-
Ka Sani?Hasumiyar Tsaro—2008 | 1 Afrilu
-
-
Yaya darajar anini biyu na Gwauruwa?
A ƙarni na farko A.Z., harajin da Yahudawa suke biya a haikali kowace shekara “rabin shekel,” ne wato kuɗin aiki na kwana biyu ke nan. (Matta 17:24) Akasarin haka, Yesu ya ce ana sayar da gwarare biyu a bakin ‘anini guda,’ wato kuɗin aiki na minti 45 ke nan. Hakika, ana iya sayan gwarare biyar da anini biyu, ko kuma kuɗin aiki na minti 90.—Matta 10:29; Luka 12:6.
Abin da gwauruwa matalauciya ta bayar a haikali da Yesu ya gani bai ma kai wannan ba. Saba biyu da ta bayar ko kuma lefta, su ne ƙananan kuɗi na ƙarshe da ake amfani da su a Isra’ila a lokacin. Sun yi daidai da kashi 1 cikin 64 na kuɗin aiki na rana, ko kuma kasa da kuɗin aiki na minti 12 wato bisa ga aikin awa 12 ke nan a rana.
Yesu ya ɗauki abin da wannan gwauruwa ta bayar da daraja fiye da dukan kuɗi mai yawa da sauran mutanen suka bayar “cikin falalassu.” Me ya sa? Labarin ya ce tana da “anini biyu,” tana iya jefa ɗaya ta riƙe ɗaya. Duk da haka, ta bayar da “abin da ta ke da shi duka, iyakar abin zaman garinta ke nan.”—Markus 12:41-44; Luka 21:2-4.
-
-
Ka Sani?Hasumiyar Tsaro—2008 | 1 Afrilu
-
-
[Hoto a shafi na 28]
Leftan, ainihinsa
-