Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • lff darasi na 16 sakin layi na 1-6
  • Mene ne Yesu Ya Yi Sa’ad da Yake Duniya?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Mene ne Yesu Ya Yi Sa’ad da Yake Duniya?
  • Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • KA YI BINCIKE SOSAI
  • TAƘAITAWA
  • KA BINCIKA
  • Mene ne Za Mu Iya Koya Daga Muꞌujizan Yesu?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
  • Wane ne Yesu?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Waɗanne Irin Halaye Ne Yesu Yake da Su?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Ya So Mutane
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
Dubi Ƙari
Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
lff darasi na 16 sakin layi na 1-6
Darasi na 16. Yesu yana koyar da maza da mata yayin da suke zaune a kan tudu.

DARASI NA 16

Mene ne Yesu Ya Yi Sa’ad da Yake Duniya?

Hoto
Hoto
Hoto

Mutane da yawa sun san game da Yesu, amma wasu sun san abin da ya faru da shi ne kawai sa’ad da yake jariri. Wasu sun san shi a matsayin annabi ne kawai, wasu kuma sun san game da mutuwarsa ne kawai. Amma za mu koyi abubuwa da yawa game da shi ta wajen yin nazarin rayuwarsa a duniya. A wannan darasin, za mu tattauna wasu abubuwa mafi muhimmanci da Yesu ya yi da yadda za su taimaka maka.

1. Wane aiki mafi muhimmanci ne Yesu ya yi?

Aiki da ya fi muhimmanci da Yesu ya yi shi ne shelar “labari mai daɗi na mulkin Allah.” (Karanta Luka 4:43.) Ya yi wa’azi cewa Allah zai kafa mulki ko gwamnatin da za ta magance dukan matsalolin ’yan Adam.a Yesu ya yi shekara uku da rabi yana iya ƙoƙarinsa don ya yi wa’azi sosai.​—Matiyu 9:35.

2. Me ya sa Yesu ya yi mu’ujizai?

Littafi Mai Tsarki ya ambata da yawa cikin “ayyukan ban mamaki, da abubuwan ban mamaki, da alamu waɗanda [Allah] ya yi ta wurin Yesu.” (Ayyukan Manzanni 2:22) Allah ya ba Yesu ikon dakatar da guguwa da ciyar da dubban mutane da warkar da marasa lafiya da kuma ta da matattu. (Matiyu 8:​23-27; 14:​15-21; Markus 6:56; Luka 7:​11-17) Mu’ujizai da Yesu ya yi sun nuna cewa Allah ne ya aiko shi. Sun kuma nuna cewa Jehobah yana da ikon magance dukan matsalolinmu.

3. Me za mu koya daga rayuwar Yesu?

Yesu ya yi wa Jehobah biyayya a kowane yanayi. (Karanta Yohanna 8:29.) Duk da cewa an tsananta wa Yesu, ya yi dukan abubuwan da Jehobah ya ce ya yi har ƙarshen rayuwarsa a duniya. Ya nuna cewa ’yan Adam za su iya yi wa Allah biyayya ko da suna cikin yanayi mai wuya. Yesu ya bar mana ‘gurbi domin mu bi hanyarsa.’—1 Bitrus 2:21.

KA YI BINCIKE SOSAI

Za mu koyi yadda Yesu ya yi wa’azi da kuma mu’ujizai.

4. Yesu ya yi wa’azi

Yesu ya je wurare masu nisa kuma ya bi hanyoyi marasa kyau don ya yi wa mutane da yawa wa’azi. Ku karanta Luka 8:​1, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Shin Yesu ya yi wa mutanen da suka zo wurinsa ne kaɗai wa’azi?

  • Mene ne Yesu ya yi don ya yi wa mutane wa’azi?

Allah ya annabta cewa Almasihu zai yi wa’azi. Ku karanta Ishaya 61:​1, 2, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Ta yaya Yesu ya cika wannan annabcin?

  • Kana ganin mutane a yau suna bukatar su ji wa’azi?

Yesu yana shiga wani kauye tare da wasu cikin almajiransa.

5. Yesu ya koya mana darussa masu muhimmanci

Ban da yin wa’azi game da Mulkin Allah, Yesu ya koyar da darussa da za su taimaka mana. Bari mu tattauna wasu misalai daga wa’azin da ya yi a kan dutse. Ku karanta Matiyu 6:​14, 34 da 7:12, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Waɗanne shawarwari ne Yesu ya bayar a waɗannan ayoyin?

  • Kana ganin shawarwarin nan za su taimaka wa mutane a yau?

Yesu yana wa taron maza da mata da yara wa’azi a kan dutse.

6. Yesu ya yi mu’ujizai

Jehobah ya ba Yesu ikon yin mu’ujizai da yawa. Don ku ga wani misali, ku karanta Markus 5:​25-​34 ko ku kalli BIDIYON nan. Sai ku tattauna tambayoyin da ke gaba.

BIDIYO: An Warƙar da Wata Mata (5:10)

  • A bidiyon, mene ne matar da take rashin lafiya ta yi imani da shi?

  • Mene ne ya burge ka game da wannan mu’ujizar?

Ku karanta Yohanna 5:36, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Mene ne mu’ujizai da Yesu ya yi suka “shaida” game da shi?

Yesu ya durkusa yana magana da wata mata da ta tsorata bayan da ta warke daga zub da jini.

Ka sani?

Littafin Matiyu da Markus da Luka da kuma Yohanna, sun koya mana yawancin abubuwa da muka sani game da Yesu. Kowane marubuci ya ambata wani abu dabam da sauran ba su faɗa ba game da Yesu. Idan muka karanta dukan waɗannan littattafan, za mu fahimci abubuwa da yawa game da rayuwar Yesu.

  • MATIYU

    ne ya fara rubuta labari game da Yesu. Ya gaya mana abubuwa da yawa game da koyarwar Yesu, musamman abin da ya koyar game da Mulkin Allah.

  • MARKUS

    ne ya rubuta labari game da Yesu da bai kai na sauran manzannin yawa ba. Ya ba da labarai dabam-dabam masu daɗi game da Yesu.

  • LUKA

    ya rubuta game da muhimmancin yin addu’a da kuma yadda Yesu ya nuna wa mata alheri.

  • YOHANNA

    ya gaya mana abubuwa da dama game da halayen Yesu da tattaunawar da Yesu ya yi da abokansa da kuma wasu mutane.

WASU SUN CE: “Yesu shi ne Allah Maɗaukaki.”

  • Mene ne ra’ayinka?

TAƘAITAWA

Yesu ya yi wa’azi game da Mulkin Allah, ya yi mu’ujizai, kuma ya yi wa Jehobah biyayya a kowane yanayi.

Bita

  • Wane aiki mafi muhimmanci ne Yesu ya yi sa’ad da yake duniya?

  • Mene ne mu’ujizai da Yesu ya yi suka nuna?

  • Waɗanne darussa masu muhimmanci ne Yesu ya koyar?

Maƙasudi

KA BINCIKA

Ku karanta talifin nan don ku san batun da Yesu ya fi magana a kai.

“Mulkin Allah​—Me Ya Sa Yake da Muhimmanci ga Yesu?” (Hasumiyar Tsaro, 1 ga Nuwamba, 2014)

Ku karanta talifin nan don ku ga abin da ya sa muke da tabbaci cewa Yesu ya yi mu’ujizai da gaske.

“Me Za Ka Iya Koya Daga Mu’ujizai da Yesu Ya Yi?” (Hasumiyar Tsaro, 15 ga Yuli, 2004)

Ku karanta talifin nan don ku ga yadda wani mutum ya canja salon rayuwarsa sa’ad da ya koyi cewa Yesu ya damu da mutane sosai.

“Na Damu da Kaina Ne Kawai a Dā” (Hasumiyar Tsaro, 1 ga Nuwamba, 2014)

Ku karanta talifin nan don ku ga abubuwa masu muhimmanci da Yesu ya yi da kuma yadda ya yi su.

“Muhimman Aukuwa a Rayuwar Yesu a Duniya” (Ƙasidar nan Taimako don Nazarin Kalmar Allah)

a A darasi na 31 zuwa 33 za mu tattauna game da Mulkin Allah dalla-dalla.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba