Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 3/15 p. 32
  • Tambayoyi Daga Masu Karatu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Tambayoyi Daga Masu Karatu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Nassosi ya ambata “litafi na Jashar” da kuma ‘litafin Yaƙin Jehobah.’ (Josh. 10:13; Lit. Lis. 21:14) Waɗannan littattafan biyu ba sa cikin Littafi Mai Tsarki. Waɗannan hurarrun rubutu ne da suka ɓace?
  • Wane Irin Littafi Ne Baibul?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Shin Littafi Mai Tsarki Ya Ba da Dukan Bayani Game da Yesu Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 3/15 p. 32

Tambayoyi Daga Masu Karatu

Nassosi ya ambata “litafi na Jashar” da kuma ‘litafin Yaƙin Jehobah.’ (Josh. 10:13; Lit. Lis. 21:14) Waɗannan littattafan biyu ba sa cikin Littafi Mai Tsarki. Waɗannan hurarrun rubutu ne da suka ɓace?

Babu wani dalilin da zai sa a ce waɗannan littatafai biyu hurarru ne kuma daga baya suka ɓace ba. Marubutan Littafi Mai Tsarki sun ambata wasu littattafai. Wataƙila waɗannan littattafai suna cikin sashen Littafi Mai Tsarki da aka kwatanta da kalamai da masu karatu a zamanin nan ba za su fahimta ba. Alal misalai, 1 Labarbaru 29:29 ta ambata “labarin Samu’ila mai-gani,” “labarin Nathan annabi” da kuma “labarin Gad mai-gani.” Waɗannan suna nufin littatafai da muka sani kamar Samuila ta ɗaya da ta biyu, ko kuma littafin Alƙalawa.

A wani ɓangare kuma, wasu littattafai da aka kwatanta suna nufin littatafai da suke da sunaye da suka yi kama da sunayen da ke cikin Littafi Mai Tsarki amma ainihi ba sa cikin Littafi Mai Tsarki. Za mu iya kwatanta hakan da littatafai guda huɗu na dā: “Litafin labarin sarakunan Yahuda,” “litafin sarakunan Yahuda da na Isra’ila,” “litafin sarakunan Isra’ila,” da “litafin sarakunan Isra’ila da na Yahuda.” Ko da yake waɗannan sunayen sun yi kama da sunayen littatafai da ke cikin Littafi Mai Tsarki da muka sani kamar Sarakuna na ɗaya da na biyu, littatafai huɗu da aka ambata ba hurarru ba ne, kuma ba sa cikin Littafi Mai Tsarki. (1 Sarakuna 14:29; 2 Labarbaru 16:11; 20:34; 27:7) Wataƙila labarai ne da aka rubuta a lokacin da annabi Irmiya da Ezra suka rubuta labarai da ke cikin Littafi Mai Tsarki.

Hakika, wasu marubutan Littafi Mai Tsarki sun ambata ko kuwa sun yi amfani da waɗannan tarihin da suka wanzu amma ba hurarru ba ne don samun ƙarin bayani. Esther 10:2 ta ambata “litafin labarin sarakunan Media da Persia.” Hakazalika, sa’ad da yake shirya Linjilarsa, Luka ya “bibbiya abu duka daidai.” Wataƙila yana nufin cewa ya bincika wasu littatafai sa’ad da yake rubutawa game da zuriyar Yesu da muke karantawa a cikin Linjilar da ya rubuta. (Luka 1:3; 3:23-38) Ko da yake littattafan da Luka ya bincika ba hurarru ba ne, Linjilar da ya rubuta hurarra ce. Kuma wannan Linjilar tana da amfani a gare mu.

Littattafai biyu da aka ambata, wato, “litafin Jashar” da kuma ‘litafin Yaƙin Jehobah’ ba hurarrun littattafai ba ne. Saboda haka, Jehobah bai adana littattafan ba. Da yake Littafi Mai Tsarki ya ambata waɗannan littattafai shi ya sa ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka kammala cewa littattafan waƙa ce game da yaƙe-yaƙe tsakanin Isra’ila da abokanan gabanta. (2 Sam. 1:17-27) Wani kundin sani na Littafi Mai Tsarki ya ce abin da ke cikin waɗannan littattafan wataƙila “waƙoƙi ne da ƙwararrun mawaƙa a Isra’ila na dā suka adana.” Wasu cikin mazan da Allah ya yi amfani da su a matsayin annabawa ko kuma masu ganin wahayi sun yi rubutu da Jehobah bai hure ba ko kuma sun haɗa su da Nassosi “mai-amfani ne ga koyarwa, ga tsautawa, ga kwaɓewa” a zamaninmu.—2 Tim. 3:16; 2 Lab. 9:29; 12:15; 13:22.

Ko da yake an ambata wasu littatafai a cikin Littafi Mai Tsarki kuma an yi amfani da su ba zai sa mu kammala cewa hurarru ne ba. Amma, Jehobah Allah ya adana dukan rubutu game da “maganar Ubangiji,” kuma waɗannan za su “tsaya har abada.” (Ishaya 40:8) Hakika, abin da Jehobah ya zaɓa ya haɗa a cikin littattafai guda 66 na Littafi Mai Tsarki su ne kawai abubuwan da muke bukata don mu zama “kamili, shiryayye sarai domin kowane managarcin aiki.”—2 Tim. 3:16, 17.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba