-
Mulkin Allah Yana Sarauta!Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
-
-
2. Ta yaya abubuwa suka canja tun shekara ta 1914?
Almajiran Yesu sun tambaye shi cewa: “Mece ce alamar dawowarka da kuma ta ƙarshen zamani?” (Matiyu 24:3) Yesu ya annabta abubuwa da yawa da za su faru bayan ya soma sarauta a sama a matsayin Sarkin Mulkin Allah. Wasu daga cikin abubuwan sun ƙunshi yaƙi da yunwa da kuma girgizar ƙasa. (Karanta Matiyu 24:7.) Littafi Mai Tsarki ya kuma annabta cewa halayen mutane “a kwanakin ƙarshe” za su jawo “sha wahala sosai.” (2 Timoti 3:1-5) Abubuwan nan kuwa sun daɗa muni tun shekara ta 1914.
3. Me ya sa mugunta ta ƙaru bayan da aka kafa Mulkin Allah?
Jim kaɗan bayan da Yesu ya zama Sarkin Mulkin Allah, ya yaƙi Shaiɗan da aljannunsa a sama. Shaiɗan bai yi nasara ba. Littafi Mai Tsarki ya ce an jefo shi “duniya tare da mala’ikunsa.” (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 12:9, 10, 12) Shaiɗan yana cike da fushi domin ya san za a halaka shi. Saboda haka, ya sa wahala ta cika duka duniya. Shi ya sa duniya take cike da mugunta! Amma Mulkin Allah zai kawar da dukan matsalolin nan.
-
-
Mulkin Allah Yana Sarauta!Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
-
-
5. Duniya ta canja sosai tun daga shekara ta 1914
Yesu ya annabta yadda duniya za ta zama bayan ya zama Sarki. Ku karanta Luka 21:9-11, sai ku tattauna tambayar nan:
Wanne cikin waɗannan yanayoyin ne ka taɓa gani ko ji?
Manzo Bulus ya bayyana irin halayen da mutane za su kasance da su a kwanakin ƙarshe na sarautar ’yan Adam. Ku karanta 2 Timoti 3:1-5, sai ku tattauna tambayar nan:
Mutane suna nuna irin waɗannan halayen a yau kuwa?
6. Abin da Mulkin Allah zai sa mu yi
Ku karanta Matiyu 24:3, 14, sai ku tattauna tambayoyin nan:
Wane aiki na musamman ne ya nuna cewa Mulkin Allah ya soma sarauta?
Ta yaya za ka iya yin wannan aikin?
Mulkin Allah yana sarauta yanzu, kuma ranar da za ta mallaki dukan duniya ta kusa. Ku karanta Ibraniyawa 10:24, 25, sai ku tattauna tambayar nan:
Me ya kamata kowannenmu ya yi da yake “ranar nan tana matsowa kusa”?
Me za ka yi idan ka san abin da zai taimaka wa mutum ko kuma ya ceci rayuwarsa?
-