Abin Da Muka Koya Daga Wurin Yesu
Game da “Matuƙa”
Menene zai ƙare?
Almajiran Yesu sun tambaye shi: “Ka faɗa mana yaushe waɗannan abu za su zama? mi ne kuma alamar zuwanka da cikar zamani?” (Matta 24:3) Sa’ad da yake amsa tambayar nan, Yesu bai ce duniyar da muke zaune a cikin ta ce za ta ƙare ba. A dā ya yi magana game da “zamani” kuma ya yi amfani da kalmar nan sa’ad da yake nuni ga dukan tsarin addinai da waɗanda ba na addinai ba da ke ƙarƙashin ikon Shaiɗan. (Matta 13:22, 40, 49) Tsarin da yake nufi ke nan sa’ad da ya ce: “Matuƙa za ta zo.”—Matta 24:14.
Yaya Yesu ya kwatanta matuƙan?
Ƙarshen wannan zamani marasa adalci ‘albishiri’ ne. Yesu ya ce: ‘Wannan bishara kuwa ta mulki za a yi wa’azinta cikin iyakar duniya domin shaida ga dukan al’ummai; sa’annan matuƙa za ta zo.’ Yesu ya kwatanta matuƙar wannan zamanin kamar haka: “Za a yi ƙunci mai-girma, irin da ba a taɓa yi ba tun farkon duniyar har yanzu, ba kuwa za a yi ba daɗai. Kuma da ba domin an gajertadda waɗannan kwanaki ba, da ba mai-rai da za ya tsira ba.”—Matta 24:14, 21, 22.
Wa za a halaka?
Mutanen da ba su ƙauna da kuma yi wa Jehobah da Yesu hidima ne kaɗai za a halaka. Irin waɗannan mutanen sun ƙi yin biyayya ga Allah. Yesu ya ce: “Kuma kamar yadda kwanakin Nuhu su ke, hakanan kuma bayanuwar Ɗan Mutum za ta zama. Gama kamar suna . . . cikin kwanakin da ke gaban ruwan Rigyawa, . . . ba su sani ba har rigyawa ta zo ta kwashe su duka.” (Matta 24:36-39) Yesu ya faɗi cewa yawancin mutane suna kan hanyar da ta nufi halaka. Amma, ya ba da tabbaci cewa da akwai “hanya kuwa matsatsiya . . . wadda ta nufa wajen rai.”—Matta 7:13, 14.
Yaushe ne ƙarshen zamanin nan zai zo?
Sa’ad da aka tambaye shi game da alamar zuwansa da “cikar zamani,” Yesu ya ce: “Al’umma za ta tasa ma al’umma, mulki kuma za ya tasa ma mulki: za a yi yunwa da rayerayen duniya . . . saboda yawaita da mugunta za ta yi kuma, ƙaunar yawancin mutane za ta yi sanyi.” (Matta 24:3-12) Saboda haka, dukan labarai marar daɗi da ake ji a yau suna da ma’ana mai ƙarfafawa, wato, ba da daɗewa ba Mulkin Allah za ta kawo salama ga mutane masu biyayya. Yesu ya ce: “Lokacinda kuka ga waɗannan al’amura suna faruwa, ku sani mulkin Allah ya kusa.”—Luka 21:31.
Menene ya kamata ka yi?
Yesu ya faɗi cewa Allah “ya bada Ɗansa, haifaffe shi kaɗai, domin dukan wanda yana bada gaskiya gareshi kada ya lalace, amma ya sami rai na har abada.” (Yohanna 3:16) Don ka ba da gaskiya ga Allah da Ɗansa, kana bukatar ka san su sosai. Shi ya sa Yesu ya ce: “Rai na har abada ke nan, su san ka, Allah makaɗaici mai-gaskiya, da shi kuma wanda ka aiko, Yesu Kristi.”—Yohanna 17:3.
Ka mai da hankali don kada alhini da matsaloli su hana ka koyon yadda za ka nuna ƙaunarka ga Allah. Yesu ya ce: “Ku yi hankali da kanku, kada ya zama zukatanku su yi nauyi . . . da shagulgula na wannan rai, har ranan nan ta hume ku ba labari, kamar tarko: gama hakanan za ta humi.” Idan kuka bi gargaɗin Yesu, za ku “sami ikon da za ku tsere ma dukan waɗannan al’amuran da za su faru.”—Luka 21:34-36.
Don ƙarin bayani, ka duba babi na 9 mai jigo, “Muna Rayuwa ne a ‘Kwanaki na Ƙarshe’?,” a littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?a
[Hasiya]
a Shaidun Jehobah ne suka wallafa.