Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 8/15 pp. 23-27
  • Wane Irin Mutum Ne Ya Kamata Ka Zama

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Wane Irin Mutum Ne Ya Kamata Ka Zama
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • YAYA SHAIƊAN YAKE YAUDARAR MUTANE A YAU?
  • SHA’AWAR “JIKI”
  • “SHA’AWAR IDANU”
  • “DARAJAR RAI TA WOFI”
  • YADDA ZA KA KĀRE DANGANTAKARKA DA JEHOBAH
  • Wane Ne Ya Fi Muhimmanci A Rayuwarka?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ka Yi Hattara, Shaidan Yana So Ka Bijire!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Wane ne Makiyinka?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
  • Muna Bukatar Mu Tsayayya Wa Jarraba
    Ka Koya Daga Wurin Babban Malami
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 8/15 pp. 23-27

Wane Irin Mutum Ne Ya Kamata Ka Zama?

“Waɗanne irin mutane ya kamata ku zama cikin tasarrufi mai-tsarki da ibada kuma?”—2 BIT. 3:11.

MECE CE AMSARKA?

  • Mene ne muke bukatar mu yi don Jehobah ya amince da mu?

  • Ta yaya Shaiɗan yake rinjayar mutane a yau?

  • Mene ne za ka iya yi don ka kāre dangantakarka da Jehobah?

1, 2. Mene ne muke bukatar mu yi idan muna son Jehobah ya amince da mu?

YAWANCIN mutane suna son su san ra’ayin wasu game da su. Amma, a matsayin Kiristoci ya kamata mu fi damuwa game da yadda Jehobah yake ɗaukanmu. Ballantana ma, shi ne “maɓulɓular rai” da kuma Maɗaukaki a dukan sararin samaniya.—Zab. 36:9.

2 Manzo Bitrus ya bayyana cewa idan muna son mu sami amincewar Jehobah, muna bukatar mu kasance da “tasarrufi mai-tsarki da ibada.” (Karanta 2 Bitrus 3:11.) Hakan ya ƙunshi tunaninmu da ayyukanmu da kuma bautarmu ga Allah. Ƙari ga haka, ya kamata ƙauna da kuma tsoron Allah su motsa mu mu yi ayyukan “ibada.” Saboda haka, Jehobah ya damu da ayyukanmu da kuma yadda muke ji game da shi. Tun da yake Jehobah ne mai “auna zukata,” ya san ko muna da halaye masu kyau ko kuma muna bauta masa shi kaɗai.—1 Laba. 29:17.

3. Waɗanne tambayoyi ne ya kamata mu yi wa kanmu?

3 Shaiɗan ba ya so mu sami amincewar Jehobah. Yana ƙoƙari ya ɓata dangantakarmu da shi. Shaiɗan yana yin amfani da ƙarya da kuma yaudara don ya sa mu daina bauta wa Allah. (Yoh. 8:44; 2 Kor. 11:13-15) Saboda haka, ya kamata mu tambayi kanmu: ‘Yaya Shaiɗan yake yaudarar mutane? Me zan iya yi don na kāre dangantakata da Jehobah?’

YAYA SHAIƊAN YAKE YAUDARAR MUTANE A YAU?

4. Mene ne Shaiɗan yake ƙoƙari ya yi don ya ɓata dangantakarmu da Allah, kuma me ya sa?

4 Almajiri Yaƙub ya ce: “Kowane mutum yakan jarabtu, sa’anda sha’awatasa ta janye shi, ta yi masa tarko. Sa’an nan, lokacin da sha’awa ta habala, takan haifi zunubi: Zunubi kuwa, sa’anda ya ƙasaita, yakan fid da mutuwa.” (Yaƙ. 1:14, 15) Don Shaiɗan ya ɓata dangantakarmu da Allah, yana ƙoƙarin gurɓata zuciyarmu. Me ya sa? Domin daga cikin zuciya ne sha’awoyinmu suke fitowa.

5, 6. (a) Ta yaya Shaiɗan yake ƙoƙari ya gurɓata zuciyarmu? (b) Waɗanne abubuwa ne Shaiɗan yake amfani da su don ya sa mu yi sha’awa marar kyau kuma me ya sa ya ƙware wajen yin hakan?

5 Ta yaya Shaiɗan yake ƙoƙarin gurɓata zuciyarmu? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Duniya duka kuwa tana kwance cikin Shaiɗan.” (1 Yoh. 5:19) Shaiɗan yana yin amfani da “abubuwan da ke cikin duniya” da dabara. (Karanta 1 Yohanna 2:15, 16.) Ya yi shekaru dubbai yana shirya duniyar nan don ta zama tarko ga mutane. Da yake muna rayuwa a cikin wannan duniyar, muna bukatar mu kāre kanmu daga dabarunsa.—Yoh. 17:15.

6 Shaiɗan yana yin amfani da abubuwa dabam-dabam don ya sa mu yi sha’awa marar kyau. Manzo Yohanna ya ambata abubuwa uku da Shaiɗan yake rinjayarmu da shi, wato na ɗaya, sha’awar “jiki” da na biyu, “sha’awar idanu” da kuma na uku “darajar rai ta wofi.” Shaiɗan ya yi amfani da su wajen gwada Yesu a cikin jeji kuma ya ƙware wajen yin amfani da waɗannan dabarun domin ya yi shekaru da yawa yana yin amfani da su, kuma ya san wanda ya fi dacewa da kowane mutum. Kafin mu tattauna yadda za mu iya kāre kanmu, ya kamata mu ga abin da ya sa Shaiɗan ya yaudari Hawwa’u amma bai yi nasara da Ɗan Allah ba.

SHA’AWAR “JIKI”

7. Ta yaya Shaiɗan ya rinjayi Hawwa’u da sha’awar jiki?

7 Dukan mutane suna bukatar abinci don su ci gaba da rayuwa. Mahalicci ya shirya duniya yadda za ta ba da abinci a yalwace. Shaiɗan zai iya yin amfani da sha’awar abinci don ya sa mu ɓata wa Jehobah rai. Ka yi la’akari da yadda ya yi da Hawwa’u. (Karanta Farawa 3:1-6.) Shaiɗan ya gaya mata cewa idan ta ci ’ya’yan “itacen sanin nagarta da mugunta,” ba za ta mutu ba amma za ta zama kamar Allah. (Far. 2:9) Ta hakan, yana nuna mata cewa ba ta bukatar ta yi biyayya ga Allah kafin ta rayu har abada. Hakan ƙarya ce! Bayan da ya saka wannan ra’ayin a zuciyar Hawwa’u, tana da zaɓi biyu. Ko ta kawar da wannan ra’ayin daga zuciyarta ko kuma ta ci gaba da yin tunani a kai har ta so ’ya’yan itacen sosai. Akwai itatuwa da yawa a cikin lambun da za ta iya ci, amma ta zaɓa ta ci gaba da yin tunani a kan abin da Shaiɗan ya ce game da itacen da ke tsakiyar gonar. A sakamako, ta tsinka ’ya’yansa kuma ta ci. Shaiɗan ya sa ta soma sha’awar abin da Allah ya haramta.

8. Ta yaya Shaiɗan ya yi niyyar ya yaudari Yesu da sha’awar jiki kuma me ya sa bai yi nasara ba?

8 Shaiɗan ya sake yin amfani da wannan dabarar don ya yaudari Yesu. Bayan da Yesu ya yi azumi na kwana arba’in dare da rana a cikin jeji, sai Shaiɗan ya yi ƙoƙari ya yaudare shi da abinci. Ya ce: “Idan kai Ɗan Allah ne, ka umurci dutsen nan shi zama gurasa.” (Luk 4:1-3) Yesu yana da zaɓi biyu. Zai iya yin amfani da ikonsa wajen cika muradinsa na abinci ko kuma ya ƙi yin hakan. Yesu ya san cewa bai kamata ya nuna son kai wajen yin amfani da ikonsa ba. Ko da yake yana jin yunwa amma dangantakarsa da Jehobah ta fi abinci muhimmanci a gare shi. Sai ya amsa Shaiɗan cewa: “An rubuta, ba da abinci kaɗai mutum za ya rayu ba amma da kowane maganar Allah da ke fitowa daga bakinsa.”—Luk 4:4.

“SHA’AWAR IDANU”

9. Mece ce “sha’awar idanu” kuma yaya Shaiɗan ya yi amfani da shi wajen ruɗin Hawwa’u?

9 Manzo Yohanna ya kuma ambata cewa Shaiɗan yana yin amfani da “sha’awar idanu.” Wannan furucin ya nuna cewa mutum zai iya soma yin sha’awar wani abu da zarar ya kalli abin. Shaiɗan ya yaudari Hawwa’u da wannan dabarar, sa’ad da ya ce mata: “Idanunku za su buɗe.” Yayin da take kallon ’ya’yan itacen, sai tana daɗa sha’awar sa. Ta lura cewa itacen “abin sha’awa ne kuma ga idanu.”

10. Ta yaya Shaiɗan ya jarabci Yesu da “sha’awar idanu” kuma mene ne Yesu ya gaya masa?

10 Yaya Shaiɗan ya yi amfani da wannan dabarar ga Yesu? Shaiɗan ya nuna masa “dukan mulkokin duniya” kuma ya ce masa: “A gareka zan bada wannan sarauta duka, da ɗaukakarsu; gama ni aka ba; dukan wanda na nufa kuma, sai in ba shi.” (Luk 4:5, 6) Yesu bai ga dukan mulkokin duniya da idanunsa ba, amma ya ga wahayin ɗaukakarsu kuma Shaiɗan ya ɗauka cewa hakan zai ja hankalin Yesu. Sai ya ce wa Yesu: “Idan fa kai ka yi sujada a gabana, duka za ya zama naka.” (Luk 4:7) Yesu ba ya so ya zama irin mutumin da Shaiɗan yake so ya zama. Sai ya amsa nan da nan, ya ce: “A rubuce yake cewa, ‘Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada, Shi kaɗai za ka bauta wa.’”—Luk 4:8.

“DARAJAR RAI TA WOFI”

11. Ta yaya Shaiɗan ya rinjayi Hawwa’u?

11 A ƙarshe, manzo Yohanna ya ambata “darajar rai ta wofi.” Wannan furucin yana nufin yin fahariya don abin da mutum yake da shi. Adamu da Hawwa’u ba su iya yin fahariya da abin da suke da shi ba, domin su kaɗai ne a duniya a lokacin. Duk da haka, suna da fahariya. Shaiɗan ya sa Hawwa’u ta amince cewa akwai wani abu mai ban sha’awa da Allah yake hana ta. Ya gaya mata cewa da zarar ta ci daga “itace na sanin nagarta da mugunta,” za ta “zama kamar Allah, [ta] san nagarta da mugunta.” (Far. 2:17; 3:5) Shaiɗan ya so ya sa Hawwa’u ta yi tunani cewa za ta iya yin rayuwa ba tare da ja-gorar Jehobah ba. Wataƙila fahariya tana cikin abubuwan da suka sa ta yi na’am da ƙaryar Shaiɗan. Ta ci ’ya’yan itacen da aka haramta kuma tana ganin ba za ta mutu ba. Hakan babban kuskure ne.

12. A wace hanya ce Shaiɗan ya yi ƙoƙarin gwada Yesu, amma mene ne Yesu ya yi?

12 Yesu bai yi kamar Hawwa’u ba, amma ya kafa mana misali mai kyau na tawali’u. Shaiɗan ya gwada shi ya yi amfani da ikonsa wajen burge mutane da kuma gwada Allah. Amma, Yesu ya ƙi domin yin haka zai nuna cewa yana da fahariya. Yesu ya amsa masa kai tsaye cewa: “An rigaya an faɗi, ba za ka jarabci Ubangiji Allahnka ba.”—Karanta Luka 4:9-12.

YADDA ZA KA KĀRE DANGANTAKARKA DA JEHOBAH

13, 14. Ta yaya Shaiɗan yake ƙoƙari ya rinjaye mu a yau?

13 A yau, Shaiɗan yana yin amfani da irin dabarun da ya yi amfani da su wajen gwada Hawwa’u da kuma Yesu. Yana yin amfani da sha’awar “jiki” wajen sa mutane su yi lalata da kuma zarin ci da sha. Yana kuma yin amfani da “sha’awar idanu” wajen sa mutane su kalli hotunan batsa musamman ma a Intane. Har ila, yana gwada mutane su biɗi “darajar rai ta wofi” ta wajen yin suna da fahariya da kuma neman tara dukiya.

14 Kamar yadda mai kamun kifi yake yin amfani da tana wajen kama kifi, Shaiɗan ma yana yin amfani da “abubuwan da ke cikin duniya.” Sa’ad da kifi ya ga tana, ba zai san cewa tarko ba ne. Hakazalika, Shaiɗan yana yin amfani da abubuwan da muke ganin sun dace wajen sa mu taka dokokin Allah. Yana so mu ji cewa kula da kanmu da kuma yin rayuwa mai gamsarwa sun fi yin nufin Allah muhimmanci. Shin za ka ƙyale Shaiɗan ya ruɗe ka?

15. Ta yaya za mu yi koyi da Yesu wajen yin tsayayya da gwajin Shaiɗan?

15 Shaiɗan ya rinjayi Hawwa’u, amma Yesu ya tsayayya masa. Duk sa’ad da Shaiɗan ya jarabce shi, sai ya yi kaulin Nassi, ya ce: “An rubuta” ko kuma “An riga an faɗi.” Idan muna yin nazarin Littafi Mai Tsarki sosai, za mu fahimci nassosi da kyau kuma za mu iya tuna da nassin da zai taimaka mana sa’ad da aka jarabce mu. (Zab. 1:1, 2) Idan muka tuna da misalan bayin Allah da suka kasance da aminci, mu ma za mu so mu yi koyi da su ta wajen riƙe amincinmu. (Rom. 15:4) Tsoron Jehobah da ƙaunar abin da yake ƙauna da kuma ƙin abin da ya tsana, za su kāre mu.—Zab. 97:10.

16, 17. Ta yaya tunaninmu zai iya shafan halinmu?

16 Manzo Bulus ya ƙarfafa mu mu yi amfani da azancinmu don mu kasance da ra’ayin Jehobah, ba na mutane ba. (Rom. 12:1, 2) Ya kuma tuna mana cewa wajibi ne mu mai da hankali da irin tunanin da muke yi. Ya ce: “Muna rushe zace-zace da kowane maɗaukakin abu wanda aka ɗaukaka domin gāba da sanin Allah, muna komo da kowane tunani cikin bauta ga biyayyar Kristi.” (2 Kor. 10:5) Tunaninmu yana shafan halinmu, shi ya sa ya kamata mu riƙa yin tunani a kan abubuwan da ke faranta wa Allah rai.—Filib. 4:8.

17 Idan muna so mu kasance da tsarki, wajibi ne mu guji yin tunani da kuma sha’awar abubuwan da ba su dace ba. Ya wajaba mu ƙaunaci Jehobah da “zuciya mai-tsabta.” (1 Tim. 1:5) Amma da yake zuciya tana da rikici, zai yiwu “abubuwan da ke cikin duniya” su shafe mu ba tare da mun ankara ba. (Irm. 17:9) Saboda haka, ya kamata mu bi shawarar da Manzo Bulus ya ba da. Ya ce: “Ku gwada kanku ko kuna cikin imani; ku yi wa kanku ƙwanƙwanto.” Sa’ad da muke karanta Littafi Mai Tsarki, mu tambayi kanmu, ‘Shin tunanina da sha’awata suna faranta wa Allah rai kuwa?’—2 Kor. 13:5.

18, 19. Me ya sa ya kamata mu ƙoƙarta don mu zama irin mutanen da Jehobah yake so mu zama?

18 Wani abin da zai taimaka mana mu yi tsayayya da “abubuwan da ke cikin duniya” shi ne kalamin da manzo Yohanna ya furta cewa: “Duniya ma tana wucewa, duk da sha’awatata: amma wanda ya aika nufin Allah ya zauna har abada.” (1 Yoh. 2:17) Duniyar nan tana kamar ba abin da zai faru da ita. Amma, wata rana za ta shuɗe. Dukan abubuwan da ke cikin duniyar Shaiɗan za su shuɗe. Tunawa da wannan gaskiyar za ta taimaka mana don kada Iblis ya ruɗe mu.

19 Manzo Bitrus ya aririce mu mu zama irin mutanen da Allah yake so yayin da muke “sauraron ranar Allah, [muna] kuwa marmarin zuwanta ƙwarai; bisa ga zuwanta kuwa sammai da suke cin wuta za su narke, rundunan kuma za su narke da ƙuna mai-zafi.” (2 Bit. 3:12) Ba da daɗewa ba, ranar nan za ta kai kuma Jehobah zai halaka kowane sashen duniyar Shaiɗan. Amma kafin lokacin, Shaiɗan zai ci gaba da gwada mu da “abubuwan da ke cikin duniya,” kamar yadda ya gwada Hawwa’u da Yesu. Kada mu yi koyi da Hawwa’u ta wajen son mu gamsar da sha’awarmu. Idan muka yi hakan, za mu mai da Shaiɗan allahnmu. Ya kamata mu bi misalin Yesu ta wajen yin tsayayya da gwajin Shaiɗan ko ma idan ya yi amfani da abubuwa masu ban sha’awa don ya janye hankalinmu.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba