Abubuwa da Aka Annabta Za Su Faru a Zamaninmu
LITTAFI MAI TSARKI ya annabta cewa Mulkin Allah zai kawo salama ta dindindin da kuma farin ciki a duniya. (Daniel 2:44) A cikin Addu’ar Ubangiji, Yesu ya koya wa almajiransa yadda za su yi addu’a: “Mulkinka shi zo. Abin da ka ke so, a yi shi, cikin duniya, kamar yadda a ke yinsa cikin sama.” (Matta 6:10) A cikin sanannen annabcinsa da ya ba wa almajiransa a kan Dutsen Zaitun, Yesu ya annabta wasu abubuwa da za su faru da kuma yanayi da zai kasance har lokacin da Mulkin zai kawo canje-canje a duniya. Waɗannan duka alamu ne da mutane masu zuciyar kirki za su gani. Alamu guda nawa ne kake gani yanzu?
Yaƙe-Yaƙe a Dukan Duniya. Yesu ya annabta: “Al’umma za ta tasa ma al’umma, mulki kuma za ya tasa ma mulki.” (Matta 24:7) Kafin yaƙin duniya na farko a shekara ta 1914, yaƙe-yaƙe ba su bazu ba. Yaƙin Duniya na I ya shafi ƙasashe da yawa kuma ya sa an ƙara ƙera kayayyakin yaƙi da suka fi na dā ƙarfi wanda ’yan adam ba su taɓa ganin irin su ba. Alal misali, an ƙera wani sabon jirgin sama da zai riƙa jefa bam ga farar hula. Kayan yaƙi da aka ci gaba da ƙerawa sun jawo mutuwar mutane da yawa da ba a yi tsammani ba, hakan ya sa kusan rabin miliyan 65 na sojoji da suka je yaƙin sun mutu ko kuma sun ji rauni. Duk da haka, a cikin ƙarni na 20, mutane sun ci gaba da mutuwa a yaƙi. Wani ɗan tarihi ya ce ba za mu taɓa sanin ainihin adadin sojoji da farar hula da suka mutu a Yaƙin Duniya na II ba. Yaƙe-yaƙen sun ci gaba har yanzu.
Yunwa a Wurare Dabam Dabam. Yesu ya annabta: “Za a yi yunwa.” (Matta 24:7) A shekara ta 2005, jaridar Science ta ce: “Akwai mutane miliyan 854 a duniya (kusan kashi goma sha huɗu cikin ɗari na yawan jama’armu) da suke fama da rashin abinci sosai.” A shekara ta 2007, ƙungiyar Abinci da Aikin Noma ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ba da rahoto cewa ƙasashe 33 suna karancin abincin da za su ciyar da ƙasarsu. Yaya hakan zai faru bayan ana noman hatsi sosai? Hakan yana faruwa saboda ana amfani da ƙasa da ya kamata a yi noma da kuma hatsi da mutane za su ci, a yi man fetur. Wata jarida daga Afirka ta Kudu mai suna The Witness ta ce: “Yawan man fetur da ake bukata don a cika babban mota sau ɗaya zai iya ciyar da mutum ɗaya na shekara.” A ƙasashe da suka bunƙasa ma, ƙarin farashin abinci ya sa mutane da yawa su zaɓi tsakanin cin abincin yamma ko kuma biyan kuɗin magani.
Girgizan Ƙasa Masu Tsanani. Yesu ya ce: “Za a yi raurawar ƙasa manya manya.” (Luka 21:11, LMT) Idan ka ce girgizan ƙasa na shafan mutane da yawa yanzu, gaskiya kake faɗa. A shekara ta 2007, R. K. Chadha wani ɗan Indiya mai ilimin girgizan ƙasa ya ce: “Yanzu muna ganin abubuwan da suke sa girgizan ƙasa ta yi yawa a dukan duniya. Babu wanda ya san dalilin.” Bugu da ƙari, yawan mutane a wuraren da girgizan ƙasa take yawan faruwa ya jawo mutuwar mutane da yawa. Wani binciken ilimin sanin ma’addinai a Amirka ya ce, girgizan ƙasa da ta faru a Tekun Indiya a shekara ta 2004 da kuma tsunami da ya biyo baya sun sa shekarar nan ta zama “shekarar da aka yi mutuwa sosai a cikin shekaru 500 na tarihin girgizan ƙasa.”
Cututtuka da Suke da Wuyan Magancewa. Yesu ya ce: “Za a yi . . . annoba.” (Luka 21:11) A duniya duka, sanannun cututtuka da kuma sababbi suna damun mutane da yawa, kuma da wuya a sami maganinsu. Alal misali, an yi ƙoƙari a kawar da zazzaɓin ciwon sauro a kai a kai a dukan duniya, amma cutar ta fi ƙarfin mutane. Tarin fuka da wasu sababbin cututtuka suna kashe mutane da yawa, (wato, wasu suna mutuwa don tarin fuka, Sida, da kuma wasu sababbin cututtuka.) Ƙungiyar kiwon lafiya ta duniya ta ce: “Kashi ɗaya cikin uku na mutane a duniya sun kamu da cutar fuka.” Ƙungiyar ta kuma lura cewa cutar Sida ce take kawo cutar fuka a ƙasashe da yawa. Kowane daƙiƙa, wani ya kamu da tarin fuka, kuma tarin fuka baya jin magani. Wata jaridar New Scientist ta ce: A shekara ta 2007 a Turai, wani yana da tarin fuka da “ta ƙi jin dukan magungunan da muke da su.”
Lalacewar Ɗabi’a da Zama da Mutane. Yesu ya ce: “Saboda yawaita da mugunta za ta yi kuma, ƙaunar yawancin mutane za ta yi sanyi.” (Matta 24:12) Bayan annabcin da Yesu ya yi, manzo Bulus ya annabta yadda dabi’a za ta lalace a nan gaba. Ya kwatanta “kwanaki na ƙarshe” mai wuya da za ta kasance kafin Mulkin Allah ta halaka wannan zamanin. “Gama mutane za su zama masu-son kansu, masu-son kuɗi, masu-ruba, masu-girman kai, masu-zagi, marasa-bin iyaye, marasa-godiya, marasa-tsarki, Marasa-ƙauna irin na tabi’a, masu-baƙar zuciya, masu-tsegumi, marasa-kamewa, masu-zafin hali, marasa-son nagarta, masu-cin amana, masu-taurin kai, masu-kumbura, ma-fiya son annishuwa da Allah; suna riƙe da surar ibada, amma sun musunci ikonta.” (2 Timothawus. 3:1-5) Kana ganin mutane suna nuna irin waɗannan mugayen halayen fiye da dā?
Yesu da Bulus ba su ambata dukan abubuwa da suka sa yanayin duniya ta canja ba. Duk da haka, annabcinsu sun nuna abubuwa da kuma irin halayen da muke gani a yau. A nan gaba kuma fa? Annabcin Ishaya da ya ambata zuwan Almasihu ya kwatanta canje-canje da Mulkin Allah zai kawo a duniya. Bari mu tattauna waɗannan a talifi na gaba.
[Hoto a shafi na 6]
“Al’umma za ta tasa ma al’umma”
[Hoto a shafi na 7]
“Za a yi . . .annoba”
[Inda aka Dauko]
© WHO/P. Virot