Ka Yi Koyi Da Yesu Ka Bauta Wa Allah Yadda Yake So
Allah ya gayyaci mutane “daga cikin kowane iri, da dukan kabilai da al’ummai da harsuna” su bauta masa. (R. Yoh. 7:9, 10; 15:3, 4) Waɗanda suka karɓi wannan gayya za su “dubi jamalin Ubangiji.” (Zab. 27:4; 90:17) Kamar mai zabura, sun ta da muryarsu suna yabon Allah suna cewa: “Mu yi sujjada mu yi ruku’u, mu durƙusa a gaban Ubangiji Mahaliccinmu.”—Zab. 95:6.
Bautar da Jehobah Yake So Sosai
A matsayinsa na maɗaukakin Ɗan Allah, Yesu yana da zarafin koyan ra’ayin Ubansa, ka’idodinsa da kuma mizanansa. Hakika, Yesu ya nuna wa mutane yadda za su bauta wa Allah. Ya ce: “Ni ne hanya, Ni ne gaskiya, Ni ne rai: ba mai-zuwa wurin Uban sai ta wurina.”—Yoh. 1:14; 14:6.
Yesu ya ƙafa misali mai kyau na yin biyayya ga Ubansa. Ya ce: “Ba na yin komi domin kaina ba, amma ina faɗin waɗannan magana yadda Uba ya koya mani.” Ya kuma ce: “Ina aika abin da ya gamshe shi.” (Yoh. 8:28, 29) A waɗanne hanyoyi ne Yesu yake faranta wa Ubansa rai?
Hakika, Yesu yana yi wa Ubansa biyayya, kuma abin da bauta wa Allah yake nufi ke nan. Yesu ya manne wa Ubansa ta wajen yi masa biyayya da yin nufinsa har a lokacin da yin haka ya kasance da wuya. (Filib. 2:7, 8) Wani fanni na bautar Yesu mai muhimmanci shi ne yin aikin wa’azi har mutane marasa bi da masu bi suna kiransa Malami. (Mat. 22:23, 24; Yoh. 3:2) Ban da haka, Yesu ya ba da kansa don mutane. Don halinsa na saɗaukar da kai ya ba da kansa a wajen hidima kuma ya yi farin cikin yi wa mutane wa’azi. (Mat. 14:13, 14; 20:28) Duk da cewa yana da aiki mai yawa, Yesu ya ba da lokaci a wajen yi wa Ubansa na samaniya addu’a. (Luka 6:12) Allah yana ɗauka bautar da Yesu yake yi da muhimmanci.
Ƙoƙarin Faranta wa Allah Rai
Jehobah ya lura da halin Ɗansa kuma ya amince da shi. (Mat. 17:5) Amma, Shaiɗan ma ya lura cewa Yesu ya yi rayuwa ta aminci. Da haka, Yesu ya zama abin faƙon Shaiɗan. Me ya sa? Saboda babu wani mutum da ya yi cikakkiyar biyayya ga Allah har ya bauta masa yadda ya cancanta. Kuma Iblis yana so ya hana Yesu yi wa Jehobah bautar da ya cancanta.—R. Yoh. 4:11.
Don ya rinjayi Yesu, Shaiɗan ya gwada shi ta wajen ba shi wani abu da zai iya jan ra’ayinsa. Ya kai Yesu zuwa wani “dutse mai-tsawo ƙwarai, ya gwada masa dukan mulkokin duniya, da ɗaukakarsu.” Sai ya ce: “Dukan waɗannan ni ba ka, idan ka fāɗi, ka yi mani sujada.” Menene Yesu ya yi? Ya ce: “Rabu da nan, ya Shaiɗan: gama an rubuta, Ka yi sujjada ga Ubangiji Allahnka, shi kaɗai ma za ka bauta masa.” (Mat. 4:8-10) Hakika, Yesu ya san cewa zunubi ne idan ya bauta wa Shaiɗan, komin amfanin da zai samu. Bai yarda ya bauta wa kowa ba, ban da Jehobah.
Shaiɗan ba zai iya ba mu duka mulkokin duniya da ɗaukakarsu don mu bauta masa ba. Amma yana ƙoƙarin ya hana bautar da Kiristocin gaske suke yi wa Allah. Shaiɗan yana so mu bauta wa wani ko kuma wani abu.—2 Kor. 4:4.
Yesu ya kasance da aminci har mutuwarsa. Ta wajen kasancewa da amincinsa ga Allah, Yesu ya ɗaukaka Jehobah a hanya da babu wanda ya taɓa yi. A matsayin Kiristoci na gaske a yau, muna ƙoƙari mu bi rayuwar Yesu na aminci ta wurin sa bautarmu ga Mahaliccinmu ta zama na farko fiye da kome. Hakika, dangantaka mai kyau da Allah ita ce dukiya mafi tamani.
Albarka da Ake Samu ta Wajen Bauta wa Allah Yadda Yake So
Yin bauta “mai-tsarki marar-ɓāci” a gaban Allah yana kawo albarka. (Yaƙ. 1:27) Alal misali, muna rayuwa a zamanin da mutane da yawa sun zama “masu-son kansu, masu-son kuɗi, masu-ruba,” kuma “marasa-son nagarta.” (2 Tim. 3:1-5) Amma a cikin ikilisiyar Allah muna da gatar yin tarayya da mutane masu tsarki da suke riƙe mizanan Allah na bauta masa. Wannan ba abin wartsakewa ba ne?
Idan muka kasance da tsabta a wannan duniya, za mu sami albarkar kasancewa da lamiri mai tsabta. Muna so mu kasance da lamiri mai tsabta ta wurin yin biyayya ga ka’idodin Allah masu aminci kuma mu yi biyayya ga dokokin Kaisar waɗanda suka jitu da na Allah.—Mar. 12:17; A. M. 5:27-29.
Bauta da zuciya ɗaya tana kuma kawo wani irin albarka. Idan muka kasance da yin nufin Allah maimakon yin abin da muke so, rayuwarmu za ta zama mai ma’ana kuma mai gamsarwa. Maimakon mu ce: “Bari mu ci mu sha, gama gobe za mu mutu,” muna da begen samun rayuwa na dindindin a aljanna a duniya.—1 Kor. 15:32.
Littafin Ru’ya ta Yohanna ya nuna cewa lokaci na zuwa da waɗanda suka riƙe amincinsu ga Jehobah za su “fito daga cikin babban tsananin.” Wannan annabcin ya ce, “shi kuma wanda ya zauna bisa kursiyin za ya inuwantadda su da alfarwatasa.” (R. Yoh. 7:13-15) Jehobah Allah wanda ya fi ɗaukaka a dukan sararin sama shi ne yake zaune a kursiyin. Ka yi tunanin irin farin cikin da zai yi idan ya marabce ka a cikin tantinsa, yana kula da kai don kada wani abu ya same ka. Za ka mori kāriyarsa har yanzu.
Amma, an kwatanta duk waɗanda suke bauta wa Allah yadda ya kamata da “maɓulɓulan ruwaye na rai.” Waɗannan maɓulɓulan rai suna wakiltar dukan tanadi da Jehobah yake yi don mu sami rai madawwami. Hakika, ta wurin fansar Kristi, “Allah kuma za ya share dukan hawaye daga idanunsu.” (R. Yoh. 7:17) ’Yan adam za su zama kamilai, waɗanda suke da begen zama a duniya har abada za su yi farin ciki sosai. Har a yanzu, masu bauta wa Allah suna farin ciki, suna furta godiyarsu ga Jehobah da kuma bauta masa tare da waɗanda suke sama da suke rera waƙa: “Ayyukanka masu-girma ne, masu-ban al’ajabi, ya Ubangiji Allah, Mai-iko duka; halullukanka kuma masu-adalci ne, masu-gaskiya kuma, ya Sarkin zamanai. Wanene za ya rasa jin tsoro, ya rasa ɗaukaka sunanka, ya Ubangiji? gama kai kaɗai mai-tsarki ne; gama dukan al’ummai za su zo su yi sujjada a gabanka; gama ayyukanka masu-adalci sun bayyanu.”—R. Yoh. 15:3, 4.
[Hoto a shafi na 27]
Menene Shaiɗan yake ba mu don mu bauta masa?