Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w07 1/1 pp. 7-11
  • “Babbar Ranar Ubangiji Ta Kusa”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Babbar Ranar Ubangiji Ta Kusa”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “Babbar Ranar Ubangiji”
  • “Masu Ba’a Za Su Zo da Ba’a”
  • Ka “Dakanta Mata”
  • Dalilin Kasancewa da Gaggawa
  • Ka Kasance da Azanci na Gaggawa
  • Ranar Shari’a Ta Jehovah Ta Gabato!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Ka Riƙa Tuna Cewa Ƙarshe Ya Yi Kusa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Yadda Za Mu Koyi Yin Wa’azi da Gaggawa
    Hidimarmu Ta Mulki—2014
  • Ka Nemi Jehovah Kafin Ranar Hasalarsa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
w07 1/1 pp. 7-11

“Babbar Ranar Ubangiji Ta Kusa”

“Babbar ranar Ubangiji ta kusa, kurkusa ce, tana kuwa gaggabta ƙwarai.”—ZEPHANIAH 1:14.

1, 2. (a) Wace rana ce ta musamman Kiristoci suke jira? (b) Waɗanne tambayoyi ne ya kamata mu yi, kuma me ya sa?

WATA budurwa tana cike da farin ciki sa’ad da take jiran ranar aurenta. Wata mata mai ciki tana jiran ranar da za ta haihu. Wani ma’aikaci ya ƙosa ya fara dogon hutu. Menene dukan su suke jira? Suna jiran rana ta musamman da za ta kawo masu farin ciki a rayuwarsu. Yadda suke ji ya bambanta. Ranar da suke jira za ta kai kuma suna son su kasance a shirye.

2 A yau Kiristoci na gaskiya suna jiran rana ta musamman. Wannan babbar “ranar Ubangiji” ce. (Ishaya 13:9; Joel 2:1; 2 Bitrus 3:12) Menene wannan “ranar Ubangiji,” kuma ta yaya ne zuwanta za ta shafe mutane? Bugu da ƙari, ta yaya za mu tabbata cewa a shirye muke kafin zuwanta? Yana da muhimmanci mu nemi amsar waɗannan tambayoyi yanzu saboda alamu sun nuna gaskiyar waɗannan kalamai na cikin Littafi Mai Tsarki: “Babbar ranar Ubangiji ta kusa, kurkusa ce, tana kuwa gaggabta ƙwarai.”—Zephaniah 1:14.

“Babbar Ranar Ubangiji”

3. Menene “Babbar ranar Ubangiji”?

3 Menene “babbar ranar Ubangiji”? A cikin Nassosi wannan furcin “ranar Ubangiji” yana nufin lokaci na musamman da Jehobah ya hukunta maƙiyansa kuma ya ɗaukaka sunansa mai girma. Mutane marasa aminci a Yahuda da Urushalima da kuma masu zalunta mutanen Babila da kuma Masar duk sun fuskanci ‘ranakun Jehobah’ sa’ad da suka fuskanci hukuncin Jehobah. (Ishaya 2:1, 10-12; 13:1-6; Irmiya 46:7-10) Duk da haka, “babbar ranar Jehobah” tana zuwa nan gaba. ‘Rana’ ce da Jehobah zai hukunta mutanen da suke ɓata sunansa. Zai soma da hallaka “Babila Babba,” wato daular duniya na addinin ƙarya da kuma wannan mugun zamani a yaƙin Armageddon.—Ru’ya ta Yohanna 16:14, 16; 17:5, 15-17; 19:11-21.

4. Me ya sa mutane da yawa suke tsoron wannan rana da ke zuwa?

4 Dole ne mutane da yawa su ji tsoron wannan rana da ke zuwa da sauri, ko sun sani ko ba su sani ba. Me ya sa? Ta bakin annabi Zephaniah, Jehobah ya ce: “Wannan rana ranar hasala ce, ranar wahala da ƙunci, ranar kaɗaici da risɓewa, ranar duhu da gama gira, ranar hadura masu-zurfi da duhu baƙi ƙirin.” Hakika rana ce mai ban tsoro! Bugu da ƙari, annabin ya ce: “Zan jawo ma mutane ɗimuwa . . . domin sun yi ma Ubangiji zunubi.”—Zephaniah 1:15, 17.

5. Menene ra’ayin miliyoyin mutane game da ranar Jehobah, kuma me ya sa?

5 Amma, waɗansu miliyoyin mutane suna jiran ranar Jehobah. Me ya sa? Saboda a gare su ranar ceto ne ga mutane masu aminci, rana ce da ake yabon Jehobah kuma ake tsarkaka sunansa mai girma. (Joel 3:16, 17; Zephaniah 3:12-17) Abin da mutane suke yi da rayuwarsu yanzu yana nuna ko suna tsoron wannan rana ne ko suna jiran ta. Menene ra’ayinka yayin da wannan rana take kusatowa? Kana shirye? Tabbacin cewa ranar Jehobah ta kusa tana shafan rayuwarka ta yau da kullum kuwa?

“Masu Ba’a Za Su Zo da Ba’a”

6. Menene ra’ayin mutane game da “ranar Ubangiji,” kuma me ya sa ba abin mamaki ba ne ga Kiristoci na gaskiya?

6 Duk da yake ranar tana zuwa da gaggawa, mutane da yawa a duniya ba su damu da zuwan “ranar Ubangiji” ba. Suna yi wa waɗanda suke yi masu gargaɗi game da zuwan wannan rana ba’a. Wannan ba abin mamaki ba ne ga Kiristoci na gaskiya. Sun tuna gargaɗin da manzo Bitrus ya rubuta: “Ku san wannan dafari, cikin kwanaki na ƙarshe masu-ba’a za su zo da ba’a, suna bin nasu sha’awoyi, suna cewa, Ina alkawarin tafowassa? gama, tun daga randa ubanni suka kwanta barci, dukan al’amura suna nan kamar yadda su ke tun farkon halitta.”—2 Bitrus 3:3, 4.

7. Menene zai taimake mu mu kasance da gaggawa?

7 Menene zai taimake mu mu guji irin wannan mugun tunani kuma mu kasance da gaggawa? Bitrus ya gaya mana: “Ina daman sahihin hankalinku yayinda ni ke yi maku tuni; domin ku tuna da zantattuka waɗanda aka faɗi a dā ta bakin annabawa masu-tsarki, da kuma umurnin Ubangiji da Mai-ceto ta bakin manzanninku.” (2 Bitrus 3:1, 2) Mai da hankali ga gargaɗin da ke cikin annabci zai taimaka mana mu faɗakar da ‘sahihan hankalinmu.’ Wataƙila mun sha jin waɗannan tunasarwa, amma yana da muhimmanci mu ci gaba da mai da hankali ga waɗannan gargaɗi yanzu fiye da dā.—Ishaya 34:1-4; Luka 21:34-36.

8. Me ya sa mutane da yawa suke banza da tunasarwa daga Littafi Mai Tsarki?

8 Me ya sa waɗansu mutane suke banza da waɗannan tunasarwa? Bitrus ya ci gaba: ‘Gama da gangan su ke manta da wannan, akwai sammai tun dā, da duniya kuma a tattare daga bisa ruwa, cikin tsakiyar ruwa kuma, bisa ga maganar Allah; bisa ga wannan fa duniya wadda ta ke a sa’an nan, yayinda ruwa ya sha kanta, ta halaka.’ (2 Bitrus 3:5, 6) Hakika, akwai waɗanda ba sa son ranar Jehobah ta zo. Domin ba sa son abin da zai takura wa rayuwarsu. Ba sa son su ba da lissafin rayuwarsu na son kai ga Jehobah! Kamar yadda Bitrus ya ce, suna rayuwa bisa ga “nasu sha’awoyi.”

9. Wane hali ne mutanen zamanin Nuhu da na Lutu suka nuna?

9 Domin ‘da gangan’ ne, waɗannan masu ba’a sun gwammace su mance cewa a dā Jehobah ya saka hannu a harkokin mutane. Yesu Kristi da manzo Bitrus sun yi magana game da waɗannan yanayi biyu, wato “zamanin Nuhu” da kuma “zamanin Lutu.” (Luka 17:26-30; 2 Bitrus 2:5-9) Kafin rigyawar, mutane sun ƙi su mai da hankali ga gargaɗin da aka yi. Kafin a hallaka Saduma da Gwamrata, Lutu “ya zama kamar mai-ba’a” a gaban surukansa.—Farawa 19:14.

10. Menene Jehobah ya yi game da waɗanda ba su lura ba?

10 Haka nan ma yake a yau. Duk da haka, ka yi la’akari da abin da Jehobah ya yi wa waɗanda ba su lura ba: ‘Zan hukunta mutanen da ke zaune lubus, masu cewa cikin zuciyarsu, Ubangiji ba za ya aika nagarta ba, ba kuwa za ya aika mugunta ba. Wadatassu za ta zama ganima, gidajensu kuma risɓewa: i, za su gina gidaje, ba kuwa za su zauna a ciki ba; za su dasa gonakin kuringar anab, ba za su sha ruwansu ba.’ (Zephaniah 1:12, 13) Mutane za su ci gaba da ‘rayuwarsu’ na yau da kullum, amma ba za su sami albarka na dindindin daga ayyukansu ba. Me ya sa? Saboda ranar Jehobah za ta zo farat ɗaya, kuma duka arziki da suka tara ba zai cece su ba.—Zephaniah 1:18.

Ka “Dakanta Mata”

11. Wane umurni ne ya kamata mu sa a zuciyarmu?

11 Ba kamar muguwar duniyar da take kewaye da mu ba, dole ne mu ci gaba da tunawa da umurnin da annabi Habakkuk ya rubuta: “Gama ru’yan har yanzu da ayanannen lokacinta, tana kuwa gaggabta zuwa matuƙan, ba kuwa za ta yi ƙarya ba; ko ta jima, dakanta mata; gama lallai za ta zo, ba za ta yi jinkiri ba.” (Habakkuk 2:3) Idan a gare mu kamar ranar tana jinkiri saboda ra’ayinmu ta ajizanci, dole ne mu tuna cewa Jehobah ba ya jinkiri. Ranarsa za ta zo a daidai lokaci, a lokacin da mutane ba sa zato.—Markus 13:33; 2 Bitrus 3:9, 10.

12. Wane gargaɗi ne Yesu ya yi, kuma yaya ne wannan ya bambanta da ayyukan mabiyansa masu aminci?

12 Da yake nanata muhimmancin jiran ranar Jehobah, Yesu ya yi gargaɗi cewa wasu daga cikin mabiyansa za su manta da lokaci na gaggawa. Ya ce game da su: “Amma idan mugun bawan nan ya faɗi cikin zuciyassa, Ubangijina yana jinkiri; har ya soma dūkan abokan bautansa, ya ci ya sha tare da masu-maye; ubangijin bawan nan za ya zo cikin rana da ba ya sa tsammani ba, cikin sa’a wadda ba ya sani ba, za ya yi masa dūka ƙwarai.” (Matta 24:48-51) Akasarin haka, bawan nan mai aminci, mai hikima ya kasance da gaggawa. Ajin bawan nan ya ci gaba da kasancewa a faɗake kuma ya nuna yana shirye. Yesu ya naɗa shi “bisa dukan abin da ya ke da shi” a nan duniya.—Matta 24:42-47.

Dalilin Kasancewa da Gaggawa

13. Ta yaya ne Yesu ya nanata muhimmancin kasancewa da gaggawa?

13 Yana da muhimmanci Kiristoci na ƙarni na farko su kasance da gaggawa. Ana bukatar su ɗauki mataki nan da nan su gudu daga Urushalima sa’ad da suka ga “tana kewaye da dāgar yaƙi.” (Luka 21:20, 21) Wannan ya faru a shekara ta 66 K.Z. Ka yi la’akari da yadda Yesu ya nanata muhimmancin kasancewa da gaggawa ga Kiristoci na dā: “Wanda ya ke a kan bene kada ya sabko garin shi kwashe kayan da ke cikin gidansa: kuma wanda ke cikin saura kada shi komo garin shi amso mayafinsa.” (Matta 24:17, 18) Ko da yake tarihi ya nuna cewa ba a kai wa Urushalima hari ba har tsawon shekaru huɗu, me ya sa ya kamata Kiristoci su yi biyayya da kalaman Yesu da gaggawa a shekara ta 66 K.Z.?

14, 15. Me ya sa yake da muhimmanci Kiristoci na ƙarni na farko su gudu sa’ad da suka ga sojoji sun kewaye Urushalima?

14 Ko da yake sojojin Roma ba su halaka Urushalima ba sai a shekara ta 70 K.Z., ba a kasance da salama ba a waɗannan shekaru huɗu. A waɗannan shekaru an yi mugunta kuma an zubar da jini. Wani ɗan tarihi ya kwatanta yanayin Urushalima a wannan lokacin da “yaƙin basasa, mai ɗauke da azaba mai tsanani.” An zaɓi matasa su tsare ganuwar, su ɗauki makamai, kuma su shiga soja. Kowace rana ana koyar da su aikin soja. Duk wanda ya goyi bayan Romawa ya zama maƙiyi. Ana ɗaukan waɗanda ba sa son irin shirin nan mai tsanani masu cin amana. Da Kiristoci sun ɗan daɗe a birnin, da sun shiga cikin wani yanayi mai tsanani.—Matta 26:52; Markus 12:17.

15 Mu tuna cewa Yesu ya ce “waɗanda ke cikin Yahudiya,” ba Urushalima kawai ba, su fara gudu. Wannan yana da muhimmanci saboda bayan watanni kaɗan da suka gudu daga Urushalima, sojojin Roma sun sake shirin yaƙi. Da farko, sun mallaki Galili a shekara ta 67 K.Z., bayan haka aka ci Yahudiya a shekara da ta gabata. Wannan ya kawo wahala mai tsanani a garin. Kuma ya kasance da wuya Yahudawa su gudu daga Urushalima. Saboda an tsare ƙofar shiga birnin, duk wanda yake son ya gudu ana ganin kamar ya fi son Romawa.

16. Wane hali ne Kiristoci na ƙarni na farko suke bukata idan suna son su tsira daga wannan lokacin wahala?

16 Domin haka, za mu iya fahimtar abin da ya sa Yesu ya nanata kasancewa da gaggawa a wannan yanayi. Ya kamata Kiristoci su yi ƙoƙari kada su bari abin duniya ta rinjaye su. Dole ne su yarda su ‘saki duk abin da suka mallaka’ domin su yi biyayya da gargaɗin Yesu. (Luka 14:33) Waɗanda suka yi biyayya suka gudu kuma suka tsallake Kogin Urdun sun tsira.

Ka Kasance da Azanci na Gaggawa

17. Me ya sa ya kamata mu kasance da azancin gaggawa?

17 Annabce-annabce na Littafi Mai Tsarki sun nuna cewa muna rayuwa a kwanaki na ƙarshe. Fiye da dā, muna bukatar mu ƙarfafa gaggawarmu. A lokacin salama soja ba ya damuwa da kuma jin tsoron haɗarin yaƙi. Amma, idan ya ga ba amfanin kasancewa a faɗake har yaƙi ya same shi hakan, wannan kuwa zai kawo mugun sakamako. Haka yake a garemu Kiristoci. Idan muka mance kasancewa da azancin gaggawa, ba za mu kāre kanmu ba daga harin da zai shafe mu, kuma ba za mu kasance a faɗake ba sa’ad da ranar Jehobah za ta zo. (Luka 21:36 1; Tassalunikawa 5:4) Idan akwai waɗanda suka yi “ridda ga barin bin Ubangiji,” yanzu ne ya kamata su neme shi kuma.—Zephaniah 1:3-6; 2 Tassalunikawa 1:8, 9.

18, 19. Menene zai taimake mu mu saurari “ranar Allah”?

18 Shi ya sa manzo Bitrus ya umurce mu mu saurari “ranar Allah”! Ta yaya za mu yi haka? Hanya ɗaya ita ce mu kasance a “cikin tasarrufi mai-tsarki da ibada.” (2 Bitrus 3:11, 12) Idan muka shagala a irin waɗannan ayyuka, za su taimake mu mu yi marmarin zuwan “ranar Allah.” Kalmar Hellenanci da aka fassara “sauraron” a zahiri tana nufin “daɗa masa hanzari.” Ba za mu iya hanzarta lokacin da ya rage ba, sai dai lokacin zuwan ranar Jehobah ya kai. Amma, sa’ad da muke jiran wannan ranar, lokacin zai shige da sauri idan muka kasance a hidimar Allah.—1 Korinthiyawa 15:58.

19 Idan muka yi bimbini a kan kalaman Littafi Mai Tsarki, kuma muka yi tunanin abubuwan da ke ciki zai taimake mu mu yi “sauraron ranar Allah.” (2 Bitrus 3:12) Waɗannan sun ƙunshi annabce-annabce da ke ɗauke da ranar zuwan Jehobah da kuma alkawarin da aka yi wa waɗanda suke ‘dakanta ma Jehobah.’—Zephaniah 3:8.

20. Wane umurni ne ya kamata mu riƙa tunawa?

20 Yanzu ne ya kamata mu bi umurnin da annabi Zephaniah ya yi: “Kafin fushin Ubangiji mai-zafi ya abko maku, tun ranar fushin Ubangiji ba ta hume ku ba. Ku biɗi Ubangiji, ku dukan masu-tawali’u na duniya, ku waɗanda kuka kiyaye shari’assa; ku biɗi adilci, ku biɗi tawali’u: ko watakila a ɓoye ku a cikin ranar fushin Ubangiji.”—Zephaniah 2:2, 3.

21. Menene ƙudurin mutanen Allah a shekara ta 2007?

21 Saboda haka, ya dace da aka zaɓi jigon shekara ta 2007 ya zama: “Babbar ranar Ubangiji ta kusa.” Mutanen Jehobah sun tabbata cewa ta “kusa, kurkusa ce, tana kuwa gaggabta ƙwarai.” (Zephaniah 1:14) “Ba za ta yi jinkiri ba.” (Habakkuk 2:3) Saboda haka, sa’ad da muke jiran wannan rana, bari mu ci gaba da mai da hankali ga wannan lokacin da muke ciki, kuma mu san cewa ƙarshen waɗannan annabce annabcen ya kusa!

Za ka Iya Ba da Amsa?

• Mecece “babbar ranar Jehobah”?

• Me ya sa mutane da yawa suka yi banza da gaggawan wannan lokaci?

• Me ya sa ya kamata Kiristoci na ƙarni na farko su kasance da gaggawa?

• Ta yaya ne za mu ci gaba da kasancewa da gaggawarmu?

[Bayanin da ke shafi na 11]

Jigo na shekara ta 2007 zai zama: “Babbar ranar Ubangiji ta kusa.”—Zephaniah 1:14.

[Hotuna a shafuffuka na 8, 9]

Kamar kwanakin Nuhu, masu ba’a za su yi mamaki sa’ad da Jehobah ya zabura

[Hoto a shafi na 10]

Ya kamata Kiristoci su aikata nan da nan sa’ad da suka ga Urushalima “tana kewaye da dāgar yaƙi”

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba