Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w02 9/1 pp. 4-8
  • “Na Yi Muku Kwatanci”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Na Yi Muku Kwatanci”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ƙauna ta Allah Gaskiya Ce da ta Daɗe
  • Ƙaunar Gaskiya da Ya Koyar
  • Yesu Ya Yi Ƙaunar Mutane da Ya Koyar da Su
  • Yi wa Mutane Hidima da Yardan Rai
  • Ka Yi Koyi Da Yesu Ta Koyarwa Da Ƙauna
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Yesu Kristi, Mai Wa’azi Mafi Girma Na Ƙasashen Waje
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • ‘Ka Zo Ka Bi Ni’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • “Kowacce Rana Shi Biyo ni”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
w02 9/1 pp. 4-8

“Na Yi Muku Kwatanci”

“Domin daɗewarku, ku zama masu-koyarwa.”—IBRANIYAWA 5:12.

1. Me ya sa kalmomi da suke Ibraniyawa 5:12 za su sa Kirista ya damu?

SA’AD da kake karanta ayar jigonmu, kana tunani game da kanka? Idan haka ne, to ba kai kaɗai ba ne. Da yake mu mabiyan Kristi ne, mun sani cewa dole ne mu zama masu koyarwa. (Matta 28:19, 20) Mun sani cewa lokaci da muke ciki ya bukaci mu ƙware wajen koyarwa da gaggawa. Mun kuma sani cewa koyarwarmu za ta sa rai ko mutuwa a gaban waɗanda muke koyar da su! (1 Timothawus 4:16) Za mu iya tambayar kanmu: ‘Ni mai koyarwa ne yadda ya kamata na zama kuwa? Ta yaya zan yi gyara?’

2, 3. (a) Yaya wani malami ya yi bayanin tushen koyarwa da kyau? (b) Yesu ya bar mana wane kwatanci ne na koyarwa?

2 Irin wannan damuwar bai kamata ta sa mu kasala ba. Idan muna ɗaukan koyarwa aba ce da ke bukatar wasu hanyoyin koyarwa na musamman, za mu ga cewa zai yi mana wuya ainu mu yi gyara. Amma, tushen koyarwa mai kyau, ba batun gwaninta ba ne amma abu ne mafi muhimmanci. Ka lura da abin da wani masani wajen koyarwa ya rubuta a wani littafi: “Koyarwa da kyau ba ta dangana a kan gwaninta na musamman ba ko wani salo, shiri, ko kuma ayyuka ba. . . . Koyarwa ainihi batun ƙauna ce.” Hakika, ra’ayinsa ba na addini ba ne. Amma, ra’ayinsa zai yi amfani a koyarwa da muke yi mu Kiristoci. Ta yaya?

3 Wanda muke bin misalinsa ba wani ba ne Yesu Kristi ne kansa, wanda ya gaya wa mabiyansa: “Na yi muku kwatanci.” (Yohanna 13:15) Yana nuni ne ga misalinsa a nuna tawali’u, amma kwatanci da Yesu ya yi mana ya ƙunshi aikinsa da ya fi muhimmanci sa’ad da yake duniya—na koyar da mutane bishara ta Mulkin Allah. (Luka 4:43) Idan za ka zaɓi kalma guda ka kwatanta hidimar Yesu, za ka zaɓi kalmar nan “ƙauna,” ko ba haka ba? (Kolossiyawa 1:15; 1 Yohanna 4:8) Ƙaunar Yesu ga Ubansa na samaniya Jehovah ne, ya fi muhimmanci. (Yohanna 14:31) Da yake Yesu mai koyarwa ne, ya nuna ƙauna a ƙarin hanyoyi biyu. Yana ƙaunar gaskiya da ya koyar, kuma ya yi ƙaunar mutane da ya koya musu. Bari mu mai da hankali sosai a kan waɗannan fannoni biyu na kwatanci da ya bar mana.

Ƙauna ta Allah Gaskiya Ce da ta Daɗe

4. Ta yaya Yesu ya gina ƙauna ga koyarwar Jehovah?

4 Halin malami ga darasi da yake koyarwa na shafan kyan koyarwarsa. Za a ga cewa ba ya son darasi da yake koyarwa kuma haka ɗalibansa za su ji. Yesu ya yi ƙaunar gaskiya mai tamani da ya koyar game da Jehovah da Mulkinsa. Ƙaunar Yesu ga wannan darasi tana da zurfi. Ya gina wannan ƙaunar lokacin da yake ɗalibi. Shekaru da yawa da ya yi kafin ya zama mutum, Ɗa makaɗaici, mai koyo ne ƙwarai. Ishaya 50:4, 5 ta rubuta waɗannan kalmomi da suka dace: “Ubangiji Yahweh ya ba ni harshe na koyayyun mutane, domin in san yadda zan tokare da magana wanda ya gaji: safiya kan safiya ya kan tashe ni, ya kan farkarda kunnena domin in ji kamar koyayyun mutane. Ubangiji Yahweh ya buɗe kunnena, ban yi tayarwa ba, ban kuwa bada baya ba.”

5, 6. (a) Menene Yesu ya gani sa’ad da ya yi baftisma, yaya wannan ya shafe shi? (b) Wane bambanci muka gani game da yadda Yesu da Shaiɗan suka yi amfani da Kalmar Allah?

5 Da ya zama mutum yake girma a duniya, Yesu ya ci gaba da ƙaunar hikima ta Allah. (Luka 2:52) Sa’annan, a lokacin baftismarsa, ya ga wani abu na musamman. “Sama ta buɗe,” in ji Luka 3:21. Yesu, babu shakka lokacin ya tuna da rayuwarsa kafin ya zama mutum. Bayan haka ya yi kwanaki 40 yana azumi cikin daji. Ya yi farin ciki sosai na bimbini a kan koyarwa da Jehovah ya koyar da shi lokacin da yake sama. Ba da daɗewa ba, aka gwada ƙaunarsa ga gaskiya ta Allah.

6 Sa’ad da Yesu ya gaji kuma yana jin yunwa, Shaiɗan ya jarabe shi. Lallai da bambanci tsakanin waɗannan ’ya’yan Allah biyu! Dukansu sun yi ƙaulin Nassosin Ibrananci—amma da nufi dabam dabam. Shaiɗan ya canja ma’anar Kalmar Allah, cikin rashin biyayya ya yi amfani da ita ya biya bukatarsa. Hakika, wannan ɗan tawayen yana ƙyamar gaskiya ta Allah ne kawai. A wani ɓangare kuma, Yesu ya yi ƙaulin Nassosi da ƙauna, yana amfani da Kalmar Allah a kowacce amsa da ya bayar. Yesu ya wanzu da daɗewa kafin a rubuta waɗannan hurarrun kalmomi, duk da haka ya daraja su. Gaskiya ne masu tamani daga Ubansa na samaniya! Ya gaya wa Shaiɗan cewa irin wannan kalmomi daga Jehovah sun fi abinci muhimmanci. (Matta 4:1-11) Hakika, Yesu ya yi ƙaunar dukan gaskiya da Jehovah ya koya masa. Amma ta yaya ya nuna wannan ƙauna da yake shi malami ne?

Ƙaunar Gaskiya da Ya Koyar

7. Me ya sa Yesu bai ƙirƙiro nasa koyarwa ba?

7 Ƙaunar Yesu ga gaskiya da ya koyar a bayyane take koyaushe. Ballantana ma, yana da sauƙi ya iya gina nasa ra’ayoyi. Yana da ilimi da hikima sosai. (Kolossiyawa 2:3) Duk da haka, ya tuna wa masu sauraronsa a kai a kai cewa kome da ya koyar ya zo daga Ubansa na samaniya ne ba daga wurinsa ba. (Yohanna 7:16; 8:28; 12:49; 14:10) Ya yi ƙaunar gaskiya da ta zo daga wajen Allah sosai da ba zai sake ta da nasa ra’ayi ba.

8. A farkon hidimarsa, yaya Yesu ya kafa misali na dogara da Kalmar Allah?

8 Sa’ad da Yesu ya soma hidimarsa ga jama’a, ya kafa kwatanci nan da nan. Yi la’akari da hanya da ya sanar wa mutanen Allah da farko cewa shi ne Almasihun da aka yi alkawarinsa. Kawai ya bayyana a gaban jama’a, ya ce shi Kristi ne, kuma ya yi mu’ujizoji na musamman don ya tabbatar da abin da ya ce? A’a. Ya je majami’a inda mutanen Allah sun saba zuwa suna karanta Nassosi. A wajen ya karanta annabcin Ishaya 61:1, 2 da murya, kuma ya yi bayanin wannan gaskiya ta annabci cewa game da shi ne. (Luka 4:16-22) Mu’ujizoji da yawa da ya yi sun taimaka wajen nuna cewa yana da goyon bayan Jehovah. Duk da haka, koyaushe ya dogara da Kalmar Allah a koyarwarsa.

9. A sha’aninsa da Farisawa, yaya Yesu ya nuna ƙauna ta gaske ga Kalmar Allah?

9 Sa’ad da ’yan adawa na addini suka zargi Yesu, bai yi ƙoƙari ya ci nasara bisa kansu ba, ko da zai iya cinsu a irin wannan batun. Maimako, ya bar Kalmar Allah ta nuna musu cewa koyarwarsu ba daidai ba ce. Alal misali, ka tuna, sa’ad da Farisawa suka ce mabiyan Yesu sun taka dokar Asabarci ta tsinkar hatsi a gona kuma suna ci sa’ad da suke wucewa. Yesu ya amsa: “Ba ku karanta abin da Dauda ya yi ba, sa’anda ya ji yunwa, da waɗanda ke tare da shi.” (Matta 12:1-5) Babu shakka, waɗannan mutane masu adalcin kai sun karanta wannan hurarren labari da ke 1 Samu’ila 21:1-6. Idan haka ne, sun kasa fahimtar muhimmin darasi da ke ƙunshe cikinsa. Amma Yesu ya yi fiye da karanta labarin. Ya yi tunani a kan ma’anarsa kuma ya amince da darasi da za a koya daga ciki. Ya yi ƙaunar ƙa’idodi da Jehovah ya koyar ta wannan ayar. Ya yi amfani da labarin, da kuma misali daga Dokar Musa, don ya bayyana amfanin Dokar. Hakanan, ƙauna ta gaske ta Yesu ta motsa shi ya goyi bayan Kalmar Allah maimakon ƙoƙarin shugabanan addinai da suka rage ma’anarta don su amfani kansu ko kuma su ɓoye ta a ƙarƙashin al’adu na mutane da ke rikitarwa.

10. Ta yaya Yesu ya cika annabce-annabce game da ingancin koyarwarsa?

10 Ƙaunar Yesu ga gaskiyar da ya koyar ba za ta ƙyale shi ya koyar ta haddacewa, a hanyar da ke gajiyarwa ko kuma ta rashin tarbiyya ba. Hurarrun annabce-annabce sun ce Almasihu zai yi magana da ‘alheri a bisa leɓunansa,’ ya yi amfani da “nagargarun zantattuka.” (Zabura 45:2; Farawa 49:21) Yesu ya cika waɗannan annabce-annabce ta sa saƙonsa ya kasance da marmari kuma a bayyane, ya yi amfani da “zantattukan alheri” sa’ad da yake koyar da gaskiya da yake so sosai. (Luka 4:22) Babu shakka ƙwazonsa ya sa ya yi murmushi, idanunsa kuma sun nuna yana son darasi da ya koyar. Abu ne mai kyautarwa mu saurare shi, misali ne mai kyau da za mu bi sa’ad da muke gaya wa wasu game da abin da muka koya!

11. Me ya sa iyawar Yesu na malanta bai sa ya zama mai fahariya ba?

11 Yadda Yesu ya fahimci gaskiya ta Allah da yadda yake amfani da kalmomi da kyau ya sa shi ya zama mai fahariya ne? Sau da yawa haka yake faruwa tsakanin malamai ’yan Adam. Amma ka tuna cewa Yesu ya nuna hikima a hanyar da ta nuna yana tsoron Allah. Irin wannan hikima ba ta sa fahariya, domin “wurin masu-tawali’u akwai hikima.” (Misalai 11:2) Har yanzu da wani abin da ya sa Yesu bai zama mai fahariya ba ko kuma mai girman kai.

Yesu Ya Yi Ƙaunar Mutane da Ya Koyar da Su

12. Ta yaya Yesu ya nuna cewa ba ya son mabiyansa su ji tsoronsa?

12 Ƙaunar da Yesu yake yi wa mutane tana bayyana kullum a koyarwarsa. Koyarwarsa ba ta tsoratar da mutane, ba kamar na mutane masu fahariya ba. (Mai-Wa’azi 8:9) Bayan ya ga wata mu’ujiza da Yesu ya yi, Bitrus ya yi mamaki sosai, sai ya faɗi a gaban Yesu. Amma Yesu ba ya son mabiyansa su ji tsoronsa. Sai ya ce, “Kada ka ji tsoro” ya gaya wa Bitrus aikin almajirantarwa da zai sa hannu. (Luka 5:8-10) Yesu yana son ƙaunar gaskiya mai tamani game da Allah ta motsa almajiransa, ba tsoron malaminsu ba.

13, 14. A waɗanne hanyoyi ne Yesu ya nuna juyayi ga mutane?

13 An ga cewa Yesu ya yi ƙaunar mutane da ya koyar, ta juyayi da ya nuna musu. “Sa’anda ya ga taron, ya yi juyayi a kansu, domin suna wahala, suna watse kuma, kamar tumakin da ba su da makiyayi.” (Matta 9:36) Ya yi juyayinsu a yanayinsu na ban tausayi kuma ya motsa ya taimaka musu.

14 Ka lura da juyayin Yesu a wani yanayi. Sa’ad da wata mace mai zuban jini ta zo wajensa cikin jama’a kuma ta taɓa gezar rigarsa ta warke cikin mu’ujiza. Yesu ya ji iko ya bar jikinsa, amma bai ga wanda aka warkar ba. Ya nace ya nemi matar. Me ya sa? Ba don ya tuhume ta da karya Dokar ko ƙa’idodi na marubuta da Farisawa ba ne, da ƙila ta tsoraci hakan. Maimako, ya ce mata: “Ɗiya, bangaskiyarki ta warkarda ke; ki tafi lafiya, ki rabu da azabarki.” (Markus 5:25-34) Ka lura cewa da juyayi cikin waɗannan kalmomin. Bai ce kawai “Ki warke” ba. Amma, ya ce mata: “Ki rabu da azabarki.” Markus a nan ya yi amfani da kalma da a zahiri tana nufin “dūka,” irin dūka da sau da yawa ana amfani da ita wajen azabtar da mutum. Saboda haka, Yesu ya sani cewa ciwo da ta yi ya sa ta wahala, wataƙila ta sha azaba mai tsanani ta zahiri da ta zuciya. Ya ji tausayinta.

15, 16. Waɗanne aukuwa cikin hidimar Yesu ya nuna cewa abu mai kyau yake nema cikin mutane?

15 Yesu ya yi ƙaunar mutane ta neman hali mai kyau da suke da shi. Ka yi la’akari da abin da ya faru sa’ad da ya sadu da Natanayilu, wanda daga baya ya zama manzo. “Yesu ya ga Natanayilu yana zuwa gareshi, ya ambace shi, ya ce, Duba, ga mutumin Isra’ila na gaske, wanda ba shi da algus!” Ta mu’ujiza, Yesu ya dubi zuciyar Natanayilu, ya fahimci abubuwa da yawa game da shi. Babu shakka, Natanayilu ajizi ne. Yana da kasawarsa, yadda dukanmu muke da ita. Sa’ad da ya ji game da Yesu, ya yi magana mai ɓata rai: “Ya yiwu wani abu mai-kyau shi fito Nazarat?” (Yohanna 1:45-51) Amma, cikin abubuwa da za a iya faɗa game da Natanayilu, Yesu ya zaɓi abu mai kyau da zai mai da hankali a kai, amincin da yake da shi.

16 Hakanan ma, sa’ad da wani soja—wataƙila na Al’umma, ɗan Roma—ya je wajen Yesu yana nema a warkar da bawansa mai ciwo, Yesu ya sani cewa sojan yana da kasawarsa. Soja na lokacin, ƙila rayuwarsa ta cika da ayyukan nuna ƙarfi, kisa, da kuma bautar ƙarya. Duk da haka Yesu ya mai da hankali a kan abu mai kyau—bangaskiya ta musamman ta mutumin. (Matta 8:5-13) Bayan haka, sa’ad da Yesu ya yi magana da mugu da aka rataye kusa da shi, Yesu bai tsauta wa mutumin ba domin ayyukan muguntarsa ta dā amma ya ƙarfafa shi da bege na nan gaba. (Luka 23:43) Yesu ya sani cewa zargin wasu zai sa su kasala. Babu shakka, ƙoƙarinsa na neman abin da yake da kyau cikin wasu na ƙarfafa su su yi gyara.

Yi wa Mutane Hidima da Yardan Rai

17, 18. Da ya karɓi aiki ya zo duniya, ta yaya Yesu ya nuna yardan rai ya yi wa wasu hidima?

17 Wani tabbaci mai girma na ƙaunar Yesu ga mutane da ya koya musu, yardan ransa ne ya yi musu hidima. Kafin ya zama mutum, Ɗan Allah yana murna da ’yan Adam. (Misalai 8:30, 31) Da yake shi “Kalmar,” Jehovah ne ko kakakinsa, ya more hulɗa da mutane. (Yohanna 1:1) Domin ya koya wa mutane kai tsaye, “ya wofinta kansa da ya ɗauki surar bawa,” ya bar matsayinsa mai girma a sama. (Filibbiyawa 2:7; 2 Korinthiyawa 8:9) Da yake duniya, Yesu bai jira a yi masa hidima ba. Maimakon haka, ya ce: “Ɗan mutum ya zo ba domin a yi masa bauta ba, amma domin shi bauta ma waɗansu, shi bada ransa kuma abin fansar mutane dayawa.” (Matta 20:28) Yesu ya cika waɗannan kalmomi.

18 Yesu cikin tawali’u ya biya bukatar waɗanda ya koya musu, ba tare da jinkiri ba ya ba da kansa dominsu. Ya zazzagaya Ƙasar Alkawari a kar, ya yi tafiya ta ɗarurruwan miloli a wa’azi don ya kai ga mutane da yawa yadda zai yiwu. Ba kamar Farisawa da marubuta masu fahariya ba, ya kasance da tawali’u kuma yana da sauƙi a je wurinsa. Mutane iri-iri—masu ɗaukaka, sojoji, lauyoyi, mata, yara, matsiyata, majiyata, tsinannu—sun je wurinsa da farin ciki, ba tare da tsoro ba. Ko da yake kamiltacce ne, Yesu mutum ne, da yake gajiya kuma yake jin yunwa. Har a lokacin da ya gaji ma ko kuma yana bukatar hutu ko lokacin yin addu’a, ya saka bukatun wasu gaba da na shi.—Markus 1:35-39.

19. Ta yaya Yesu ya kafa misali a bi da almajiransa cikin tawali’u, haƙuri, da kuma alheri?

19 Yesu kuma yana shirye ya yi wa almajiransa hidima. Ya yi hakan ta koya musu a hankali kuma cikin haƙuri. Sa’ad da ba su fahimci muhimman darussa da sauri ba, bai gaji da su ba, bai fusata ba ko kuma ya tsauta musu. Ya ci gaba da neman sababbin hanyoyi ya taimaka musu su fahimta. Alal misali, ka yi tunanin lokatai da yawa da almajiran suka yi jayayya game da wanda ya fi girma tsakaninsu. A kai a kai, har dare kafin a kashe shi, Yesu ya nemi sababbin hanyoyi ya koya musu su bi da juna cikin tawali’u. A wannan batu na tawali’u, da wasu al’amura, Yesu ya ce: “Na yi muku kwatanci.”—Yohanna 13:5-15; Matta 20:25; Markus 9:34-37.

20. Wace hanyar koyarwa ce ta bambanta Yesu da Farisawa, me ya sa hanyar nan take da amfani?

20 Ka lura cewa Yesu bai gaya wa almajiran kwatancin ba kawai; ya ‘yi musu kwatanci.’ Ya koya musu da misali. Bai yi musu magana da reni ba kamar yana ɗaukan kansa mafifici ne, ya fi ƙarfin aikata abubuwa da ya gaya musu su yi. Haka Farisawa suke yi. “Su kan faɗi, ba su kuwa aikawa,” Yesu ya ce game da su. (Matta 23:3) Yesu cikin tawali’u ya nuna wa ɗalibansa daidai abin da koyarwarsa take nufi ta yin amfani da su. Saboda haka sa’ad da ya aririce mabiyansa su yi rayuwa mai sauƙi ba tare da son abin duniya ba, sun san abin da yake nufi. Sun ga hakikancin maganarsa: “Yanyawa suna da ramummuka, tsuntsayen sama kuma suna da sheƙuna; amma Ɗan mutum ba shi da wurin da za ya kwanta.” (Matta 8:20) Yesu ya yi wa almajiransa hidima ta yi musu kwatanci cikin tawali’u.

21. Menene za a bincika a talifi na gaba?

21 Babu tantama, Yesu ne babban Malami da ya taɓa rayuwa a duniya! Ƙaunarsa ga abin da ya koyar da ƙaunarsa ga mutane da ya koyar da su a bayyane suke ga dukan mutane masu zuciyar kirki da suka ga kuma suka ji shi. A bayyane yake a gare mu a yau da muke nazarin misali da ya kafa. To, ta yaya za mu bi misalin Kristi mafi kyau? Talifi na gaba zai amsa wannan tambayar.

Yaya Za Ka Amsa?

• Menene tushen koyarwa da kyau, kuma wa ya nuna?

• A waɗanne hanyoyi ne Yesu ya nuna ƙauna ga gaskiya da ya koyar?

• Ta yaya Yesu ya nuna ƙauna ga mutane da ya koyar da su?

• Waɗanne misalai suka nuna yardan Yesu ya yi wa waɗanda ya koyar da su hidima cikin tawali’u?

[Hoto a shafi na 6]

Ta yaya Yesu ya nuna cewa yana ƙaunar ƙa’idodi da ke cikin Kalmar Allah?

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba