Ka Ɗaukaka Jehobah Ta Wajen Kasancewa Da Mutunci
“Aikin [Jehobah] girma ne da sarauta.”—ZAB. 111:3.
1, 2. (a) Ta yaya za ka ba da ma’anar kalmar nan “girma”? (b) Waɗanne tambayoyi ne za a tattauna a wannan talifin?
SA’AD da aka ce Madison ’yar shekara goma ta ba da ma’anar “mutunci,” ta ce “ado ne mai kyau.” Abin da yarinyar nan ba ta sani ba shi ne Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da Allah cewa yana ‘yafe da girma [mutunci].’ (Zab. 104:1) Ga mutane kasancewa da mutunci wani lokaci ya ƙunshi yin ado da kyau. Alal misali, manzo Bulus ya ce mata Kirista su riƙa “yafa tufafi na ladabi tare da tsantseni da hankali; ba da tubkakken gashi ba, ko da zinariya ko da lu’ulu’ai, ko da tufafi masu-yawan tamani.” (1 Tim. 2:9) Amma hali mai kyau da ke ɗaukaka ‘girma da sarauta’ na Jehobah ya fi hakan.—Zab. 111:3.
2 A cikin Littafi Mai Tsarki, za a iya fassara kalmar nan “girma” a Ibrananci zuwa “jamala,” “ɗaukaka,” da kuma “daraja.” Wani ƙamus ya ba da ma’anar “girma” cewa “yanayi ne na zama wanda ya cancanta, mai ɗaukaka, da kuma mai daraja.” Amma babu wanda ya cancanci ɗaukaka da daraja fiye da Jehobah. Saboda haka, da yake mu bayinsa ne da muka keɓe kanmu, ya kamata abin da muke furtawa da kuma ayyukanmu su ɗaukaka shi. Me ya sa ’yan adam suke iya kasancewa da mutunci? Ta yaya ne aka bayyana ɗaukakar Jehobah da darajarsa? Ta yaya girman Allah zai shafe mu? Menene Yesu Kristi ya koya mana game da yadda za mu iya kasancewa da wannan halin? Ta yaya za mu iya nuna wannan halin?
Abin da ya Sa ya Kamata Mu Kasance da Daraja
3, 4. (a) Me muke bukatar mu yi da yake an ɗaukaka mu? (b) A annabce, wanene Zabura 8:5-9 yake maganarsa? (Dubi hasiya.) (c) Su wanene Jehobah ya ɗaukaka a dā?
3 Domin an halicce su cikin surar Allah, dukan ’yan adam suna iya kasancewa da daraja. Jehobah ya ɗaukaka mutum na farko ta wajen ba shi aikin kula da duniya. (Far. 1:26, 27) Bayan da mutum na farko ya yi zunubi, Jehobah ya sake furta hakkin ’yan adam game da duniya. Da haka, har ila Allah ya ‘daraja’ ’yan adam. (Ka karanta Zabura 8:5-9.)a Da yake ana ɗaukaka mu, muna bukatar mu yabi sunan Jehobah mai girma da ɗaukaka da daraja.
4 Jehobah yana ɗaukaka waɗanda suke bauta masa. Allah ya ɗaukaka Habila ta wajen karɓan hadayarsa kuma ya ƙi hadayar ɗan’uwansa Kayinu. (Far. 4:4, 5) An umurci Musa ya ba Joshua ‘darajarsa,’ wanda zai ɗauki matsayinsa na shugaban Isra’ilawa. (Lit. Lis. 27:20) Game da Sulemanu ɗan Dauda, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ubangiji kuma ya ɗaukaka Solomon ƙwarai a idanun dukan Isra’ila, ya ɗibiya masa maɗaukakiyar sarauta irin da ba a taɓa yi ma kowane sarki da ya rigaye shi cikin Isra’ila” ba. (1 Laba. 29:25) Allah zai ba da ɗaukaka da babu kamarta ga shafaffu Kiristoci da suka tashi daga matattu, waɗanda cikin aminci aka sanar da su “masu-iko, da darajar ɗaukaka ta mulkinsa.” (Zab. 145:11-13) Ta wajen girmama Jehobah, “waɗansu tumaki” na Yesu da ke ƙaruwa su ma suna da hakki mai girma da ɗaukaka.—Yoh. 10:16.
An Bayyana Ɗaukakar Jehobah da Darajarsa
5. Yaya girman ɗaukakar Jehobah yake?
5 A waƙar da ta nuna bambancin girman Allah da ƙanƙancin ’yan adam, mai zabura Dauda ya ce: “Ya Ubangiji, Ubangijinmu, Ina misalin darajar sunanka cikin duniya duka! Kai da ka sa girmanka bisa sammai.” (Zab. 8:1) Kafin halittar “sama da ƙasa” har zuwa lokacin da Allah zai cika nufinsa na mai da duniya ta zama aljanna da kuma mai da ’yan adam su zama kamilai har abada, Jehobah Allah shi ne mafi girma da ɗaukaka a sararin sama.—Far. 1:1; 1 Kor. 15:24-28; R. Yoh. 21:1-5.
6. Me ya sa mai zabura ya ce Jehobah yana yafe da ɗaukaka?
6 Sa’ad da mai zabura mutum mai tsoron Allah ya ga kyaun taurari masu yawa da ke fitowa daddare a sararin samaniya, suna ƙyalli, hakan ya motsa shi sosai. Da yake mamaki yadda Allah ya ‘shimfiɗa sammai kamar zani,’ mai zabura ya kwatanta Jehobah yana yafe da ɗaukaka domin gwaninsa na halitta. (Ka karanta Zabura 104:1, 2.) An bayyana ɗaukaka da darajar Mahalicci maɗaukaki ta ayyukansa.
7, 8. Waɗanne ɗaukakar Jehobah ne da darajarsa muke gani a sama?
7 Alal misali, ka yi la’akari da duniyar da muke ciki wadda ta ƙunshi rana da damin taurari, duniyar tana kama da ƙwayar yashi a babban teku. Wannan damin taurari yana ɗauke da fiye da taurari biliyan ɗari. Idan za ka ƙidaya tauraro ɗaya a kowane daƙiƙa babu hutawa har na rana guda, zai ɗauki fiye da shekaru 3,000 kafin ka kai biliyan ɗari.
8 Idan duniyar da muke ciki kawai tana ɗauke da taurari biliyan ɗari, sauran sararin samaniyar kuma fa? Masanan taurari sun kimanta cewa duniyar da muke ciki tana ɗaya daga cikin damin taurari biliyan 50 zuwa biliyan 125. Taurari nawa ne suke cikin sararin samaniya? Adadin taurarin sun yi yawa da ba za mu iya ƙirgawa ba. Duk da haka, Jehobah “yana ƙididigan yawan taurari; dukansu yana ba su sunayensu.” (Zab. 147:4) Da yake ka fahimci yadda Jehobah ke yafa kansa da ɗaukaka da daraja, hakan zai motsa ka ka yabe shi.
9, 10. Ta yaya ne yadda aka yi tanadin burodi yake girmama hikiman Mahaliccinmu?
9 Bari yanzu mu mai da hankali ga burodi. Jehobah ne “Mai-halittan sama da ƙasa,” kuma “Mai-bada abinci [burodi] ga mayunwata.” (Zab. 146:6, 7) ‘Girma da sarautar’ Allah sun bayana ta ayyukansa masu girma, har da tanadinsa na hatsi da ake yin burodi da shi. (Ka karanta Zabura 111:1-5.) Yesu ya koya wa mabiyansa yadda za su yi addu’a: “Ka ba mu yau abincin [burodi] yini.” (Mat. 6:11) Burodi shi ne ainihin abincin da ake ci a dā, har da Isra’ilawa. Da yake burodi abinci ne mai sauƙi, abubuwan da ake yin burodi da shi don ya zama abinci mai daɗi ba shi da sauƙi sosai.
10 Sa’ad da aka rubuta Littafi Mai Tsarki, Isra’ilawa suna yin amfani da garin alkama da ruwa wajen yin burodi. Wani lokaci ana sa yisti sa’ad da ake yin burodi. Waɗannan abubuwa da ake haɗawa suna da amfani ga juna. Ba a fahimtar yadda waɗannan abubuwa suke aiki. Bugu da ƙari, yadda burodi yake aiki a cikin jiki wani abu ne mai ban mamaki. Shi ya sa mai zabura ya ce: “Ya Ubangiji, ayyukanka ina misalin yawansu! Da hikima ka yi su duka.” (Zab. 104:24) Hakan yana motsa ka ka yabi Jehobah?
Ta Yaya Ne Girman Allah da Ɗaukakarsa Suke Shafan Ka?
11, 12. Ta yaya yin bimbini bisa ayyukan Allah zai shafe mu?
11 Ba sai mun zama masanan taurari ba ne kafin mu ga kyaun sararin sama ba ko kuma mu zama masu yin burodi kafin mu more shi ba. Don mu fahimci girman Mahaliccinmu, muna bukatar mu keɓe lokaci don mu yi tunanin aikinsa. Ta yaya irin wannan bimbini zai iya amfane mu? Amfanin daidai ne da yin bimbini a kan ayyukan Jehobah a wasu abubuwa.
12 Game da ayyuka masu girma da Jehobah ya yi wa mutanensa, Dauda ya ce: “Zan yi bimbini da mashahuriyar ɗaukaka ta darajarka, da dukan ayukanka masu-ban mamaki.” (Zab. 145:5) Muna nuna godiya ga waɗannan ayyukan ta wajen nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma yin bimbini bisa abin da muka karanta a ciki. Menene sakamakon yin wannan bimbini? Godiyarmu ga girmar da ɗaukakarsa za ta ƙaru. Hakika, kamar Dauda za mu girmama Jehobah muna cewa: “Ni ma in bayana girmanka.” (Zab. 145:6) Yin bimbini bisa ga ayyukan Allah masu ban al’ajabi zai ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah kuma ya motsa mu mu sa ƙwazo a wajen gaya wa wasu game da shi. Kana shelar bishara kuma kana taimakon mutane su nuna godiya da ɗaukaka, da kuma darajar Jehobah Allah?
Yesu ya Nuna Yadda Za a Girmama Allah
13. (a) Menene Daniel 7:13, 14, ya ce Jehobah ya ɗanka wa Ɗansa? (b) Da yake Yesu Sarki ne, yaya ya bi da talakawansa?
13 Ɗan Allah, Yesu Kristi ya yi bishara sosai kuma ya ɗaukaka Ubansa na Samaniya. Jehobah ya ɗaukaka Ɗansa makaɗaici ta wajen ba shi ‘sarauta da mulki.’ (Ka karanta Daniel 7:13, 14.) Amma, Yesu ba mai girman kai ba ne. Sarki ne mai juyayi wanda ya fahimci kasawan talakawansa kuma yana bi da su cikin daraja. Ka yi la’akari da wani misali na yadda Yesu da aka naɗa Sarki ya bi da mutane da ya sadu da su, musamman ma waɗanda mutane suka ƙi kuma ba sa son su.
14. Yaya ake ɗaukan kutare a Isra’ila ta dā?
14 Mutane da suka kamu da kuturta a zamanin dā sau da yawa suna mutuwa sannu sannu don baƙin ciki. A hankali, ciwon na yaɗuwa zuwa dukan gaɓoɓin jikin. Ana ɗaukan warkar da kuturu kamar ta da mutum daga matattu. (L. Li 12:12; 2Sa 5:7, 14) Ana ɗaukan kutare marasa tsabta kuma ana ƙinsu kuma ana ware su daga jama’a. Idan suna isan inda mutane suke, za su riƙa cewa: “Marar-tsarki; marar tsarki!” (Le 13:43-46) Ana ɗaukan kuturu a matsayin matacce. Koyarwar malaman addinai ta ce, kuturu zai yi nisan kusan kafa shida daga wurin Bayahude. An ba da rahoto cewa idan shugaban addini ya ga kuturu da nesa, yana jifansa da duwatsu don kada ya yi kusa da shi.
15. Yaya Yesu ya bi da wani kuturu?
15 Amma, abu ne mai ban sha’awa a ga yadda Yesu ya bi da wani kuturu da ya zo wajensa kuma ya roƙe shi ya warkar da shi. (Ka karanta Markus 1:40-42.) Maimakon ya gaya wa kuturun ya tafi, Yesu ya yi juyayin mutumin kuma ya daraja shi. Yesu ya ɗauke shi a matsayin mutum mai son a warkar da shi. Da yake zuciyarsa ta motsa shi, Yesu ya nuna yadda yake jin tausayin mutumin. Ya taɓa kuturun kuma ya warkar da shi.
16. Wane darassi muka koya daga yadda Yesu ya bi da wasu mutane?
16 Da yake mu mabiyan Yesu ne, ta yaya za mu yi koyi da yadda Yesu ya nuna ɗaukakar Ubansa? Hanya ɗaya, ita ce ta wajen fahimta cewa dukan ’yan adam ko da menene matsayinsu, lafiyarsu, ko shekarunsu sun cancanci mu daraja su kuma mu yi musu ladabi. (1Bi 2:17) Ya kamata musamman waɗanda suke da matsayin shugabanci, kamar magidanta, iyaye, da kuma dattawa Kirista su ɗaukaka waɗanda suke kula da su don su ci gaba da samun darajar kansu. Littafi Mai Tsarki ya nanata cewa ana bukatar hakan daga dukan Kiristoci ta wajen cewa: “Ku yi zaman daɗin soyayya da junanku cikin ƙaunar ’yan’uwa; kuna gabatarda juna cikin bangirma.”—Ro 12:10.
Nuna Daraja ga Bauta
17. Menene za mu iya koya daga Nassosi game da nuna ɗaukaka sa’ad da muke bauta wa Jehobah?
17 Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa ya kamata mu mai da hankali sosai wajen nuna ɗaukaka sa’ad da muke bauta wa Jehobah. Mai Wa’azi 5:1 ta ce: “Lura da ƙafarka sa’anda ka tafi gidan Allah.” An umurci Musa da Joshua su cire takalmansu sa’ad da suke tsaye a wuri mai tsarki. (Fit 3:5; Jos 5:15) Za su yi hakan don su nuna daraja ko bauta. An umurci firistoci Baisra’ila su saka wanduna na linin “domin a suturta tsiraicinsu.” (Fit 28:42, 43) Hakan yana hana su buɗe jikinsu sa’ad da suke hidima a bagadi. Kowanne da ke cikin iyalin firist zai ɗaukaka mizani na Allah game da girma.
18. Ta yaya ake nuna daraja a bautarmu ga Jehobah?
18 Ɗaukaka a bauta ya ƙunshi nuna daraja da ladabi. Don a daraja mu kuma a ba mu ladabi, dole ne mu yi hakan. Bai kamata mu nuna cewa muna da daraja ba. Ya kamata Allah ya ga zuciyarmu cewa mu masu nuna daraja ne ba don mutane su gani ba. (1Sam 16:7; Mis 21:2) Ya kamata nuna daraja ya zama halinmu kuma ya shafi dangantakarmu da mutane, har da yadda muke ɗaukan kanmu da kuma yadda muke ji game kanmu. Hakika, ya kamata a ga cewa mu masu nuna daraja ne a kowane lokaci da kuma dukan abubuwa da muke yi da kuma faɗa. Idan ya zo ga halinmu, da tufafinmu da kuma adonmu, ya kamata mu tuna da kalmomin manzo Bulus: “Kada mu bada dalilin tuntuɓe cikin komi, domin kada a yi zargin hidimarmu; amma cikin kowace matsala mu koɗa kanmu masu-hidimar Allah.” (2Ko 6:3, 4) Ya kamata mu yi “ado ga koyaswa ta Allah Mai-cetonmu cikin dukan abu.”—Tit 2:10.
Ka Ci Gaba da Nuna Ɗaukaka na Allah
19, 20. (a) Wace hanya ce mai kyau na ɗaukaka wasu? (b) Me ya kamata mu kuɗuri aniyar yi game da ɗaukaka?
19 Shafaffu Kiristoci “manzanni . . . madadin Kristi” suna nuna ɗaukaka. (2Ko 5:20) “Waɗansu tumaki” da suke tallafa musu, wakilai ne masu ɗaukaka Mulkin Almasihu. Wakili yana magana da gaba gaɗi da kuma mutunci a madadin gwamnatinsa. Saboda haka, ya kamata mu yi magana da mutunci da gaba gaɗi wajen tallafa wa Mulkin Allah. (Afi 6:19, 20) Muna ba mutane mutunci ta wajen gaya musu “bishara ta alheri.”—Ish 52:7.
20 Ya kamata mu kuɗuri aniya mu ɗaukaka Allah ta wajen aikatawa cikin jituwa da darajarsa. (1Bi 2:12) Bari koyaushe mu ɗaukaka shi, bautarsa da kuma ’yan’uwanmu masu bi. Kuma bari Jehobah, wanda ya yafa kansa da girma da daraja, ya yi farin ciki da yadda muke bauta masa da daraja.
[Hasiya]
a A annabce, furcin Dauda a Zabura ta 8 yana nuni ga Yesu Kristi mutum kamiltacce.—Ibran. 2:5-9.
Ta Yaya Za Ka Amsa?
• Ta yaya nuna godiya game da girman Jehobah da kuma ɗaukakarsa ya kamata ya shafe mu?
• Menene za mu koya game da daraja ta yadda Yesu ya bi da wani kuturu?
• Ta yaya za mu ɗaukaka Jehobah a hanyoyi da za su daraja shi?
[Hoto a shafi na 14]
Ana ganin ayyukan Jehobah masu girma ta wajen tanadin burodi da ya yi
[Hoto a shafi na 15]
Menene ka koya game da ɗaukaka ta yadda Yesu ya bi da wani kuturu?
[Hoto a shafi na 16]
Bauta mai ɗaukaka ta ƙunshi daraja Jehobah