Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 11/15 pp. 28-31
  • “Ku Yi Tsayayya Da Shaiɗan” Yadda Yesu Ya Yi

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Ku Yi Tsayayya Da Shaiɗan” Yadda Yesu Ya Yi
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Jehobah Yana Kāre Bayinsa
  • Misali Mafi Kyau Wajen Yin Tsayayya da Iblis
  • “Ku Yi Tsayayya da Shaiɗan, Za Ya fa Guje Muku”
  • Ka Yi Tsayayya Da Shaiɗan, Kuma Zai Guje ka!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • “Ku Yi Tsayayya Da Iblis”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Wane ne ko kuma mene ne Iblis?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2016
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 11/15 pp. 28-31

“Ku Yi Tsayayya Da Shaiɗan” Yadda Yesu Ya Yi

“Ku yi tsayayya da Shaiɗan, za ya fa guje muku.”—YAƘ. 4:7.

1. Wace hamayya ce Yesu ya san zai fuskanta a duniya, da wane sakamako?

YESU KRISTI ya san cewa zai fuskanci hamayya daga Iblis. Wannan gaskiyar a bayyane take daga abin da Allah ya gaya wa macijin, wato, mugun ruhun da ya yi tawaye da ya yi magana ta hanyar maciji: “Tsakaninka da macen [sashen ƙungiyar Jehobah na sama mai kama da mata] kuma zan kafa magabtaka, da tsakanin zuriyarka da zuriyarta kuma: shi [Yesu Kristi] za ya ƙuje kanka, kai kuma za ka ƙuje duddugensa.” (Far. 3:14, 15, R. Yoh. 12:9) Ƙuje diddigen Yesu yana nufin cewa zai sha wahala na ɗan lokaci domin za a kashe shi a duniya, kuma Jehobah zai ta da shi zuwa ɗaukaka ta samaniya. Amma ƙuje kan macijin yana nufin cewa za a kashe Iblis kuma ba zai taɓa farfaɗowa ba.—Karanta Ayukan Manzanni 2:31, 32; Ibraniyawa 2:14.

2. Me ya sa Jehobah yake da tabbaci cewa Yesu zai yi nasara wajen yin tsayayya da Iblis?

2 Jehobah yana da tabbaci cewa Yesu zai cika aikinsa kuma ya yi tsayayya da Iblis sa’ad da yake duniya. Me ya sa Jehobah yake wannan tabbacin? Domin ya halicci Yesu a sama shekaru aru aru, ya san halinsa kuma ya san cewa wannan “gwanin mai-aiki” da kuma ‘ɗan fari gaban dukan halitta’ mai yin biyayya ne kuma ya kasance da aminci. (Mis. 8:22-31; Kol. 1:15) Saboda haka, sa’ad da aka aiko Yesu zuwa duniya kuma aka ƙyale Iblis ya gwada shi har mutuwa, Allah yana da tabbaci cewa Ɗansa makaɗaici zai yi nasara.—Yoh. 3:16.

Jehobah Yana Kāre Bayinsa

3. Menene halin Iblis ga bayin Jehobah?

3 Yesu ya kira Iblis “mai-mulkin wannan duniya” kuma ya gargaɗi almajiransa cewa za a tsananta musu, yadda aka tsananta masa. (Yoh. 12:31; 15:20) Duniyar da ke hannun Shaiɗan Iblis, ta ƙi jinin Kiristoci na gaskiya domin suna bauta wa Jehobah kuma su masu wa’azin adalci ne. (Mat. 24:9; 1 Yoh. 5:19) Iblis yana mai da hankali ne musamman ga shafaffu da suka rage da za su yi sarauta da Kristi a Mulkinsa na samaniya. Shaiɗan yana kuma fakon Shaidun Jehobah da yawa da suke da begen yin rayuwa har abada a cikin aljanna a duniya. Kalmar Allah ta gargaɗe mu: “Magabcinku Shaiɗan, kamar zaki mai-ruri, yana yawo, yana neman wanda za ya cinye.”—1 Bit. 5:8.

4. Menene ya nuna cewa mutanen Allah sun yi nasara wajen yin tsayayya da Iblis a zamaninmu?

4 Da yake Jehobah Allah yana goyon bayan ƙungiyarsa, muna yin nasara wajen yin tsayayya da Iblis. Ka yi la’akari da waɗannan abubuwan da suka faru: Shekaru 100 da suka shige, wasu cikin waɗanda suka yi mugun mulki na kama-karya sun yi ƙoƙarin su kawar da Shaidun Jehobah. Amma adadin Shaidun sai ci gaba da ƙaruwa yake yi kuma a yanzu sun kai kusan miliyan bakwai cikin ikilisiyoyi fiye da dubu ɗari a dukan duniya. Azzalumai masu mulkin kama karya da ke tsananta wa Shaidun Jehobah ne aka kawar!

5. Ta yaya Ishaya 54:17 ta kasance gaskiya a batun bayin Jehobah?

5 Da yake magana ga ikilisiya ta Isra’ila ta dā a matsayin “matarsa,” Allah ya yi alkawari: “Babu alatun da aka halitta domin ciwutanki da za ya yi albarka; iyakar harshe kuma da za shi tashi gaba da ke, a shari’a za ki kayar da shi. Gadōn bayin Ubangiji ke nan, adalcinsu wanda shi ke daga wurina.” (Isha. 54:11, 17) Hakan ya zama gaskiya a batun mutanen Jehobah a dukan duniya a cikin waɗannan “kwanaki na ƙarshe.” (2 Tim. 3:1-5, 13) Za mu ci gaba da yin tsayayya da Iblis, kuma babu makamin da yake ƙoƙarin ya yi amfani da shi don ya kawar da mutanen Allah da zai yi nasara, domin Jehobah yana tare da mu.—Zab. 118:6, 7.

6. Menene littafin Daniel ya gaya mana zai sami sarautar Iblis a nan gaba?

6 A ƙarshen wannan mugun zamani da ke gabatowa da sauri, za a kawar da dukan fannoni na sarautar Shaiɗan. Da yake rubuta abin da Allah ya hure shi ya rubuta, annabi Daniel ya annabta: “A cikin zamanin waɗannan sarakuna kuwa [na zamaninmu], Allah mai-sama za ya kafa wani mulki [a sama], wanda ba za a rushe shi ba daɗai, sarautassa kuwa ba za a bar ma wata al’umma ba; amma za ya parpashe dukan waɗannan mulkoki [da suke ci a yanzu] ya cinye su, shi kuwa za ya tsaya har abada.” (Dan. 2:44) Sa’ad da hakan ya faru, sarautar Shaiɗan da ta ’yan adam ajizai za ta ɓace. Za a kawar da kowane fanni na zamanin Iblis har abada, kuma babu wanda zai yi hamayya da Mulkin Allah a dukan duniya.—Karanta 2 Bitrus 3:7, 13.

7. Ta yaya muka sani cewa bayin Jehobah ɗaɗɗaya suna iya yin nasara wajen yin tsayayya da Iblis?

7 Babu shakka cewa za a kāre ƙungiyar Jehobah kuma za ta ci gaba da samun tagomashin Allah. (Karanta Zabura 125:1, 2.) Mu kuma fa? Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa za mu iya yin nasara wajen yin tsayayya da Iblis yadda Yesu ya yi. Hakika, annabci da Kristi ya yi ta bakin manzo Yohanna ya nuna cewa duk da hamayya daga wajen Shaiɗan, “taro mai-girma” na waɗanda suke da begen zama a duniya za su tsira a ƙarshen wannan zamanin. Bisa abin da Nassosi ya ce, sun ta da murya da ƙarfi suka ce: “Ceto ga Allahnmu ne wanda ya zauna bisa kursiyin, ga Ɗan ragon [Yesu Kristi] kuma.” (R. Yoh. 7:9-14) An nuna cewa shafaffu sun yi nasara bisa Shaiɗan, kuma abokansu, “waɗansu tumaki,” su ma sun yi nasara wajen yin tsayayya da shi. (Yoh. 10:16; R. Yoh. 12:10, 11) Amma hakan na bukatar ƙoƙari sosai da yin addu’a don a “cece mu daga Mugun.”—Mat. 6:13.

Misali Mafi Kyau Wajen Yin Tsayayya da Iblis

8. Wane gwaji na farko ne da aka rubuta Iblis ya yi amfani da shi ga Yesu a cikin jeji, kuma yaya Kristi ya amsa?

8 Iblis ya yi ƙoƙarin ya karya amincin Yesu. A cikin jeji, Shaiɗan ya yi amfani da gwaji don Yesu ya daina yi wa Jehobah biyayya. Amma, Yesu ya kafa misali mafi kyau wajen yin tsayayya da Shaiɗan. Bayan ya yi azumi kwana arba’in dare da rana, wataƙila Yesu ya ji yunwa sosai. Shaiɗan ya ce: “Idan kai Ɗan Allah ne, ka umurci waɗannan duwatsu su zama gurasa.” Amma Yesu ya ƙi ya yi amfani da ikon da Allah ya ba shi don ya amfani kansa. Maimakon haka, Yesu ya ce: “An rubuta, Ba da abinci kaɗai ba mutum za ya rayu, amma da kowace magana da ke fitowa daga bakin Allah.”—Mat. 4:1-4; K. Sha 8:3.

9. Me ya sa za mu ƙi ƙoƙarce-ƙoƙarcen da Iblis yake yi na son yin amfani da sha’awarmu?

9 A yau, Iblis yana amfani da abubuwan da bayin Jehobah suke sha’awa. Saboda haka, dole ne mu dage wajen ƙin gwaji na yin lalata, da ya zama ruwan dare a wannan malalaciyar duniya. Kalmar Allah ta faɗi sarai cewa: “Ko kuwa ba ku sani ba marasa-adalci ba za su gaji mulkin Allah ba? Kada ku yaudaru; da masu-fasikanci, da masu-bautan gumaka, da mazinata, da baran mata, da masu-kwana da maza . . . , ba za su gāji mulkin Allah ba.” (1 Kor. 6:9, 10) A bayyane yake cewa ba za a ƙyale mutanen da suke lalata kuma suka ƙi tuba su kasance a cikin sabuwar duniya ta Allah ba.

10. A cikin Matta 4:5, 6, wane gwaji ne kuma Shaiɗan ya yi amfani da shi don ya karya amincin Yesu?

10 Game da ɗaya cikin gwaji da Yesu ya fuskanta a cikin jeji, Nassosi sun ce: “Shaitan ya ɗauke shi zuwa cikin birni mai-tsarki; ya tsayasda shi a kan hasumiya ta haikali, ya ce masa, Idan kai Ɗan Allah ne, faɗa da kanka: gama an rubuta, Za ya ba mala’ikunsa umurni a kanka: a bisa hannuwansu za su ɗauke ka, kada halama ka buga ƙafarka bisa dutse.” (Mat. 4:5, 6) Shaiɗan yana nufin cewa hakan zai sa Yesu ya nuna cewa shi Almasihu ne. Amma, gaskiyar ita ce, hakan zai nuna girman kai da Allah ba zai amince da shi ba ko kuma ya goyi bayansa. A wannan karin ma, Yesu ya kasance da amincinsa ga Jehobah kuma ya amsa ta wajen yin ƙaulin wani nassi. Ya ce: “An kuma rubuta, Ba za ka gwada Ubangiji Allahnka ba.”—Mat. 4:7; K. Sha 6:16.

11. Ta yaya ne Shaiɗan zai iya jarraba mu, kuma menene zai iya zama sakamakon?

11 Shaiɗan yana iya jarraba mu mu nemi ɗaukaka a hanyoyi dabam dabam. Yana iya rinjayarmu mu yi koyi da salon duniya wajen sa tufafi da yin ado ko kuma mu yi nishaɗin da ba shi da kyau. Amma idan ba mu bi gargaɗin Littafi Mai Tsarki ba kuma muka yi koyi da duniya, muna tsammanin cewa mala’iku za su kāre mu daga mugun sakamako na bin wannan tafarkin ne? Ko da yake Sarki Dauda ya tuba daga zunubin da ya yi da Bath-sheba, ba a kāre shi ba daga sakamakon ayyukansa. (2 Sam. 12:9-12) Kada mu gwada Jehobah ta hanyoyi da ba su dace ba, wataƙila ta ƙulla abota da duniya.—Karanta Yaƙub 4:4; 1 Yohanna 2:15-17.

12. Wane gwaji ne aka ambata a Matta 4:8, 9, kuma menene Ɗan Allah ya ce?

12 Wani gwaji kuma da Iblis ya yi amfani da shi a cikin jeji shi ne miƙa wa Yesu ikon siyasa. Shaiɗan ya nuna wa Yesu dukan mulkokin duniya da ɗaukakarsu kuma ya ce: “Dukan waɗannan ni ba ka, idan ka fāɗi, ka yi mani sujada.” (Mat. 4:8, 9) Wannan hanya ce ta ruɗu don ya samu bautar da ya kamata a yi wa Jehobah kuma ya sa Yesu ya yi rashin aminci ga Allah! Ta wajen yin sha’awar a riƙa bauta masa, wannan mala’ika mai aminci a dā ya faɗa cikin zunubi domin haɗamarsa, da hakan, ya zama mugu mai gwaji, Shaiɗan Iblis. (Yaƙ. 1:14, 15) Amma, Yesu dabam yake kuma ya kuɗiri aniya ya kasance da aminci ga Ubansa na samaniya, saboda haka, ya ce: ‘Rabu da nan, ya Shaiɗan: gama an rubuta, Ka yi sujjada ga Ubangiji Allahnka, shi kaɗai ma za ka bauta masa.’ Ta hakan, Yesu ya sake yin tsayayya da Iblis ta wajen gaya masa matsayinsa sarai. Ɗan Allah ba ya son ya kasance sashe na duniyar Shaiɗan kuma ba zai taɓa bauta wa wannan mugun ba!—Mat. 4:10; K. Sha 6:13; 10:20.

“Ku Yi Tsayayya da Shaiɗan, Za Ya fa Guje Muku”

13, 14. (a) Ta wajen nuna wa Yesu dukan mulkokin duniya, menene Iblis ya miƙa masa? (b) Ta yaya Shaiɗan yake ƙoƙarin ya lalata mu?

13 Ta wajen nuna wa Yesu dukan mulkokin duniya, Iblis ya miƙa masa ikon da babu ɗan adam da ya taɓa samu. Shaiɗan ya yi tsammanin cewa Yesu zai so abin da ya gani kuma ya tabbatar da shi cewa zai iya zama shugaban siyasa na duniya mafi iko. A yau, Iblis ba ya miƙa mana mulkoki, amma yana ƙoƙarin ya ɓata zukatanmu ta hanyar abubuwan da muke gani, muke ji, da waɗanda muke tunaninsu.

14 Iblis ne yake mulkin wannan duniya. Shi ya sa, yake ja-gorar hanyoyin watsa labarai. Saboda haka, ba abin mamaki ba ne da abubuwa da duniya take karantawa, kallo, da kuma saurarawa suka cika da lalata da kuma mugunta. Ta wurin talla, wannan duniya tana sa mu yi sha’awar sayan kaya da yawa da ba ma bukata. Ta hakan, Iblis a koyaushe yana gwada mu mu yi sha’awar kayan duniya da za mu so mu gani, mu ji, kuma mu yi tunaninsa. Amma idan muka ƙi karanta abubuwan da suka saɓa wa Nassi ko mu kalle su, muna cewa ne: “Rabu da nan, ya Shaiɗan!” Ta hakan muna yin koyi da Yesu ta wajen dagewa da ƙin duniya marar tsabta ta Shaiɗan. Yadda muke nuna kanmu da gaba gaɗi a matsayin Shaidun Jehobah a wajen aiki, a makaranta, a unguwarmu, da kuma tsakanin danginmu yana nuna cewa mu ba na duniyar Shaiɗan ba ne.—Karanta Markus 8:38.

15. Me ya sa yin tsayayya da Shaiɗan yana nufin kasancewa a faɗake a kowane lokaci?

15 Bayan da Iblis ya kasa samun nasara a jarrabarsa na uku don ya sa Yesu ya karya amincinsa ga Allah, “Shaiɗan ya rabu da shi.” (Mat. 4:11) Amma fa, Shaiɗan bai da niyyar daina jarraba Yesu, domin an gaya mana cewa: “Lokacinda Shaiɗan ya gama kowace jaraba [a cikin jeji,] ya rabu da shi tukuna.” (Luk 4:13) Sa’ad da muka yi nasara wajen yin tsayayya da Iblis, ya kamata mu gode wa Jehobah. Muna kuma bukatar mu ci gaba da neman taimakon Allah, domin Iblis zai dawo ya sake jarraba mu a wani lokacin da ya ga ya dace, wato, a lokacin da ba ma sa ran fuskantar jarraba. Saboda haka, muna bukatar mu kasance a faɗake a kowane lokaci, kuma mu nace wa hidima mai tsarki da muke yi wa Jehobah duk da irin jarrabar da za mu iya fuskanta.

16. Wane iko mai ƙarfi ne Jehobah yake ba mu, kuma me ya sa muke bukatar mu roƙi a ba mu shi?

16 Don mu sami taimako a ƙoƙarce-ƙoƙarcenmu na yin tsayayya da Iblis, muna bukatar mu yi addu’a don mu sami iko mafi ƙarfi a dukan duniya, wato, ruhu mai tsarki na Allah. Zai sa mu yi abubuwan da ba za mu iya yi ba da ƙarfinmu. Yesu ya ba mabiyansa tabbacin samun ruhun Allah sa’ad da ya ce: “Idan ku fa [ajizai] da ku ke miyagu, kun san yadda za ku ba ’ya’yanku alherai, balle fa Ubanku na sama za ya bada Ruhu Mai-tsarki ga waɗanda su ke roƙonsa?” (Luk 11:13) Bari mu ci gaba da roƙon Jehobah don samun ruhunsa mai tsarki. Tare da taimakon wannan iko mafi ƙarfi, za mu yi nasara a ƙudurinmu na yin tsayayya da Iblis. Ƙari ga yin addu’a a kowane lokaci, muna bukatar mu saka cikakken maƙami na ruhaniya daga Allah don mu “yi tsayayya da dabarun Shaiɗan.”—Afis. 6:11-18.

17. Wane farin ciki ne ya taimaka wa Yesu ya yi tsayayya da Iblis?

17 Akwai wani abu kuma da ya taimaka wa Yesu ya yi tsayayya da Iblis, kuma zai iya taimaka mana. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Domin farinzuciya da aka sa gabansa [Yesu], yana rena kunya, ya kuwa zauna ga hannun dama na al’arshen Allah.” (Ibran. 12:2) Muna iya samun irin wannan farin cikin ta wajen ɗaukaka ikon mallaka na Jehobah, daraja sunansa mai tsarki, da kuma saka lada na rai madawwami a gabanmu. Za mu yi farin ciki sosai sa’ad da aka kawar da Shaiɗan da dukan ayyukansa har abada kuma ‘masu tawali’u za su gāji ƙasan; su faranta zuciyarsu kuma cikin yalwar salama’! (Zab. 37:11) Saboda haka, ka ci gaba da yin tsayayya da Iblis kamar yadda Yesu ya yi.—Karanta Yaƙub 4:7, 8.

Yaya Za Ka Amsa?

• Menene ya nuna cewa Jehobah yana kāre mutanensa?

• Ta yaya ne Yesu ya kafa misali wajen yin tsayayya da Shaiɗan?

• Ta waɗanne hanyoyi ne za ka iya yin tsayayya da Iblis?

[Hoto a shafi na 31]

Yesu ya ƙi tayin da Shaiɗan ya yi masa na dukan mulkin duniya

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba