Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w14 1/1 p. 12
  • Ka Sani?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Sani?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Sani?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
  • Darussa Daga Littattafan Nahum, Habakkuk, da Zephaniah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Ku Bi Gurbin Annabawa—Nahum
    Hidimarmu Ta Mulki—2014
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
w14 1/1 p. 12

KA SANI?

Me Ya Sa Aka Kira Nineba Ta Dā “Birni Mai-jini”?

Nineba ce birnin tarayya na masarautar Assuriya. Babban birni ne mai fāda da haikali masu kyan gaske da manya-manyan tituna da ganuwa masu tsawo sosai. Wani annabi Ba’ibrane mai suna Nahum ya kira Nineba “birni mai-jini.”—Nahum 3:1.

Wannan kwatanci ne da ya dace domin zane-zanen da ke bangon fādar sarki Sennacherib da ke Nineba sun nuna cewa Assuriyawa azzalumai ne sosai. A wani zanen, an nuna yadda ake murɗe harshen wani fursuna da aka danne a ƙasa. Zane-zane da aka yi a jikin allunan laƙa sun nuna cewa Assuriyawa sukan saka wa bayinsu ƙugiya a hanci ko leɓe kuma su haɗa ta da wata igiya da za a riƙa jan su da ita. Sukan tilasta wa manyan ma’aikatan masarautar da suka ci da yaƙi su rataye kawunan sarakunansu, kamar mummunan abin wuya.

Wani manazarcin tarihin Assuriyawa mai suna Archibald Henry Sayce ya kwatanta irin ƙeta da Assuriyawa suke yi wa mazauna gari bayan sun ci su da yaƙi. Ya ce: “Waɗanda suka ci nasara sukan tattara kawuna a kan kawuna a duk inda suka wuce; ana ƙona ’yammata da ’yan maza da rai; ana rataye maza ko kuma sa’ad da suke raye, a feɗe fatunsu, a cire idanunsu ko kunnuwansu ko hancinsu ko kuma a yayyanke hannuwansu da ƙafafunsu.”

Me ya sa ake gina rawani a rufin gidajen Yahudawa?

Allah ya umurci kowane Bayahude da cewa: “Sa’anda ka gina sabon gida, sai ka ja rawani bisa bene, domin kada ka ja wa gidanka alhakin jini, idan wani ya faɗo daga can.” (Kubawar Shari’a 22:8) Rawani yana da muhimmanci wajen kāre rayukan mutane, domin iyalan Yahudawa a zamanin dā suna amfani da rufin gidajensu sosai.

Yawancin rufin gidajen Isra’ilawa suna da bai ɗaya. Kan rufin gida wuri ne mai kyau don hutu ko shan iska, ko kuma yin aikace-aikacen gida. A lokacin zafi ma, kwanciya a wurin tana da daɗi sosai. (1 Sama’ila 9:26) Manomi yana iya zuwa wurin don ya busar da hatsi kafin a niƙa, ko kuma ’ya’yan ɓaure da inabi.—Joshua 2:6.

Ƙari ga haka, wasu suna amfani da shi a bauta ta ƙarya amma wasu suna zuwa wurin don su bauta wa Allah na gaskiya. (Nehemiya 8:16-18; Irmiya 19:13) Akwai lokacin da manzo Bitrus ya hau rufin gida don ya yi addu’a da rana. (Ayyukan Manzanni 10:9-16) Idan da ganyayen inabi ko kwakwa ne aka yi inuwar rufin gidan, za a ji daɗin hutu a wurin sosai.

Littafin nan The Land and the Book ya bayyana cewa Isra’ilawa sukan gina matakala ko tsani har kan rufin gidajensu, kuma suna “gina ta waje da gidan, amma a cikin farfajiyar.” Saboda haka, mutum zai iya sauka daga saman gidan ba tare da ya shiga cikin ɗaki ba. Mai yiwuwa hakan ne ya sa a lokacin da Yesu yake gargaɗar da mabiyansa game da gudun gaggawa da za su yi kafin halakar birnin, ya ce: “Wanda yake a kan bene kada ya sauko garin shi kwashe kayan da ke cikin gidansa.”—Matta 24:17.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba