Makiyaya, Ku Yi Koyi Da Makiyaya Mafi Girma
“Kristi kuma ya sha azaba dominku, yana bar maku gurbi, domin ku bi sawunsa.”—1 BIT. 2:21.
1, 2. (a) Wane sakamako ake samu sa’ad da aka kula da tumaki sosai? (b) Me ya sa mutane da yawa a zamanin Yesu suke kamar tumaki da ba su da makiyayi?
IDAN tumaki suna da makiyayi mai kula sosai, suna yin yalwa. Wani littafi da ya yi magana game da yin kiwon tumaki ya ce idan makiyayi ya fito da tumakinsa fili don su ci ciyayi kawai amma ba ya kula da su, ba za su daɗe kafin su yi rashin lafiya ba. Amma idan makiyayi yana kula da kowane tumakinsa, dukansu za su zama lafiyayyu.
2 Hakan ma yake a cikin ikilisiya. Yadda dattawa suke kula da kowane Kirista zai shafi ikilisiyar baki ɗaya. Ka tuna lokacin da Yesu ya ji tausayin jama’a “domin suna wahala, suna watse kuma, kamar tumakin da ba su da makiyayi.” (Mat. 9:36) Me ya sa mutane a zamanin Yesu suka samu kansu a cikin irin wannan yanayin? Domin waɗanda suke da hakkin su koyar da su game da Dokar Allah suna da ɗacin rai da taurin zuciya kuma su munafukai ne. Maimakon su ƙaunaci mutanen kuma su kula da su, waɗannan limaman sun sa bauta wa Allah ta zama jar aiki a gare su. Mutanen sun ji kamar suna ɗauke da “kaya masu-nauyi” a kafaɗarsu.—Mat. 23:4.
3. Me ya kamata dattawa su riƙa tunawa yayin da suke kula da tumakin?
3 A yau, dattawa suna da babban hakki. Suna kula da tumakin Jehobah da kuma na Yesu. Waɗannan tumakin sun da daraja sosai ga Yesu wanda shi ne “makiyayi mai-kyau.” (Yoh. 10:11) Yesu ya “saye” tumakin da jininsa “mai-daraja.” (1 Kor. 6:20; 1 Bit. 1:18, 19) Ya kamata dattawa su riƙa tuna cewa Yesu Kristi ne “babban makiyayin tumakin” kuma za su ba da lissafin yadda suka bi da tumakinsa.—Ibran. 13:20.
4. Mene ne za mu koya a wannan talifin?
4 Jehobah ya ƙarfafa kowa a cikin ikilisiya ya ‘yi biyayya da waɗanda ke shugabanninsu.’ Ya kuma gaya wa dattawa cewa kada su zama ‘masu-nuna sarauta bisa abin kiwo da aka sanya a hannunsu.’ (Ibran. 13:17; karanta 1 Bitrus 5:2, 3.) Ta yaya dattawa za su ci gaba da yin shugabanci ba tare da yin sarauta bisa tumakin Allah ba? Wato, ta yaya dattawa za su kula da bukatun tumakin Allah ba tare da wuce gona da iri ba?
ZAI “ƊAUKE SU A CIKIN ƘIRJINSA”
5. Mene ne muka koya game da Jehobah a littafin Ishaya 40:11?
5 Annabi Ishaya ya yi furuci na gaba game da Jehobah. Ya ce: “Za ya yi kiwon garkensa kamar makiyayi, za ya tattara ’ya’yan tumaki a hannunsa, ya ɗauke su a cikin ƙirjinsa, a hankali kuma za ya bida masu-bada mama.” (Isha. 40:11) Wannan nassin ya bayyana yadda Jehobah yake kula da bukatun waɗanda suka kasala kuma suke bukatar kāriya. Makiyayi ya san da bukatun kowane tumakinsa, hakazalika, Jehobah ya san da bukatun kowane ɗan’uwa a cikin ikilisiya kuma yana farin cikin taimaka musu. Kamar yadda makiyayi yake nannaɗe ɗan rago ko ’yar tunkiya a tsumma kuma ya riƙe ta a ƙirjinsa, hakan ma Jehobah yake ta’azantar da kuma kula da mu sa’ad da muke mawuyacin yanayi. Shi “Uban jiyejiyenƙai” ne.—2 Kor. 1:3, 4.
6. Ta yaya dattijo zai iya yin koyi da misalin Jehobah?
6 Makiyaya a cikin ikilisiya za su iya koyan darussa masu kyau daga Ubanmu na sama! Wajibi ne su kula da tumakin, kamar yadda Jehobah yake yi. Idan dattawa sun san matsalolin da ’yan’uwa suke ciki, za su san sa’ad da ya kamata su taimaka musu da yadda za su ƙarfafa da kuma tallafa musu. (Mis. 27:23) Hakan yana nufin cewa ya wajaba dattijo ya riƙa keɓe lokaci don ya tattauna da ’yan’uwa kuma ya saurare su. Bai kamata ya yi shisshigi ba, amma ya riƙa lura da abin da ke faruwa a cikin ikilisiya kuma ya nuna ƙauna ta wajen taimaka wa “marasa-ƙarfi.”—A. M. 20:35; 1 Tas. 4:11.
7. (a) Yaya limamai suka bi da tumakin Allah a zamanin Ezekiyel da Irmiya? (b) Wane darasi ne za mu iya koya daga yadda Jehobah ya ƙi da makiyaya marasa aminci?
7 Ka yi la’akari da halin makiyayan bayin Allah a zamanin Ezekiyel da Irmiya. Jehobah ya ƙi da su domin ba su kula da tumakinsa a hanyar da ta dace ba. Jehobah ya ce: “Tumakina sun zama abinci ga dukan naman jeji, domin babu makiyayi, makiyayana kuwa ba su biɗi tumakina ba, amma makiyaya suka yi kiwon kansu, ba su yi kiwon tumakina ba.” Mutanen sun sha wahala domin makiyayan suna son kai da kuma kwaɗayi. (Ezek. 34:7-10; Irm. 23:1) Hakazalika, Jehobah ya ƙi da limaman Kiristendom. Wane darasi mai muhimmanci ne dattawa za su iya koya daga yadda Jehobah ya ƙi da makiyaya marasa aminci? Wajibi ne su kula da garken sosai kuma su ƙaunace su.
“NA YI MUKU KWATANCI”
8. A wace hanya ce dattawa za su iya yin koyi da Yesu sa’ad da suke wa ’yan’uwansu gyara?
8 Ajizanci zai iya sa wasu tumakin Allah su yi jinkirin bin umurnin Jehobah. Za su iya yanke shawara da ba ta jitu da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ba, ko kuma za su iya yin abin da ya nuna cewa ba su manyanta ba tukun a matsayin Kiristoci. Wane mataki ne ya kamata dattawa su ɗauka? Almajiran Yesu sun yi mūsu sau da yawa a kan wanda ya fi girma a Mulkin Allah, amma duk da haka, Yesu ya bi da su cikin haƙuri. Maimakon Yesu ya yi fushi da su, ya ci gaba da koya musu darasi a kan kasancewa da tawali’u. Ya kamata dattawa ma su yi koyi da shi. (Luk 9:46-48; 22:24-27) Yesu ya wanke ƙafafunsu kuma hakan ya koya musu darasi a kan nuna tawali’u. A yau ma, wajibi ne dattawa su nuna tawali’u.—Karanta Yohanna 13:12-15; 1 Bit. 2:21.
9. Wane hali ne Yesu ya koya wa almajiransa?
9 Manzo Yaƙub da Yohanna sun ɗauka cewa aikin makiyaya yana nufin yin sarauta bisa wasu. Sun ce Yesu ya ba su babban muƙami a Mulkin Allah. Amma Yesu ya yi musu gyara, ya ce: “Kun sani sarakunan Al’ummai suna nuna musu sarauta, manyansu kuma suna gwada musu iko. Ba haka za ya zama a cikinku ba: amma dukan wanda ya ke so shi zama babba a cikinku, bawanku za ya zama.” (Mat. 20:25, 26) Almajiran suna bukatar su yi tir da halin yin “shugabanci” bisa ’yan’uwansu, wato su riƙa gaya musu abin da za su yi a kowane lokaci.
10. Yaya Yesu yake so dattawa su bi da garken Allah, kuma wane misali mai kyau ne Bulus ya kafa?
10 Yesu yana so dattawa Kirista su bi da garken Allah kamar yadda shi ma ya bi da su. Wajibi ne su kasance a shirye su yi wa ’yan’uwansu hidima, maimakon su riƙa yin shugabanci a kansu. Manzo Bulus yana da tawali’u, shi ya sa ya gargaɗi dattawan ikilisiyar da ke Afisa. Ya ce: “Ku da kanku kun sani, tun randa na fara sa ƙafa cikin Asiya, irin zaman da na yi tare da ku dukan kwanaki, Ina bautar Ubangiji da iyakacin tawali’u.” Bulus yana so dattawan su kasance da tawali’u kuma su yi aiki tuƙuru don ’yan’uwansu. Ya daɗa cewa: “A cikin abu duka na yi muku gurbi, da wahalar kanku haka nan ya kamata ku taimaki marasa-ƙarfi.” (A. M. 20:18, 19, 35) A wani wasiƙa da Bulus ya rubuta wa Korintiyawa, ya gaya musu cewa ba ya sarauta bisa bangaskiyarsu. Maimakon haka, shi abokin aikinsu ne domin ya taimake su su bauta wa Allah da farin ciki. (2 Kor. 1:24) Ya kamata dattawa ma a yau su yi koyi da yadda Bulus ya kasance da tawali’u kuma ya yi aiki tuƙuru.
‘KU RIƘE TABBATACCIYAR MAGANAR KANKAN’
11, 12. Ta yaya dattijo zai iya taimaka wa wani ɗan’uwa ya yanke shawara?
11 Wajibi ne dattijo Kirista ya ‘riƙe tabbatacciyar maganan nan kankan, daidai yadda aka koya masa.’ (Tit. 1:9, Littafi Mai Tsarki) Amma ya kamata ya yi hakan cikin “tawali’u.” (Gal. 6:1) Dattijo mai kirki ba zai tilasta wa ɗan’uwa ya yi wani abu ba, amma zai taimaka masa ya yanke shawara domin yana ƙaunar Allah da kuma Kalmarsa. Alal misali, dattijo zai iya taimaka wa wani ɗan’uwa ya yanke wata shawara mai muhimmanci ta wajen tattauna ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da shi ko kuma wani talifi a mujallunmu. Zai iya ce wa ɗan’uwan ya yi tunani a kan yadda zaɓi dabam-dabam zai iya shafan dangantakarsa da Jehobah. Sai ya tuna masa muhimmancin neman ja-gorar Allah ta wajen yin addu’a kafin ya tsai da shawarar. (Mis. 3:5, 6) Bayan ya tattauna waɗannan batutuwan da ɗan’uwan, dattijon ya ƙyale shi ya yanke shawara.—Rom. 14:1-4.
12 Littafi Mai Tsarki ne kaɗai littafin da ya kamata dattawa su yi amfani da shi sa’ad da suke ja-gora. Saboda haka, yana da muhimmanci su yi amfani da Littafi Mai Tsarki yadda ya dace kuma su yi amfani da shi sa’ad da suke ba da shawara. Idan dattawa suka yi hakan, ba za su wuce gona da iri a ikon da Allah ya ba su ba. Ballantana ma, tumakin ba nasu ba ne. A ƙarshe, kowane mutum a cikin ikilisiya zai ba da lissafin kansa ga Jehoba da kuma Yesu a kan shawarar da ya yanke.—Gal. 6:5, 7, 8.
“KU ZAMA ABIN KOYI GA GARKEN”
13, 14. A waɗanne hanyoyi ne ya wajaba dattawa su kafa wa garken Allah misali mai kyau?
13 Bayan Bitrus ya ce kada dattawa su yi “sarauta” bisa ’yan’uwansu, sai ya ƙarfafa su cewa su zama “abin koyi ga garken.” (1 Bit. 5:3, LMT) Ta yaya dattijo zai iya zama abin koyi ga garken? Ka yi la’akari da halaye biyu da ya wajaba ɗan’uwa ya kasance da shi kafin ya zama dattijo. Na farko, yana bukatar ya zama “mai-shimfiɗaɗen hankali.” Hakan yana nufin cewa zai fahimci ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki kuma ya san yadda zai yi amfani da su a rayuwarsa. Ba ya firgita a yanayi mai wuya kuma yana la’akari sosai kafin ya yanke shawara. Na biyu kuma, zai riƙa “mulkin nasa gida da kyau.” Hakan yana nufin cewa idan dattijo yana da iyali, yana bukatar ya riƙa kula da matarsa da kuma yaransa sosai, domin ‘idan mutum ya rasa yadda za shi mallaki nasa gida, ƙaƙa za ya goyi ikilisiyar Allah?’ (1 Tim. 3:1, 2, 4, 5) ’Yan’uwa a cikin ikilisiya suna fi dogara ga dattawan da suke da waɗannan halayen.
14 Dattawa kuma suna kafa misali mai kyau ta wajen yin ja-gora a wa’azi kamar yadda Yesu ya yi. Yin wa’azin bisharar Mulkin Allah ne abu mafi muhimmanci a rayuwar Yesu sa’ad da yake duniya, kuma ya koya wa almajiransa yadda za su yi hakan. (Mar. 1:38; Luk 8:1) A yau, masu shela suna more yin wa’azi tare da dattawa. Suna ganin yadda dattawa suke da ƙwazo ga wannan aiki mai muhimmanci kuma suna yin koyi da yadda suke koyarwa. Idan dattawa sun yi amfani da lokacinsu da kuma kuzarinsu wajen yin wa’azin bishara ko da suna da wasu ayyuka da yawa, hakan zai sa ikilisiyar ma ta yi koyi da su. Dattawa za su iya kafa wa ’yan’uwa misali mai kyau ta wajen yin shiri don taro da yin kalami da kuma saka hannu a tsabtace da kuma gyara Majami’ar Mulki.—Afis. 5:15, 16; karanta Ibraniyawa 13:7.
“KU TAIMAKI MARASA-ƘARFI”
15. Mene ne wasu cikin dalilan da suka sa dattawa suke ziyarar ƙarfafawa?
15 Makiyayi mai kirki yana saurin taimaka wa tunkiyar da ta ji rauni ko take rashin lafiya. Hakazalika, dattawa suna bukatar su yi hanzarin taimaka wa waɗanda suke shan wahala ko suke bukatar shawara ko kuma ƙarfafa. Tsofaffi da kuma marasa lafiya suna iya bukatar taimako a wasu fannonin rayuwa, amma abin da suka fi bukata shi ne ƙarfafa da kuma ta’aziya daga Nassosi. (1 Tas. 5:14) Wataƙila, matasa a cikin ikilisiya suna fama da “sha’awoyin ƙuruciya.” (2 Tim. 2:22) Dattawa suna taimaka wa kowa a cikin ikilisiya ta wajen yi musu ziyarar ƙarfafawa. Sa’ad da suke wannan ziyarar, suna ƙoƙari su fahimci matsalolin da ’yan’uwa suke ciki kuma suna yin amfani da Littafi Mai Tsarki don su ƙarfafa su. Idan dattawa suna hanzarin taimaka wa ’yan’uwansu, matsaloli da yawa masu tsanani ba za su taso ba.
16. Mene ne dattawa za su iya yi idan wani ɗan’uwa a cikin ikilisiya yana da wata matsala mai tsanani?
16 Amma idan ɗan’uwa a cikin ikilisiya ya faɗa cikin matsala mai tsanani fa kuma dangantakarsa da Jehobah tana cikin haɗari? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Akwai mai-ciwo a cikinku? sai shi kira dattiɓan ikilisiya su yi addu’a a bisansa, suna shafe shi da mai cikin sunan Ubangiji: addu’ar bangaskiya kuwa za ta ceci mai-ciwo, Ubangiji kuwa za ya tashe shi; idan kuma ya yi zunubai, za a gafarta masa.” (Yaƙ. 5:14, 15) Ko da ɗan’uwan da ke “ciwo” bai ‘kira dattiɓai’ ba, ya kamata su yi hanzarin taimaka masa idan sun samu labari. Idan dattawa suka yi addu’a a madadin ’yan’uwansu kuma da su sa’ad da suke fuskantar mawuyacin yanayi, suna nuna cewa su makiyaya masu kirki ne waɗanda suke ƙarfafa ’yan’uwansu su ci gaba da bauta wa Allah da farin ciki.—Karanta Ishaya 32:1, 2.
17. Wane sakamako ne za a iya samu idan dattawa suka yi koyi da “babban makiyayi”?
17 A dukan ayyukan da dattawa suke yi a cikin ƙungiyar Jehobah, suna aiki tuƙuru don su yi koyi da Yesu Kristi, wanda shi ne “babban makiyayi.” Waɗannan mazan suna taimaka wa garken Allah su ci gaba da yin ƙarfi kuma su bauta wa Allah da aminci. Muna matuƙar farin ciki don Makiyayanmu da kuma babban Makiyayinmu, Jehobah.