“Ku Natsu”
“Ƙarshen dukan abubuwa ya gabato. . . . Ku natsu, domin ku yi addu’a.”—1 BIT. 4:7, Littafi Mai Tsarki.
1. Menene jigon koyarwar Yesu?
SA’AD da Yesu Kristi yake duniya, jigon koyarwarsa shi ne Mulkin Allah. Ta hanyar wannan Mulkin, Jehobah zai ɗaukaka ikon mallakarsa kuma ya tsarkake sunansa. Shi ya sa Yesu ya koya wa almajiransa su yi addu’a ga Allah cewa: “Mulkinka shi zo. Abin da ka ke so, a yi shi, cikin duniya, kamar yadda a ke yinsa cikin sama.” (Mat. 4:17; 6:9, 10) Ba da daɗewa ba, wannan Mulkin zai kawo ƙarshen duniyar Shaiɗan kuma ya sa a yi nufin Allah a dukan duniya. Kamar yadda Daniel ya annabta, Mulkin Allah “za ya farfashe dukan waɗannan mulkoki [na zamani] ya cinye su, shi kuwa za ya tsaya har abada.”—Dan. 2:44.
2. (a) Yaya mabiyan Yesu za su san cewa ya soma Mulki? (b) Menene kuma alamar za ta nuna?
2 Domin zuwan Mulki Allah yana da muhimmanci sosai ga mabiyan Yesu, hakan ya sa suka tambaye shi: “Mi ne kuma alamar zuwanka da cikar zamani?” (Mat. 24:3) Za a ba su alama na zahiri domin waɗanda suke duniya ba za su ga bayyanuwar Kristi a ikon Mulki a zahiri ba. Wannan alama za ta ƙunshi fannoni dabam dabam da aka annabta a cikin Nassosi. Saboda haka, mabiyan Yesu da suke zama a lokacin za su iya fahimtar cewa ya soma sarauta a sama. Zai kuma nuna somawar lokacin da aka kira “kwanaki na ƙarshe” cikin Littafi Mai Tsarki, wato, mugun tsari da yanzu yake mallakar duniya.—2 Tim. 3:1-5, 13; Mat. 24:7-14.
Ku Natsu a Kwanaki na Ƙarshe
3. Me ya sa Kiristoci suke bukatar su natsu?
3 Manzo Bitrus ya rubuta: “Ƙarshen dukan abubuwa ya gabato. Saboda haka sai ku kame kanku, ku natsu, domin ku yi addu’a.” (1 Bit. 4:7, LMT) Mabiyan Yesu suna bukatar su natsu, su lura da abubuwan da ke faruwa a duniya da suka nuna cewa ya soma sarauta. Kasancewarsu a faɗake zai fi zama da gaggawa yayin da ƙarshen wannan muguwar duniya ta kusa. Yesu ya gaya wa almajiransa: “Ku yi tsaro fa: gama ba ku san lokacin da ubangijin gida yana zuwa [ya zartar da hukunci a kan duniyar Shaiɗan].”—Mar. 13:35, 36.
4. Ka nuna bambancin da ke tsakanin halin mutanen da ke bin duniyar Shaiɗan da na bayin Jehobah. (Ka haɗa da akwati.)
4 Mutane gabaki ɗaya suna ƙarƙashin ja-gorar Shaiɗan, kuma ba sa mai da hankali ga ma’anar abubuwan da ke faruwa a duniya. Ba su fahimci cewa Kristi ya soma sarauta ba. Amma mabiyan Kristi na gaskiya sun natsu kuma sun fahimci ainihin ma’anar abin da ya faru a ƙarnin da ya wuce. Tun shekara ta 1925, Shaidun Jehobah sun fahimci cewa Yaƙin Duniya na ɗaya da abubuwa da suke faruwa tun lokacin sun ba da tabbaci cewa Kristi ya soma sarauta a sama a shekara ta 1914. Da haka, kwanaki na ƙarshe na wannan muguwar duniya da ke ƙarƙashin Shaiɗan ya soma. Ko da yake mutane da yawa da suke lura da abubuwan da ke faruwa ba su san ma’anar ba, sun fahimci cewa da akwai bambanci sosai kafin Yaƙin Duniya na ɗaya da kuma bayan lokacin.—Ka duba akwati “Lokacin Wahala ya Soma.”
5. Me ya sa yake da muhimmanci mu ci gaba da natsuwa?
5 A kusan ƙarni ɗaya yanzu, mugun abubuwa da suke faruwa a dukan duniya sun nuna cewa muna zama a kwanaki na ƙarshe. Lokaci kaɗan ne kawai ya rage kafin Jehobah ya ba Kristi umurni ya ja-goranci rundunar mala’iku masu iko su yaƙi duniyar Shaiɗan. (R. Yoh. 19:11-21) An gaya wa Kiristoci na gaskiya su yi tsaro. Saboda haka, yana da gaggawa mu ci gaba da yin hakan sa’ad da muke jiran ƙarshen wannan duniyar. (Mat. 24:42) Dole ne mu kasance a faɗake, kuma a ƙarƙashin ja-gorancin Kristi, dole ne mu cim ma wani aiki na musamman a dukan duniya.
Aikin da Ake Yi a Dukan Duniya
6, 7. Yaya aikin wa’azin Mulki ya samu ƙaruwa a kwanaki na ƙarshe?
6 An annabta cewa aikin da Shaidun Jehobah za su yi sashe ne na alamar da ta nuna cewa muna zama a cikin kwanaki na ƙarshe na wannan muguwar duniya. Yesu ya bayyana wannan aiki na dukan duniya sa’ad da ya lissafa abubuwa dabam dabam da za su faru a lokaci na ƙarshe. Ya yi wannan furci mai muhimmanci a cikin annabcinsa: “Wannan bishara kuwa ta mulki za a yi wa’azinta cikin iyakar duniya domin shaida ga dukan al’ummai; sa’annan matuƙa za ta zo.”—Mat. 24:14.
7 Ka yi tunanin wasu abubuwan da suke da nasaba da wannan fanni na annabcin Yesu. Mutanen da suke bisharar ba su da yawa sa’ad da kwanaki na ƙarshe ya soma a shekara ta 1914. A yanzu wannan adadin ya ƙaru sosai. Shaidun Jehobah da suke wa’azi a dukan duniya sun fi 7,000,000, kuma suna cikin ikilisiyoyi fiye da 100,000. Ƙarin mutane 10,000,000 ne suka taru da Shaidun Jehobah a shekara ta 2008 sa’ad da suke Tuna mutuwar Kristi. Wannan ƙari ne mai yawa fiye da ta shekarar da ta wuce.
8. Me ya sa hamayya bai hana mu yin nasara a wa’azinmu ba?
8 Hakika, ana ba da shaida sosai game da Mulkin Allah a dukan al’ummai kafin ƙarshen wannan zamani ya zo! Ana hakan duk da cewa Shaiɗan ne “allah na wannan zamani.” (2 Kor. 4:4) Shi ne ke ja-gorar dukan siyasa, addinai, kasuwanci, da dukan hanyar watsa labarai. To, menene ya sa ake samun nasara mai ban al’ajabi a aikin ba da shaida? Goyon bayan Jehobah ne. Saboda haka, aikin wa’azin Mulki yana ci gaba sosai duk da cewa Shaiɗan yana ƙoƙari ya sa a daina aikin.
9. Me ya sa za a kira ci gabanmu na ruhaniya mu’ujiza?
9 Ana iya cewa mu’ujiza ce nasarar da mutanen Jehobah suke samu a aikin wa’azin Mulki, ƙaruwar da suke yi, da kuma ci gaban da suke samu a ruhaniya. Idan ban da goyon bayan Allah, da ya ƙunshi ja-gora da kāriya da yake yi wa mutanensa, aikin wa’azi ba zai yiwu ba. (Karanta Matta 19:26.) Muna da tabbaci cewa sa’ad da ruhu mai tsarki na Allah yake aiki a zuciyar mutanen da suka natsu kuma suke son su bauta masa, za a yi wannan aikin wa’azi har ƙarshe, “sa’annan matuƙa za ta zo.” Wannan lokacin yana ƙara gabatowa.
“Babban Tsananin”
10. Ta yaya Yesu ya kwatanta ƙunci mai girma da ke zuwa?
10 Ƙarshen wannan mugun zamani zai zo a lokacin “babban tsananin.” (R. Yoh. 7:14) Littafi Mai Tsarki bai gaya mana tsawon lokaci da hakan zai kasance ba, amma Yesu ya ce: “Sa’annan za a yi ƙunci mai-girma, irin da ba a taɓa yi ba tun farkon duniya har yanzu, ba kuwa za a yi ba daɗai.” (Mat. 24:21) Idan muka yi la’akari da ƙunci da wannan duniya ta riga ta fuskanta, kamar a Yaƙin Duniya na biyu sa’ad da kusan mutane miliyan 50 zuwa 60 suka mutu, ƙunci mai zuwa a nan gaba zai yi tsanani sosai. Zai ƙare a yaƙin Armageddon. A wannan lokacin ne Jehobah zai yi amfani da rundunarsa ya halaka duk wani tsarin Shaiɗan da ya rage a duniya.—R. Yoh. 16:14, 16.
11, 12. Wane aukuwa ne zai nuna somawar babban tsanani?
11 Annabcin Littafi Mai Tsarki bai faɗi lokacin da sashe na farko na ƙunci mai girma zai soma ba, amma ya gaya mana aukuwa na musamman da zai nuna cewa ya soma. Wannan aukuwa shi ne halaka dukan addinan ƙarya da masu sarauta za su yi. A cikin annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki da ke Ru’ya ta Yohanna surori 17 da 18, an kamanta addinin ƙarya da karuwa da ta yi lalata da tsarin siyasa na duniya. Ru’ya ta Yohanna 17:16 ta nuna cewa ba da daɗewa ba waɗannan masu sarauta “za su ƙi karuwan, su lalatadda ita su tsiraitadda ita kuma, za su cinye namanta, su ƙoƙone ta sarai da wuta.”
12 Idan lokacin ya kai, Allah zai “sa cikin zuciyarsu [masu sarauta na siyasa] su yi nufinsa” su halaka dukan addinin ƙarya. (R. Yoh. 17:17) Saboda haka, za a iya cewa Allah ne ya yi wannan halakar. Wannan hukuncinsa ne bisa addinin ƙarya wanda tun da daɗewa yake koyar da abin da ya saɓa wa nufin Allah kuma yana tsananta wa bayinsa. Duniya gabaki ɗaya ba ta zaton halakar da addinin ƙarya. Amma bayin Jehobah masu aminci sun san za a halakar da ita. Kuma a waɗannan kwanaki na ƙarshe, suna ta gaya wa mutane game da ita.
13. Menene ya nuna cewa ƙarshen addinin ƙarya zai faru cikin hanzari?
13 Mutane za su yi mamaki sosai cewa an halaka addinin ƙarya. Game da wannan halakar, annabcin Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa har wasu cikin “sarakunan duniya” za su ce: “Kaito, kaito, . . . gama cikin sa’a ɗaya hukumcinki ya zo.” (R. Yoh. 18:9, 10, 16, 19) Da yake Littafi Mai Tsarki ya yi amfani da furcin nan “sa’a ɗaya,” hakan ya nuna cewa wannan aukuwa zai faru babu ɓata lokaci.
14. Sa’ad da maƙiyan Jehobah suka kai farmaki ga bayinsa, menene Allah zai yi?
14 Mun fahimci cewa bayan an halaka addinin ƙarya, za a kai wa bayin Jehobah farmaki, waɗanda suke shelar saƙon hukuncinsa. (Ezek. 38:14-16) Sa’ad da aka soma wannan farmakin, waɗanda suka kai farmakin za su fuskanci Jehobah wanda ya yi alkawari cewa zai kāre mutanensa masu aminci. Jehobah ya ce: “Cikin kishina da wutar fushina na yi magana . . . za su kuwa sakankance ni ne Ubangiji.” (Karanta Ezekiel 38:18-23.) A cikin Kalmarsa, Allah ya faɗi cewa: “Wanda ya taɓa [bayinsa masu aminci], ya taɓa ƙwayar [idona].” (Zech. 2:8) Saboda haka, sa’ad da maƙiyansa suka soma kai wa bayinsa farmaki, Jehobah zai ɗauki mataki. Zai ɗauki matakin da zai kai ga sashe na ƙarshe na ƙunci mai girma, wato, kammalawarsa a Armageddon. A ƙarƙashin ja-gorancin Kristi, rundunar mala’iku masu iko za su zartar da hukuncin Jehobah bisa duniyar Shaiɗan.
Yadda Ya Kamata Hakan Ya Shafe Mu
15. Ta yaya sanin cewa ƙarshen wannan zamani ya kusa ya kamata ya shafe mu?
15 Yaya ya kamata sanin cewa ƙarshen wannan zamani yana gabatowa zai shafe mu? Manzo Bitrus ya rubuta: “Da shi ke fa dukan waɗannan abu za su narke hakanan, waɗanne irin mutane ya kamata ku zama cikin tasarrufi mai-tsarki da ibada kuma?” (2 Bit. 3:11) Waɗannan kalaman sun nuna cewa muna bukatar mu yi tsaro mu tabbata cewa halinmu ya jitu da ƙa’idodin Allah kuma muna ayyuka na ibada da ke nuna ƙaunarmu ga Jehobah. Irin waɗannan ayyuka sun ƙunshi yin iya ƙoƙarinmu a wa’azin bisharar Mulki kafin ƙarshen ya zo. Bitrus ya kuma rubuta: “Ƙarshen dukan abubuwa ya gabato. . . . Ku natsu, domin ku yi addu’a.” (1 Bit. 4:7) Muna kusantar Jehobah kuma muna nuna ƙaunarmu a gare shi ta wajen yin addu’a a gare shi a kai a kai, muna roƙonsa ya yi mana ja-gora ta wajen ruhunsa mai tsarki da kuma ikilisiyarsa na dukan duniya.
16. Me ya sa muke bukatar mu manne wa umurnin Allah sosai?
16 A wannan lokaci mai haɗari, muna bukatar mu manne wa gargaɗin Kalmar Allah: “Ku duba fa a hankali yadda ku ke yin tafiya, ba kamar marasa-hikima ba, amma kamar masu-hikima; kuna rifta zarafi, tun da shi ke miyagun kwanaki ne.” (Afis. 5:15, 16) A yanzu, mugunta ta fi yawa fiye da dā. Shaiɗan ya tsara abubuwa da yawa don ya hana mutane yin nufin Jehobah ko kuma kawai ya janye hankalinsu. A matsayinmu na bayin Allah, mun san da hakan, kuma ba za mu ƙyale kome ya hana mu kasancewa da aminci ga Allah ba. Mun san abin da zai faru ba da daɗewa ba, kuma mun dogara ga Jehobah da nufe-nufensa.—Karanta 1 Yohanna 2:15-17.
17. Ka kwatanta yadda waɗanda suka tsira daga Armageddon za su aikata sa’ad da aka yi tashin matattu.
17 Alkawari mai girma da Allah ya yi na ta da matattu zuwa rai zai cika don “za a yi tashin matattu, na masu-adalci da na marasa-adalci.” (A. M. 24:15) Ka lura yadda aka yi wannan alkawarin da ƙwazo: ‘Za a yi tashin matattu’! Babu wata tantama game da wannan alkawarin, don Jehobah ya riga ya faɗi kalmarsa! Ishaya 26:19 ya yi alkawari: “Matattunka za su yi rai. . . . ku rera waƙa, ku da ke zaune cikin turɓaya, . . . ƙasa kuwa za ta fitar da matattu.” Waɗannan kalaman sun sami cika na farko a lokacin da aka mai da mutanen Allah na dā zuwa ƙasarsu, hakan ya ba mu tabbaci cewa wannan zai cika a zahiri a sabuwar duniya. Za a yi farin ciki sosai sa’ad da waɗanda suka tashi daga matattu suka sake haɗuwa da ƙaunatattunsu! Hakika, ƙarshen duniyar Shaiɗan ta kusa, kuma sabuwar duniya ta Allah ta yi kusa sosai. Yana da muhimmanci mu natsu!
Ka Tuna?
• Menene jigon koyarwar Yesu?
• Yaya aka yaɗa aikin wa’azin Mulki yanzu?
• Me ya sa yake da muhimmanci mu natsu?
• Menene ya ƙarfafa ka game da alkawarin da ke A. M. 24:15?
[Akwati/Hotunan da ke shafi na 16, 17]
Lokacin Wahala Ya Soma
The Age of Turbulence: Adventures in a New World (Lokacin Wahala: Abubuwa da za su Faru a Sabuwar Duniya) shi ne jigon littafin da Alan Greenspan ya rubuta a shekara ta 2007. Kusan shekara 20, shi ne mai shugaban ƙungiyar Federal Reserve Board na Amirka, da ke kula da dukan cibiyar tsarin ajiyar kuɗi na ƙasar. Greenspan ya nanata bambancin da ke tsakanin yanayin duniya kafin shekara ta 1914 da kuma bayan hakan:
“Ta wajen duka rahoton da muka samu, kafin shekara ta 1914, mutane da ƙasashe suna daraja juna kuma ana samun ci gaba a al’ada da kuma fasaha; ’yan adam sun sami ci gaba sosai da kamar za a kai kamiltawa. A ƙarni na goma sha tara ne aka daina kasuwancin bayi. Kamar mugunta tana raguwa a lokacin. . . . An sami ci gaba na fasaha a dukan duniya a dukan ƙarni na goma sha tara, hakan ya sa aka samu hanyar jirgin ƙasa, tarho, wutan lantarki, silima, mota, da kuma kayan gida iri-iri masu yawa ainu. Kula da lafiyar jiki ta hanyar kimiyyar, abinci mai kyau, da kuma ruwa mai tsabta sun ƙara tsawon rayuwa . . . Dukan mutane suna gani cewa wannan yanayin zai ci gaba.”
Amma . . “Yaƙin Duniya na ɗaya ya yi ɓarna sosai ga wannan ci gaba fiye da Yaƙin Duniya na biyu da ake gani ya fi yin ɓarna a zahiri: yaƙi na farkon ya halakar da ra’ayi. Ba zan iya mance yanayin waɗannan shekarun kafin Yaƙin Duniya na ɗaya, lokacin da’yan adam suka sami ci gaba marar iyaka kuma cikin sauri. A yau yanayinmu dabam yake sosai da ƙarni da ya shige amma wataƙila hakan ya fi jituwa da ainihin yanayin. Shin ta’addanci, ƙaruwar zafi, ko siyasa zai hallaka wannan zamanin fiye da Yaƙin Duniya na ɗaya? Babu wanda ya san amsar.”
Lokacin da yake makarantar jami’a, Greenspan ya tuna furcin Benjamin M. Anderson, farfesa na ilimin tattalin arziki (1886-1949): “Waɗanda suka tuna kuma suka fahimci yadda duniya take kafin Yaƙin Duniya na ɗaya, suna kewar wancan lokacin sosai. A wannan lokacin da akwai kwanciyar hankali wanda babu irinsa kuma.”—Economics and the Public Welfare.
Littafin nan A World Undone da G. J. Meyer ya rubuta, wanda aka wallafa a shekara ta 2006 ya ce. Mu karanta: “Manyan abubuwan da suka faru a tarihi sun ‘canja kome.’ Hakan gaskiya ne game da Babban Yaƙi da aka yi a shekara ta 1914 zuwa 1918. Da gaske wannan yaƙin ya canja kome: Ya canja iyakan ƙasashe, gwamnatoci, yanayin ƙasashe, ya kuma canja yadda mutane suke ɗaukan duniya da kuma kansu tun lokaci. Ya fito da wata duniya ta zamani da ba ta yi kama da duniya ta dā inda ake da kwanciyar rai ba.”
[Hotunan da ke shafi na 18]
A Armageddon, Jehobah zai yi amfani da rundunar mala’iku masu iko