Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 12/15 pp. 13-17
  • Me Ya Sa Ruhun Allah Zai Yi Mana Ja-gora?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Me Ya Sa Ruhun Allah Zai Yi Mana Ja-gora?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ma’anar Ruhu Mai Tsarki
  • Ba Za Mu Iya Yi Wa Kanmu Ja-Gora Ba
  • Ruhun Allah Ya Yi wa Yesu Ja-gora
  • Ruhun Duniya Zai Sa Mu Bijire
  • Ruhu Mai Tsarki Yana Haifar da ’Yar Ruhu Mai Kyau
  • Kana Ƙyale Ruhun Allah Ya Yi Maka Ja-Gora Kuwa?
  • Ka Yi Tafiya Bisa Ga Ruhu Kuma Ka Yi Rayuwar Da Ta Jitu Da Keɓe Kanka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Yadda Ruhun Allah Ya Yi Ja-gora A Ƙarni Na Farko Da Kuma A yau
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Mene ne Ruhu Mai Tsarki?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 12/15 pp. 13-17

Me Ya Sa Ruhun Allah Zai Yi Mana Ja-gora?

“Kai ne Allahna: ruhunka mai-nagarta ne; ka bishe ni.”—ZAB. 143:10.

1. Mene ne ke sa maganaɗisu ya ja ƙarfe?

KA TAƁA ajiye allura kusa da maganaɗisu kuwa? Nan da nan maganaɗisu zai ja allurar. Me ya sa hakan yake faruwa? Domin maganaɗisu yana da ƙarfi da ba a gani da ke sa ya ja ƙarafa. A ƙarnuka da yawa, mutane da yawa sun yi amfani da maganaɗisu don su nema ƙarafa.

2, 3. (a) Wane iko mai ƙarfi ne Jehobah ya yi amfani da shi shekaru aru-aru da suka shige? (b) Ta yaya muka sani cewa ruhun Allah zai iya yi mana ja-gora a yau?

2 Da akwai wani iko kuma da ba a gani da ya fi muhimmanci don ja-gorarmu. Mene ne wannan ikon? Iko ne da muka karanta game da shi a ayoyi biyu na farko na Littafi Mai Tsarki. Da yake magana game da abin da Jehobah ya cim ma shekaru aru-aru da suka shige, littafin Farawa ya ce: “A cikin farko Allah ya halitta sama da ƙasa.” Yayin da ya yi hakan, ya aika da iko mai ƙarfi, gama labarin halitta ya daɗa: “Ruhun Allah kuwa yana tafiya a bisa ruwaye.” (Far. 1:1, 2) Wane iko ne Allah yake amfani da shi? Ruhunsa ne mai tsarki, wanda ya yi amfani da shi wajen halitta. Muna godiya cewa Jehobah ya yi amfani da ruhu mai tsarki don ya ba mu rai kuma ya halicci sauran abubuwa.—Ayu. 33:4; Zab. 104:30.

3 Mun san cewa Jehobah ya yi amfani da ikonsa don ya halicce mu, amma shin wannan ikon zai iya shafan rayuwarmu a wata hanya? Ɗan Allah ya san cewa ya kamata ya yi hakan, gama Yesu ya gaya wa almajiransa: “Ruhu na gaskiya . . . zai bishe ku cikin dukan gaskiya.” (Yoh. 16:13) Mene ne wannan ruhun, kuma me ya sa za mu so ya yi mana ja-gora?

Ma’anar Ruhu Mai Tsarki

4, 5. (a) Waɗanda suka gaskata da Allah Uku-Cikin-Ɗaya suna da wane ra’ayi game da ruhu mai tsarki? (b) Ta yaya za ka bayyana ruhu mai tsarki?

4 Wasu mutane da muke tattaunawa da su sa’ad da muke wa’azi suna iya gaskata da abin da juyin Littafi Mai Tsarki na King James Version da kuma wasu fassara suke kiran Fatalwa Mai Tsarki. Waɗanda suka yi imani da Allah Uku-Cikin-Ɗaya suna da ra’ayin da ba daidai ba, suna tunani cewa ruhu mai tsarki mutumi ne da ya yi daidai da Allah Uba. (1 Kor. 8:6) A shekara ta 1833, Noah Webster ya wallafa The Webster Bible, inda ya yi magana a kan King James Version. Abin sha’awa ne mu lura cewa ya yi amfani da kalmomin nan “Ruhu Mai Tsarki” maimakon “Fatalwa Mai Tsarki.” Webster ya yi hakan domin ya sani cewa a cikin Nassosi waɗannan kalmomin ba sa nufin “fatalwa.”a

5 To, mene ne ruhu mai tsarki? Wata hasiya da ke Farawa 1:2 a cikin New World Translation of the Holy Scriptures—With References ta ce kalmar nan ruʹach a Helenanci da aka fassara “ruhu” a Farawa 1:2, an fassara ta “iska” ko kuma kalmomi da suke da ma’ana ɗaya a cikin wasu ayoyi. (Gwada hasiyar da ke Farawa 3:8; 8:1.) Ko da yake ba ma ganin iska, muna iya ganin abin da take yi. Hakan nan ma, ba a ganin ruhu mai tsarki, amma ana ganin aikinsa. Ruhu mai tsarki ba mutum ba ne, amma iko ne da Allah yake aiki da shi. Yana amfani da shi a kan mutane ko abubuwa don ya tabbata cewa duk abin da yake so ya faru. Shin yana da wuya ne a gaskata cewa Allah maɗaukaki yana da irin wannan iko mai girma? Ko kaɗan!—Karanta Romawa 1:20.

6. Wane roƙo mai muhimmanci ne Dauda ya yi ga Jehobah?

6 Shin Jehobah zai iya ci gaba da yin amfani da ruhunsa don ya yi mana ja-gora a rayuwa? Ya yi wa Dauda marubucin wannan zabura alkawari: “Ni sanarda kai, ni koya maka cikin tafarkin da za ka bi.” (Zab. 32:8) Shin Dauda yana son hakan? E, don ya roƙi Jehobah: “Ka koya mini in aika nufinka; gama kai ne Allahna: ruhunka mai-nagarta ne; ka bishe ni.” (Zab. 143:10) Ya kamata mu kasance da irin wannan muradi da yardan rai don ruhun Allah ya yi mana ja-gora. Me ya sa? Ka yi la’akari da dalilai huɗu.

Ba Za Mu Iya Yi Wa Kanmu Ja-Gora Ba

7, 8. (a) Me ya sa ba za mu iya yi wa kanmu ja-gora ba? (b) Wane misali ne ya taimaka mana mu fahimci dalilin da ya sa muke bukatar ja-gorar Allah a wannan muguwar duniya?

7 Na farko, ya kamata mu so ruhun Allah ya yi mana ja-gora domin ba za mu iya yi wa kanmu ja-gora ba. A yi wa mutum “ja-gora” yana nufin “nuna masa hanya da ta dace ya bi.” Amma, Jehobah bai halicce mu mu yi wa kanmu hakan ba, musamman yanzu da mu ajizai ne. Annabinsa Irmiya ya rubuta: “Ya Ubangiji, na tabbata hanyar mutum ba cikin nasa hannu ta ke ba; mutum kuwa ba shi da iko shi shirya tafiyarsa.” (Irm. 10:23) Me ya sa hakan? Allah ya gaya mana dalilin ta bakin Irmiya sa’ad da ya ce: “Zuciya ta fi komi rikici, cuta gareta ƙwarai irin ta fidda zuciya: wa za ya san ta?”—Irm. 17:9; Mat. 15:19.

8 A ce mutum zai yi tafiya ta hanya mai haɗari da bai sani ba sosai, kamar ta kurmi ko kuma hamada. Ba zai dace ya tafi shi kaɗai ba, ba tare da mai ja-gora ba ko kuma taswira. Idan mutumin bai san yadda zai tsira a irin wannan wurin ba kuma bai san yadda zai fita ba, ransa zai kasance cikin haɗari. Hakan nan ma, mutumin da yake gani zai iya yi wa kansa ja-gora a wannan muguwar duniya ba tare da barin Allah ya nuna masa hanyar da ta dace ba yana cikin haɗari sosai. Kamar Dauda, ya kamata mu yi addu’a don taimakon Jehobah. Ya ce: “Ya Ubangiji, ka nuna mini tafarkunka; ka koya mani hanyoyinka.” (Zab. 25:4; 23:3) Ta yaya za mu samu irin wannan ja-gorar?

9. Kamar yadda aka nuna a shafi na 17, ta yaya ruhun Allah zai yi mana ja-gora da kyau?

9 Idan muna da tawali’u kuma muna a shirye mu dogara ga Jehobah, zai ba mu ruhunsa mai tsarki don ya yi mana ja-gora. Ta yaya wannan ikon zai taimaka mana? Yesu ya bayyana wa almajiransa: “Mai-taimako, wato Ruhu Mai-tsarki, wanda Uban zai aiko a cikin sunana, zai koya muku abubuwa duka, ya tuna muku kuma dukan abin da na faɗa muku.” (Yoh. 14:26) Idan muka yi addu’a sa’ad da muke nazarin Kalmar Allah, har da koyarwar Kristi, ruhu mai tsarki zai taimaka mana mu fahimci hikima mai zurfi ta Jehobah, don mu yi masa biyayya. (1 Kor. 2:10) Sa’ad da abubuwan da ba mu tsammani ba suka faru a rayuwarmu, ruhun Allah zai taimaka mana mu san abin da za mu yi. Ruhunsa zai taimake mu mu tuna ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da muka koya kuma ya taimaka mana mu fahimci yadda za mu iya amfani da su wajen tsai da shawarwari masu kyau.

Ruhun Allah Ya Yi wa Yesu Ja-gora

10, 11. Mene ne Ɗa makaɗaici na Allah ya yi tsammani cewa ruhu mai tsarki zai yi masa, kuma ta yaya ruhu mai tsarki ya taimake shi?

10 Dalili na biyu da ya sa za mu so ruhu mai tsarki ya yi mana ja-gora shi ne cewa Allah ya yi wa Ɗansa ja-gora da shi. Kafin ya zo duniya, Ɗan Allah makaɗaici ya san game da wannan annabcin: “Ruhun Ubangiji za ya zauna bisansa, ruhun ilimi da na ganewa, ruhun shawara da iko, ruhun sani da na tsoron Ubangiji.” (Isha. 11:2) Ka yi tunanin yadda Yesu ya yi ɗokin samun taimakon ruhun Allah yayin da yake cikin yanayin da ya fuskanta a nan duniya!

11 Maganar Jehobah ta cika. Linjila ta faɗa abin da ya faru nan da nan bayan Yesu ya yi baftisma: “Yesu kuwa, cike da Ruhu Mai-tsarki, ya komo daga Urdun, Ruhu kuwa ya bishe shi cikin jeji.” (Luk 4:1) A wajen, yayin da Yesu yake azumi da addu’a da kuma yin bimbini, mai yiwuwa Jehobah ya ba Ɗan umurni da kuma shirya shi ga abin da zai faru. Ruhun Allah yana aiki a tunanin Yesu da kuma zuciyarsa, yana masa ja-gora a tunaninsa da kuma yadda yake tsai da shawarwari. A sakamako, Yesu ya san dukan abin da Ubansa yake son ya yi kuma ya yi hakan.

12. Me ya sa muke bukatar mu yi roƙo don ruhun Allah ya yi mana ja-gora?

12 Yesu ya san yadda ruhun Allah yake da muhimmanci a rayuwarsa, saboda haka ya ƙarfafa almajiransa su roƙa a ba su ruhun kuma su ƙyale shi ya yi musu ja-gora a rayuwarsu. (Karanta Luka 11:9-13.) Me ya sa muke bukatar mu roƙi ruhun Allah ya yi mana ja-gora? Domin yana iya canja tunaninmu kuma ya taimaka mana mu kasance da nufin Kristi. (Rom. 12:2; 1 Kor. 2:16) Hakan yana nufin cewa idan mun bar ruhun Allah ya yi mana ja-gora a rayuwa, za mu yi tunani yadda Kristi yake yi kuma mu yi koyi da misalinsa.—1 Bit. 2:21.

Ruhun Duniya Zai Sa Mu Bijire

13. Mene ne ruhun duniya, kuma me yake sa mutane su yi?

13 Dalili na uku da zai sa mu so ruhun Allah ya yi mana ja-gora shi ne cewa idan ba haka ba ruhu marar tsarki da ke ja-gorar rayuwar yawancin mutane a yau yana iya sa mu bijire. Ruhun duniya ne ke ja-gorar yawancin mutane a yau. Wannan iko ne mai ƙarfi da ke sa mutane kada su yi abin da ruhu mai tsarki ya ja-gorance su su yi. Maimakon taimaka wa mutane su kasance da nufin Kristi, ruhun duniya yana sa mutane su yi tunani kuma su aikata kamar sarkin duniya, wato, Shaiɗan. (Karanta Afisawa 2:1-3; Titus 3:3.) Idan mutum ya ƙyale ruhun duniya ya yi masa ja-gora kuma ya soma yin ayyukan jiki, hakan zai kawo mugun sakamako, kuma ya hana shi gādan Mulkin Allah.—Gal. 5:19-21.

14, 15. Ta yaya za mu iya tsayayya wa ruhun duniya?

14 Jehobah ya shirya mu don mu tsayayya wa ruhun duniya. Manzo Bulus ya ce “ku ƙarfafa cikin Ubangiji, cikin ƙarfin ikonsa kuma . . . da za ku iya tsayayya cikin mugunyar rana.” (Afis. 6:10, 13) Ta hanyar ruhunsa, Jehobah yana ƙarfafa mu mu yi tsayayya da ƙoƙarce-ƙoƙarcen Shaiɗan don ya yaudare mu. (R. Yoh. 12:9) Ruhun duniya yana da ƙarfi, kuma ba za mu iya guje masa gabaki ɗaya ba. Amma muna iya tsayayya masa. Ruhu mai tsarki ya fi ƙarfi, kuma zai taimaka mana!

15 Manzo Bitrus ya yi magana game da waɗanda suka bar Kiristanci a ƙarni na farko sa’ad da ya ce: “Masu-saken hanyar gaskiya, suka ɓace.” (2 Bit. 2:15) Muna godiya sosai cewa “ba ruhun duniya muka karɓa ba, amma ruhun da ke daga wurin Allah”! (1 Kor. 2:12) Ta wajen barin ruhu mai tsarki ya yi mana ja-gora da kuma yin amfani da dukan abin da Jehobah ya ba mu don dangantakarmu da shi ta yi ƙarfi, za mu iya yin abin da ya dace kuma mu tsayayya wa ruhun wannan muguwar duniya.—Gal. 5:16.

Ruhu Mai Tsarki Yana Haifar da ’Yar Ruhu Mai Kyau

16. Wace ’yar ruhu ce ruhu mai tsarki zai sa mu nuna?

16 Dalili na huɗu da zai sa mu so ruhun Allah ya yi mana ja-gora shi ne cewa yana haifar da lafiyayyar ’yar ruhu a rayuwar waɗanda suke bari ya yi musu ja-gora. (Karanta Galatiyawa 5:22, 23.) Babu shakka, dukanmu za mu so mu ƙara nuna ƙauna kuma mu yi farin ciki da kuma kasance masu salama. Dukanmu za mu so mu ƙara nuna kamewa da alheri da kuma nagarta. Zai fi kyau dukanmu mu kasance da bangaskiya sosai kuma mu ƙara nuna tawali’u da kamewa. Waɗannan halaye masu kyau suna amfanar mu da waɗanda suke cikin iyalinmu da kuma ikilisiya. Dole ne mu ci gaba da ƙoƙari sosai don mu nuna wannan ’yar ruhun, tun da yake babu iyaka ga yadda muke bukatar mu nuna wannan ruhun.

17. Ta yaya za mu yi aiki tuƙuru don mu nuna ’yar ruhu?

17 Zai yi kyau mu yi tunani game da wannan: Shin kalaminmu da ayyukanmu suna nuna cewa ruhu mai tsarki yana yi mana ja-gora kuma muna nuna ruhunsa? (2 Kor. 13:5a; Gal. 5:25) Idan mun ga cewa muna bukatar taimako don mu nuna wasu halaye da ke cikin ’yar ruhu kuma fa? Muna iya yin ƙoƙari sosai don ruhu mai tsarki ya yi mana ja-gora don mu nuna waɗannan halaye. Muna yin hakan ta wajen yin nazari game da kowane cikin waɗannan halaye, ta yin amfani da Littafi Mai Tsarki da kuma littattafanmu na Kirista. Ya kamata mu yi tunani game da yadda za mu iya nuna ’yar ruhu a rayuwarmu na kullum kuma mu yi ƙoƙari sosai mu nuna shi. Muna sanin yadda muke bukatar taimakon ruhu mai tsarki sa’ad da muke ganin sakamako mai kyau na ja-gorarsa a rayuwarmu da kuma na ’yan’uwanmu.

Kana Ƙyale Ruhun Allah Ya Yi Maka Ja-Gora Kuwa?

18. Mene ne za mu iya koya daga misalin Yesu na barin ruhun Allah ya yi mana ja-gora?

18 A matsayinsa na “gwanin mai-aiki” na Allah wajen halittar sararin samaniya, Yesu ya san kome game da maganaɗiso na duniya, da ke taimakon mutane su zagaya duniya. (Mis. 8:30; Yoh. 1:3) Littafi Mai Tsarki bai faɗa ba cewa wannan ikon ya yi wa Yesu ja-gora sa’ad da yake duniya ba. Amma Littafi Mai Tsarki ya faɗa cewa ruhu mai tsarki iko ne mai ƙarfi a rayuwar Yesu sa’ad da yake duniya. Yesu yana son ruhun ya yi masa ja-gora kuma sa’ad da ya gaya masa ya yi wani abu yana amincewa da kuma yin hakan. (Mar. 1:12, 13; Luk 4:14) Kana hakan ne?

19. Mene ne ya wajaba mu yi don ruhu mai tsarki ya yi mana ja-gora a rayuwarmu?

19 A yau, ikon aiki na Allah har ila yana ja-gorar waɗanda suke a shirye su bi ja-gorar. Ta yaya za ka ƙyale shi ya yi maka ja-gora a hanyar da ta dace? Ka riƙa addu’a a kai a kai ga Jehobah don ya aika maka da ruhunsa kuma ya taimaka maka ka bi ja-gorarsa. (Karanta Afisawa 3:14-16.) Ka nuna ta wurin nazarin Littafi Mai Tsarki, wanda Allah ya hure ta wurin ruhunsa cewa kana son ruhun Allah ya yi maka ja-gora. (2 Tim. 3:16, 17) Ka yi biyayya ga umurni mai kyau da ke cikinsa kuma ka amince da ja-gorar ruhu mai tsarki. Ta wajen yin waɗannan abubuwa, kana nuna cewa kana da bangaskiya a iyawar Jehobah na yi maka ja-gora a hanya mafi kyau a wannan muguwar duniya.

[Hasiya]

a A gabatarwar Littafi Mai Tsarkin, Webster ya rubuta: “Ba zai yi daidai ba a yi amfani da kalma idan mutane sun fahimce ta dabam yanzu da lokacin da aka yi amfani da ita da farko a cikin King James Version ko kuma yana nufin wani abu dabam daga abin da aka faɗa a cikin harsuna na asali na Littafi Mai Tsarki.”

Ka Tuna da Muhimman Darussan?

• Ta yaya ruhu mai tsarki zai iya shafan rayuwarmu?

• Don waɗanne dalilai huɗu ne za mu so ruhun Allah ya yi mana ja-gora?

• Ta yaya za mu iya yin iya ƙoƙarinmu don mu amfana daga ja-gorar da ruhu mai tsarki yake ba da?

[Hoto a shafi na 15]

Ruhun Allah ya ja-goranci Yesu a rayuwarsa

[Hoto a shafi na 17]

Ruhun Allah yana ja-gora da kuma motsa zukatan mutane

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba