Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w05 2/1 pp. 7-11
  • Annabcin Mulkin Allah Ya Tabbata

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Annabcin Mulkin Allah Ya Tabbata
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Sa’ad da Annabci ya Tabbata
  • Kristi Ya Gama Cin Nasara
  • An Yi Watsi da Begen Mulki
  • Ka Yi Shiri Domin Babbar Ranar Allah
  • Ka Natsu
  • Ka Saurara Ga Kalmomin Annabci Na Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Domin Kristi Aka Yi Annabce-annabce
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Ka Kasance Da Bangaskiya Cikin Kalmomin Annabci Na Allah!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
w05 2/1 pp. 7-11

Annabcin Mulkin Allah Ya Tabbata

“Ya kuwa kyautu a gare ku ku mai da hankali gare ta [kalmar annabci], kamar fitila take mai haskakawa a wuri mai duhu.”—2 BITRUS 1:19.

1. Wane bambanci ne muke gani a duniya a yau?

TARZOMA ta zama ruwan dare gama duniya a yau. Matsalolin mutane sai daɗa ƙaruwa suke yi, daga gurɓacewar ƙasa zuwa ta’addanci a dukan duniya. Har ma addinai na duniya sun kasa taimakawa. Sau da yawa suna ƙara munanta al’amura ta wajen hura wutar son ƙasa, ƙiyayya, da kuma kishin ƙasa da ke rarraba kan mutane. Hakika, kamar yadda aka annabta, “Duhu” ya rufe “sauran al’umma.” (Ishaya 60:2) Amma kuma, akwai miliyoyi da suke duba gaba da gaba gaɗi. Me ya sa? Domin suna mai da hankali ga maganar annabci ta Allah wadda “kamar fitila take mai haskakawa a wuri mai duhu.” Sun yarda “maganar” Allah, da ke cikin Littafi Mai Tsarki ta yi musu ja-gora.—2 Bitrus 1:19.

2. In ji annabcin Daniyel game da “ƙarshen lokaci,” su wanene suka sami gatar fahimtar abubuwa na ruhaniya?

2 Game da “ƙarshen lokaci,” annabi Daniyel ya rubuta: “Mutane da yawa za su yi ta kai da kawowa, ilimi kuma zai ƙaru. Mutane da yawa za su tsarkake kansu, su zama masu tsabta tsab tsab, amma mugaye ba za su gane ba, za su yi ta muguntarsu, amma masu hikima za su gane.” (Daniyel 12:4, 10) An keɓe fahimtar abubuwa na ruhaniya wa waɗanda suke “kai da kawowa” da gaske wajen yin nazarin Kalmar Allah sosai, suna ba da kai ga mizanansa, kuma suke ƙoƙarin yin nufinsa.—Matiyu 13:11-15; 1 Yahaya 5:20.

3. A cikin shekarun 1870, wace muhimmiyar gaskiya ce ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka fahimta?

3 Tun farkon shekarun 1870, kafin somawar “zamanin ƙarshe,” Jehobah Allah ya soma ƙara ba da haske a kan “asiran Mulkin Sama.” (2 Timoti 3:1-5; Matiyu 13:11) A lokacin, wasu rukunin ɗalibai na Littafi Mai Tsarki suka gano cewa dawowar Kristi marar ganuwa ne, kuma hakan ya bambanta da ra’ayin mutane. Bayan an ɗora shi a kan kursiyi a sama, Yesu zai dawo a azancin maido hankalinsa ga duniya. Akwai alamar da almajiransa za su gani da za ta nuna musu cewa bayyanuwar Kristi marar ganuwa ya soma.—Matiyu 24:3-14.

Sa’ad da Annabci ya Tabbata

4. Ta yaya ne Jehobah ya ƙarfafa bangaskiyar bayinsa na zamani?

4 Wahayin sake kamani alama ce ta Kristi a cikin ɗaukakar Mulki. (Matiyu 17:1-9) Wannan wahayin ya ƙarfafa bangaskiyar Bitrus, Yakubu, da Yahaya sa’ad da mutane da yawa suka daina bin Yesu domin ya ƙi cika ra’ayoyinsu wanda ba su jitu da nassi ba. Hakazalika, a wannan lokaci na ƙarshe, Jehobah ya ƙarfafa bangaskiyar bayinsa na zamani ta wajen ƙara ba da haske a kan cikar wannan wahayi mai ban mamaki da kuma sauran annabce-annabce da suke da nasaba da shi. Bari mu tattauna wasu daga cikin waɗannan tabbaci na ruhaniya da ke ƙarfafa bangaskiya yanzu.

5. Wanene Gamzaki mai haske, yaushe kuma ta yaya ya “bayyana”?

5 Sa’ad da yake maganar sake kamani, manzo Bitrus ya rubuta: “Har wa yau kuma aka ƙara tabbatar mana da maganar annabcin nan, ya kuwa kyautu a gare ku ku mai da hankali gare ta, kamar fitila take mai haskakawa a wuri mai duhu har ya zuwa asubahin ranan nan, gamzaki kuma yā bayyana a zukatanku.” (2 Bitrus 1:19) “Gamzaki mai haske,” shi ne Yesu Kristi da aka ɗaukaka. (Wahayin Yahaya 22:16) Ya “bayyana” a shekara ta 1914 sa’ad da aka kafa Mulkin Allah a sama wanda ke nuna somawar sabuwar zamani. (Wahayin Yahaya 11:15) A cikin wahayin sake kamani, Musa, da Iliya sun bayyana a gefen Yesu, suna tattaunawa da shi. Wanene suke wakilta?

6, 7. Su wanene suke wakiltan Musa da Iliya a cikin sake kamani, kuma waɗanne muhimman bayanai ne Nassosi suka bayyana game da su?

6 Tun da yake Musa da Iliya sun bayyana a ɗaukakar Kristi, waɗannan shaidu amintattu guda biyu dole ne su wakilci waɗanda suke sarauta da Yesu a Mulkinsa. Fahimtar cewa Yesu yana da abokanan sarauta ta jitu da wahayi na alama na Almasihu da aka ɗaura a kan kursiyi wanda annabi Daniyel ya gani. Daniyel ya ga “wani kamar Ɗan Mutum” yana karɓan ‘madawwamin mulki’ daga wurin “wanda yake Tun Fil Azal,” Jehobah Allah. Ka lura da abin da aka nuna wa Daniyel ba da daɗewa ba bayan haka. Ya rubuta: “Sa’an nan za a ba da sarauta da girman dukan mulkokin duniya ga tsarkaka na Maɗaukaki.” (Daniyel 7:13, 14, 27) Hakika, fiye da ƙarni biyar kafin aukuwar sake kamani, Allah ya bayyana cewa wasu masu “tsarkaka” za su saka hannu a sarautar Kristi.

7 Su wanene masu tsarkaka da ke cikin wahayin Daniyel? Game da waɗannan mutanen ne manzo Bulus ya ce: “Ruhu kansa ma tare da namu ruhu suna yin shaida, cewa mu ’ya’yan Allah ne. In kuwa ’ya’ya muke, ashe, magada ne kuma, magadan Allah, abokan gādo kuma da Almasihu, in dai har muna shan wuya tare da shi, a kuwa ɗaukaka mu tare.” (Romawa 8:16, 17) Masu tsarkakan sune almajiran Yesu waɗanda aka shafa da ruhu. A cikin Wahayin Yahaya, Yesu ya ce: “Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi iznin zama tare da ni a kursiyina, kamar yadda ni ma na ci nasara, na kuma zauna tare da Ubana a kursiyinsa.” Waɗannan masu “nasara” da aka ta da daga matattu wanda adadinsu 144,000 ne, za su yi mulki bisa duniya tare da Yesu.—Wahayin Yahaya 3:21; 5:9, 10; 14:1, 3, 4; 1 Korantiyawa 15:53.

8. Ta yaya ne shafaffun almajiran Yesu suke irin aikin Musa da Iliya, kuma da wane sakamako?

8 Me ya sa Musa da Iliya suke wakiltan Kiristoci shafaffu? Dalili shi ne, sa’ad da waɗannan Kiristocin suke duniya, suna irin aikin da Musa da Iliya suka yi. Alal misali, sun yi wa Jehobah shaida, duk da tsanantawa. (Ishaya 43:10; Ayyukan Manzanni 8:1-8; Wahayin Yahaya 11:2-12) Kamar Musa da Iliya, suna fallasa addinin ƙarya da gaba gaɗi, sa’an nan kuma suna yi wa sahihan mutane gargaɗi su bauta wa Allah shi kaɗai. (Fitowa 32:19, 20; Maimaitawar Shari’a 4:22-24; 1 Sarakuna 18:18-40) Aikinsu ya ba da amfani kuwa? Babu shakka! Ban da taimakawa da suke yi na tattara sauran shafaffu, sun kuma taimaka wa miliyoyin “waɗansu tumaki” su miƙa kai ga Yesu Kristi.—Yahaya 10:16; Wahayin Yahaya 7:4.

Kristi Ya Gama Cin Nasara

9. Ta yaya ne Wahayin Yahaya 6:2 ta kwatanta yadda Yesu yake a yau?

9 Yanzu Yesu ba mutum ba ne kamar lokacin da ya hau jaki, amma Sarki ne mai iko. An kwatanta shi a kan doki—wadda alama ce ta yaƙi a Littafi Mai Tsarki. (Karin Magana 21:31) “Duba, ga farin doki,” in ji Wahayin Yahaya 6:2, “mahayinsa kuma yana da baka, aka ba shi kambi, ya kuwa fita yana mai nasara domin ya ƙara cin nasara.” Bugu da ƙari, game da Yesu, mai zabura Dauda ya rubuta: “Tun daga Sihiyona Ubangiji zai faɗaɗa sarautarka, ya ce, ‘Ka yi mulki bisa maƙiyanka.’ ”—Zabura 110:2.

10. (a) Ta yaya ne hawan da Yesu ya yi na cin nasara ke da ɗaukaka? (b) Ta yaya ne nasarar da Kristi ya fara samu ta shafi duniya gaba ɗaya?

10 Yesu ya soma samun nasara ne a kan abokan gabansa masu ƙarfi—Shaiɗan da aljanunsa. Ya fitar da su daga sama zuwa duniya. Domin sun sani cewa suna da ɗan ƙanƙanin lokaci, waɗannan mugayen ruhohi suna nuna muguwar fushinsu a kan mutane, kuma suna jawo kaito. A cikin Wahayin Yahaya alamar wannan kaiton mahayan dawakai uku ne. (Wahayin Yahaya 6:3-8; 12:7-12) Daidai da annabcin Yesu game da ‘alamar dawowarsa, da ta ƙarewar zamani,’ hawan dokin da suka yi ya jawo yaƙi, yunwa, da muguwar annoba. (Matiyu 24:3, 7; Luka 21:7-11) Kamar naƙuda, “azaba” za ta ci gaba da ƙaruwa har sai Kristi ya gama “cin nasara” sa’ad da ya share duk wata alamar ƙungiyar Shaiɗan da ake gani a duniya.a—Matiyu 24:8.

11. Ta yaya ne tarihin ikilisiyar Kirista ta tabbatar da ikon sarauta na Kristi?

11 Ikon Yesu na sarauta ya bayyana da ya kāre ikilisiyar Kirista don ta cika umurnin da ya ba ta na yin wa’azin saƙon Mulki a dukan duniya. Duk da tsanantawa ta zalunci daga Babila mai Girma, daular duniya ta addinin ƙarya, da kuma gwamnatoci masu hamayya, aikin wa’azi ya ci gaba kuma ya sami ƙaruwa sosai a cikin tarihin ’yan adam. (Wahayin Yahaya 17:5, 6) Lallai, wannan tabbaci ne mai ƙarfi na sarautar Kristi!—Zabura 110:3.

12. Me ya sa mutane da yawa ba su gane bayyanuwar Kristi marar ganuwa ba?

12 Abin baƙin ciki, yawancin mutane har da miliyoyin da suke da’awar cewa su Kiristoci ne, sun kasa gano waɗanda ba su ganuwa, da suke haddasa abubuwan da ke faruwa a duniya. Har ma suna yi wa masu sanar da Mulkin Allah ba’a. (2 Bitrus 3:3, 4) Me ya sa? Domin Shaiɗan ya makantar da hankalinsu. (2 Korantiyawa 4:3, 4) Shaiɗan ya soma makantar da waɗanda suke da’awar cewa su Kiristoci ne da duhu na ruhaniya tun ƙarnuka da yawa da suka wuce, har ma ya sa sun yi watsi da begen Mulki mai tamani.

An Yi Watsi da Begen Mulki

13. Menene duhu na ruhaniya ya jawo?

13 Yesu ya annabta cewa ’yan ridda, da suka yi kama da irin ciyawa da aka shuka a tsakiyar iri mai kyau, za su shiga cikin ikilisiyar Kirista su janye mutane da yawa. (Matiyu 13:24-30, 36-43; Ayyukan Manzanni 20:29-31; Yahuza 4) Da sannu sannu, waɗannan da suke da’awar cewa su Kiristoci ne, suka fara yin bukukuwan arna, ayyukansu, da koyarwarsu, har ma suna kiransu bukukuwan “Kiristoci.” Alal misali, Kirsimati ya samo tushe ne daga bautar allolin ƙarya Mithra da Saturn. Amma menene ya zuga waɗannan masu da’awa cewa su Kiristoci ne yin irin waɗannan bukukuwa da ba na Kiristoci ba? In ji littafin nan The New Encyclopædia Britannica (1974) (Kundin Sani na Britaniya): “An kafa Kirsimati, bikin haihuwar Yesu Kristi, domin rashin sauraron dawowar Kristi da ya kurkusa.”

14. Ta yaya ne koyarwar Origen da Augustine suka murguɗa gaskiyar Mulki?

14 Ka yi la’akari da yadda aka karkata ma’anar kalmar nan “mulki.” Littafin nan The Kingdom of God in 20th-Century Interpretation (Mulkin Allah a Fassarar Ƙarni na 20) ya ce: “Origen [wani ɗan tauhidi a ƙarni na uku] ne ya canja yadda Kirista ke amfani da kalmar nan ‘mulki’ zuwa sarautar Allah na cikin zuciya.” A kan wane tushe ne Origen ya kafa koyarwarsa? Ba a kan Nassosi ba ne, amma “a kan ra’ayin falsafa da kuma na duniya waɗanda sun bambanta da tunanin Yesu da na cocin farko.” A cikin littafinsa De Civitate Dei (Birnin Allah), Augustine na Hippo (354-430 A.Z.) ya ce coci ne Mulkin Allah. Irin wannan tunanin da ya saɓa wa Nassosi ya sa cocin Kiristendom su karɓi ikon siyasa. Kuma sun yi amfani da wannan ikon wajen zalunci a ƙarnuka masu yawa.—Wahayin Yahaya 17:5, 18.

15. Ta yaya ne Galatiyawa 6:7 ta sami cika game da yawancin cocin Kiristendom?

15 A yau, coci yana girbe abin da ya shuka. (Galatiyawa 6:7) Da yawa sun fara rasa ikon da suke da shi har da mabiyansu. Wannan shi ne abin da ke faruwa a ƙasashen Turai. In ji jaridar nan Christianity Today, (Kiristanci a Yau) “manyan cocin Turai yanzu ba wuraren yin ibada ba ne, sun zama ma’adanar kayayyakin tarihi, in da ba ka ganin kowa sai ’yan ziyara kawai.” Kana iya ganin makamancin wannan a wasu ɓangarorin duniya. Wace alama ce wannan ke nuna wa addinin ƙarya? Za ta halaka ne domin rashin taimako? Ta yaya ne hakan zai shafi ibada ta gaskiya?

Ka Yi Shiri Domin Babbar Ranar Allah

16. Me ya sa ƙiyayya da ke ƙaruwa bisa Babila Babba ke da muhimmanci?

16 Kamar yadda hayaƙi da toka da ke fitowa daga kan dutse ke ba da alamar aukuwar gobarar dutse, haka nan ƙiyayya na addini da ke ƙaruwa a wasu ɓangarorin duniya ke nuna cewa ƙarshen addinin ƙarya ya kusa. Nan ba da daɗewa ba, Jehobah zai sa ’yan siyasa na duniya su haɗa hannu domin su fallasa kuma su halaka karuwa ta ruhaniya, Babila Babba. (Wahayin Yahaya 17:15-17; 18:21) Ya kamata Kiristoci na gaskiya su ji tsoron wannan aukuwa da sauran abubuwa da za su biyo bayan “matsananciyar wahala” kuwa? (Matiyu 24:21) Ko kaɗan! Domin za su sami dalilai na yin farin ciki sa’ad da Allah ya aikata bisa miyagu. (Wahayin Yahaya 18:20; 19:1, 2) Yi la’akari da misalin Urushalima ta ƙarni na farko da kuma Kiristocin da ke zaune a cikin ta.

17. Me ya sa bayin Jehobah masu aminci suke iya fuskantar ƙarshen wannan zamanin da gaba gaɗi?

17 Sa’ad da sojojin Roma suka kewaye Urushalima a shekara ta 66 A.Z., hakan bai ba Kiristoci da suke a faɗake a ruhaniya tsoro ko mamaki ba. Domin ɗalibai ne masu nazarin Kalmar Allah sosai, sun sani cewa “ana kusan ribɗe ta.” (Luka 21:20) Sun san cewa Allah zai buɗe musu hanyar da za su sami tsira. Sa’ad da hakan ya faru, Kiristoci sun gudu. (Daniyel 9:26; Matiyu 24:15-19; Luka 21:21) Hakazalika a yau, waɗanda suka san Allah kuma suke yi wa Ɗansa biyayya, za su iya fuskantar ƙarshen wannan zamanin da gaba gaɗi. (2 Tasalonikawa 1:6-9) Hakika, sa’ad da matsananciyar wahala ta auku, cikin murna za su ‘ɗaga kai su dubi sama, domin sun san cewa fansarsu ta yi kusa.’—Luka 21:28.

18. Menene zai kasance sakamakon hari na ƙarshe da Gog zai kai wa bayin Jehobah?

18 Bayan an halakar da Babila Babba, Shaiɗan wanda shi ne Gog na Magog, zai kai wa Shaidun Jehobah masu salama hari na ƙarshe. “Kamar yadda girgije yakan rufe sararin sama,” rundunar Gog za su yi zaton samun nasara cikin sauƙi. Za su sha mamaki kuwa! (Ezekiyel 38:14-16, 18-23) Manzo Yahaya ya rubuta: “Sai na ga sama ta dāre, sai ga wani farin doki! Mahayinsa kuwa ana ce da shi Amintacce . . . Daga cikin bakinsa wani kakkaifan takobi ke fitowa, wanda zai sare al’ummai da shi.” Wannan “Sarkin sarakuna” marar ganuwa zai ceci bayin Jehobah masu aminci kuma zai halaka dukan maƙiyansu. (Wahayin Yahaya 19:11-21) Wannan zai kawo ƙarshen cikar wahayin sake kamani!

19. Ta yaya ne nasarar da Kristi zai samu za ta shafi almajiransa masu aminci, kuma menene ya kamata su ƙoƙarta su yi yanzu?

19 “Duk masu ba da gaskiya kuma [za] su yi al’ajabinsa [Yesu] a ranan nan.” (2 Tasalonikawa 1:10) Kana son ka kasance a cikin waɗanda za su ɗaukaka Ɗan Allah a lokacin da zai sami nasara? Sai ka ci gaba da gina bangaskiyarka kuma ‘ka zauna a kan shiri, domin a lokacin da ba ka zata ba, Ɗan Mutum zai zo.’—Matiyu 24:43, 44.

Ka Natsu

20. (a) Ta yaya ne za mu iya nuna godiyarmu ga tanadin da Allah ya yi na “amintaccen bawan nan”? (b) Waɗanne tambayoyi ne ya kamata mu yi wa kanmu?

20 “Amintaccen bawan nan” yana yi wa mutanen Allah gargaɗi a kowane lokaci su kasance a faɗake a ruhaniya kuma su kasance da natsuwa. (Matiyu 24:45, 46; 1 Tasalonikawa 5:6) Kana nuna godiya ga wannan tunasarwa na kan kari kuwa? Kana amfani da su wajen daidaita makasudi na rayuwanka? Ka tambayi kanka: ‘Na fahimci wahayi na ruhaniya da zai sa in gane cewa Ɗan Allah yana mulki a sama kuwa? Ina ganinsa a shirye zai zartar da hukuncin Allah a kan Babila Babba da kuma sauran zamanin Shaiɗan?’

21. Me ya sa wasu suka yi hasarar fahiminsu na ruhaniya, kuma me ya kamata su yi da gaggawa?

21 Wasu da suke tarayya da mutanen Jehobah sun yi hasarar fahiminsu na ruhaniya. Sun yi rashin jimiri ne kamar yadda wasu a cikin almajiran Yesu na farko suka yi? Son abin duniya, alhinin rayuwa, ko tsanani ne ya shafe su? (Matiyu 13:3-8, 18-23; Luka 21:34-36) Wataƙila wasu sun iske wani bayani da “amintaccen bawan nan mai hikima” ya buga da wuyar fahimta. Idan ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa ya faru a gare ka, muna ariritarka ka yi nazarin Kalmar Allah da sabuwar ƙwazo kuma ka roƙi Jehobah domin ka sake samun dangantaka mai kyau da shi.—2 Bitrus 3:11-15.

22. Ta yaya ne tattauna wahayin sake kamani da kuma annabce-annabce da suke da nasaba da shi suka shafe ka?

22 An bai wa almajiran Yesu wahayin sake kamani ne sa’ad da suke bukatar ƙarfafa. A yau muna da wani abu mafi girma da zai ƙarfafa mu—cikar sake kamani da sauran annabce-annabce da suke da nasaba da shi. Yayin da muke bimbini a kan wannan tabbataccen ɗaukaka da kuma muhimmancinsu na gaba, bari mu furta da dukan zuciyarmu abin da manzo Yahaya ya ce: “Amin. Zo, ya Ubangiji Yesu.”—Wahayin Yahaya 22:20.

[Hasiya]

a A Helenanci na asali, kalmar nan “azaba” a zahiri tana nufin “naƙuda.” (Matiyu 24:8, Kingdom Interlinear) Wannan ya nuna cewa kamar naƙuda, matsaloli a duniya za su ƙaru, wanda hakan zai kawo matsananciyar wahala.

Ka Tuna?

• Menene wani ƙaramin rukuni na ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka fahimta game da dawowar Kristi a shekarun 1870?

• Ta yaya ne wahayin sake kamani ya cika?

• Ta yaya ne hawan da Yesu ya yi na yin nasara ya shafi duniya da kuma ikilisiyar Kirista?

• Menene za mu yi idan muna son mu kasance a cikin waɗanda za su sami ceto sa’ad da Yesu ya gama yin nasara?

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba