Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb17 Disamba p. 5
  • Wani Sabon Fasali a Taron Tsakiyar Mako

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Wani Sabon Fasali a Taron Tsakiyar Mako
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2017
  • Makamantan Littattafai
  • Jehobah Yana Daraja “Amin” da Muka Furta
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2017
mwb17 Disamba p. 5
Littafin Matta a cikin New World Translation of the Holy Scriptures na nazari

RAYUWAR KIRISTA

Wani Sabon Fasali a Taron Tsakiyar Mako

Daga watan Janairu na 2018, za a riƙa tattauna ƙarin bayanai da hotuna da kuma bidiyoyin da ke New World Translation of the Holy Scriptures na nazari (nwtsty). Za ku riƙa amfani da shi ko da ba ku da Littafi Mai Tsarkin a yarenku. Babu shakka, wannan bayanin zai sa ku amfana sosai sa’ad da kuke shirya taro. Mafi muhimmanci ma, muna fatan zai sa ku kusaci Ubanmu mai ƙauna da ke sama, wato Jehobah!

ƘARIN BAYANAI DON NAZARI

Wannan tanadin na ba da ƙarin bayani game da al’adu da yankuna da kuma harsunan da ke ayoyi dabam-dabam na Littafi Mai Tsarki.

Matta 12:20

Atafa mai-hayaƙi: Fitila ce da aka yi da laƙa kuma ana saka mān zaitun a ciki. Atafar, wato lagwanin ne ake cinna wa wuta. Furucin nan Atafa mai-hayaƙi a Helenanci na iya nufin lagwanin da ke hayaƙi saboda akwai garwashi a jikinsa amma wutar ta kusan mutuwa ko kuma ta riga ta mutu. Annabcin da ke Ishaya 42:3 ya nuna cewa Yesu zai zama mai tausayi sosai, ya ce ba za ya ɓice, wato kashe begen da talakawa suke da shi ba.

Matta 26:13

Hakika: A·menʹ furucin Helenanci ne da aka samo daga ʼa·menʹ a Ibrananci, kuma yana nufin “amin” ko “ya kasance haka.” Yesu yana yawan amfani da shi sa’ad da yake magana don ya nuna cewa abin da ya faɗa gaskiya ne. An ce furucin nan “hakika” ko amin da Yesu ya yi amfani da shi yana da muhimmanci sosai. Idan an maimaita furucin fiye da sau ɗaya, wato (a·menʹ a·menʹ) kamar yadda yake a Linjilar Yohanna, ana rubuta “hakika, hakika” a Hausa.​—Yoh 1:51.

HOTUNA DA BIDIYO

Hotuna da zane-zane da kuma bidiyoyin da babu sauti suna ba da ƙarin haske a kan bayanan da ke Littafi Mai Tsarki.

Baitfaji, Dutsen Zaitun, da Urushalima

Wannan gajeren bidiyon ya nuna hanyar da ke kusa da Urushalima ta gabashin birnin, daga ƙauyen et-Tur a yau wanda aka ce shi ne Baitfaji a Littafi Mai Tsarki. Wannan wurin ne ya fi tsayi a Dutsen Zaitun. Bait’anya yana gabashin Baitfaji a gangaren Dutsen Zaitun. Sa’ad da Yesu yake Urushalima, shi da almajiransa suna yawan kwana a Bait’anya, wanda a yau ake kiran el-ʽAzariyeh (El ʽEizariya). Wannan sunan Larabci ne da ke nufin “Wurin Su Li’azaru.” Babu shakka, Yesu ya zauna a gidan su Martha da Maryamu da kuma Li’azaru. (Mt 21:17; Mk 11:11; Lu 21:37; Yoh 11:⁠1) Sa’ad da yake zuwa Urushalima daga gidan su Li’azaru, wataƙila yana bin hanyar da aka nuna a wannan bidiyon. Sa’ad da Yesu ya hau jaki a Dutsen Zaitun zuwa Urushalima a ranar 9 ga Nisan, shekara ta 33, wataƙila ya bi wannan hanyar daga Baitfaji zuwa Urushalima.

Hanyar da watakila Yesu ya bi daga Bait’anya zuwa Urushalima
  1. Hanya daga Baitfaji zuwa Bait’anya

  2. Baitfaji

  3. Dutsen Zaitun

  4. Kwarin Kidron

  5. Dutsen Haikalin

Ƙusa a Ƙashin Sawun Wani

An kafa wata kusa a sawun wani mutum

Wannan hoton ƙashin sawun wani ne da aka kafa wa ƙusa mai tsawon inci 4 da ɗigo 5. An samo ƙashin a shekara ta 1968, sa’ad da ake tone-tonen ƙasa a arewacin Urushalima. An ce ƙashin na tun zamanin Romawa ne. Hakan ya sa mu kasance da tabbaci cewa wataƙila ana kafa wa mutanen da aka kashe a kan gungume ƙusa. Wannan ƙusar ta yi kama da wanda sojojin Roma suka kafa wa Yesu a kan gungume. An samo ƙashin a wani akwatin da ake saka ƙasusuwan gawar da ta ruɓe. Hakan ya nuna cewa ana iya binne mutumin da aka kashe a kan gungume.​—Mt 27:35.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba