-
Me Ake Nufi da Cewa “Ku Kaunaci Masu Gāba Da Ku”?Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
-
-
“Ku sa wa masu zaginku albarka.” (Luka 6:28) Za mu iya sa wa abokan gābanmu albarka ta wajen yi musu magana da kyau kuma cikin kwanciyar hankali, ko da suna zagin mu. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kada ku rama . . . zagi da zagi. Ku rama dai da albarka.” (1 Bitrus 3:9) Bin shawarar nan za ta taimaka mana mu dakatar da kiyayya
“Ku kuma yi wa masu ba ku wahala adduꞌa.” (Luka 6:28) Idan wani ya zage ka ko ya wulakanta ka, kada ka “saka masa da mugunta.” (Romawa 12:17) A maimakon haka, ka roki Allah ya gafarce mutumin. (Luka 23:34; Ayyukan Manzanni 7:59, 60) Maimakon ka rama abin da mutumin ya yi maka, ka bar ma Allah ya saka masa bisa ga adalcinsa.—Littafin Firistoci 19:18; Romawa 12:19.
“Ku kaunaci masu gāba da ku, ku yi wa wadanda ba sa son ganinku alheri. Ku sa wa masu zaginku albarka, ku kuma yi wa masu ba ku wahala adduꞌa.”—Luka 6:27, 28.
-