Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 1/15 pp. 29-31
  • Darussa Daga Littafin Matta

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Darussa Daga Littafin Matta
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “MULKIN SAMA YA KUSA”
  • (Mat. 1:1–20:34)
  • “AM BADA ƊAN MUTUM”
  • (Mat. 21:1–28:20)
  • “Lokaci Ya Yi”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Darussa Daga Littafin Markus
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Darussa Daga Littafin Yohanna
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Darussa Daga Littafin Luka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 1/15 pp. 29-31

Maganar Jehobah Rayayya Ce

Darussa Daga Littafin Matta

MUTUM na farko da ya soma rubuta labari mai daɗi game da hidima da rayuwar Yesu shi ne Matta, abokin Yesu na kud da kud kuma wanda a dā mai karɓan haraji ne. Ainihi an rubuta shi ne a harshen Ibrananci kuma daga baya aka fassara shi zuwa harshen Helenanci, an kammala Linjilar Matta a kusan shekara ta 41 A.Z., kuma shi ne mahaɗa a tsakanin Nassosin Ibrananci da Nassosin Kirista na Helenanci.

Domin an rubuta shi ne ainihi ga Yahudawa, wannan Linjila mai ma’ana ta nuna cewa Yesu shi ne Almasihun da aka yi alkawarinsa, kuma shi Ɗan Allah ne. Idan muka mai da hankali sosai ga saƙon da ke cikinta, hakan zai ƙarfafa bangaskiyarmu ga Allah na gaskiya, da Ɗansa, da kuma alkawuransa.—Ibran. 4:12.

“MULKIN SAMA YA KUSA”

(Mat. 1:1–20:34)

Matta ya tattauna jigon Mulki da kuma koyarwar Yesu, duk da cewa yin hakan na nufin ƙin manne wa jerin bayanai na yadda abubuwa suka faru. Alal misali, an ambata Huɗuba Bisa Dutse ne a farkon littafin, duk da cewa Yesu ya faɗi huɗubar ne a kusan rabin hidimarsa.

A lokacin da yake hidima a Galili, Yesu ya yi mu’ujizai, ya ba manzanninsa guda goma sha biyu umurni game da hidima, ya la’anci Farisawa, kuma ya ba da kwatanci game da Mulki. Bayan haka, ya bar Galili kuma ya tafi “cikin ƙasar Yahudiya, ƙetaren Urdun.” (Mat. 19:1) Sa’ad da suke kan hanya, Yesu ya gaya wa almajiransa: ‘Za mu Urushalima; kuma Ɗan mutum za a hukumta masa mutuwa, a rana ta uku kuma za a tashe shi.’—Mat. 20:18, 19.

Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:

3:16—Ta yaya ne ‘sammai suka buɗe’ a lokacin baftismar Yesu? Kamar dai hakan na nufin cewa Yesu ya tuna abubuwan da ya sani kafin ya zo duniya.

5:21, 22—Nuna fushi ya fi riƙewa a zuciya tsanani ne? Yesu ya yi gargaɗi cewa duk mutumin da ya ci gaba da riƙe ɗan’uwansa a zuciya yana mugun zunubi. Amma, nuna fushi ta wajen faɗin kalmar wulakanci ya fi tsanani, hakan yana sa mutum ya ba da lissafi a kotu da ya fi girma da kotu na ’yan adam.

5:48—Zai yiwu mu zama “cikakku, kamar yadda Uban[mu] na sama cikakke ne”? E, a wata hanya. A nan Yesu yana tattauna game da ƙauna, kuma ya gaya wa masu sauraronsa su yi koyi da Allah kuma su zama cikakku wajen nuna ƙauna. (Mat. 5:43-47) Ta yaya? Ta wajen nuna wa magabtansu ƙauna.

7:16—Waɗanne “ya’ya” ne ke sa a san addini na gaskiya? Waɗannan ’ya’yan ba halayenmu ba ne kawai. Sun haɗa da imaninmu, wato, koyarwa da muke bi.

10:34-38—Saƙon Nassi yana kawo jayayya tsakanin iyali ne? A’a. Maimakon haka, matakin da marasa bi da suke cikin iyali suka ɗauka ne ke kawo jayayya. Suna iya zaɓa su ƙi ko su yi hamayya da Kiristanci, ta hakan su kawo rabuwa cikin iyalin.—Luka 12:51-53.

11:2-6—Idan saboda muryar Allah na amincewa da ya ji ya sa Yohanna ya san cewa Yesu ne Almasihu, me ya sa ya yi tambaya ko Yesu ne “mai-zuwan nan”? Wataƙila Yohanna ya yi wannan tambayar ne don ya ji daga bakin Yesu. Ban da haka, Yohanna yana son ya san ko akwai “wani” da zai zo da ikon Mulki kuma ya biya dukan bukatun Yahudawa. Amsar Yesu ta nuna cewa ba za a samu magaji ba.

19:28—Menene “ƙabilan goma sha biyu na Isra’ila” da za a yi wa shari’a yake wakilta? Ba ta wakiltan ƙabilu goma sha biyu na Isra’ila na ruhaniya. (Gal. 6:16; R. Yoh. 7:4-8) Manzanni da Yesu yake gaya wa za su zama sashe na Isra’ila ta ruhaniya, ba masu shari’ar waɗanda ke cikinta ba. Yesu ya yi ‘musu alkawarin mulki,’ kuma za su zama ‘mulki da firistoci ga Allah.’ (Luk 22:28-30; R. Yoh. 5:10) Waɗanda suke cikin Isra’ila na ruhaniya za su “yi ma duniya shari’a.” (1 Kor. 6:2) Saboda haka, “ƙabilan goma sha biyu na Isra’ila,” da waɗanda suke kursiyi na samaniya za su yi wa shari’a, suna wakiltar duniyar ’yan adam da ba sa cikin rukunin sarauta, da firistoci kamar yadda ƙabilu goma sha biyu na Ranar Kafara ke nunawa.—Lev., sura 16.

Darussa Dominmu:

4:1-10. Wannan labarin ya koya mana cewa Shaiɗan mutum ne na gaskiya ba halin mugunta ba. Yana amfani da “kwaɗayin jiki, da sha’awar idanu, da darajar rai ta wofi” don ya jarraba mu. Duk da haka, bin mizanan da ke cikin Nassi zai taimaka mana mu kasance da aminci ga Allah.—1 Yoh. 2:16.

5:1–7:29. Ka ci gaba da lura da bukatarka ta ruhaniya. Ka kasance mai haƙuri. Ka guji yin tunanin banza. Ka kasance mai cika alkawari. Sa’ad da ka ke yin addu’a, ka fi mai da hankali ga abubuwa na ruhaniya fiye da abin duniya. Ka kasance mawadaci ga Allah. Ka fara biɗar Mulkin Allah da adalcinsa. Kada ka sūki mutane. Ka yi nufin Allah. Waɗannan darussa ne masu kyau da suke cikin Huɗuba Bisa Dutse!

9:37, 38. Ya kamata mu aikata daidai da roƙonmu ga Ubangiji na ‘aika ma’aikata cikin girbinsa,’ ta wajen nuna ƙwazo a aikin almajirantarwa.—Mat. 28:19, 20.

10:32, 33. Kada mu ji tsoron yin magana game da bangaskiyarmu.

13:51, 52. Fahimtar gaskiyar Mulki yana kawo hakkin koyar da mutane da kuma taimakonsu su fahimci wannan muhimmiyar gaskiya.

14:12, 13, 23. Ya dace mutum ya yi bimbini mai kyau lokacin da ya kasance shi kaɗai.—Markus 6:46; Luka 6:12.

17:20. Muna bukatar bangaskiya don mu sha kan tangarɗa masu kama da babban dutse da ke hana mu ci gaba a ruhaniya da kuma jimre wa matsaloli. Ya kamata mu mai da hankali mu ƙarfafa bangaskiyarmu ga Jehobah da kuma alkawuransa.—Markus 11:23; Luka 17:6.

18:1-4; 20:20-28. Ajizancin ’yan adam da kuma addinin da suke bi da ke ɗaukaka matsayi ya sa almajiran Yesu su damu ainu game da yin suna. Ya kamata mu kasance da tawali’u yayin da muke mai da hankali da muradi na yin zunubi kuma mu kasance da ra’ayin da ya dace game da gata da kuma hakki.

“AM BADA ƊAN MUTUM”

(Mat. 21:1–28:20)

Yesu ya zo Urushalima a ranar 9 ga Nisan na shekara ta 33 A.Z., a “bisa kan jaki.” (Mat. 21:5) Washegari, ya shiga cikin haikali kuma ya tsarkake shi. A ranar 11 ga Nisan, ya koyar a cikin haikali, ya hukunta marubuta da Farisawa, kuma bayan haka ya ba almajiransa “alamar zuwan[sa] da cikar zamani.” (Mat. 24:3) Washegari kuma ya gaya musu: “Kun sani bayan kwana biyu sai paska, am bada Ɗan mutum kuma domin a giciye shi.”—Mat. 26:1, 2.

A ranar 14 ga Nisan, bayan ya kafa Tuna mutuwarsa da ta yi kusa, aka ci amanar Yesu, aka kama shi, aka yi masa gwaji, kuma aka rataye shi. A rana ta uku aka ta da shi daga matattu. Kafin ya hau sama, Yesu da aka ta da daga matattu, ya ba mabiyansa umurni: “Ku tafi fa, ku almajirtadda dukan al’ummai.”—Mat. 28:19.

Tambayoyin Nassi da aka Amsa:

22:3, 4, 9—Yaushe ne aka yi gayyata sau uku na zuwa bikin aure? An yi gayyata na farko don a tattara ajin amarya sa’ad da Yesu da mabiyansa suka soma wa’azi a shekara ta 29 A.Z., kuma hakan ya ci gaba har shekara ta 33 A.Z. An yi na biyu daga lokacin da aka zuba wa almajirai ruhu mai tsarki a ranar Fentakos na shekara ta 33 A.Z., zuwa 36 A.Z. Yahudawa, shigaggu Yahudawa, da Samariyawa ne kaɗai aka yi wa waɗannan gayyatar. Amma, an kai gayyata na uku ga mutane da ke kan hanya waje da birnin, wato, ’Yan Al’ummai, an fara hakan daga shekara ta 36 A.Z., sa’ad da Karniliyus, hafsa na Roma ya tuba kuma aka ci gaba da yin haka har zamaninmu.

23:15—Me ya sa shigagge na Farisawa ya zama “ɗan Jahannama fiye da . . . har so biyu” kamar Farisawa da kansu? Wasu da suka zama shigaggu na Farisawa wataƙila a dā masu zunubi ne sosai. Ta wajen koma bin addinin Farisawa, suka fi malamansu da aka hukunta mugunta. Da haka suka zama ‘’ya’yan Jahannama,’ fiye da Yahudawa Farisawa.

27:3-5—A kan menene Yahuda ya yi nadama? Babu abin da ya nuna cewa nadamar da Yahuda ya yi tuba na gaske ne. Maimakon ya nemi gafara daga wajen Allah, sai ya faɗi zunubinsa ga manyan Firistoci da dattawa. Bayan ya yi “zunubi wanda ya kai ga mutuwa,” Yahuda ya yi baƙin ciki sosai saboda laifin da ya yi. (1 Yoh. 5:16) Ya yi nadama domin yanayin rashin bege da yake ciki.

Darussa Dominmu:

21:28-31. Abin da ainihi Jehobah yake ɗauka da muhimmanci shi ne mu yi nufinsa. Alal misali, mu yi himma a wajen yin shelar Mulki da almajirantarwa.—Mat. 24:14; 28:19, 20.

22:37-39. Dokoki biyu mafi girma ya takaita abin da Allah yake bukata daga wurin waɗanda suke bauta masa.

[Hoto a shafi na 31]

Kana da himma a wajen yin aikin girbi kuwa?

[Inda aka Dauko]

© 2003 BiblePlaces.com

[Hoto a shafi na 31]

Matta ya nanata jigon Mulkin

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba