Ruhu Mai Tsarki Yana Ba Da Ƙarfi A Jimre Da Gwaji Da Kuma Sanyin Gwiwa
“Za ku karɓi iko lokacin da Ruhu Mai-tsarki ya zo bisanku.”—A. M. 1:8.
1, 2. Yesu ya yi wa almajiransa alkawarin wanne taimako, kuma me ya sa za su bukace taimakon?
YESU ya san cewa almajiransa ba za su iya cim ma abubuwan da ya umurce su ba da ikon kansu. Yin la’akari da yawan yadda za su yi wa’azi, ƙarfin waɗanda za su yi wa wa’azi, da kuma kasawar ’yan Adam ya nuna cewa suna bukatar ikon Allah. Saboda haka, kafin ya hau sama, Yesu ya tabbatar da almajiransa: “Za ku karɓi iko lokacin da Ruhu Mai-tsarki ya zo bisanku; za ku zama shaiduna kuma cikin Urushalima da cikin dukan Yahudiya da Samariya, har kuma iyakan duniya.”—A. M. 1:8.
2 Wannan alkawarin ya soma cikawa a ranar Fentakos ta 33 A. Z. sa’ad da ruhu mai tsarki ya ƙarfafa mabiyan Yesu Kristi su cika Urushalima da wa’azinsu. Babu hamayya da ta iya dakatar da aikin. (A. M. 4:20) “Kullayaumi har matuƙar zamani,” mabiyan Yesu, haɗe da mu, za su bukaci ikon Allah da gaggawa.—Mat. 28:20.
3. (a) Ka bayyana bambancin da ke tsakanin ruhu mai tsarki da iko. (b) Mene ne iko daga wurin Jehobah zai iya sa mu cim ma?
3 Yesu ya yi wa almajiransa alkawari cewa ‘za su karɓi iko lokacin da Ruhu Mai-tsarki ya zo bisansu.’ Kalmomin nan “iko” da “ruhu” suna da ma’ana dabam dabam. Ruhun Allah iko ne da yake amfani da shi don ya taimaki abubuwa masu rai da marasa rai don ya cim ma nufinsa. Ikon kuma yana nufin ingancin aikatawa ko kuma yi wasu abubuwa. Zai iya kasance marar amfani sai an bukace shi. Saboda haka, za a iya kwatanta ruhu mai tsarki da wutan lantarki da ke cikin batir da ake cazawa, amma iko yana kama da wutar da ke kasancewa a cikin batirin. Ikon da Jehobah yake ba wa bayinsa ta ruhunsa mai tsarki yana ba kowannenmu ingancin cim ma keɓe kanmu da muka yi a matsayin Kiristoci, idan bukata ta kama don tsayayya wa ikoki marasa kyau da muke fuskanta.—Karanta Mikah 3:8; Kolosiyawa 1:29.
4. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin, kuma me ya sa?
4 Mene ne ke nuna cewa muna da ruhu mai tsarki? Ta yaya ruhu mai tsarki zai iya motsa mu mu aikata ga yanayoyi dabam dabam? Yayin da muke ƙoƙari mu bauta wa Allah cikin aminci, muna fuskantar matsaloli da yawa da Shaiɗan, zamaninsa, ko kuma ajizancinmu yake jawowa. Yana da muhimmanci mu magance irin waɗannan matsaloli don mu nace a matsayin Kiristoci, mu saka hannu a hidima a kai a kai, kuma mu kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah. Bari mu yi la’akari da yadda ruhu mai tsarki yake taimaka mana mu tsayayya wa gwaji kuma mu jimre wa gajiya da kuma sanyin gwiwa.
An Ƙarfafa Mu Mu Tsayayya wa Gwaji
5. Ta yaya addu’a za ta iya ƙarfafa mu?
5 Yesu ya koya wa almajiransa yin addu’a: “Kada ka kai mu cikin jaraba, amma ka cece mu daga mugun.” (Mat. 6:13) Jehobah ba zai yi watsi da amintattun bayinsa da suka yi wannan roƙon ba. A wani lokaci kuma, Yesu ya ce ‘Uba na sama za ya ba da Ruhu Mai-tsarki ga waɗanda suke roƙonsa.’ (Luk 11:13) Abin tabbaci ne cewa Jehobah yana ba mu ruhunsa mai tsarki da ke taimaka mana mu yi abin da ya dace! Amma wannan ba ya nufin cewa Jehobah zai hana mu fuskanci gwaji. (1 Kor. 10:13) Amma a lokacin da muke fuskantar gwaji ne ya kamata mu yi addu’a sosai.—Mat. 26:42.
6. Amsar da Yesu ya ba Shaiɗan sa’ad da ya jarabce shi ya dangana ga mene ne?
6 Yesu ya yi ƙaulin nassosi, sa’ad da yake mayar da martani ga gwajin Iblis. Kalmar Allah tana zuciyar Yesu sa’ad da ya amsa: “An rubuta . . . An kuma rubuta, Rabu da ni, ya Shaiɗan: gama an rubuta, Ka yi sujada ga Ubangiji Allahnka, shi kaɗai ma za ka bauta wa.” Ƙauna ga Jehobah da kuma Kalmarsa ta motsa Yesu ya ƙi abubuwan rinjaya da Mai Jarrabar ya saka a gabansa. (Mat. 4:1-10) Shaiɗan ya rabu da Yesu bayan ya tsayayya wa jarrabobinsa.
7. Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya taimaka mana mu tsayayya wa jarraba?
7 Da yake Yesu ya dogara ga Nassosi don ya tsayayya wa jarrabobin Iblis ya nuna cewa muna bukatar yin hakan sosai! Hakika, don mu yi tsayayya da Iblis muna bukatar mu san mizanan Allah kuma mu yi rayuwa da ta jitu da su. Mutane da yawa sun yi rayuwa da ta jitu da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki yayin da suke nazarin Nassosi kuma suka fahimci da kuma daraja hikimar Allah da adalcinsa. Hakika, “kalmar Allah” tana da iko don sanin “tunanin zuciya da nufe-nufenta.” (Ibran. 4:12) Yayin da muka karanta da kuma yi bimbini a kan Nassosi, za mu san ‘gaskiyar Ubangiji.’ (Dan. 9:13) Saboda haka, ya kamata mu yi bimbini a kan nassosi da suka yi magana game da matsalolinmu.
8. Ta wacce hanya ce za mu iya samun ruhu mai tsarki?
8 Yesu yana da damar yin tsayayya da jarraba domin ƙari ga sanin Nassosi, yana “cike da Ruhu Mai-tsarki.” (Luk 4:1) Domin mu samu irin wannan ƙarfi da kuma inganci, muna bukatar mu kasance kusa da Jehobah ta yin amfani da dukan tanadodin da ya yi don mu cika da ruhu mai tsarki. (Yaƙ. 4:7, 8) Waɗannan sun haɗa da nazarin Littafi Mai Tsarki, da kuma yin tarayya da ’yan’uwa masu bi. Mutane da yawa kuma sun amfana daga saka hannu sosai a ayyukan Kirista, waɗanda suke taimakawa wajen sa a mai da hankali a kan abubuwa na ruhaniya masu ginawa.
9, 10. (a) Waɗanne jarrabobi ne mutane suke yawan fuskanta a yankinku? (b) Ta yaya bimbini da addu’a za su iya taimaka mana mu yi tsayayya da jarraba har sa’ad da muka gaji?
9 Waɗanne jarrabobi ne za ka tsayayya wa? Ka taɓa fuskantar gwajin yin kwarkwasa da wanda ko wadda ba abokiyar aurenka ba ce? Idan ba ka yi aure ba tukuna, ka taɓa yin sha’awar fitan zance da wanda ko wadda ba mai bi ba ne? Sa’ad da suke kallon talabijin ko yin amfani da intane, Kiristoci za su iya fuskantar jarraba farat ɗaya na kallon abin da ba nagari ba. Hakan ya taɓa faruwa da kai, idan haka ne, yaya ka aikata? Abin hikima ce a yi bimbini a kan yadda zunubi ɗaya zai iya kai ga yin zunubi mai tsanani. (Yaƙ. 1:14, 15) Ka yi tunani a kan yadda Jehobah, ikilisiya, da iyalinka za su ji idan ka yi abu marar kyau. Ana samun lamiri mai tsabta idan an kasance da aminci ga ƙa’idodin Allah. (Karanta Zabura 119:37; Misalai 22:3.) Duk sa’ad da ka fuskanci irin wannan gwajin, ka ƙuduri anniyar yin addu’a don samun ikon yin tsayayya da su.
10 Akwai wani abu kuma da za mu tuna game da jarrabobin Iblis. Shaiɗan ya je wurin Yesu bayan ya yi azumi na kwanaki arba’in a cikin jeji. Babu shakka Iblis ya yi tunani cewa wannan “zarafin” mai kyau ne na gwada nagartar Yesu. (Luk 4:13) Shaiɗan yana neman lokatai da suka dace don gwada nagartarmu. Yana da muhimmanci mu kasance da ƙarfi a ruhaniya. Shaiɗan yakan kawo farmaki sa’ad da ya ga cewa wanda yake wa fako ya raunana. Saboda haka duk sa’ad da muka gaji ko kuma muka yi sanyin gwiwa, ya kamata mu ƙuduri anniya sosai mu roƙi Jehobah don ya taimaka mana kuma ya ba mu ruhunsa mai tsarki.—2 Kor. 12:8-10.
An Ƙarfafa Mu Mu Jimre da Gajiya da Sanyin Gwiwa
11, 12. (a) Me ya sa mutane da yawa suke sanyin gwiwa a yau? (b) Mene ne zai iya ƙarfafa mu mu jimre wa sanyin gwiwa?
11 A matsayin ’yan Adam ajizai, muna yin sanyin gwiwa a kai a kai. Hakan zai iya kasancewa da gaske a yau domin lokacin da muke zama cike yake da alhini. Muna fuskantar lokaci mafi wuya da ’yan Adam gabaki ɗaya ba su taɓa fuskanta ba. (2 Tim. 3:1-5) Yayin da Armageddon yake kusa, matsi na tattalin arziki, na motsin rai da na wasu abubuwa za su daɗa tsanani. Bai kamata mu yi mamaki cewa wasu suna ganin wuyan cika hakkinsu na kula da kuma yi wa iyalinsu tanadi ba. Suna yin sanyi gwiwa da sannu sannu. Idan kana fuskantar irin wannan yanayin, ta yaya za ka iya jimre da matsin?
12 Ka tuna cewa Yesu ya tabbatar da mabiyinsa cewa zai ba su mataimaki, ruhu mai tsarki na Allah. (Karanta Yohanna 14:16, 17.) Wannan iko mafi ƙarfi ne a dukan sararin samaniya. Jehobah zai iya ba da iko da jimiri “gaba da dukan abin da muke roƙo ko tsammani” don mu jimre da kowanne irin gwaji. (Afis. 3:20) Ta yin dogara ga ikon, in ji manzo Bulus, za mu samu “mafificin girman iko,” ko da “mun matsu ga kowane sashi.” (2 Kor. 4:7, 8) Jehobah ba ya alkawarin cire alhini, amma ya tabbatar mana cewa ta ruhunsa mai tsarki, zai ba mu ikon jimre da alhini.—Filib. 4:13.
13. (a) Ta yaya wata matashiya ta samu ƙarfi don ta jimre da mawuyacin yanayi? (b) Ka san wani da yake fuskantar irin wannan yanayin kuwa?
13 Ka yi la’akari da misalin wata majagaba na kullum ’yar shekara sha tara mai suna Stephanie. Ta yi ciwon shan inna da na ƙwaƙwalwa sa’ad da take ’yar shekara sha biyu. Tun lokacin, an yi mata aiki sau biyu, da kuma jinyar kansar ƙwaƙwalwa, kuma ta sake yin ciwon shan inna sau biyu da ya naƙasa gefen jikinta na hagu kuma ta daina gani sosai. Stephanie ta yi amfani da kuzarinta don yin abubuwa da suka fi muhimmanci, kamar su tarurrukan Kirista da hidimar fage. Duk da haka, ta ga alamar ƙarfafar Jehobah da ya taimaka mata ta jimre a hanyoyi da yawa. Littattafai da suke bayyana Littafi Mai Tsarki da suke ɗauke da labaran Kiristoci sun ƙarfafa ta sa’ad da take baƙin ciki. ’Yan’uwa maza da mata sun tallafa mata ta wajen aika mata wasiƙu ko kuma faɗa mata kalaman ƙarfafawa kafin tarurruka da kuma bayan hakan. Ɗalibanta ma sun nuna godiya don abin da Stephanie take koya musu ta zuwa gidanta don ta yi nazarin Littafi Mai Tsarki da su. Stephanie tana wa Jehobah godiya sosai don dukan waɗannan abubuwan. Nassin da ta fi so shi ne Zabura 41:3, wanda ta gaskata cewa ya samu cikawa a kanta.
14. Mene ne dole mu guji sa’ad da muka yi sanyin gwiwa, kuma me ya sa?
14 Sa’ad da muka gaji ko kuma muke cikin matsi, bai kamata mu yi tunanin cewa hanyar bi da wannan alhinin shi ne rage ayyukanmu na ruhaniya ba. Abu mafi muni da za mu yi kenan. Me ya sa? Domin ta irin waɗannan ayyuka kamar su nazarin Littafi Mai Tsarki na kai da na iyali, hidimar fage, da halartar taro ne muke samun ruhu mai tsarki. Ayyukan Kirista suna kawo wartsakewa a ko da yaushe. (Karanta Matta 11:28, 29.) Sau da yawa ’yan’uwa sukan halarci taro suna cike da gajiya, amma sa’ad da lokacin tafiya gida ya yi sai su ji sun samu ƙarfi, kamar an sake caza batirinsu na ruhaniya!
15. (a) Shin Jehobah ya yi wa Kiristoci alkawari cewa zai sa rayuwa ta kasance musu da sauƙi? Ka bayyana da Nassi. (b) Mene ne Allah ya yi mana alkawarinsa, kuma ya kawo wacce tambaya?
15 Hakan ba ya nufin cewa hakki na almajiranci na Kirista ba shi da nauyi. Kasancewa da aminci a matsayin Kirista yana bukatar ƙoƙari. (Mat. 16:24-26; Luk 13:24) Duk da haka, ta ruhunsa mai tsarki, Jehobah yana iya ƙarfafa gajiyayyu. “Waɗanda ke sauraro ga Ubangiji za su sabonta ƙarfinsu,” in ji annabi Ishaya. “Da fukafukai kamar gaggafa za su tashi sama; za su yi gudu, ba za su gaji ba; za su kama tafiya, ba su yi suwu ba.” (Isha. 40:29-31) Tun da haka ne, ya kamata mu tambayi kanmu, Mene ne ainihi yake sa muke ji cewa ayyukanmu na Kirista suna sa mu gajiya?
16. Mene ne za mu iya yi don mu kawar da abubuwan da suke gajiyar da mu da kuma sa mu sanyin gwiwa?
16 Kalmar Jehobah ta aririce mu mu “gwada mafifitan al’amura.” (Filib. 1:10) Da yake gwada rayuwar Kirista da tsere mai nisa, manzo Bulus da aka hure ya ba da shawara: “Bari mu tuɓe kowane abin nauwaitawa . . . , kuma mu yi tseren da an sa gabanmu.” (Ibran. 12:1) Bayaninsa shi ne cewa wajibi ne mu guji biɗe-biɗe marar amfani, abin nauwaitawa, da za su gajiyar da mu. Zai iya zama cewa wasu cikinmu suna ƙoƙari su daɗa taƙure kansu da ayyuka. Saboda haka, idan kana yawan gajiya kuma kana alhini, za ka iya amfana don bincika kuzari da kake sakawa a aikinka, yawan lokacin da kake tafiya don shaƙatawa, da kuma yadda kake biɗin wasanni da ayyukan nishaɗi. Sanin ya kamata da filako ya kamata ya motsa mu mu san kasawarmu kuma mu rage ayyuka marar muhimmanci.
17. Me ya sa wasu za su iya yin sanyin gwiwa, amma wane tabbaci ne Jehobah ya ba mu a kan wannan batun?
17 Zai iya kuma kasance cewa wasu cikinmu suna sanyin gwiwa domin ƙarshen wannan zamanin bai zo ba tukuna yadda muke zato. (Mis. 13:12) Duk wanda yake jin hakan zai iya samun ƙarfafa daga kalaman da ke Habakkuk 2:3: “Ru’yan har yanzu da ayanannen lokacin ta, tana kuwa gaggauta zuwa matuƙan, ba kuwa za ta yi ƙarya ba; ko ta jima, ka dakata mata; gama lallai za ta zo, ba za ta yi jinkiri ba.” Jehobah ya tabbatar da mu cewa ƙarshen wannan zamanin zai zo a lokacin da ya tsara!
18. (a) Waɗanne alkawura ne suke ƙarfafa ka? (b) Ta yaya talifi na gaba zai amfane mu?
18 Hakika, dukan bayin Jehobah amintattu suna ɗokin ganin wannan ranar da gajiya da sanyin gwiwa ba za su kasance kuma ba, kuma dukan rayayyu za su more ‘ƙuruciyarsu.’ (Ayu. 33:25) Har yanzu ma za mu iya samun ƙarfafa ta ruhu mai tsarki yayin da muke saka hannu a ayyuka da suke ƙarfafa mu a ruhaniya. (2 Kor. 4:16; Afis. 3:16) Kada ka bari gajiya ya sa ka yi hasarar albarka ta har abada. Kowanne gwaji, ko da jarraba ne ya jawo shi, gajiya, ko sanyin gwiwa za su daina nan da nan, ko kuma a sabuwar duniya na Allah. A talifi na gaba, za mu bincika yadda ruhu mai tsarki yake ƙarfafa Kiristoci su jimre da tsanantawa, matsi na tsara marar kyau, da kuma matsaloli masu yawa.
Yaya Za Ka Amsa?
• Ta yaya karatun Littafi Mai Tsarki yake ƙarfafa mu?
• Ta yaya addu’a da bimbini suke ƙarfafa mu?
• Ta yaya za ka iya kawar da abubuwa da za su iya kawo sanyin gwiwa?
[Hoton da ke shafi na 24]
Tarurruka na Kirista za su iya ƙarfafa mu a ruhaniya