Ka Sa Ci Gabanka Ya Bayyana
“Ka yi ƙwazo cikin waɗannan al’amura; ka bada kanka garesu sosai; domin cigabanka ya bayyanu ga kowa.”—1 TIMOTHAWUS 4:15.
1. Yaya za ka iya sanin cewa ’ya’yan itace ya nuna kuma ya dace a ci?
KA ZANA hoton zuci a zuciyarka na ’ya’yan itace da ka fi so—lemo, goba, mangwaro, ko kuma wani abu. Za ka iya sanin sa’ad da ya nuna kuma ya dace a ci? Babu shakka. Ƙanshin ’ya’yan itacen, launi, jikin duka, suna gaya maka cewa abu mai daɗi yana jiranka. Muddin ka gutsura, za ka iya jan numfashi na gamsuwa. Abu mai ɗanɗano! Kai, da zaƙi! Kana jin daɗinsa ƙwarai.
2. Yaya ake sanin mutum ya manyanta, yaya yake shafan dangantaka?
2 Wannan labarin mai sauƙi amma mai daɗi ya yi daidai da wasu fannoni a rayuwa. Alal misali, yadda yake da ’ya’yan itace da ya nuna, ana ganin mutum da ya manyanta a ruhaniya a hanyoyi dabam dabam. Muna gane cewa mutum ya manyanta in mun ga fahimi, basira, hikima da sauransu. (Ayuba 32:7-9) Babu shakka, abin farin ciki ne mu yi tarayya kuma mu yi aiki da mutane da suke nuna irin halayen nan da kuma ayyukansu.—Misalai 13:20.
3. Menene kwatancin Yesu na mutanen zamaninsa ya bayyana game da manyantaka?
3 A wata sassa, mutum zai manyanta a zahiri, amma yadda yake magana da kuma halinsa zai iya bayyana cewa bai manyanta ba a jiye-jiye da kuma a ruhaniya. Alal misali, da yake magana game da tsara masu taurin kai na zamaninsa, Yesu Kristi ya ce: “Gama Yohanna ya zo, ba da ci ba, ba da sha ba, suna kuwa cewa, Yana da aljan. Ɗan mutum ya zo, yana ci yana sha, suna kuwa cewa, Ga mutum mai-zarin ci, mai-zarin sha.” Ko da waɗancan mutane sun manyanta a zahiri, Yesu ya ce sun yi abubuwa kamar “yara”—ba su manyanta ba. Da haka, ya daɗa: “Hikima kuwa ta barata bisa ga ayyukanta.”—Matta 11:16-19.
4. A waɗanne hanyoyi ne ci gaba da manyantaka suke bayyana?
4 Daga kalmomin Yesu, za mu iya ganin cewa ko mutum yana da hikima ta gaske—alama ta manyantaka—ana ganinta ta ayyuka da yake yi da kuma sakamakonsu. Game da wannan, ka lura da gargaɗin manzo Bulus ga Timothawus. Bayan ya lissafa abubuwa da Timothawus zai biɗa, Bulus ya ce: “Ka yi ƙwazo cikin waɗannan al’amura; ka bada kanka garesu sosai; domin cigabanka ya bayyanu ga kowa.” (1 Timothawus 4:15) Hakika ci gaban Kirista zuwa manyantaka yana ‘bayyane,’ ko kuma ana gane shi sarai. Manyantaka ta Kirista, kamar haske da yake haskakawa, ba hali ba ne da ba a ganewa ko kuma ake ɓoyewa. (Matta 5:14-16) Saboda haka, za mu bincika hanyoyi biyu na musamman da ci gaba da manyantaka za su bayyana: (1) ƙaruwa a sani, fahimi, da hikima; (2) nuna ɗiyan ruhu.
Ɗayantuwar Imani da Sani
5. Yaya za a ba da ma’anar manyanta?
5 Yawancin ƙamus sun kwatanta manyanta yanayin cikakke, yin dattako, kai yanayi na ƙarshe ko kuma mizani da ake so. ’Yar itace, yadda aka ambata da farko, ya isa, ko nuna, lokacin da ya gama girma da yadda ya bayyana, launi, ƙanshi, da ɗanɗano sun kai abin da ake so. Saboda haka, manyantaka na da ma’ana ɗaya da, gwanin kyau, cikakke, har ma kamilta.—Ishaya 18:5; Matta 5:45-48; Yaƙub 1:4.
6, 7. (a) Menene ya nuna cewa Jehovah yana son duka masu bauta masa su ci gaba zuwa manyantaka ta ruhaniya? (b) Ga menene manyantaka na ruhaniya ke da dangantaka ta kusa?
6 Jehovah Allah yana son duka masu bauta masa su ci gaba zuwa manyantaka ta ruhaniya. Don a cim ma wannan, ya ba da kyauta mai girma ga ikilisiyar Kirista. Zuwa ga Kiristoci a Afisus, manzo Bulus ya rubuta: “Ya kuma bada waɗansu su zama manzanni; waɗansu, annabawa; waɗansu, masu-wa’azin bishara; waɗansu, makiyaya da masu-koyarwa; domin kamaltawar tsarkaka, domin aikin hidima, domin ginin jikin Kristi: har dukanmu mu kai zuwa ɗayantuwar imani da sanin Ɗan Allah, zuwa cikakken mutum, zuwa misalin tsawon cikar Kristi: kada nan gaba mu zama yara, waɗanda ana wofadda su suna shillo ga kowacce iskan sanarwa, ta wurin wawa-idon mutane masu-gwaninta zuwa makidar saɓo.”—Afisawa 4:11-14.
7 A cikin waɗannan ayoyi, Bulus ya bayyana cewa cikin dalilai da sun sa Allah ya yi wannan tanadi na ruhaniya cikin ikilisiya shi ne duka su ‘kai zuwa ɗayantuwar bangaskiya da cikakken sani,’ “cikakken mutum,” kuma su kasance da “misalin tsawon Kristi.” Sa’annan ne kawai ba za a jujjuya mu ba kamar yara a ruhaniya ta ra’ayoyin ƙarya da koyarwa. Da haka muna ganin dangantaka ta kusa tsakanin ci gaba zuwa manyantaka ta Kirista da samun “ɗayantuwar imani da sanin Ɗan Allah.” Akwai darussa da yawa cikin gargaɗi da Bulus ya bayar da zai yi kyau mu yi biyayya da shi.
8. Menene “ɗayantuwar” bangaskiya da cikakken sani suke bukata?
8 Na farko, da yake za a kiyaye “ɗayantuwa,” Kirista da ya manyanta dole ya kasance da haɗin kai da jituwa da ’yan’uwa masu bi a batun bangaskiya da sani. Ba ya goyon baya ko kuma nacewa a kan ra’ayoyin kansa ko kuma ya riƙe ra’ayoyinsa yayin da ya zo ga fahimtar Littafi Mai Tsarki. Maimako, yana da cikakken gaba gaɗi cikin gaskiyar yadda Jehovah Allah da Ɗansa, Yesu Kristi da “bawan nan mai-aminci, mai-hikima,” suka bayyana ta. Ta cin abinci na ruhaniya da ake tanadinsa a kai a kai “a lotonsa”—ta wurin littattafai na Kirista, taro, manyan taro, da taron gunduma—za mu tabbata cewa za mu riƙe ‘ɗayantuwa’ da Kiristoci ’yan’uwa cikin bangaskiya da sani.—Matta 24:45.
9. Ka bayyana ma’anar furcin nan “imani” yadda Bulus ya yi amfani da shi cikin wasiƙarsa zuwa ga Afisawa.
9 Na biyu, furcin nan “imani” yana nuni ne ga abin da muka gaskata gabaki ɗaya “fāɗin da ratar da tsawon da zurfin,” ba tabbaci da kowanne Kirista yake da shi ba. (Afisawa 3:18; 4:5; Kolossiyawa 1:23; 2:7) Hakika, yaya Kirista zai kasance cikin ɗayantuwa da ’yan’uwa masu bi idan ya gaskata ko kuma amince da wasu sashen “imani” kawai? Wannan yana nufin cewa bai kamata mu gamsu kawai ba da sanin muhimman koyarwa na Littafi Mai Tsarki ko kuma mu kasance da ɗan fahimtar gaskiyar. Maimako, za mu so mu yi amfani da dukan tanadi da Jehovah yake yi ta ƙungiyarsa mu yi bincike sosai cikin Kalmarsa. Dole ne mu yi ƙoƙari mu samu cikakke fahimin nufin Allah da ƙudurinsa yadda zai yiwu. Wannan ya haɗa da ba da lokaci a karatu da nazarin Littafi Mai Tsarki da littattafan Littafi Mai Tsarki, yin addu’a ga Allah don taimakonsa da ja-gora, halartar taron Kirista a kai a kai, da sa hannu sosai cikin aikin wa’azin Mulki da aikin almajirantarwa.—Misalai 2:1-5.
10. Menene ma’anar furcin nan “har dukanmu mu kai,” yadda aka yi amfani da shi a Afisawa 4:13?
10 Na uku, Bulus ya fara kwatancin makasudi da ke kashi uku da kalmomin nan “har dukanmu mu kai.” Game da furcin nan “dukanmu,” wani littafi na Littafi Mai Tsarki ya ba da ma’anar “ba jam’i ba, ɗai-ɗai, dabam dabam, amma tare.” Watau, kowannenmu ya kamata ya yi ƙoƙari ya biɗi makasudi na manyantaka ta Kirista tare da ’yan’uwanci duka. The Interpreter’s Bible ya ce: “Mutum ba ya ci gaba a ruhaniya ta ware kansa daga wasu, yadda bangare ɗaya a jiki ba zai yi girma ba sai dai dukan jiki ya ci gaba da girma sosai.” Bulus ya tunasar da Kiristoci na Afisus cewa “tare da dukan tsarkaka” ya kamata su yi ƙoƙari su fahimci ma’anar imani gabaki ɗaya.—Afisawa 3:18a.
11. (a) Menene ci gaba a ruhaniya ba ta nufi? (b) Menene muke bukata mu yi don mu ci gaba?
11 A bayyane yake daga kalmomin Bulus cewa ci gaba a ruhaniya ba ya nufin kawai cika zuciyarmu da ilimi da yawan karatu. Kirista da ya manyanta ba wanda yake nuna wa wasu yana da ilimi ba ne. Maimakon haka, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Tafarkin mai-adalci yana kama da haske na ketowar alfijir, wanda ya ke haskakawa gaba gaba har zuwa cikakkiyar rana.” (Misalai 4:18) Hakika, “tafarkin” ne, ba mutumin ba ke “haskakawa gaba gaba.” Idan mun yi ƙoƙari sosai mu ci gaba da fahimi na Kalmar Allah da ke haskakawa da Jehovah yake ba mutanensa, za mu ci gaba a ruhaniya. A wannan yanayin, a ci gaba yana nufin a yi gaba gaba, kuma abu ne da dukanmu za mu iya yi.—Zabura 97:11; 119:105.
Ka Nuna “Ɗiyan Ruhu”
12. Me ya sa nuna ɗiyan ruhu yake da muhimmanci a son mu ci gaba a ruhaniya?
12 Yayin da samun ‘ɗayantuwar imani da cikakken sani’ yana da muhimmanci, yana da muhimmanci kuma mu nuna ɗiyan ruhun Allah a kowanne fanni na rayuwarmu. Me ya sa? Wannan domin manyanta, yadda muka gani, ba abin da yake ciki ba ne ko a ɓoye, amma ana iya gane shi sarai ta halaye da zai amfani wasu kuma ya gina su. Dama fa, son mu ci gaba a ruhaniya ba kawai ƙoƙarin kwaikwayon halaye da aka koya ba ne. Maimako, yayin da muke girma a ruhaniya, muna bin ja-gora na ruhu mai tsarki, za a ga halayenmu da ayyukanmu sun juya a hanya ta ban mamaki. “Ku yi tafiya bisa ga Ruhu, ba kuwa za ku biya sha’awar jiki ba,” in ji manzo Bulus.—Galatiyawa 5:16.
13. Wane canji ne alamar ci gaba?
13 Bulus ya ci gaba da lissafa “ayyukan jiki,” da suke da yawa kuma a “bayyane.” Kafin mutum ya kai gane amfanin farillan Allah, rayuwarsa lallai tana bin tsari na duniya kuma ƙila yana yin wasu abubuwa da Bulus ya ambata: “Fasikanci ke nan, ƙazanta, lalata, bautar gumaka, sihiri, magabtaka, husuma, kishe-kishe, hasala, tsatsaguwa, rabuwa, hamiya, hassada, maye, nishatsi da irin waɗannan al’amura.” (Galatiyawa 5:19-21) Amma yayin da mutumin yake ci gaba a ruhaniya, a hankali zai sha kan waɗannan munanan “ayyukan jiki” ya sake su da “ɗiyan ruhu.” Wannan canjin a zahiri alama ce cewa mutumin yana ci gaba zuwa manyantaka ta Kirista.—Galatiyawa 5:22.
14. Ka yi bayani a kan furci biyun nan “ayyukan jiki” da “ɗiyan ruhu.”
14 Ya kamata mu lura da furci biyun nan “ayyukan jiki” da “ɗiyan ruhu.” “Ayyuka” sakamakon abin da mutum yake yi ne. A wasu kalmomi, abubuwan da Bulus ya lissafa ayyukan jiki sakamako ne na zaɓe da mutum ya yi da gangan ko kuma rinjayar jiki na zunubi. (Romawa 1:24, 28; 7:21-25) A wata sassa, furcin nan “ɗiyan ruhu,” yana nufin cewa halaye da aka lissafa ba don ƙoƙarce-ƙoƙarce na koyar wani hali ko kuma gyara a mutumtaka ba ne, amma sakamakon aikin ruhun Allah ne a kan mutumin. Yadda itace zai ba da ’ya’ya idan an kula da shi sosai, hakanan mutum zai nuna ɗiyan ruhu lokacin da ruhu mai tsarki yake aiki sosai a rayuwarsa.—Zabura 1:1-3.
15. Me ya sa yake da muhimmanci a mai da hankali ga duka fannoni na “ɗiyan ruhu”?
15 Wani darasi da za a bincika shi ne yadda Bulus ya yi amfani da wannan kalmar “ɗiyan” da ya haɗa duka inganci masu kyau da ya ambata.a Ruhu ba ya ba da ’ya’ya dabam dabam don mu zaɓa wanda muka fi so ba. Duka inganci da Bulus ya lissafa—ƙauna, farin ciki, salama, tsawon jimrewa, nasiha, nagarta, aminci, tawali’u, da kamewa—suna da muhimmanci, kuma a tare suna sa mutum ya samu sabon hali na Kirista. (Afisawa 4:24; Kolossiyawa 3:10) Saboda haka, yayin da muka ga cewa wasu cikin waɗannan inganci suna a bayyane a rayuwarmu don mutumtakarmu da halinmu, yana da muhimmanci mu mai da hankali ga duka fannoni da Bulus ya ambata. Ta yin haka, za mu fi nuna hali irin na Kristi a rayuwarmu.—1 Bitrus 2:12, 21.
16. Menene manufarmu a biɗan manyantaka ta Kirista, kuma yaya za a cim ma wannan?
16 Muhimmin darasi da za mu iya koya daga maganar Bulus shi ne cewa a biɗan manyantaka ta Kirista, manufarmu ba samun yawan ilimi da koyo ko kuma koyan mutumtaka da aka gyara ba ne. Don ruhun Allah yana aiki ne a rayuwarmu. Har yadda muke tunani da ayyukanmu ya bi ja-gorar ruhun Allah, har ya sa mu manyanta a ruhaniya. Yaya za mu cim ma wannan manufar? Dole ne mu buɗe zuciyarmu da azancinmu ga tasiri na ruhun Allah. Wannan ya ƙunshi muna halartar taro a kai a kai da yin furci a taron Kirista. Ya kamata muna yin nazari a kai a kai da yin bimbini a kan Kalmar Allah, muna barin ƙa’idodinta su ja-goranci sha’aninmu da wasu zaɓe da shawarwari da muke yi. Sa’annan babu shakka ci gabanmu zai bayyana sarai.
Ka Ci Gaba don Ka Ɗaukaka Allah
17. Ta yaya ci gaba ta haɗa da ɗaukaka Ubanmu na samaniya?
17 Duka dai, sa ci gabanmu ta bayyana yana kawo ɗaukaka da yabo, ba gare mu ba, amma ga Ubanmu na samaniya, Jehovah, wanda ya sa ya yiwu mu manyanta a ruhaniya. Daddare kafin a kashe Yesu, ya gaya wa almajiransa: “Inda a ke ɗaukaka Ubana ke nan, ku bada ’ya’ya dayawa; hakanan kuma za ku zama almajiraina.” (Yohanna 15:8) Ta ɗiyan ruhu da ta ’ya’yan Mulki na hidimarsu, almajiran suka ɗaukaka Jehovah.—Ayukan Manzanni 11:4, 18; 13:48.
18. (a) Wane girbi na farin ciki ne ake yi a yau? (b) Wane kalubale wannan girbi yake kawowa?
18 A yau, albarkar Jehovah na kan mutanensa yayin da suke sa hannu cikin girbi na ruhaniya na dukan duniya. Shekaru da yawa yanzu, misalin sababbi 300,000 kowacce shekara suna keɓe kansu ga Jehovah kuma nuna alamar keɓe kansu ta baftisma cikin ruwa. Wannan yana sa mu farin ciki kuma babu shakka yana faranta wa Jehovah rai. (Misalai 27:11) Amma, don wannan ya ci gaba da zama tushen farin ciki da kuma yabo ga Jehovah, sababbin nan suna bukata su “yi tafiya a cikinsa [Kristi] hakanan, dasassu, ginannu kuma cikinsa, kafaffu cikin bangaskiyar[su].” (Kolossiyawa 2:6, 7) Wannan ya kawo kalubale kashi biyu ga mutanen Allah. A ɓangare ɗaya, idan kai sabo ne da yin baftisma, za ka fuskanci kalubale na sa “cigabanka ya bayyanu ga kowa”? A wata sassa, idan kana cikin gaskiya da daɗewa, za ka fuskanci kalubale ka ɗauki hakki na kula da lafiya ta ruhaniya na sababbi? Ko yaya dai, bukatar ci gaba zuwa manyantaka na bayyane.—Filibbiyawa 3:16; Ibraniyawa 6:1.
19. Wace gata da albarka za su zama naka idan ka sa ci gabanka ya bayyana?
19 Albarka mai girma na jiran duka da suke aiki tuƙuru su sa ci gabansu ta bayyana. Ka tuna kalmomi masu ban ƙarfafa na Bulus bayan ya aririci Timothawus ya ci gaba: “Ka maida hankali da kanka, da kuma koyarwarka. Ka lizima cikin waɗannan; gama garin yin wannan za ka ceci kanka duk da masu-jinka.” (1 Timothawus 4:16) Ta sa ci gabanka ya bayyana da ƙwazo, kai ma za ka sa hannu cikin gatar ɗaukaka sunan Allah da morar albarkarsa.
[Hasiya]
a Kalmar nan “ɗiyan” na nufin “ ’ya’ya” ne a yare na asali.— Galatiyawa 5:22, Kingdom Interlinear Translation.
Ka Tuna?
• A waɗanne hanyoyi ne za a bayyana manyantaka ta ruhaniya?
• Wane irin sani da fahimi ke nuna manyantaka?
• Ta yaya nuna “ɗiyan ruhu” ke nuna ci gaba a ruhaniya?
• Wane kalubale ya kamata mu samu yayin da muke ci gaba zuwa manyantaka?
[Hoto a shafi na 25]
Nunanne, ko manyantaka, ana gane su sarai
[Hoto a shafi na 27]
Muna ci gaba a ruhaniya ta bin gaskiyar da aka bayyana
[Hotuna a shafi na 29]
Addu’a tana taimaka mana mu nuna “ɗiyan ruhu”