Kana Da “Nufin Kristi”?
“Allah na haƙuri da na ta’aziya shi yarda maku ku zama da hankali ɗaya . . . bisa ga Kristi Yesu.”—ROMAWA 15:5.
1. A wace hanya ce aka zana Yesu a zane-zane da yawa na Kiristendom, kuma me ya sa wannan ba gaskiyar kamanin Yesu ba ne?
“BA A taɓa ganin shi ya yi dariya ba.” Haka aka kwatanta Yesu a wata takarda da take da’awar wai wani ma’aikacin Roma ne na dā ya rubuta. Wannan takarda, wadda aka sani a yadda take yanzu tun kusan ƙarni na 11, an ce ya yi tasiri akan masu zane da yawa.a A cikin zane-zane da yawa da aka yi, an zana Yesu mutum ne mai baƙin ciki wanda da ƙyar yake murmushi, idan ma ya taɓa yi kenan. Amma wannan da ƙyar zai zama gaskiyar kamanin Yesu, wanda Lingila suka kwatanta shi mutum ne mai ƙauna, mai kirki da zurfin juyayi.
2. Ta yaya za mu gina ‘hali irin na Kristi Yesu,’ kuma menene wannan zai shirya mu mu yi?
2 Babu shakka, don mu san ainihin Yesu, dole ne mu cika ƙwaƙwalwarmu da kuma zukatanmu da cikakken fahimtar irin mutumin da Yesu yake da gaske lokacin da yake a nan duniya. Saboda haka, bari mu bincika labaran Lingila da suka bada fahimi cikin “nufin Kristi”—watau, juyayinsa, fahiminsa, tunaninsa, da kuma amfani da dalilansa. (1 Korinthiyawa 2:16) Yayin da muke bincike, bari mu duba yadda za mu gina ‘hali irin na Kristi Yesu.’ (Romawa 15:5) Da haka, za mu zama a shirye a rayuwarmu da kuma a wajen sha’ani da wasu mu bi tafarki da ya kafa mana.—Yohanna 13:15.
Da Sauƙi a Zo Gareshi
3, 4. (a) Yaya yanayin labari da ke rubuce a cikin Markus 10:13-16 yake? (b) Yaya Yesu ya yi lokacin da almajiransa suke ƙoƙarin hana yara ƙanƙanana zuwa wurinsa?
3 Mutane suna son matsowa kusa da Yesu. Wasu lokutta mutane dabam dabam manya da yara suna zuwa wurinsa babu fargaba. Ka yi la’akari da abin da ya faru da ke rubuce a Markus 10:13-16. Ya faru ne a kusan ƙarshen hidimarsa, da yake kan hanyarsa zuwa Urushalima a lokaci na ƙarshe, don ya fuskanci mutuwar azaba.—Markus 10:32-34.
4 Ka ƙaga yadda yanayin yake. Mutane suka fara kawo yara, har da jarirai, don Yesu ya yi masu albarka.b Amma dai, almajiran suka yi ƙoƙarin su hana yaran zuwa wurin Yesu. Wataƙila almajiran suna jin cewa hakika Yesu ba ya son a dame shi da yara cikin waɗannan makonni na musamman. Amma ba daidai ba ne. Da Yesu ya gano abin da almajiran suke yi, bai ji daɗinsa ba. Yesu ya kira yaran, yana cewa: “Ku bar yara ƙanƙanana su zo gareni; kada ku hana su.” (Markus 10:14) Sai ya yi abin da ya nuna hali mai kyau kuma na ƙauna da gaske. Labarin ya ce: “Ya rungume su, ya sa masu albarka.” (Markus 10:16) Babu shakka yaran sun sake yayin da Yesu ya rungume su.
5. Menene labari da ke cikin Markus 10:13-16 ya gaya mana game da irin mutumin da Yesu yake?
5 Wancan gajeran labarin ya gaya mana ƙwarai irin mutumin da Yesu yake. Ka lura cewa yana da sauƙi a zo gareshi. Ko da yake yana da mukami mai girma a sama, ba ya tsoratar da mutane ajizai ko kuma ya rena su ba. (Yohanna 17:5) Ba muhimmin abu ba ne a cewa yara sun sake a wurin shi? Hakika ba za su je wurin mutumin da ba shi da juyayi, ba ya murna, bai taɓa murmushi ba ko dariya! Mutane manya da yara sun zo wurin Yesu domin sun ga yana da ƙauna, yana kula da mutane, kuma sun tabbata cewa ba zai kore su ba.
6. Ta yaya dattiɓai za su mai da kansu don a zo wurinsu da sauƙi?
6 A yin tunani akan wannan labarin, za mu iya tambayar kanmu, ‘Ina da nufin Kristi kuwa? Yana da sauƙi a zo wurina kuwa?’ A waɗannan lokutta masu wuya, tumakin Allah suna bukatar maƙiyaya da yake da sauƙi a je wurinsu, mutane waɗanda suna kama da “maɓoya daga iska.” (Ishaya 32:1, 2; 2 Timothawus 3:1) Dattiɓai, idan ku ka gina marmari da gaske game da yan’uwanku, kuma kuna bada kanku garesu da son ranku, za su ga yadda ku ke damuwa. Za su ga haka a fuskokinku, za su ji cikin muryoyinku, kuma za su gani a cikin halayenku na kirki. Irin wannan ƙauna da damuwa na gaskiya za su kawo yanayi wanda za a iya dogara da ku kuma wanda zai zama da sauƙi wasu, har ma da yara, su zo wurinku. Wata Kirista ta bayyana dalilin da ya sa ta gaya wa wani dattijo abin da yake damunta: “Ya yi mini magana a hanya ta ƙauna kuma da juyayi. Da ba haka ba, wataƙila ba zan ce uffan ba. Ya sa na ji ina kāre.”
Yin La’akari da Wasu
7. (a) Yaya Yesu ya nuna cewa yana la’akari da wasu? (b) Mai yiwuwa me ya sa Yesu ya mai da ganin gari na wani makaho a hankali?
7 Yesu yana la’akari da wasu. Yana kula da yadda wasu suke ji. Ganin mashawuya yana taɓa shi sosai har ya motsa shi ya sauƙaƙa masu wahalarsu. (Matta 14:14) Yana kuma la’akari da kasawa da kuma bukatun wasu. (Yohanna 16:12) Sau ɗaya ma, mutane suka kawo masa makaho suka roƙi Yesu ya warkar da shi. Yesu ya mai da ma mutumin idanunsa, amma ya yi hakan a hankali. Da farko, mutumin ya ga mutane amma ba sosai ba yake ganinsu—“kamar itatuwa; suna yawo.” Sai, Yesu ya sa yana ganin gari sarai. Me ya sa ya warkar da mutumin a hankali? Wannan wataƙila don ya sa wanda ya saba da duhu ya daidaita ma ganin hasken rana farat ɗaya kuma cikin duniya mai faɗi.—Markus 8:22-26.
8, 9. (a) Menene ya auku jim kaɗan bayan Yesu da almajiransa suka shiga lardin Decapolis? (b) Ka kwatanta yadda Yesu ya warkar da kurma.
8 Ka yi la’akari kuma da abin da ya wakana bayan Faska na 32 A.Z. Yesu da almajiransa suka shigo cikin lardin Decapolis, gabas da Tekun Galili. A can, taro mai girma suka same su suka kawo wa Yesu mutane da yawa da suke jinya da kuma naƙasassu, kuma ya warkar da su duka. (Matta 15:29, 30) Abin marmari kuma, Yesu ya mai da hankalinsa musamman ga wani mutum. Markus marubucin Lingilar, wanda shi kaɗai ya bada wannan labarin, ya faɗi abin da ya auku.—Markus 7:31-35.
9 Mutumin kurma ne ba ya iya magana. Wataƙila Yesu ya kula da rawar jikinsa ko kuma kunya da yake ji. Sai Yesu ya yi wani abin mamaki. Ya fid da mutumin daga tsakanin taron, zuwa gefe ɗaya. Sai Yesu ya yi masa bebenci ya nuna wa mutumin abin da yake son ya yi. Ya “sa yatsotsinsa a cikin kunnuwansa, ya tofa miyau, ya taɓa harshensa.” (Markus 7:33) Sai, Yesu ya dubi sama ya yi addu’a. Waɗannan ayyuka zai sanar da mutumin cewa ‘Abin da na ke so na yi maka ta wurin ikon Allah ne.’ A ƙarshe Yesu ya ce: “Ka buɗe.” (Markus 7:34) Sai, kunnuwan mutumin suka buɗe, kuma ya fara magana daidai.
10, 11. Ta yaya za mu nuna muna la’akari da yadda wasu suke ji a cikin ikklisiya? a cikin iyali?
10 Lallai Yesu ya yi la’akari da wasu! Yana kula da yadda suke ji, kuma wannan juyayi ga wasu, ya motsa shi ya yi aiki a hanyar da ya nuna kula da yadda suke ji. Yadda muke Kirista, ya kamata mu gina kuma mu nuna nufi irin na Kristi a wannan hanyar. Littafi Mai-Tsarki ya yi mana gargaɗi: “Dukanku ku zama hankalinku ɗaya, masu-juyayi, kuna yin ƙauna kamar yan’uwa, masu-tabshin zuciya, masu-tawali’u.” (1 Bitrus 3:8) Babu shakka wannan ya bukaci mu yi magana kuma mu aikata a hanyar da zai nuna muna tunawa da yadda wasu suke ji.
11 A cikin ikklisiya, za mu nuna muna tunawa da yadda wasu suke ji ta wurin ba su daraja, muna bi da su kamar yadda muke so a bi da mu. (Matta 7:12) Wannan zai haɗa da kula da abin da za mu faɗa kuma da yadda za mu faɗe su. (Kolossiyawa 4:6) Ka tuna fa cewa ‘magana da garaje kamar sussukan takobi ne.’ (Misalai 12:18) A cikin iyali kuma fa? Mata da miji waɗanda suna ƙaunar juna da gaske suna kula da juyayin juna. (Afisawa 5:33) Ba sa baƙar magana, ba sa suka, ba sa zagin juna—dukan waɗannan da suke sa fushi da ba ya hucewa da wuri. Yara ma suna da juyayi, kuma iyaye masu ƙauna suna kula da waɗannan. Lokacin da ake bukatar gyara, waɗannan iyaye suna yin haka ta hanyar da za ta nuna suna daraja ’ya’yansu kuma suna kawar da su daga kunya.c (Kolossiyawa 3:21) Lokacin da muka nuna muna la’akari da wasu, muna nuna cewa muna da nufin Kristi.
Amincewa da Wasu da Son Rai
12. Wane daidaitacen ra’ayi Yesu yake da shi, na gaske game da almajiransa?
12 Yesu yana ganin almajiransa daidai, yadda suke da gaske. Ya sani sarai cewa su ba kamiltattu ba ne. Ban da haka ma, yana iya sanin zukatan mutane. (Yohanna 2:24, 25) Duk da haka, ba kallon ajizancinsu yake yi ba amma ingancinsu masu kyau yake kallo. Ya ga abin da waɗannan mutane da Jehovah ya jawo za su iya zama. (Yohanna 6:44) Ra’ayi mai kyau na Yesu game da almajiransa ya bayyana a yadda ya bi da su kuma da abin da ya yi masu. Abu ɗaya shine, ya nuna son amincewa da su.
13. Ta yaya Yesu ya nuna cewa ya amince da almajiransa?
13 Yaya Yesu ya nuna wannan amincewar? Lokacin da ya bar duniya, ya ba almajiransa shafaffu nawaya mai nauyi. Ya saka hakin kula da al’amarin Mulkinsa na dukan duniya a hannunsu. (Matta 25:14, 15; Luka 12:42-44) A lokacin hidimarsa, ya nuna har a ƙananan abubuwa cewa ya amince da su. Lokacin da ya ninka abinci don a ciyar da jama’a, ya ba almajiransa nawayar rarraba abincin.—Matta 14:15-21; 15:32-37.
14. Yaya za mu taƙaita labarin da yake cikin Markus 4:35-41?
14 Ka yi la’akari kuma, da labari da ke rubuce a cikin Markus 4:35-41. A wannan lokaci Yesu da almajiransa sun shiga jirgin ruwa suna hayewa ta gabashin Tekun Galili. Bada jimawa ba bayan sun tashi, Yesu ya kwanta a bayan jirgin kuma barci mai zurfi ya ɗauke shi. Amma dai, bada jimawa ba, “babban hadari kuwa na iska ya tashi.” Irin wannan hadarin abu ne na kullum a Tekun Galili. Domin yana ƙasa ƙasa (wajen ƙafa 700 ƙasa da teku), iska ya fi zafi a wajen fiye da wajaje da suka kewaye wurin, kuma yana haddasa wahala a yanayin wurin. Ƙari ga wannan, iska mai ƙarfi tana busawa zuwa kwarin Urdun daga Dutsen Hermon wanda yake arewanci. In wuri ya yi shuru yanzu an jima hadari zai fara. Ka yi tunani game da wannan: Yesu babu shakka ya san game da hadari na kullum na wurin, domin ya yi girma a Galili. Duk da haka, ya yi barci cikin sukuni, ya dogara da iyawar almajiransa, waɗanda wasu cikinsu ’yan sū ne.—Matta 4:18, 19.
15. Ta yaya za mu iya yin kwaikwayon amincewar da Yesu ya yi ga almajiransa?
15 Za mu iya kwaikwayon amincewar da Yesu ya yi ga almajiransa? Wasu suna iske shi da wuya su bada nawaya ga wasu. A ce dai, suna so kullum suna da mukaminsu. Suna iya tunani cewa, ‘Idan ina son a yi abin nan daidai, to sai dai na yi da kai na!’ Amma idan kome sai dai mu yi da kanmu, to muna cikin haɗarin gajiyar da kanmu sosai, wataƙila kuma muna ɓad da lokaci da bai kamata ba a waje daga iyalinmu. Ban da haka ma, idan ba mu bada ayyuka da kuma nawaya ga wasu ba, muna hana su gwaninta da kuma koyo da ya dace. Yana da kyau mu koyi amincewa da wasu domin mu ba su wasu ayyuka. Mu yi ƙoƙari mu tambayi kanmu da gaskiya, ‘Ina da nufin Kristi a wannan al’amari? Ina raba ayyuka ga wasu, da amincewar za su yi iyakar ƙoƙarinsu?’
Ya Nuna Yarda da Almajiransa
16, 17. A dare na ƙarshe na rayuwarsa a duniya, wane tabbatarwa ne Yesu ya yi wa manzanninsa, ko da yake ya san za su yashe shi?
16 Yesu ya nuna yana da ra’ayi mai kyau game da almajiransa a wata muhimmiyar hanya. Ya nuna masu cewa ya yarda da su. Wannan ya fita sarai daga cikin kalmomin tabbatarwa da ya gaya ma manzanninsa a darensa na ƙarshe na rayuwarsa a duniya. Ka lura da abin da ya faru.
17 Da akwai ayyuka da yawa ma Yesu a maraicen. Ya ba manzanninsa darasi game da tawali’u ta hanyar wanke sawayensu. Daga baya, ya kafa abincin maraice wanda zai zama abin tunin mutuwarsa. Sai, manzannin suka sake hargitsewa da musu game da wanda ake gani ya fi girma a tsakaninsu. Sarkin haƙuri, Yesu bai tsauta masu ba amma ya sa su su yi tunani. Sai ya gaya masu abin da ke zuwa a nan gaba: “A cikin daren nan dukanku za ku yi tuntuɓe saboda ni: gama an rubuta, Zan buga makiyayi, tumakin garke kuma za su watse.” (Matta 26:31; Zechariah 13:7) Ya san cewa abokansa na kusa kusa za su yashe shi a lokacin da yake bukatarsu. Har illa yau, bai hukunta su ba. Akasin haka, ya gaya masu: “Amma bayanda na tashi, zan tafi gabanku zuwa cikin Galili.” (Matta 26:32) I, ya tabbatar masu cewa ko da yake za su yashe shi, shi ba zai yashe su ba. Lokacin da wannan wahala mai tsanani ta wuce, zai sake haɗuwa da su.
18. A Galili, Yesu ya ba wa almajiransa wane aiki ne mai nauyi, kuma ta yaya manzannin suka yi aikin?
18 Yesu ya cika maganarsa. Daga baya, a Galili, Yesu da ya tashi daga matattu ya bayyana ga amintattun manzanninsa 11 ɗin, waɗanda babu shakka sun taru haɗe da wasu da yawa. (Matta 28:16, 17; 1 Korinthiyawa 15:6) A wurin, Yesu ya ba su aiki mai nauyi: “Ku tafi fa, ku almajirtadda dukan al’ummai, kuna yi masu baftisma zuwa cikin sunan Uba da na Ɗa da na Ruhu Mai-tsarki: kuna koya masu su kiyaye dukan iyakar abin da na umurce ku.” (Matta 28:19, 20) Littafin Ayukan Manzanni ya ba mu tabbaci sarai cewa manzannin sun yi wannan aikin. Sun yi ja-goranci a aikin wa’azin bishara da aminci a ƙarni na farko.—Ayukan Manzanni 2:41, 42; 4:33; 5:27-32.
19. Menene ayyukan Yesu bayan tashinsa daga matattu ya koya mana game da nufin Kristi?
19 Menene wannan labari da ke a bayyane ya koya mana game da nufin Kristi? Yesu ya ga sa’i da manzanninsa suka fi fusatawa, duk da haka ya “ƙaunace su har matuƙa.” (Yohanna 13:1) Duk da kurakuransu, ya nuna masu cewa ya yarda da su. Ka lura cewa amincewar Yesu garesu ba kuskure ba ne. Amincewa da kuma bangaskiya da ya nuna a garesu babu shakka ya ƙarfafa su su yi niyya a zukatansu su yi aikin da ya umurce su su yi.
20, 21. Ta yaya za mu kasance da ra’ayi mai kyau game da yan’uwanmu masu bi?
20 Ta yaya za mu nuna nufin Kristi a wannan hanyar? Kada ka nuna ra’ayin baƙin ciki game da yan’uwa masu bi. Idan kana mummunar tunani, kalmominka da kuma ayyukanka ƙila sa bayyana shi. (Luka 6:45) Amma dai, Littafi Mai-Tsarki ya gaya mana cewa ƙauna “tana gaskata abu duka.” (1 Korinthiyawa 13:7) Ƙauna nagari ce, ba mummuna ba. Tana ginawa ne ba rushewa ba. Mutane suna na’am ga ƙauna da kuma ƙarfafawa maimakon ga tsoratarwa. Za mu iya gina wasu kuma ƙarfafa su ta nuna mun amince da su. (1 Tassalunikawa 5:11) Idan kamar Kristi, muna da ra’ayi mai kyau game da yan’uwanmu, za mu bi da su a ta hanyar da za mu gina su kuma mu zaro ingancinsu.
21 Ginawa da kuma nuna nufin Kristi ta wuce kwaikwayon wasu abubuwan da Yesu ya yi kawai. Kamar yadda aka ambata a talifin da ya gabata, idan za mu yi abu kamar yadda Yesu ya yi, dole ne mu fara ɗaukan abubuwa kamar yadda ya yi. Lingila ta taimake mu mu ga wani ɓangare na mutumtakarsa, tunaninsa da kuma juyayinsa game da aiki da aka ba shi, kamar yadda talifi na gaba zai tattauna.
[Hasiya]
a A cikin takardar, wanda ya buga jabun ya kwatanta kamanin da ya ke zaton na Yesu ne na zahiri, har ma da launin gashinsa, gemunsa, da ƙwayoyin idanunsa. Mafassarin Littafi Mai-Tsarki Edgar J. Goodspeed ya yi bayani cewa wannan jabun takarda “an yi ta ne don a yarda da kwatanci da yake cikin littafin mai zanen kamanin Yesu na zahiri.”
b Babu shakka, shekarun yaran sun bambanta. Kalmar da aka yi amfani da ita anan “yara ƙanƙanana” an yi amfani da ita wajen ’yar Jairus mai shekara 12. (Markus 5:39, 42; 10:13) Duk da haka, a cikin labari da ke hannun riga da wannan, Luka ya yi amfani da kalmar da aka yi amfani da ita ma jarirai.—Luka 1:41; 2:12; 18:15.
c Duba talifin nan “Kuna Daraja Ɗaukakarsu” a Hasumiyar Tsaro fitar 1 ga Afrilu, 1998, (Turanci).
Za Ka Iya Bayyanawa?
• Yaya Yesu ya yi lokacin da almajiransa suke ƙoƙarin su hana yara daga zuwa wurinsa?
• A waɗanne hanyoyi ne Yesu ya nuna juyayi ga wasu?
• Ta yaya za mu yi kwaikwayon amincewar Yesu ga almajiransa?
• Ta yaya za mu yi kwaikwayon yarda da Yesu ya nuna wa manzanninsa?
[Hoto a shafi na 9]
Yara sun kasance a sake wurin Yesu
[Hoto a shafi na 10]
Yesu ya bi da wasu da tausayi
[Hoto a shafi na 11]
Dattiɓai da suke da sauƙi a zo wurinsu albarka ce