Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 2/15 p. 28-p. 29 par. 12
  • Darussa Daga Littafin Markus

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Darussa Daga Littafin Markus
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • FITACCIYAR HIDIMA A GALILI
  • (Markus 1:1–9:50)
  • WATA NA ƘARSHE
  • (Mar. 10:1–16:8)
  • Wane ne Yesu Kristi?
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
  • Mene ne Yesu Ya Yi Sa’ad da Yake Duniya?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Markus Bai Karaya Ba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Markus ‘Yana da Amfani Wajen Hidima’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 2/15 p. 28-p. 29 par. 12

Maganar Jehobah Rayayyiya Ce

Darussa Daga Littafin Markus

LINJILAR Markus ita ce marar yawa a cikin Linjila guda huɗu. Markus ne ya rubuta wannan littafin shekaru 30 bayan mutuwar Yesu Kristi da kuma tashinsa daga matattu, littafin yana ɗauke da abubuwa masu kyau da suka faru a shekaru uku da rabi da Yesu ya yi a hidimarsa a duniya.

Ko da yake an rubuta shi ne domin waɗanda ba Yahudawa ba, musamman Romawa, littafin Markus ya nuna cewa Yesu Ɗan Allah ne mai mu’ujiza wanda yake aikin wa’azi tuƙuru. Littafin ya nanata abubuwan da Yesu ya yi fiye da koyarwarsa. Idan muka mai da hankali ga Linjilar Markus hakan zai ƙarfafa bangaskiyarmu ga Almasihu kuma hakan zai motsa mu mu zama masu himma a wajen sanar da saƙon Allah a hidimar Kirista.—Ibran. 4:12.

FITACCIYAR HIDIMA A GALILI

(Markus 1:1–9:50)

Bayan ya ambata hidimar Yohanna mai Baftisma da kuma kwanaki arba’in da Yesu ya yi a jeji a cikin ayoyi sha huɗu kawai, Markus ya fara ba da rahoto mai ban al’ajabi game da hidimar Yesu a Galili. Yadda aka maimaita wannan furcin “Nan da nan” ya nuna gaggawar wannan labarin.—Mar. 1:10, 12.

A ƙasa da shekara uku, Yesu ya kewaye dukan ƙasar Galili sau uku yana wa’azi. Markus ya rubuta labarin ne bisa kwanan watan da suka faru. An cire Huɗuba Bisa Dutse, da kuma jawaban Yesu masu tsawo.

Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:

1:15—‘Lokacin’ menene ya cika? Yesu yana cewa lokacin soma hidimarsa ya yi. Domin yana duniya a matsayinsa na Sarki mai jiran gado, shi ya sa ya ce Mulkin Allah ta kusa. Mutane masu zuciya mai kyau za su iya sauraron wa’azin da yake yi kuma su ɗauki matakan da zai sa su sami amincewar Allah.

1:44; 3:12; 7:36—Me ya sa Yesu ba ya son mutane su yaɗa mu’ujizar da ya yi? Maimakon mutane su kammala bisa rahotanni masu daɗi ko na ƙarya da suka ji, Yesu yana son su gani da idanunsu cewa shi ne Kristi kuma su yanke shawara a kan abin da suka gani. (Isha. 42:1-4; Mat. 8:4; 9:30; 12:15-21; 16:20; Luka 5:14) Wani wanda ya bambanta a cikinsu shi ne na mutumin da ke da aljanu a dā a gefen ƙasar Garasinawa. Yesu ya ce masa ya je gida kuma ya gaya wa ’yan’uwansa abin da ya faru. Saboda mutanen yankunan sun roƙi Yesu ya bar yankinsu, wataƙila bai samu damar tattaunawa da mutanen yankin ba. Ganin mutumin da Yesu ya warkar da idanunsu zai iya hana duk wani maganar banza da za a yi game da aladun da suka mutu.—Mar. 5:1-20; Luka 8:26-39.

2:28—Me ya sa aka kira Yesu “Ubangiji ne har na ran assabbaci”? Manzo Bulus ya rubuta cewa: “Shari’a, . . . tana da inuwar kyawawan [abubuwa] masu-zuwa.” (Ibran. 10:1) Kamar yadda Doka ta ce, ana yin Assabaci ne bayan ranakun aiki guda shida, kuma Yesu ya warkar da mutane masu yawa a wannan ranar. Hakan na nuna hutu na salama da kuma albarka mai yawa da mutane za su samu a ƙarƙashin Sarauta ta Shekara Dubu na Kristi bayan an kawar da muguwar sarautar Shaiɗan. Saboda haka, Sarkin wannan Mulkin shi ne ‘Ubangijin assabbaci.’—Mat. 12:8; Luka 6:5.

3:5; 7:34; 8:12—Ta yaya ne Markus ya san yadda Yesu yake ji a yanayi dabam dabam? Markus ba ya cikin manzanni sha biyu kuma shi ba abokin Yesu na kud da kud ba ne. In ji al’ada na dā, abokin Markus na kud da kud, manzo Bitrus ne tushen abubuwan da Markus ya rubuta.—1 Bit. 5:13.

6:51, 52—Mecece ma’anar ‘gurasa’ da almajiran ba su fahimta ba? Sa’o’i kaɗan kafin wannan aukuwar, Yesu ya ciyar da maza dubu biyar, ban da mata da yara ƙanana da gurasa guda biyar da kifi guda biyu kawai. ‘Al’amarin gurasan’ da ya kamata manzannin su fahimta daga abin da ya faru shi ne cewa Jehobah Allah ya ba Yesu ikon yin mu’ujizai. (Mar. 6:41-44) Inda sun fahimci yawan ikon da aka ba Yesu, da ba su cika da mamaki ba sa’ad da ya yi tafiya a kan ruwa.

8:22-26—Me ya sa Yesu ya raba warkar da idanun makahon gida biyu? Wataƙila Yesu ya yi hakan ne domin ya tausaya wa makahon. Warkar da idon mutumin da ya riga ya saba da duhu tun da daɗewa a hankali zai iya ba shi lokacin sabawa da hasken rana.

Darussa Dominmu:

2:18; 7:11; 12:18; 13:3. Markus ya bayyana al’adu, kalamai, imani, da wuraren da ba sanannu ba ne ga masu karatu da ba Yahudawa ba. Ya bayyana sarai cewa Farisawa suna “yin azumi,” sun ce korban kyauta ce da aka “bayar ga Allah,” ya ce Sadukiyawa sun ce “babu tashi daga matattu,” kuma ya ce za a iya ganin haikali daga “dutsen Zaitun.” Markus bai ambata asalin Almasihu ba, domin Yahudawa ne ainihin waɗanda suke da sha’awar saninsa. Da haka, Markus ya kafa mana misali. Ya kamata mu yi la’akari da asalin masu sauraronmu sa’ad da muke yin hidima ta Kirista ko kuwa sa’ad da muke ba da jawabi a taron ikilisiya.

3:21. ’Yan’uwan Yesu ba masu bi ba ne. Saboda haka, yana jin tausayin waɗanda danginsu suke yi ma ba’a ko hamayya domin imaninsu.

3:31-35. Sa’ad da ya yi baftisma, Yesu ya zama Ɗan Allah na ruhaniya, kuma “Urushalima da ke sama” ce mamarsa. (Gal. 4:26) Tun daga wannan lokacin, ’yan’uwan Yesu na ruhaniya sun fi kusa da kuma tamani a gare shi fiye da danginsa. Hakan ya koya mana cewa muna bukatar mu mai da abubuwa na ruhaniya da farko a rayuwarmu.—Mat. 12:46-50; Luka 8:19-21.

8:32-34. Ya kamata mu guje wa duk wani alheri marar kyau da wasu za su yi mana. Mabiyin Kristi yana bukatar ya kasance a shirye don ya “yi musun kansa,” wato, yana bukatar ya hana kansa wasu abubuwa kuma ya guje wa muradin da ke nuna son kai da kuma dogon buri. Yana bukatar ya “ɗauki” gungumen azabansa da son rai, wato, ya sha wahala, idan da bukata ko kuwa a wulakanta shi ko a tsananta masa, ko kuma a kashe shi domin shi Kirista ne. Kuma dole ne ya ci gaba da ‘bin’ Yesu, ta wajen manne wa irin salon rayuwarsa. Bin tafarkin almajiranci yana bukatar mu ci gaba da kasancewa da halin sadaukar da kai kamar Yesu Kristi.—Mat. 16:21-25; Luka 9:22, 23.

9:24. Bai kamata mu ji kunyar furta bangaskiyarmu ba ko kuwa mu yi addu’ar samun ƙarin bangaskiya.—Luka 17:5.

WATA NA ƘARSHE

(Mar. 10:1–16:8)

A kusan ƙarshen shekara ta 32 A.Z., Yesu ya je “cikin iyakan ƙasar Yahuda da kuma ƙetaren Urdun,” kuma mutane da yawa suka zo wurinsa. (Mar. 10:1) Sa’ad da ya gama wa’azi a wurin, sai ya tafi Urushalima.

A ranar Nisan ta 8, Yesu yana Bait’anya. Yana cikin cin abinci sa’ad da wata mata ta zo ta zuba māi mai ƙamshi a kansa. An kwatanta abubuwan da suka faru daga shigar da Yesu ya yi Urushalima zuwa tashinsa daga matattu bisa kwanakin watan da suka faru.

Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:

10:17, 18—Me ya sa Yesu ya yi wa mutumin da ya kira shi “Malam Managarci” gyara? Domin ya ƙi amincewa da wannan lakabin da aka yi cikin daɗin baƙi, Yesu ya miƙa ɗaukakar ga Jehobah kuma ya nuna cewa Allah na gaskiya ne tushen dukan abubuwa masu kyau. Bugu da ƙari, Yesu ya jawo hankali ga wannan muhimmiyar gaskiya cewa Mahaliccin dukan abubuwa, Jehobah Allah kaɗai ne yake da ikon cewa ga abubuwa masu kyau da marar kyau.—Mat. 19:16, 17; Luka 18:18, 19.

14:25—Menene Yesu yake nufi sa’ad da ya gaya wa manzanninsa masu aminci cewa: “Ba ni ƙara sha ruwan ’ya’yan kuringar anab ba, har wancan rana da zan sha shi sabo cikin mulkin Allah”? Ba wai Yesu yana nufin cewa akwai ruwan anab a sama ba ne. Tun da yake a wasu lokatai ana kwatanta murna da ruwan anab, a nan Yesu yana nuni ne ga murnar kasancewa tare a cikin Mulki da mabiyansa shafaffu da aka ta da daga matattu.—Zab. 104:15; Mat. 26:29.

14:51, 52—Wanene saurayin da “ya gudu tsirara”? Markus kaɗai ne ya ambata wannan aukuwar, saboda haka muna iya kammalawa cewa yana magana ne game da kansa.

15:34—Kalaman Yesu “ya Allahna, Ya Allahna, don mi ka yashe ni?” suna nufin cewa ba shi da bangaskiya ne? A’a. Ko da yake ba mu san abin da ya sa ya ce haka ba, amma wataƙila kalamansa suna nuna cewa Yesu ya fahimci cewa Jehobah ya ɗauke kāriyarsa domin a gwada amincin Ɗansa sosai. Wataƙila kuma Yesu ya faɗi hakan ne domin yana son ya cika abin da Zabura 22:1 ta annabta game da shi.—Mat. 27:46.

Darussa Dominmu:

10:6-9. Nufin Allah ne cewa dukan ma’aurata su kasance tare. Saboda haka, maimakon neman kashe aure da wuri, ya kamata magidanta da matansu su yi amfani da mizanan da ke cikin Littafi Mai Tsarki don su magance duk wata matsalar da za ta iya tasowa a aure.—Mat. 19:4-6.

12:41-44. Misalin gwauruwar nan talaka ya koya mana cewa bai kamata mu nuna son kai ba wajen tallafa wa bauta ta gaskiya.

[Hoto a shafi na 29]

Me ya sa Yesu ya gaya wa wannan mutumin cewa ya je ya gaya wa danginsa abubuwan da suka same shi?

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba