Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 5/15 pp. 12-16
  • Ceto Ta Wurin Mulkin Allah Ya Kusa!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ceto Ta Wurin Mulkin Allah Ya Kusa!
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ana Bukatar Ceto Sosai Yanzu
  • Tabbataccen Tushe na Ceto
  • Gwamnati Mai Adalci
  • Kwanaki na Ƙarshe ya Kusan Ƙarewa!
  • Menene Mulkin Allah?
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Abin Da Mulkin Allah Zai Yi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Mene ne Mulkin Allah?
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
  • Mulkin Allah—Sabuwar Sarauta Ta Duniya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 5/15 pp. 12-16

Ceto Ta Wurin Mulkin Allah Ya Kusa!

“Mulkinka shi zo. Abin da ka ke so, a yi shi, cikin duniya, kamar yadda a ke yinsa cikin sama.”—MATTA 6:10.

1. Menene ainihin koyarwar Yesu?

SA’AD da Yesu Kristi ya yi Huɗubarsa a kan Dutse, ya haɗa da addu’ar misali da ya taƙaita ainihin koyarwarsa. Ya koya wa mabiyansa su yi addu’a ga Allah: “Mulkinka shi zo. Abin da ka ke so, a yi shi, cikin duniya, kamar yadda a ke yinsa cikin sama.” (Mat. 6:10) Yesu “ya yi ta yawo a cikin birane da ƙauyuka, yana wa’azi, yana kawo bishara ta mulkin Allah.” (Luka 8:1) Kristi ya aririce mabiyansa: ‘Ku fara biɗan mulkinsa, da adalcin Allah.’ (Mat. 6:33) Yayin da kake nazarin wannan talifin, ka nemi hanyoyin da za ka yi amfani da shi a hidimarka. Alal misali, ka yi tunanin yadda za ka amsa waɗannan tambayoyin: Yaya muhimmancin saƙon Mulki? Daga menene za a ceci ’yan adam? Ta yaya Mulkin Allah zai kawo ceto?

2. Yaya muhimmancin saƙon Mulki?

2 Yesu ya annabta: “Wannan bishara kuwa ta mulki za a yi wa’azinta cikin iyakar duniya domin shaida ga dukan al’ummai; sa’annan matuƙa za ta zo.” (Mat. 24:14) Yin bishara game da Mulkin Allah shi ne yana da muhimmanci sosai. Hakika, ita ce saƙo mafi muhimmanci a duniya! A cikin fiye da ikilisiyoyi 100,000 na Shaidun Jehobah a dukan duniya, bayin Allah wajen miliyan bakwai suna aikin wa’azi da babu na biyunsa, suna gaya wa mutane cewa an kafa Mulkin. Kafawarsa labari ne mai daɗi domin hakan yana nufin cewa Allah ya kafa gwamnati a sama da zai ja-goranci harkokin duniya. A ƙarƙashin sarautar Mulkin, za a yi nufin Jehobah a duniya yadda ake yinsa a duniya.

3, 4. Menene zai faru sa’ad da aka yi nufin Allah a duniya?

3 Menene zai faru da ’yan adam sa’ad da nufin Allah ya cika a duniya? Jehobah “za ya share dukan hawaye kuma daga idanunsu: mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba; ba kuwa za a ƙara yin baƙin zuciya, ko kuka, ko azaba: al’amura na fari sun shuɗe.” (R. Yoh. 21:4) Mutane ba za su yi ciwo ba ko kuma su mutu domin zunubin da suka gāda da kuma ajizanci. Matattu da Allah yake tunawa da su za su samu zarafin rayuwa har abada, gama Littafi Mai Tsarki ya yi alkawari: “Za a yi tashin matattu, na masu-adalci da na marasa-adalci.” (A. M. 24:15) Ba za a ƙara yin yaƙi ba, ko yunwa, kuma duniya za ta zama aljanna. Har dabbobin da a yanzu mugaye ne za su zauna lafiya da ’yan adam da kuma junansu.—Zab. 46:9; 72:16; Isha. 11:6-9; 33:24; Luka 23:43.

4 Da irin wannan albarka da sarautar Mulki za ta kawo, ba abin mamaki ba ne da annabcin Littafi Mai Tsarki ya yi maganar rayuwa a wannan lokacin da waɗannan kalmomi masu ban ƙarfafa: “Masu-tawali’u za su gāji ƙasan; za su faranta zuciyarsu kuma cikin yalwar salama.” Waɗanda suke haddasa wahala kuma fa? Nassosi ya annabta: “In an jima kaɗan, sa’annan mai-mugunta ba shi.” Amma, “waɗanda ke sauraro ga Ubangiji, su ne za su gāji duniya.”—Zab. 37:9-11.

5. Menene zai faru da wannan tsarin abubuwa?

5 Don dukan waɗannan abubuwan su faru, za a kawar da wannan zamanin da gwamnatocinsu, addinai, da kuma tsarin kasuwancinsu. Kuma wannan shi ne ainihin abin da gwamnati ta samaniya za ta yi. An hure annabi Daniel ya annabta: “A cikin zamanin waɗannan sarakuna [na yanzu] kuwa, Allah mai-sama za ya kafa wani mulki [a sama], wanda ba za a rushe shi ba daɗai, sarautassa kuwa ba za a bar ma wata al’umma ba; amma za ya farpashe dukan waɗannan mulkoki [na yanzu] ya cinye su, shi kuwa za ya tsaya har abada.” (Dan. 2:44) Mulkin Allah, wato, sabuwar gwamnati ta samaniya, za ta yi sarauta bisa sabuwar duniya. Za a sami “sabobin sammai da sabuwar duniya, inda adalci yake zaune.”—2 Bit. 3:13.

Ana Bukatar Ceto Sosai Yanzu

6. Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya kwatanta muguntar wannan duniyar?

6 Sa’ad da Shaiɗan, Adamu da Hauwa’u suka yi tawaye ga Allah, domin suna son su zaɓi abin da ke da nagarta da mugunta da kansu, wannan shi ne somawar mugun tarihi na iyalin ’yan adam. Shekaru 1,600 bayan haka, “muguntar mutum ta yi yawa cikin duniya, kuma kowacce shawara ta tunanin zuciyarsa mugunta ce kaɗai kullayaumi.” (Far. 6:5) Misalin shekaru 1,300 bayan haka, Sulemanu ya ga cewa yanayin duniya ya yi muni sosai kuma hakan ya sa ya rubuta: “Na kuwa aza matattu waɗanda suka rigaya mutuwa sun fi masu-rai da ke da rai yanzu arziki: i, na aza wanda ba ya kasance ba tukuna ya fi su duka arziki, gama ba ya ga muguntar da a ke yi a cikin duniya ba.” (M. Wa. 4:2, 3) Bayan shekaru 3,000 ne muka kai zamaninmu, inda mugunta ta ci gaba da ƙaruwa.

7. Me ya sa ake bukatar ceto daga Allah a yanzu fiye da dā?

7 Ko da yake gaskiya ne cewa mugunta ta daɗe tana faruwa, ana bukatar ceto ta Mulkin Allah sosai a yanzu fiye da kowane lokaci. Yanayin duniya cikin shekaru 100 da suka shige ya fi muni da kowane lokaci, kuma sun ci gaba da daɗa muni. Alal misali, ƙungiyar Worldwatch ta ce: “Mutanen da suka mutu a yaƙi a ƙarni [na 20] sun yi ninki uku na mutanen da suka mutu a dukan yaƙe-yaƙe daga ƙarni na fari A.Z., zuwa shekara ta 1899.” Fiye da mutane miliyan 100 ne suka mutu saboda yaƙe-yaƙe tun daga shekara 1914! Wani kundin sani ya kamanta cewa mutane kusan miliyan 60 ne suka mutu a Yaƙin Duniya ta biyu. A yanzu da wasu ƙasashe suke da makaman nukiliya, ’yan adam suna iya kashe mutane masu yawa sosai a duniya. Duk da ci gaban da aka samu a kimiyya da kuma magani, a kowace shekara yunwa har ila tana kashe yara fiye da miliyan biyar.—Ka duba babi na 9 na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

8. Menene shekaru da yawa na sarautar mutane ya tabbatar?

8 ’Yan adam ba su yi nasara ba a ƙoƙarce-ƙoƙarcensu na kawar da mugunta. ’Yan siyasar wannan duniyar, da ’yan kasuwa da kuma ƙungiyoyi na addinai ba su taɓa cika ainihin bukatun ’yan adam ba, wato, samun salama, arziki, da lafiyar jiki. Waɗannan ƙungiyoyin sun daɗa ga matsalolin da suke fuskantar ’yan adam a yau maimakon su magance su. Hakika, shekaru dubbai da mutane suka yi suna sarauta ya tabbatar da gaskiyar waɗannan kalmomin: “Na tabbata hanyar mutum ba cikin nasa hannu ta ke ba; mutum kuwa ba shi da iko shi shirya tafiyarsa.” (Irm. 10:23) Hakika, “waɗansu sukan sami mulki, waɗansu kuwa su sha wuya a ƙarƙashinsu.” (M. Wa. 8:9, Littafi Mai Tsarki) Bugu da ƙari, “dukan talikai suna nishi suna naƙuda tare.”—Rom. 8:22.

9. Waɗanne yanayi ne Kiristoci na gaskiya suke bukatar su gani a waɗannan “kwanaki na ƙarshe”?

9 Game da zamaninmu, Littafi Mai Tsarki ya annabta: “Cikin kwanaki na ƙarshe miyagun zamanu za su zo.” Bayan ya kwatanta yanayi na kwanaki na ƙarshe a ƙarƙashin sarautar mutane, annabcin ya ce: “Miyagun mutane da masu-hila za su daɗa mugunta gaba gaba.” (Ka karanta 2 Timothawus 3:1-5, 13.) Kiristoci sun san cewa hakan zai faru, domin “duniya duka kuwa tana kwance cikin Shaiɗan.” (1 Yoh. 5:19) Amma, abin farin cikin shi ne, nan ba da daɗewa ba Allah zai ceci waɗanda suke ƙaunarsa. Za a cece su daga wannan duniyar, wadda take daɗa taɓarɓarewa.

Tabbataccen Tushe na Ceto

10. Me ya sa Jehobah kaɗai ne tabbataccen Tushe na ceto?

10 Sa’ad da kake wa’azin bishara, ka bayyana cewa Jehobah kaɗai ne tabbataccen Tushe na ceto. Shi kaɗai ne yake da iko da muradin ceton bayinsa daga kowane irin mugun yanayi. (A. M. 4:24, 31; R. Yoh. 4:11) Muna da tabbaci cewa a kowane lokaci Jehobah zai ceci mutanensa kuma ya cika nufe-nufensa, don ya yi alkawari cewa: “Yadda na sa tsammani, hakanan za ya faru.” Maganarsa “ba za ta koma wurin[sa] wofi ba.”—Ka karanta Ishaya 14:24, 25; 55:10, 11.

11, 12. Wane tabbaci ne Allah ya ba bayinsa?

11 Jehobah ya ba da tabbacin cewa zai ceci bayinsa sa’ad da ya zartar da hukunci a kan miyagu. Sa’ad da ya aika annabi Irmiya ya je ya yi magana da gaba gaɗi ga masu aikata zunubi, Allah ya ce: “Kada ka ji tsoronsu.” Me ya sa? “Ina tare da kai domin in cece ka.” (Irm. 1:8) Hakazalika, sa’ad da Jehobah yake son ya halaka Saduma da Gwamrata, ya aika mala’iku biyu su raka Lutu da iyalinsa su bar yankin. “Sa’annan Ubangiji ya zubarda Kibiritu da wuta . . . bisa Sodom da Gomorrah.”—Far. 19:15, 24, 25.

12 A dukan duniya ma, Jehobah yana iya ceton waɗanda suke yin nufinsa. Sa’ad da ya halaka muguwar duniya ta dā da Rigyawa, “ya ceci Nuhu mai-shelan adalci, tare da waɗansu bakwai.” (2 Bit. 2:5) Jehobah zai sake ceton masu adalci sa’ad da ya halaka wannan mugun zamanin. Shi ya sa Kalmarsa ta ce: “Ku biɗi Ubangiji, ku dukan masu-tawali’u na duniya, . . . ku biɗi adilci, ku biɗi tawali’u: ko watakila a ɓoye ku a cikin ranar fushin Ubangiji.” (Zeph. 2:3) Domin wannan halaka ta dukan duniya, ‘masu-adalci za su zauna cikin ƙasan, amma za a datse miyagu daga cikin ƙasan.’—Mis. 2:21, 22.

13. Ta yaya za a ceci bayin Jehobah da suka mutu?

13 Amma, bayin Allah masu yawa sun riga sun mutu domin rashin lafiya, tsanantawa, da sauransu. (Mat. 24:9) Ta yaya za a ceci dukan waɗannan? Kamar yadda aka ambata ɗazu, “za a yi tashin matattu, na masu-adalci.” (A. M. 24:15) Yana da ban ƙarfafa mu san cewa babu wani abin da zai hana Jehobah ya ceci bayinsa!

Gwamnati Mai Adalci

14. Me ya sa muke da tabbacin cewa Mulkin Allah gwamnati ce mai adalci?

14 A hidimarka za ka iya bayyana cewa Mulkin Jehobah na samaniya mai adalci ne. Hakan gaskiya ce domin yana nuna halayen Allah masu kyau, kamar adalci, aminci, da kuma ƙauna. (K. Sha. 32:4; 1 Yoh. 4:8) Allah ya riga ya miƙa Mulkin ga Yesu Kristi, wanda ya fi cancanta ya yi sarautar wannan duniya. Nufin Jehobah ne cewa a ɗauki shafaffun Kiristoci 144,000 daga duniya kuma a ta da su zuwa rai a sama su zama masu yin sarauta tare da Kristi wajen yin mulki bisa duniya.—R. Yoh. 14:1-5.

15. Ka faɗi bambancin da ke tsakanin Mulkin Allah da sarautar mutane.

15 Bambancin da zai kasance a tsakanin sarautar mutane da ta Yesu da abokan sarautarsa 144,000 ba ƙarami ba ne! Masu yin sarauta a wannan duniyar a yawancin lokaci sukan yi mugunta kuma sun tura talakawansu su je su yi yaƙe-yaƙe, wanda hakan ya jawo mutuwar miliyoyin mutane. Shi ya sa Nassosi ya ce kada mu dogara ga mutum, “wanda babu taimako gareshi”! (Zab. 146:3) Ita kuwa sarautar Kristi za ta kasance mai kyau! “Ku zo gareni, dukanku da ku ke wahala, masu-nauyin kaya kuma,” in ji Yesu, “ni kuwa in ba ku hutawa. Ku ɗauka ma kanku karkiyata, ku koya daga wurina; gama ni mai-tawali’u ne, mai-ƙasƙantar zuciya: za ku sami hutawa ga rayukanku. Gama karkiyata mai-sauƙi ce, kayana kuma mara-nauyi.”—Mat. 11:28-30.

Kwanaki na Ƙarshe ya Kusan Ƙarewa!

16. Ta yaya ne waɗannan kwanaki na ƙarshe za su ƙare?

16 Wannan duniyar tana a kwanakinta na ƙarshe, ko kuwa “cikar zamani,” tun shekara ta 1914. (Mat. 24:3) Nan ba da daɗewa ba, abin da Yesu ya kira “ƙunci mai-girma” zai auku. (Ka karanta Matta 24:21.) Wannan ƙuncin da ba a taɓa yin irinsa ba zai kawo ƙarshen dukan duniya ta Shaiɗan. Amma ta yaya ƙunci mai girma zai soma? Kuma ta yaya zai ƙare?

17. Menene Littafi Mai Tsarki ya nuna game da somawar ƙunci mai girma?

17 Ƙunci mai girma zai soma ne ba zato ba tsammani. Hakika, “ranar Ubangiji” za ta zo ba zato sa’ad da “suna cikin faɗin, Kwanciyar rai da lafiya.” (Ka karanta 1 Tassalunikawa 5:2, 3.) Wannan ƙuncin da aka annabta zai soma ne sa’ad da al’ummai suke tunanin cewa suna gab da magance wasu cikin manyan matsalolinsu. Halaka ta ba zato ta “Babila Babba,” babbar daular addinin ƙarya za ta ba duniya mamaki. Sarakuna da sauransu za su yi mamaki sa’ad da aka hukunta Babila Babba.—R. Yoh. 17:1-6, 18; 18:9, 10, 15, 16, 19.

18. Wane mataki ne Jehobah zai ɗauka game da harin da Shaiɗan zai kai wa mutanensa?

18 Sa’ad da abin ya yi tsanani sosai, za a ga alamu “a cikin rana da wata da tamrari” kuma “alama ta Ɗan mutum za ta bayana a sama.” A wannan lokacin muna iya ‘ta da kanmu; gama fansarmu ta kusa.’ (Luka 21:25-28; Mat. 24:29, 30) Shaiɗan, ko kuwa Gog, zai sa mabiyansa su kai hari ga mabiyan Allah. Amma Jehobah ya ce game da mutanen da suke kai hari ga bayinsa masu aminci: ‘Shi wanda ya taɓa ku, ya taɓa ƙwayar idona.’ (Zech. 2:8) Saboda haka, Shaiɗan ba zai yi nasara ba a ƙoƙarin da yake yi na halaka su. Me ya sa? Domin Ubangiji Jehobah mai ikon mallaka zai ɗauki mataki nan da nan don ya ceci bayinsa.—Ezek. 38:9, 18.

19. Me ya sa za mu kasance da tabbaci cewa sojojin Allah za su halaka zamanin Shaiɗan?

19 Sa’ad da Allah ya ɗauki mataki a kan al’ummai, ‘za su san cewa shi ne Ubangiji.’ (Ezek. 36:23) Zai aika sojojinsa, wato, halittun ruhu masu yawa a ƙarƙashin ja-gorancin Yesu Kristi, don su halaka sauran sashen Shaiɗan da ke duniya. (R. Yoh. 19:11-19) Sa’ad da muka tuna cewa akwai lokacin da mala’ika ɗaya tak a cikin dare guda ya kashe maƙiyan Allah “mutum zambar ɗari da tamanin da biyar,” hakan zai sa mu kasance da tabbaci cewa sojoji na sama za su halaka duk wani sashen zamanin Shaiɗan a duniyar nan cikin sauƙi, yayin da ƙunci mai girma ya ƙare a Armageddon. (2 Sar. 19:35; R. Yoh. 16:14, 16) Za a ɗaure Shaiɗan da aljanunsa har tsawon shekara dubu. Daga baya, za a halaka su.—R. Yoh. 20:1-3.

20. Menene Jehobah zai cim ma ta hanyar Mulkinsa?

20 Mugunta ba za ta ƙara kasancewa a sama da duniya ba, kuma mutane masu adalci za su kasance a wannan duniyar har abada. A lokacin, Jehobah zai tabbatar da cewa shi ne Mai Ceto Mai Girma. (Zab. 145:20) Ta hanyar Mulkinsa, zai kunita ikon mallakarsa, ya tsarkake sunansa mai tsarki, kuma ya cika ainihin manufarsa ga duniya. Bari ka samu farin ciki sosai a hidimarka yayin da kake sanar da wannan bisharar kuma kake taimaka wa “waɗanda aka ƙadara su ga rai na har abada” su fahimci cewa ceto ta hanyar Mulkin Allah ya yi kusa!—A. M. 13:48.

[Hoto a shafi na 16]

Ka Tuna?

• Ta yaya ne Yesu ya bayyana muhimmancin Mulkin?

• Me ya sa ake bukatar ceto a yanzu fiye da dā?

• Waɗanne abubuwa ne za su auku a lokacin ƙunci mai girma?

• Ta yaya ne Jehobah ya tabbatar da cewa shi ne Mai Ceto Mai Girma?

[Hotuna a shafuffuka na 12, 13]

Kalmar Allah ta annabta aikin wa’azi na dukan duniya da za a yi a lokacinmu wanda ba za a ƙara yin makamancinsa ba

[Hoto a shafi na 15]

Jehobah zai iya cetonmu kamar yadda ya ceci Nuhu da iyalinsa

[Hoto a shafi na 16]

Jehobah “za ya share dukan hawaye kuma . . . mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba.”—R. Yoh. 21:4

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba