Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 10/1 pp. 8-11
  • Mata Suna da Mutunci A Gaban Allah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Mata Suna da Mutunci A Gaban Allah
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Yadda Yesu Ya Bi da Mata
  • Bin Ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki Zai Sa A Daraja Mata
  • Shin Allah Ya Damu da Mata Kuwa da Gaske?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Mene ne Matsayin Mata a Tsarin Jehobah?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 10/1 pp. 8-11

Mata Suna da Mutunci A Gaban Allah

YESU ya bayyana halin Ubansa Jehobah da kuma yadda Jehobah yake gudanar da abubuwa a lokacin da yake duniya. Shi ya sa ya ce: “Ba na yin komi domin kaina ba, amma ina faɗin waɗannan magana yadda Uba ya koya mani. . . . Gama kullum ina aika abin da ya gamshe shi.” (Yohanna 8:28, 29; Kolosiyawa 1:15) Ta wajen bincika yadda Yesu ya bi da mata, za mu fahimci yadda Allah ya ɗauki mata kuma za mu gane ra’ayinsa game da abin da ya san za su iya yi.

Masana da dama sun yarda cewa bisa ga abin da aka rubuta a cikin Lingila, ra’ayin Yesu game da mata ya bambanta sosai da na mutanen zamaninsa. Ta yaya? Shin koyarwar Yesu tana ’yantar da mata har wa yau ne?

Yadda Yesu Ya Bi da Mata

◼ Yesu bai ɗauki mata a matsayin masu sa jaraba ba. Shugabannin addinin Yahudawa suna da ra’ayi cewa yin sha’ani da mata zai kai ga jima’i ne kawai. Da yake an ɗauka cewa mata suna yaudarar maza, an hana su yin magana da maza a cikin jama’a kuma ba a bari su fita daga cikin gida ba tare da yafa gyale ba. Akasin haka, Yesu ya gargaɗi maza cewa su kasance da kamun kai sa’ad da suke sha’ani da mata kuma su bi da mata cikin mutunci da ladabi maimakon su hana su shiga cikin jama’a.—Matta 5:28.

Yesu ya ce: ‘Dukan wanda ya saki matatasa, ya kuwa auri wata, zina yake yi [ya ci amanar matarsa, NW].’ (Markus 10:11, 12) Ta hakan, Yesu ya yi watsi da koyarwar malaman Yahudawa da ke sa maza su saki matansu “a kan kowane dalili.” (Matta 19:3, 9, Littafi Mai Tsarki) Yawancin Yahudawa sun ɗauka cewa idan maigida ya kwana da wadda ba matarsa ba, ba cin amana ba ne. Malamansu sun koya musu cewa mace ce take yin zina, amma maigida ba ya zina! Saboda haka, wani littafin da ke bayyana Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da koyarwar Yesu, bayanin ya ce: “Yesu ya kāre mutuncin mata sa’ad da ya ce mutumin da ya kwana da wadda ba matarsa ba shi ma mazinaci ne.”

Yadda koyarwar Yesu take amfanar mutane a yau: A cikin ikilisiyoyin Shaidun Jehobah, mata suna tarayya da maza. Amma matan ba sa tsoron cewa za a riƙa yi musu kallon hadarin kaji ko kuma wasan banza. Kiristoci maza suna mai da hankali sa’ad da suke bi da mata don sun ɗauki “dattijai mata kuma kamar uwaye; ƙanƙanana kamar ’yan’uwa mata, cikin dukan tsabtar rai.”—1 Timotawus 5:2.

◼ Yesu ya ba da kai don ya koya wa mata. Yesu bai bi da mata kamar yadda malaman Yahudawa suka bi da su ba, amma ya koyar da su kuma ya ƙarfafa su su bayyana ra’ayinsu. Sa’ad da Yesu ya ba da kansa don koyar da Maryamu, Yesu ya nuna cewa ba a halicci mata don su riƙa dahuwa kawai ba. (Luka 10:38-42) Kalamin da ’yar’uwar Maryamu mai suna Martha ta yi bayan mutuwar Li’azaru ya nuna cewa ta amfana daga koyarwar Yesu.—Yohanna 11:21-27.

Ra’ayin mata yana da muhimmanci sosai a wurin Yesu. A lokacin da yake duniya, yawancin matan Yahudawa suna ganin cewa farin ciki ya dangana ga samun ɗa namiji mai ibada ko kuma wanda zai girma ya zama annabi. Sa’ad da wata mata take yabon Yesu, ta ce: “Cikin da ya haife ka mai-albarka ne.” Amma sai Yesu ya gaya mata cewa yin biyayya ga maganar Allah ya fi muhimmanci. (Luka 11:27, 28) Ta hakan, Yesu ya nuna cewa mace tana iya kasancewa da muhimmanci fiye da yadda ake ɗaukanta bisa ga al’adar Yahudawa idan tana da dangantaka mai kyau da Allah.—Yohanna 8:32.

Yadda koyarwar Yesu take amfanar mutane a yau: ’Yan’uwa masu gudanar da taro a ikilisiyoyin Shaidun Jehobah suna ba wa mata damar bayyana ra’ayinsu sa’ad da ake taro. Suna girmama mata masu ibada don suna “koyar da nagarta” a gidajensu da kuma ta halinsu. (Titus 2:3) Bugu da ƙari, mata suna yin wa’azi game da Mulkin Allah.—Zabura 68:11; ka duba akwatin nan “Manzo Bulus Ya Hana Mata Faɗin Ra’ayinsu ne?” a shafi na 9.

◼ Yesu ya kula da mata. A zamanin dā, ba a ɗaukan ’ya’ya mata da muhimmanci kamar ’ya’ya maza. Littafin Yahudawa da ake kira Talmud yana ɗauke da irin wannan ra’ayin domin wata aya a ciki ta ce: “Duk wanda ya haifi ’ya’ya maza zai yi farin ciki, amma kaiton wanda ya haifi ’ya’ya mata.” Wasu iyaye suna gani cewa kasancewa da ’ya ta mace nawaya ce domin za a nema mata miji kuma iyayenta za su biya sadaki wa iyayen mijin da zai aure ta. Ƙari ga haka, sa’ad da suka tsufa, ba za su iya dogara ga ita don ta kula da su ba.

Yesu ya nuna cewa ran ’ya ta mace yana da muhimmanci kamar yadda ran ɗa namiji yake. Ya ta da ’yar Jayirus kamar yadda ya ta da ɗan wata gwauruwa a birnin Nayin. (Markus 5:35, 41, 42; Luka 7:11-15) Bayan ya warƙar da wata mata da ta yi shekara 18 tana fama da wata cuta mai tsanani, Yesu ya kira ta “ɗiyar Ibrahim.” Samun wannan furucin a littattafan Yahudawa yana da wuya. (Luka 13:10-16) Da Yesu ya yi amfani da wannan furucin, ya amince cewa tana da ’yanci kamar sauran mutane kuma ya nuna cewa ita mace ce mai imani sosai.—Luka 19:9; Galatiyawa 3:7.

Yadda koyarwar Yesu take amfanar mutane a yau: Wani ƙarin magana na mutane Asiya ya ce: “Rainon ’ya ta mace tamkar yi wa lambun maƙwabcinka ban ruwa ne.” Kiristoci maza ba sa bin wannan ra’ayin, maimakon haka, suna ƙaunar yaransu maza da mata kuma suna kula da su sosai. Iyaye Kirista suna ƙoƙari wajen ilimantar da ’ya’yansu maza da mata kuma suna kula da lafiyarsu.

◼ Yesu ya amince da mata. Idan mace ta ba da shaida a kotun Yahudawa, ba a ɗaukawa da muhimmanci. Wani ɗan tarihi mai suna Josephus da ya yi rayuwa shekaru 1900 da suka shige, ya ce: “Kada a ɗauki shaidar da mace ta bayar da muhimmanci saboda mata sun cika garaje.”

Akasin haka, sa’ad da Yesu ya tashi daga matattu, ya fara bayyana kansa wa mata ne. (Matta 28:1, 8-10) Waɗannan matan sun shaida mutuwar Yesu da kuma jana’izarsa, amma sa’ad da suka gaya wa manzanninsa cewa Yesu ya tashi, manzannin ba su gaskata ba. (Matta 27:55, 56, 61; Luka 24:10, 11) A bayyane yake cewa Yesu ya bayyana kansa wa matan ne don ya ɗauke su da muhimmanci kamar yadda ya ɗauke sauran almajiransa da muhimmanci kuma ya amince cewa mata za su iya ba da shaida game da shi.—Ayyukan Manzanni 1:8, 14.

Yadda koyarwar Yesu take amfanar mutane a yau: A cikin ikilisiyoyin Shaidun Jehobah, maza masu koyarwa suna kāre mutuncin mata ta yin la’akari da shawarar da suka bayar. Maza masu aure kuma suna kasa kunne sa’ad da matansu suna bayyana ra’ayinsu. Ta hakan, suna “girmama su.”—1 Bitrus 3:7, LMT; Farawa 21:12.

Bin Ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki Zai Sa A Daraja Mata

Sa’ad da maza suka yi koyi da yadda Kristi ya bi da mata, hakan yana sa mata su kasance da mutunci da kuma ’yanci a cikin jama’a. Ainihin abin da Allah ya shirya ke nan. (Farawa 1:27, 28) Maimakon nuna wa mata wariya, maza Kirista suna bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki sa’ad da suke sha’ani da matansu kuma hakan yana tabbatar da farin ciki tsakanin ma’aurata.—Afisawa 5:28, 29.

Lokacin da wata mata mai suna Yelena ta fara nazarin Littafi Mai Tsarki, maigidanta yana yi mata wulaƙanci. Maigidan ya girma ne a inda ake yawan nuna rashin imani, wato, inda mutane suka saba sata macen da suke so su aura idan iyayenta ba su amince da auren ba, kuma ana yawan zalunci a wurin. Yelena ta ce: “Na zo na gane cewa Allah yana ƙauna ta sosai, yana ganina da mutunci kuma ya damu da ni. Ƙari ga haka, na san cewa idan maigidana ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki, zai canja halinsa da kuma yadda yake bi da ni.” Sa’ad da maigidanta ya soma nazarin Littafi Mai Tsarki kuma daga baya ya yi baftisma a matsayin Mashaidin Jehobah, Yelena ta yi farin ciki sosai. Ta ci gaba da cewa: “Maigidana ya zama mai kamun kai sosai yanzu. Muna gafarta wa juna a kowane lokaci. Littafi Mai Tsarki ya sa maigidana yana daraja ni da kuma mutunta ni.”—Kolosiyawa 3:13, 18, 19.

Yelena ɗaya ce daga cikin mata da yawa da suke jin daɗin zama da mazajensu. Mata Shaidun Jehobah suna farin ciki domin su da mazajensu suna bin umurnin da Littafi Mai Tsarki ya ba da game da aure. Sa’ad da suka yi tarayya da ’yan’uwa a ikilisiya, ana daraja su kuma suna samun ƙarfafa.—Yohanna 13:34, 35.

Kiristoci maza da mata sun fahimci cewa su ajizai ne kuma suna cikin halittun Allah da aka ƙaskantar zuwa “banza.” Ta wajen ƙulla dangantaka da Jehobah Allah, wanda ke kamar uba mai ƙauna, suna da bege cewa za su “tsira daga bautar ɓacewa zuwa cikin ’yancin darajar ’ya’yan Allah.” Wannan bege ne mai ban farin ciki wa maza da mata da Allah yake ƙauna.—Romawa 8:20, 21.

[Akwati a shafi na 9]

Manzo Bulus Ya Hana Mata Faɗin Ra’ayinsu Ne?

Mene ne manzo Bulus yake nufi sa’ad da ya rubuta cewa: ‘Bari mata su yi shuru cikin ikilisiyoyi?’ (1 Korintiyawa 14:34) Shin ya raina mata ne cewa ba su san kome ba? A’a. A maimakon haka, ya sha yin magana game da koyarwa mai kyau da mata suke yi. (2 Timotawus 1:5; Titus 2:3-5) A wasiƙar da Bulus ya rubuta zuwa ga ’yan’uwa a Korinti, ya ba da shawara cewa ’yan’uwa maza da mata da suke da baiwar annabci da kuma na yin magana da wani harshe su yi “shuru” sa’ad da wani ɗan’uwa yake koyarwa.a Saboda haka, ba mata ne kawai aka ba wa wannan shawarar ba. (1 Korintiyawa 14:26-30, 33) Wataƙila, bisa ga al’adar Helenawa a lokacin, matan da ba su daɗe da zama Kiristoci ba sukan katse wanda yake magana don su yi tambaya, kuma hakan yakan sa abubuwa su kasance babu tsari. Bulus ya ba mata shawara cewa su “tambayi mazajensu cikin gida” domin a hana irin wannan abin faruwa.—1 Korintiyawa 14:35.

[Hasiya]

a Don ƙarin bayani game da matsayin mata a cikin ikilisiya, ka duba talifin nan “Shaidun Jehobah Suna Barin Mata Su Koyar da Mutane Ne?” a shafi na 23.

[Hoto a shafi na 10]

Yesu ya mutunta Maryamu Magdaliya sa’ad da ya ba ta zarafin kai wa manzanninsa rahoton tashinsa daga matattu

[Hoto a shafi na 11]

Waɗanda suke bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki suna ganin mata da mutunci

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba