Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 11/15 pp. 10-14
  • Ta Yaya Za Mu Kasance da Haƙuri Yayin da Muke “Jira”?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ta Yaya Za Mu Kasance da Haƙuri Yayin da Muke “Jira”?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • MENE NE ZA MU IYA KOYA DAGA MISALIN MIKAH?
  • WAƊANNE AUKUWA NE ZA SU NUNA CEWA CETONMU YA KUSA?
  • TA YAYA ZA MU NUNA CEWA MUNA GODIYA DON HAƘURIN ALLAH?
  • Za Mu Yi Tafiya Cikin Sunan Jehovah Har Abada!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Bayin Jehovah Suna Da Bege Na Gaske
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Menene Jehovah Yake Bukata A Gare Mu?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Ku Bi Gurbin Annabawa—Mikah
    Hidimarmu Ta Mulki—2014
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 11/15 pp. 10-14

Ta Yaya Za Mu Kasance Da Haƙuri Yayin Da Muke “Jira”?

“Zan jira Allah na cetona.”—MI. 7:7.

MECE CE AMSARKA?

  • Wane darasi ne za mu iya koya daga misalin Mikah?

  • Waɗanne aukuwa ne muke jira mu gani?

  • Ta waɗanne hanyoyi ne za mu iya nuna godiya don haƙurin da Jehobah yake yi?

1. Me zai iya sa mu gaji da jira?

SA’AD DA aka naɗa Yesu Sarki a sama a shekara ta 1914 ne aka shiga kwanaki na ƙarshe. A wannan shekarar ne aka yi yaƙi a sama kuma a sakamako, Yesu ya jefo Shaiɗan da aljanunsa zuwa duniya. (Karanta Ru’ya ta Yohanna 12:7-9.) Shaiɗan ya san cewa “sauran zarafinsa kaɗan ya rage.” (R. Yoh. 12:12) Amma wannan ‘zarafi kaɗan’ ya yi shekaru da yawa yanzu kuma wasu sun ɗauka cewa kwanaki na ƙarshen sun cika daɗewa. Shin mun gaji da jira ne yayin da muke sauraron Jehobah ya ɗauki mataki?

2. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

2 Rashin haƙuri bai da kyau don zai iya sa mu yi garaje. Ta yaya za mu kasance da haƙuri yayin da muke jira? Wannan talifin zai taimaka mana wajen amsa waɗannan tambayoyi uku. (1) Mene ne za mu iya koya daga misalin annabi Mikah? (2) Waɗanne aukuwa ne za su nuna cewa cetonmu ya yi kusa? (3) Ta yaya za mu iya nuna godiya ga haƙurin Jehobah?

MENE NE ZA MU IYA KOYA DAGA MISALIN MIKAH?

3. Yaya yanayin Isra’ilawa yake a zamanin Mikah?

3 Karanta Mikah 7:2-6. A lokacin da mugun Sarki Ahaz yake mulki, annabi Mikah ya ga yadda Isra’ilawa suka ɓata dangantakarsu da Jehobah da kuma yadda yanayinsu ya yi muni sosai. Mikah ya kwatanta Isra’ilawa marasa aminci da “ƙaya” da kuma “shimgen ƙaya.” Kamar yadda ƙaya take raunata duk wanda ya taka ta, waɗannan mugayen Isra’ilawan sukan cutar da duk wanda suka yi harka da shi. Yanayinsu ya yi muni sosai har waɗanda suke cikin iyali ɗaya ba sa ƙaunar juna kuma. Sa’ad da Mikah ya fahimci cewa yanayin ya zama kamar na karen da ya yi nisa da ba ya jin kira, sai ya yi addu’a ga Jehobah da dukan zuciyarsa. Kuma ya zuba ido ya jira lokacin da Allah zai ɗauki mataki. Mikah ya tabbata cewa Jehobah zai ɗauki mataki a lokacin da ya dace.

4. Wane yanayi na baƙin ciki ne muke fuskanta?

4 Kamar Mikah, mu ma muna zama ne tsakanin mutane masu son kai. A yau mutane da yawa “marasa-godiya, marasa-tsarki, marasa-ƙauna irin na tabi’a” ne. (2 Tim. 3:2, 3) Sa’ad da abokan aiki da na makaranta da kuma maƙwabtanmu suka nuna halin son kai, hakan yakan sa mu baƙin ciki. Amma akwai wasu bayin Allah da baƙin cikinsu ya fi namu. Yesu ya ce mabiyansa za su fuskanci hamayya daga iyalinsu kuma ya yi amfani da furucin da ke littafin Mikah 7:6 don ya kwatanta yadda bishara za ta shafi mutane. Ya ce: “Gama na zo domin in haɗa mutum da ubansa, ’ya kuma da uwarta, surukuwa kuma da surukuwatata. Maƙiyan mutum za su kasance daga iyalin gidansa.” (Mat. 10:35, 36) Sa’ad da danginmu da ba Shaidu ba suka yi mana ba’a da hamayya, hakan yakan sa mu baƙin ciki sosai! Idan muna fuskantar irin wannan yanayin daga iyalinmu, kada mu karaya. Maimakon haka, ya kamata mu kasance da aminci kuma mu yi zaman haƙuri yayin da muke jiran lokacin da Jehobah zai daidaita yanayin. Idan muka ci gaba da roƙonsa ya taimake mu, zai tanadar mana da iko da kuma hikimar da muke bukata don mu jure.

5, 6. Ta yaya Jehobah ya albarkaci Mikah, kuma wane annabci ne bai ga cikarsa ba?

5 Jehobah ya albarkaci Mikah don haƙurin da ya nuna. Mikah ya gan ƙarshen mugun Sarki Ahaz da kuma sarautarsa. Yana nan lokacin da ɗan Ahaz, wato Hezekiya ya zama Sarki kuma ya taimaka wa Isra’ilawa su koma bauta ta gaskiya. Ƙari ga haka, Mikah ya shaida cikar annabcin da aka yi game da Samariya sa’ad da Assuriyawa suka mamaye Mulkin Arewaci na Isra’ila.—Mi. 1:6.

6 Amma Mikah bai ga cikar dukan annabcin da Jehobah ya sa shi ya yi ba. Alal misali, Mikah ya rubuta cewa: “A cikin kwanaki na ƙarshe dutsen gidan Ubangiji za ya kafu a bisa ƙwankolin duwatsu, za ya ɗaukaka kuma bisa tuddai; al’ummai za su rugungunto zuwa gareshi. Al’ummai da yawa za su hau, su ce, Ku zo mu hau zuwa dutsen Ubangiji.” (Mi. 4:1, 2) Mikah ya mutu da daɗewa kafin wannan annabcin ya cika. Duk da haka, ya ƙudura niyyar kasancewa da aminci har mutuwarsa ko da yake yana zama cikin mutane marasa aminci. Hakan ya sa Mikah ya rubuta cewa: “Gama dukan ƙabilan mutane za su yi biyayya da sunan allahnsu, mu kuwa za mu yi biyayya da sunan Ubangiji Allahnmu har abada abadin.” (Mi. 4:5) Mikah ya yi zaman jira da haƙuri a wannan lokaci mai wuya don ya tabbata cewa Jehobah zai cika dukan alkawuransa. Wannan annabi mai aminci ya dogara ga Jehobah.

7, 8. (a) Wane dalili ne muke da shi na kasancewa da aminci? (b) Mene ne zai sa ƙarshen ya zo da wuri?

7 Shin muna da irin wannan aminci ga Jehobah? Muna da dalili mai kyau na kasancewa da irin wannan aminci. Mun ga cikar annabcin Mikah. A “kwanakin na ƙarshe” miliyoyin mutane daga dukan al’ummai da ƙabilu da harsuna sun zo “dutsen gidan Ubangiji.” Duk da cewa sun zo daga al’ummai dabam-dabam, waɗannan mutanen sun “buga takubansu su zama garmuna” kuma sun ƙi “koyon yaƙi.” (Mi. 4:3) Gata ne babba mu kasance a cikin mutanen Jehobah masu zaman lafiya!

8 Hakika, muna son Jehobah ya gaggauta kawo ƙarshen wannan mugun zamanin. Amma don mu kasance da haƙuri yayin da muke jira, wajibi ne ra’ayinmu ya jitu da na Jehobah. Ya riga ya sanya ranar da zai yi wa ’yan Adam shari’a kuma ya zaɓi Yesu Kristi a matsayin wanda zai yi hakan. (A. M. 17:31) Amma kafin wannan ranar ta isa, Allah yana ba wa dukan mutane dama su zo ga “sanin gaskiya” kuma su yi rayuwar da ta jitu da abin da suka koya don su sami ceto. Mu tuna cewa rayukan mutane na cikin haɗari. (Karanta 1 Timotawus 2:3, 4.) Idan muka yi amfani da lokacinmu wajen taimaka wa mutane su san ainihin abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa game da Allah, ba za mu san lokacin da ƙarshen zai zo ba. Nan ba da daɗewa ba, lokaci zai kure. Kuma idan ƙarshen ya zo, za mu yi farin ciki cewa mun duƙufa a yin wa’azi game da Mulkin Allah!

WAƊANNE AUKUWA NE ZA SU NUNA CEWA CETONMU YA KUSA?

9-11. Shin 1 Tasalonikawa 5:3 ta cika ne? Ka bayyana.

9 Karanta 1 Tasalonikawa 5:1-3. Nan ba da daɗewa ba, al’ummai za su yi sanarwar “kwanciyar rai da lafiya.” Don kada su yaudare mu da wannan sanarwar, wajibi ne mu “zauna a faɗake, da natsuwa.” (1 Tas. 5:6, Littafi Mai Tsarki) Bari mu tattauna wasu aukuwa da za su sa a yi wannan sanarwa mai muhimmanci.

10 Bayan yaƙin duniya na fari, al’ummai sun biɗi zaman lafiya ruwa a jallo, hakan ma suka yi bayan yaƙin duniya na biyu. An kafa Majalisar Ɗinkin Duniya ta farko bayan yaƙin duniya na ɗaya don tabbatar da zaman lafiya. Bayan yaƙin duniya na biyu kuma, aka ƙafa sabuwar Majalisar Ɗinkin Duniya kuma mutane suka sa rai cewa za ta tabbatar da zaman lafiya a duniya. Gwamnatoci da kuma shugabannin addinai sun dogara ga waɗannan ƙungiyoyi biyu. Alal misali, Majalisar Ɗinkin Duniya ta sanar cewa shekara ta 1986 ce Shekarar Salama na Dukan Ƙasashe. A wannan shekarar, shugabannin addinai da na siyasa sun haɗu da shugaban Cocin Katolika kuma suka yi addu’a don a sami zaman lafiya.

11 Duk da haka, wannan sanarwar zaman lafiya da kuma wasu makamantan ta ba su cika annabcin da aka rubuta a 1 Tasalonikawa 5:3 ba. Me ya sa? Domin “halaka farat” ɗaya da aka annabta ba ta faru ba tukuna.

12. Mene ne muka sani game da sanarwar “kwanciyar rai da lafiya”?

12 Wane ne zai yi wannan sanarwar “kwanciyar rai da lafiya”? Mene ne shugabannin Kiristendom da na wasu addinai za su yi a lokacin? Ta yaya gwamnatocin ƙasashe dabam-dabam za su saka hannu a wannan sanarwar? Littafi Mai Tsarki bai bayyana mana ba. Abin da muka sani shi ne duk yadda za a yi wannan sanarwar da kuma tabbacinta, ba za ta kasance “kwanciyar rai da lafiya” na gaske ba. Shaiɗan zai ci gaba da mulkin duniya. Wannan zamanin ta lalace sosai kuma ba za ta gyaru ba. Zai zama abin baƙin ciki idan muka amince da wannan ƙaryar kuma muka ƙi kasancewa tsakatsaki!

13. Me ya sa mala’iku suka riƙe iskokin halaka?

13 Karanta Ru’ya ta Yohanna 7:1-4. Yayin da muke jiran cikar annabcin da ke 1 Tasalonikawa 5:3, mala’iku masu iko suna riƙe da iskoki huɗu na halaka na ƙunci mai girma. Mene ne suke jira? Manzo Yohanna ya ce sai an buga wa “bayin Allahnmu” wato, shafaffu, hatimi na ƙarshe tukuna.a Muddin an gama buga musu hatimin, mala’ikun za su sake iskokin halaka. Mene ne zai faru a lokacin?

14. Mene ne yake nuna alama cewa ƙarshen Babila Babba ya kusa?

14 Za a halaka Babila Babba, daular addinan ƙarya, kuma hakan ya dace. Muna ganin alama cewa ƙarshenta ya kusa. Kuma sa’ad da hakan ya faru, babu wanda zai iya ceton ta. (R. Yoh. 16:12; 17:15-18; 18:7, 8, 21) Yanzu hakan ma, yadda ake sūkar addinai da shugabannin addinai ta kafofin yaɗa labarai ya nuna cewa jama’a ba sa goyon bayansu kamar dā. Duk da haka, shugabannin addinai suna ganin cewa hakan ba babbar matsala ba ce. Amma wannan tunanin ɓatan basira ne gare su! Bayan sanarwar “kwanciyar rai da lafiya,” gwamnatoci za su kai wa addinan ƙarya hari farat ɗaya kuma su halaka ta gaba ɗaya. Babila Babba ba za ta sake kasancewa ba! Hakika, za mu yi dace domin haƙurin da muke yi don shaida waɗannan muhimman aukuwar.—R. Yoh. 18:8, 10.

TA YAYA ZA MU NUNA CEWA MUNA GODIYA DON HAƘURIN ALLAH?

15. Me ya sa Jehobah yake haƙuri?

15 Duk da cewa mutane sun ɓata sunan Jehobah, ya yi haƙuri don ya ɗauki mataki a lokacin da ya dace. Jehobah ba ya so mai zuciyar kirki ko ɗaya ya halaka. (2 Bit. 3:9, 10) Shin hakan muke ji? Kafin ƙarshen ya zo, za mu iya nuna wa Jehobah cewa muna godiya saboda haƙurinsa ta hanyoyin da aka ambata a gaba.

16, 17. (a) Me ya sa ya kamata mu taimaka wa waɗanda suka yi sanyin gwiwa a ibadarsu? (b) Me ya sa ya kamata mu yi hakan da gaggawa?

16 Ku taimaki waɗanda suka yi sanyi gwiwa a ibadarsu. Yesu ya ce ana murna a sama sa’ad da aka ga tunkiya ɗaya da ta ɓace. (Mat. 18:14; Luk 15:3-7) Jehobah yana kula da waɗanda suke ƙaunar sunansa sosai, ko da ba sa bauta masa da ƙwazo a yanzu. Jehobah da mala’iku suna farin ciki sa’ad da muka taimaka wa mutane su sake soma bauta masa da ƙwazo.

17 Shin kana cikin waɗanda suka yi sanyin gwiwa a bauta wa Jehobah? Wataƙila ka daina zuwa taro ne don wani a cikin ikilisiya ya ɓata maka rai. Kuma mai yiwuwa hakan ya ɗan kwana biyu, ka tambayi kanka: ‘Shin rayuwata tana da ma’ana fiye da dā? Jehobah ne ya ɓata mini rai ko kuma ɗan Adam ajizi? Jehobah Allah ya taɓa cutar da ni ne?’ Hakika, Jehobah yana yi mana alheri a kowane lokaci. Ko da ba ma cika alkawarin da muka yi na bauta masa, yana bari mu mori dukan abubuwa masu kyau da yake tanadarwa. (Yaƙ. 1:16, 17) Ba da daɗewa ba, ranar Jehobah za ta zo. Yanzu ne lokacin da ya kamata mu dawo wurin Ubanmu mai ƙauna, wato Jehobah da kuma cikin ikilisiya don nan ne kawai za mu iya tsira a wannan kwanaki na ƙarshe.

18. Me ya sa ya kamata mu nuna goyon bayanmu ga waɗanda suke mana ja-gora?

18 Ku nuna goyon bayanku ga waɗanda suke ja-gora. A matsayin makiyayi mai ƙauna, Jehobah yana yi mana ja-gora kuma yana kāre mu. Ya naɗa ɗansa ya zama Babban makiyayin garke. (1 Bit. 5:4) Dattawa a cikin ikilisiyoyi fiye da 100,000 suna kula da kowane bawan Allah. (A. M. 20:28) Sa’ad da muka nuna goyon bayanmu ga waɗanda suke mana ja-gora, muna nuna godiyarmu ga Jehobah da kuma Yesu don dukan abubuwan da suka yi mana.

19. Ta yaya za mu zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya?

19 Ku kusaci juna. Mene ne hakan yake nufi? Sa’ad da abokan gaba suka kai wa ƙwararren rundunar sojoji hari, sojojin sukan matso kusa da juna don kada a ci su da yaƙi. Shaiɗan yana daɗa kai wa mutanen Allah hari. Yanzu ba lokacin yin faɗa da ’yan’uwanmu ba ne. Amma lokaci ne da ya kamata mu zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya, mu ƙaunaci ’yan’uwanmu duk da kasawarsu kuma mu dogara ga Jehobah yayin da yake yi mana ja-gora.

20. Mene ne ya kamata mu yi yanzu?

20 Saboda haka, bari mu kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah kuma mu kasance da haƙuri yayin da muke jiran ƙarshen. Bari mu yi haƙuri muna jiran lokacin da za a yi sanarwar “kwanciyar rai da lafiya” da kuma buga wa shafaffu hatimi na ƙarshe. Bayan haka, mala’iku huɗun nan za su sake iskokin halaka, kuma za a halaka Babila Babba. Yayin da muke jiran waɗannan aukuwa masu muhimmanci, bari mu ci gaba da bin umurnin waɗanda aka naɗa su yi mana ja-gora a cikin ƙungiyar Jehobah. Mu kusaci juna don mu iya yin tsayayya da Iblis da kuma aljanu! Yanzu ne lokacin bin shawarar mai zabura, wanda ya ce: “Ku ƙarfafa, bari zuciyarku ta yi gaba gaɗi, dukanku masu-sauraro ga Ubangiji.”—Zab. 31:24.

a Don ƙarin bayani game da bambancin buga wa shafaffu hatimi na farko da kuma na ƙarshe, ka duba Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Janairu, 2007, shafuffuka na 30-31 na Turanci.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba