ceci Isra’ilawa daga ƙasar Masar. (Kubawar Shari’a 4:34) Daga baya, ya yi musu tanadin abinci cikin mu’ujiza kuma ya kai su cikin ƙasarsu mai ni’ima.

23. (a) Ta yaya kalmomin Mai Zabura ya tabbatar mana cewa Jehovah yana damuwa da kowannenmu sosai? (b) A waɗanne hanyoyi Jehovah ke taimakonmu?

23 Jehovah ba ya nuna juyayinsa ga mutanensa a rukuni kawai ba. Allahnmu mai ƙauna yana damuwa ƙwarai game da mu. Yana sane da duk wata wahala da muke sha. Mai Zabura ya ce: “Idanun Ubangiji suna fuskanta wajen masu-adalci; kunnuwansa kuma a buɗe su ke ga jin ƙararsu. Ubangiji yana kusa da masu-karyayyar zuciya, yana ceton irin waɗanda su ke da ruhu mai-tuba.” (Zabura 34:15, 18) Yaya Jehovah yake taimakonmu ɗai-ɗai? Ba dole ba ne ya cire tushen wahalarmu. Amma ya yi tanadi mai yawa domin waɗanda suke kuka gare shi. Kalmarsa, ta ba da shawara mai kyau da za ta yi amfani. A cikin ikilisiya, ya yi tanadin masu kula ƙwararru a ruhaniya, waɗanda suke ƙoƙari su nuna irin juyayinsa wajen taimakon wasu. (Yaƙub 5:14, 15) Da yake “mai-jin addu’a ne,” Jehovah yana ba da “ruhu mai-tsarki ga waɗanda su ke roƙonsa.” (Zabura 65:2; Luka 11:13) Dukan waɗannan tanadodin nuni na ‘juyayi mai-taushi na Allahnmu’ ne.—Luka 1:78.

24. Yaya za ka amsa ga ƙaunar Jehovah?

24 Ba abin farin ciki ne mu yi tunanin ƙauna ta Ubanmu na samaniya ba? A cikin talifin da ya shige an tunasar da mu cewa Jehovah yana nuna iko, shari’a, da kuma hikima a hanyoyi na ƙauna domin amfaninmu. Kuma a cikin wannan talifin mun ga cewa Jehovah ya nuna ƙaunarsa kai tsaye ga mutane—kuma gare mu ɗai-ɗai—a hanya ta musamman. To, zai dace kowannenmu ya yi tambaya, ‘Yaya zan amsa ga ƙaunar Jehovah?’ Bari ka amsa ta wurin ƙaunace shi da dukan zuciyarka, azancinka, ranka, da kuma ƙarfinka. (Markus 12:29, 30) Bari yadda kake rayuwarka kowacce rana ta nuna sha’awarka ta zuci ka kusaci Jehovah. Kuma bari Jehovah, Allah na ƙauna, ya matso kusa da kai—dukan dawwama!—Yaƙub 4:8.

[Hasiya]

a Wani manazarci ya ce mulufi “launi ne da ba ya wankewa. Ba raɓa, ba ruwan sama, ba kuma wanki ba, ko kuma yawan amfani da zai iya ya fid da shi.”

Ka Tuna?

• Yaya muka sani cewa ƙauna ce halin Jehovah na musamman?

• Me ya sa za a iya cewa ƙauna mafi girma da Jehovah ya nuna mana ita ce aiko da Ɗansa ya wahala kuma ya mutu dominmu?

• Ta yaya Jehovah ya tabbatar da mu cewa yana ƙaunarmu ɗai-ɗai?

• A waɗanne hanyoyi da ke bayyane Littafi Mai Tsarki ya kwatanta gafartawan Jehovah?

[Hoto a shafi na 27]

“Allah . . . ya bada Ɗansa, haifaffe shi kaɗai”

[Hoto a shafi nas 28, 29]

“Kun fi gwarare masu-yawa daraja”

[Inda aka Dauko]

© J. Heidecker/VIREO

[Hoto a shafi na 30]

Yadda uwa take ji game da jaririnta na iya koya mana game da jinƙan Jehovah

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba