-
Su Waye Ne Suke Wa’azin Bishara?Hasumiyar Tsaro—2011 | 1 Afrilu
-
-
Su Waye Ne Suke Wa’azin Bishara?
“ . . . za a yi wa’azinta cikin iyakar duniya.”—MATTA 24:14.
SHAIDUN Jehobah ne suke yin wa’azin bishara a dukan duniya. Suna yin hakan a hanyoyi dabam-dabam. Hanya ɗaya ita ce . . .
Ta Maganar Baki. Kamar Yesu da almajiransa, Shaidun Jehobah suna kai wa mutane bishara. (Luka 8:1; 10:1) Ba sa sa rai cewa mutane za su zo wurinsu. Yin wa’azi ga mutane game da Mulkin Allah wani abu ne da dukan Shaidu fiye da miliyan bakwai suke yi. Suna yin wa’azi daga gida zuwa gida, a kan hanya, ta hanyar tarho, da wasu hanyoyi dabam-dabam. A shekarar da ta shige, Shaidu sun yi amfani da awoyi fiye da biliyan ɗaya da rabi a wannan aikin.
Suna koya wa mutane game da Mulkin Allah da kuma ‘dukan iyakar abin da Yesu ya umurta.’ (Matta 28:20) Suna yin nazarin Littafi Mai Tsarki na gida kyauta fiye da miliyan takwas a kai a kai.
Shaidu suna yin wa’azi a dukan duniya a ƙasashe 236. Suna yin wa’azi ga kowa. Suna yin wa’azi a birni da ƙauye, a kurmin Amazon da na Siberia, a hamadar Afirka da Duwatsun Himalaya. Ba a biyan su kuɗi domin wannan aikin, suna amfani ne da kuɗinsu da kuma lokacinsu, ƙaunar da suke yi wa Allah da kuma maƙwabtansu ne take motsa su. Suna kuma yin shelar bisharar ta hanyar . . .
Littattafai. Ana buga wannan mujallar, wadda cikakken jigonta ita ce Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah, a harsuna 185 kuma ana rarraba fiye da miliyan 42 a kowace fitowa. Ana buga mujallar nan Awake!, wadda ita ma tana shelar Mulkin, a harsuna 83 kuma ana rarraba wajen miliyan 40 a kowace fitowa.
Akwai littattafai, mujallu, warƙoƙi, fayafayan CD/MP3, da DVD da suke bayyana koyarwar Littafi Mai Tsarki a harsuna 540. Shaidu sun buga kuma sun rarraba fiye da kofi biliyan 20 na waɗannan abubuwan a cikin shekaru goma da suka shige, hakan yana nufin cewa kowane mutum guda a duniya zai iya samun wajen guda uku na waɗannan abubuwan!
Shaidun Jehobah sun buga fassarar Littafi Mai Tsarki dabam-dabam ko kuma sun ba da aikin yin hakan ga wasu. A yanzu za a iya samun New World Translation of the Holy Scriptures, gabaki ɗayansa ko rabinsa wanda Shaidu ne suka fassara shi, suka buga shi kuma suka rarraba shi, a harsuna 96. An rarraba fiye da miliyan 166. Shaidu suna kuma yaɗa bisharar Mulkin . . .
A Taron Kirista. Taron da ake yi a kowane mako a Majami’un Mulki ba hidimar addini kawai ba ne; an tsara su ne don ilimantarwa. Ana ba da jawabai a kan batutuwa dabam-dabam daga cikin Littafi Mai Tsarki, ana kuma yin nazarin Littafi Mai Tsarki ta wajen yin amfani da Hasumiyar Tsaro da wasu littattafai. A waɗannan taron, Shaidu suna koyan yadda za su ƙara ƙwarewa a shelar bishara.
Shaidu suna nazarin abubuwa iri ɗaya a cikin ikilisiyoyi fiye da 107,000 a dukan duniya, kuma hakan yana ƙarfafa haɗin kansu. Kowa zai iya halartan waɗannan taron. Ba a yawo da tire don a karɓi kuɗi a taron sam. Hakika, dukan waɗannan abubuwan za su zama banza idan Shaidu suka ƙi aikata abin da suke yin wa’azinsa. Saboda haka, suna yin bisharar . . .
Ta Wurin Halayen Su. Suna ƙoƙartawa su kasance da hali mai kyau na Kirista, ta wajen bi da mutane a hanyar da za su so mutane su bi da su. (Matta 7:12) Ko da yake su ajizai ne kuma a wasu lokatai sukan kasa, suna son su nuna ƙauna ga dukan mutane ba kawai ta wajen yaɗa bishara ba amma ta wajen ba da taimako a duk lokacin da hakan ya yiwu.
Ba wai Shaidun Jehobah suna son su juya dukan duniya ta hanyar wa’azinsu ba ne. A maimakon haka, sa’ad da Jehobah ya gamsu da aikin, ƙarshen zai zo, kamar yadda Yesu ya annabta. Mene ne hakan yake nufi ga duniya da kuma mutanen da ke cikinta?
[Hoton da ke shafi na 7]
Shaidun Jehobah suna wa’azin bisharar a dukan duniya
-
-
Mene Ne “Ƙarshen”?Hasumiyar Tsaro—2011 | 1 Afrilu
-
-
Mene Ne “Ƙarshen”?
“. . . sa’an nan kuma sai ƙarshen ya zo.”—MATTA 24:14, Littafi Mai Tsarki.
A KWANAN nan, yin magana game da ƙarshen duniya ya zama ruwan dare. Littattafai, siliman, da jaridu na ban dariya da kuma na kimiya, suna nuna yadda ƙarshen duniya za ta zo a fasaloli dabam-dabam. Hakan ya haɗa da yin yaƙi da makaman nukuliya, da kuma karon da duwatsun da suke kewaye rana za su yi kuma su faɗo duniya, ƙwayoyin muguwar cuta, har da canjin yanayi da aka kasa sarrafawa.
Ra’ayoyin addinai ma sun bambanta; addinai da yawa suna koyar da cewa “ƙarshen” zai halaka dukan wani abu mai rai a duniya. Sa’ad da yake furuci game da Matta 24:14, wani ɗan tauhidi ya rubuta waɗannan kalmomi masu ban tsoro: “Wannan ayar tana ɗaya daga cikin ayoyi mafi muhimmanci a cikin dukan Kalmar Allah . . . Tsaranmu yana fuskantar halaka mai girma kuma mutane da yawa sun kasa hangar wannan mummunar halakar da ke tafe.”
Irin waɗannan ra’ayoyin sun yi watsi da wata gaskiya mai muhimmanci: Jehobah Allah ya “kafa” duniya; ya “halicce ta ba wofi ba, [amma] ya kamanta ta domin wurin zama.” (Ishaya 45:18) Saboda haka, sa’ad da Yesu ya yi maganar “ƙarshen,” ba ya nufin cewa za a halaka duniya, ko kuma za a share ’yan Adam gabaki ɗaya daga doron duniya ba. Abin da yake nufi shi ne, za a halaka miyagu, waɗanda suka ƙi yin rayuwar da ta jitu da ja-gora mai kyau na Jehobah.
Ka yi la’akari da wannan misalin. A ce kana da gida mai kyau kuma ka yarda mutane su zauna a cikinsa kyauta. Wasu daga cikin mazauna gidan suna zaune lafiya da juna kuma suna kula da gidanka sosai. Amma, sauran fitinannu ne, suna faɗa da juna, kuma suna zagin sauran mazauna gidan da suke da hali mai kyau. Sun lalata dukiyarka kuma sun yi kunnen uwar shegu ga duk ƙoƙarce-ƙoƙarcen da ka yi na hana su yin hakan.
Mene ne za ka yi don ka magance wannan matsalar? Za ka rushe gidanka ne? Da ƙyar. Wataƙila abin da za ka yi shi ne, za ka kori fitinannun da ke zaune a gidanka kuma ka gyara ɓarnar da suka yi.
Abin da Jehobah zai yi ke nan. Ya hure mai zabura ya rubuta: “Za a datse masu-aika mugunta: amma waɗanda ke sauraro ga Ubangiji, su ne za su gāji duniya. Gama in an jima kaɗan, sa’annan mai-mugunta ba shi: Hakika, da anniya za ka duba wurin zamansa, ba kuwa za ya kasance ba. Amma masu-tawali’u za su gāji ƙasan; za su faranta zuciyarsu kuma cikin yalwar salama.”—Zabura 37:9-11.
Manzo Bulus ma ya yi magana game da wannan batun. An hure shi ya rubuta: “Akwai sammai tun dā, da duniya kuma a tattare daga bisa ruwa, cikin tsakiyar ruwa kuma, bisa ga maganar Allah; bisa ga wannan fa duniya wanda take a sa’an nan, yayin da ruwa ya sha kanta, ta halaka.” (2 Bitrus 3:5, 6) A nan manzon yana magana ne game da Rigyawar zamanin Nuhu. Miyagun mutane ne aka halaka, amma ba a halaka duniya ba. Wannan Rigyawar da ta faru a dukan duniya “ishara [ce] ga marasa bin Allah.”—2 Bitrus 2:6, LMT.
Sai Bitrus ya daɗa cewa: ‘Sama da ƙasa da ke nan yanzu, an tanada su ga wuta.’ Idan muka tsaya a nan, muna iya kasancewa da masaniyar da ba daidai ba. Za ka lura cewa ayar ta ci gaba da cewa: “Za a yi wa marasa bin Allah . . . hallaka.” Halakar ba ta duniya ba ce amma ta marasa bin Allah. Me zai bi bayan haka? Bitrus ya rubuta: “Amma bisa ga alkawarinsa muna jiran sababbin sammai [Mulkin Allah ta hanyar Almasihu] da sabuwar ƙasa [al’ummar ’yan Adam masu aminci], inda adalci zai yi zamansa.”—2 Bitrus 3:7, 13, LMT.
Annabcin da ke cikin Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa lokacin “ƙarshen” ya kusa. Ka karanta Matta 24:3-14 da 2 Timotawus 3:1-5 domin ka ga abubuwan da suka tabbatar da hakan.a
Kana tunanin cewa bahagon abu ne a ce akwai rashin fahimta sosai game da Matta 24:14, ayar da ko yaro ma zai iya ganewa? Akwai dalilan da suka jawo hakan. Shaiɗan ya makantar da mutane don kada su ga gaskiya masu tamani da ke cikin Kalmar Allah. (2 Korintiyawa 4:4) Allah ya ɓoye nufe-nufensa daga mutane masu girman kai kuma ya bayyana su ga masu tawali’u. Game da wannan batun, Yesu ya ce: “Ina yabonka, ya Uba, Ubangijin sama da ƙasa, da ka ɓoye ma masu-hikima da masu-fahimi waɗannan al’amura, ka bayyana su ga jarirai.” (Matta 11:25) Gata ne mai girma mu kasance cikin masu tawali’un da suka fahimci ainihin ko mene ne Mulkin Allah, waɗanda suke ɗokin samun albarkar da Mulkin zai kawo ga dukan waɗanda suke goyon bayansa!
-